Showing 9001 words to 12000 words out of 209297 words
haka?"
"babansu Fahad ne, yace inaje yana son ganina"
"ba zaka ba" ta faɗa kanta tsaye.
"Mummy meyasa?"
"saboda haka naga dama, akanme zece kaje bayan ba irin sintirim da ba ba akan yasa baki a sake ka yaƙi"
Anwar yace "haba Mummy, kidinga yiwa mutane uzuri mana, a baya kinsha neman Alfarma yayi miki, dan wannan karon be miki ba be kamata ki manta baya ba, kiyi haƙuri i je i ji meze ce"
"shikenan tunda kace haka, amma ba dan haka ba Wallahi da bazaka ba"
"kiyi haƙuri, kar hakan yayi sanadiyyar lalacewar zumjncinku"
Da yamma Hindu tayi kwalliya itada su Hanne da ƙannensu zeuje biki, Widad na ganin Hindu tace "Masha Allah, you look so beautiful Hindatu, kina da kyau masha Allah"
Hindu tace "Rufani ki saya Amarya, ai daga kanku kyau ya ƙare, kina ganina baƙa kirin ina wani kyau yake?"
Widad tace "waye yace miki baki da kyau? Ke nima fa ba wata kyakkyawa bace, dan dai ina da haske ne, amma baki ganki ba, kinyi kyau Allah ya baki miji nagari ɗan birni"
"hmm Amarya kenan, ni da ban taɓa zuwa birni ba, banyi boko ba ta ina ɗan birni ze ganni ya aura"
Widad tace "da ina da Yaya namiji zance ya aure ki Hindu, kina da kirki kaman Mama, wai ina zakune?"
"biki ne zamuje, a gangare"
Widad tace "laaa shine babu gayyata, ku jirani zan biku, dama ban taɓa fita waje ba"
Hindu tace "to ai Amarya baki da kaya irin Atamfa, duk kayanki ba irin namu bane, idan muka je seki zama abin kallo, kuma dama gaki ba kalarmu ba"
"se in saka hijjabi"
Gwaggo tace "A'a amarya bekamata ki fita ba, baki tambayi mijinki ba, se da yaddar sa sannan zaki fita"
"Mama baze ce komai bafa"
"dukda haka, kuda kukayi ilimi ma Amarya, ai kunfi mu sanin hukuncin hakan"
Hak Widad tana ji tana gani aka tafi biki aka barta a gidan.
Bata ji daɗin hanatan da Gwaggo tayi ba, sedai bata son yi mata musune.
Daf da la'asar Yusuf ya dawo, ya taho da kayan da Saleh ya bayar a siyo musu, seda Gwaggo ta kalli Widad sannan ta tashi, ta taya shi kai kayan ɗaki.
Ya fito ya ɗauki buta yana alwala, yace "Mama yau naga gidan shiru, ina mutan gidan ne?"
Gwaggo tace "sun tafi biki, tace zata bisu nace karta je seta tambayeka, shine taƙi kulani"
Yusuf yayi dariya yace "babbar magana, faɗa tsakanin 'ya da uwa yau"
Widad tace "tunda nazo fa ban taɓa fita ba, kullum ina gida"
Yusuf yace "idan kin fita Meza kiyi? Sarkin rigima"
"kaikuma kaji ka, Yoseef ka kiyayeni nice sarkin rigimar?"
Gwaggo tace "ɗiyar albarka a dinga saya masa sunan mana, idan daga ke se shine seki faɗa, amma a gaban mutane mu nan abun kunyane mace ta dinga faɗan sunan mijinta kai tsaye"
Yusuf yace "yawwa gaya mata dai Gwaggo"
Cikin Shagwaɓa tace "to me zance masa?"
Gwaggo tace "ki dai samo wani sunan mi dinga gaya masa, kafin Allah ya baku rabo, in kin haihu seki dinga cewa baban wane ko wance"
Haɗa ido sukayi da Yusuf, ga mamakinsa se yaga ta kwashe da dariya tace "taɓ sedai inya Auri Hanne ta haifa masa, amma ni babu wannan Kalamin, ai Yayana ne kai ko Yoseef?"
Tai maganar cikin sigar zolaya, tayi gaba ta bar tsakar gidan, Gwaggo ta zata kishine yake damunta, saboda tasan yadda basa shiri da Hanne, shi kuwa Yusuf, a wata cakwalkwalin cakwakiyar tunani ta kuma sashi, duk jikinsa yayi sanyi.
Bayan yayi sallar la'asar ya koma gida, ya tarar da Widad tana gyaran Akwati, ya kalleta yace "Queen waye yace miki zan Auri Hanne? Idan kuma Gwaggo ba taji daɗin abunda kika faɗa bafa?"
"Ai naga ita Hanne kaman she's having the same feelings on you, she also believes in love"
"Se kuma akace miki ni Aurenta zanyi?"
"to waye yasan muku? Ranar da zamu koma gida, idan ka sake ni base ka Aure ta ba, ka tafi da sabuwar Amaryarka ba"
Tsaki Yusuf yayi, saboda yaji haushi sosai, ya miƙe ya bar ɗakin, bin bayansa Widad tayi da kallo, ta taɓe baki ta cigaba da aiki ta.
Tunda ya fita be dawo gida ba se bayan sallar isha'i, sannan yaƙi kulata kwata kwata, dukda taji ba daɗin dena kulatan da yayi da yawan tsokanar ta da yake, yaji ba daɗi amma ta maze ta basar dashi itama, haka kowa ya kwanta be kula kowa ba.
Da Asuba ma da yayi salla, suka zauna zaman karatu seda gari ya fara haske sannan ya taho gidan, tun bayan da aka idar da sallar Asuba kafin a fara karatu, Saleh ya janyo Yusuf waje yace "Nifa zan koma, sammako zanyi in tafi tunda kaji sauƙi" .
Yusuf yace "da wuri haka Saleh?"
Saleh yace "eh mana dole, in tafi bana son mutanen nan su farga su fara zargin wani abu"
Yusuf yace "hakane, mungode Saleh Allah yasaka maka da alheri"
"Ameen ya Allah, nace ka gaya mata kuwa?"
Yusuf ya ɗanyi shiru sannan ya girgiza kai yace "A'a amma zan gayamata insha Allah"
Saleh yace "gara ka gaya mata, tayi duk borin da zata yi ta gama a nan, sedai Kayi haƙuri, ina son insha Allah idan na koma zanje in gaida Ummanka, in gaya mata kana cikin ƙoshin lafiya"
Yusuf yayi murmushi yace "ka gaya mata ina lafiya, kuma ina kewarta, sannan ta kwantar da hankalinta"
Saleh yace "zan gaya mata insha Allah, sena sake dawowa"
Sukayi Sallama Saleh ya tafi.
Widad kam wanke wanke suke ita da Hindu, Hindu tace "Amarya ban taɓa tsammanin kin iya faɗa haka ba, ashe kina sane kike ƙyale Hanne se kace bakya kishin mijinki"
Widad tace "Meye kishi?"
Buɗe baki Hindu tayi tace "baki san meye kishi ba?"
Widad ta jinjina mata kai tace "ni ban san wani kishi ba, banajin komai ina dai ji ana faɗa amma ban san me ake jiba"
"Lallai Amarya abun mamakin ki da yawa yake, se kace wadda akayiwa Auren dole? Zakice ba kya kishinsa, Amma dai ai kina sonshi ko?"
Taɓe baki Widad tayi tace "Nifa ban san me ake ji ba a son nan, nifa kawai gani nake wannan son shirme ne, babu wani so mutanene kawai ke abunsu"
Dariya Hindu tayi tace "Yanzu dai bakya son Yusuf ɗin kenan?"
"To base na yadda akwai son sannan zan iya banbance idan ina sonshi ko bana sonshi ba?"
Hindu tace "ina mamakin kalar taki rayuwar Amarya, gaba ɗaya abubuwan ki wani lokacin sun saɓa da na sauran mutane, anya gidan ku akwai mutane kuwa?"
Widad tayi dariya tace "eh mana, akwai mutane, sedai nikaɗai nake rayuwata"
"Amma meyasa kika dinga kuka, kika kasa cin Abinci da mijinki bashi da lafiya?"
Ɗan shiru Widad tayi tace "Saboda idan Yoseef ya mutu, nima tamkar matacciya nake, ban san kowa anan ba se Allah se shi, sannan ya sha wahala sosai sabodani, yana shiga damuwa idan bani da lafiya ko ina cikin damuwa, shiyasa naji rashin lafiyarsa har cikin raina, kuma kinga ni bani da wa ko ƙani, Mamana ta rasu ina Yarinya Babana kawai nasani, Yanzu Yusuf shine yaya na, shine ƙanina shine ɗan uwana, shine komai nawa anan"
Hindu tace "Allah sarki Amarya, kin bani tausayi wallahi, amma Saleh yace mana ɗan uwanki ne Yusuf"
Widad tace "ɗan uwana ne mana, Allah ne ya bawa Babana shi, ya zama garkuwa a gareni, Hindu kina da kirki sosai naga garin nan kun ɗau Aure da mahimmanci sosai, Allah ba yadda be iya ba, na dage ba zanyi Aure a rayuwa ta ba, babu Aure a gabana saboda wani ƙuduri da nake dashi a raina, babu zato ƙaddara tasa na Auri Yusuf, ina yiwa mazanmu na Hausawa kallon wanda basu san darajar Aure ba, gaba ɗaya ina yiwa Aure kallon rayuwar muzgunawa, Amma ina miki fatan ki Auri Namji kamar Yoseef, idan akace akwai mutum me haƙuri kamarsa zance ƙaryane, Amma yana da haƙuri sosai, nasan yana haƙuri dani, ni gaba ɗaya tausayinsa nake ji Hindu saboda.....
Ta kasa ƙare maganar se Hawaye dake bin idonta, Yusuf yana tsaye a soro yana jin duk hirar da sukeyi, a hankali Yusuf yayi gyaran murya tare da yin sallama.
Da sauri Widad ta basar ta share hawayenta, Yusuf yace "Sannunku da aiki"
Hindu tace "Yawwa ina kwana"
"lafiya ƙalau Alhamdilillah"
Ya kalli Widad yace "My Queen, let's go inside"
Ta kalle shi tace "ka gama fushin?"
"ni dama nace ina fushi da ke ne?"
"ni dai ka bari in gama wanke wanke na"
Hindu tace "kije zan ƙarasa"
Yusuf yace "ƙyaleta, idan bata tashi ba, zan ɗauketa ne cak in kaita"
Hindu ta sunkuyar da kai, dan abun nasu Yusuf wani lokacin basa jin kunya.
Ɗaki suka shiga, ta kalle shi tace "gani meye?"
"Ƙwanki dama zan soya miki, tunda bakya so shikenan"
Murmushi tayi tace "Au ai na manta, soyamin inci"
Murmushi Yusuf yayi, ta zauna ta zuba masa ido, ya fasa ƙwan ya kaɗa yasa gishiri, dan su nan babu Seasoning.
"Wai dan Allah Mamanka ce duk ta koya maka wannan aikin?"
"Eh mana gashi kuwa kina gani"
"taɓ gaskiya kaji daɗi, ina Baban ka, baka maganarsa kullum se Ummanka kake faɗa"
Yusuf yace "Allah yayi masa rasuwa"
"Eyya Allah ya jiƙansa, yayi masa rahama"
"Ameen"
Ya miƙo mata ƙwan a plate, ya dafa mata tea ya haɗa mata, Widad tace "Allah sarki rayuwa, yau ni nake murna zan ci ƙwai, alhalin har kamfanine dani da'ake fitar da ƙwai har wajen Nigeria"
Yusuf yace "haka lamarin ubangiji yake, sedai dama da bredi se yafi daɗi"
"hakan ma nagode, zama da kai ka koyamin ci kuma da ni ba haka nake ba"
"Eh mana, so nake idan muka koma gida kar aga rama a tare da ke"
Dariya tayi tace "matso muci"
"A'a ci abinki, dama ke na saiwa, ni in aka ɗumama tuwo se inci"
"Aikuwa ba zance kaci dole ba, cikinka ni ci zan in ƙoshi, kaita jin ƙamshinsa"
Ta soma cin ƙwan nan, kawai yaga tayi murmushi tace
"ban taɓa cin ƙwai mara daɗin wannan ba"
Yusuf yace "to mutum ya soya wanda yafi wannan in an isa"
Tai murmushi tace "Gwaggo tana koyamin ai, zakayi mamakin yadda zan iya girki, inyi girki me daɗin da baka taɓa cin irinsa ba"
Ta cigaba da cin Abincinta, ƙura mata ido yayi yaga yadda take nishaɗi, tana cin Abincinta cikin nishaɗi, tunani yake ko ya gayamata yanzu? Tunda tana cikin nishaɗi, to idan kuma ya ɓata mata nishaɗin da take fa?.
Ba tare da ta kalli Yusuf ba tace "gayamin abunda kake son gayamin ka dena kallona kar in ƙware"
Jin maganar tata yayi a bazata, dan be zaci tana kallonsa ba, kuma yaji muryarta ta a asalin Widad ɗinta me cike da izza da jin kai.
Cikin kame kame Yusuf yace "Amm. Bakomai dama....
" bana son ƙarya, kuma bana son wasa da hankali Yoseef, ina jinka ka gayamin abunda kake son faɗa "
Gaban Yusuf ya faɗi, yace " dan Allah ina son ki fahimceni dama... "
"ni mutum ce kamarka, ban isa inyi maka abunda Allah be maka ba, sedai kome bakinka ze furta, karka kuskura kayi min ƙarya"
"to ai ƙaryar ma nayi miki Widad, shiyasa nake fargabar ta ina zan fara miki maganar ban san yanda zaki fahimci abun ba"
Wani irin sheɗanin kallo ta ɗago idonta tayi masa, me cike da tarin tuhuma, da gargaɗi gami da kashedi.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA, BA DANNI BA DA GIRMAN ALLAH.
A TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 52_53
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH
07063065680
Gaba ɗaya Yusuf ya shiga taradaddi, gumi ya tsasttsafo masa a goshi, saboda irin kallon da take masa, dan tun a nan yaga alamar rashin nasara.
Ɗauke idonta tayi daga kallonsa tace "ina jinka" tai maganar tana zuƙar tea ɗinta, Yusuf yace
"Da farko zan fara da baki haƙuri dan Allah... "
Katseshi tayi ta hanyar cewa "bana son wani ban haƙuri, ka tafi kai tsaye kawai ina jinka"
Cikin damuwa yace "dole in baki haƙuri, saboda a karon farko da ƙarya na fara miki, tun a zuwana akan ƙarya nazo miki, saboda nima ban san ya akai hakan ta faru ba, saboda" Se kuma yayi shiru.
Ba tare da ta kalle shi ba tace
"to tunda ka kasa gayamin ni bari in gaya maka abunda kake son faɗa ɗin ka kasa, na farko kai jam'in ɗan sanda ne na sirri ko ba haka ba?"
Ƙuuuu cikin Yusuf ya kaɗa, ya kalle ta a razane, ta ci gaba da cin Abincinta tace "cigaba na fara maka, ƙarasa ina jinka, saura me kuma?"
Kasa magana yayi, ya dinga binta da kallo cike da ban al'ajabi, kamar yaga wata halitta daban.
"yanzun ma zaka cigaba ne ko in cigaba da gaya maka"? Tai maganar tana kallonsa
"Amma ya akayi kika sani?"
Cikin isa da taƙama tace "An turo ka ne a matsayin jami'in sirri, da sunan wai ka bani kariya ko?"
Buɗe baki Yusuf yayi yana kallonta, amma ya kasa cewa komai dama tasan waye shi?
Ta kalle shi tace "shikenan ko akwai saura?"
Wani irin yawu Yusuf ya haɗiye da ƙyar, kai da ka ganshi kaga mara gaskiya, yadda yake ta gumi kuma ya kasa cewa komai.
"tunda ka kasa magana bari in ƙarasa maka, bayan bani kariya da kake, kuma kana yin bincike akan maƙiyan mahaifina, da wanda suke bibiya ta, ka maida hankali sosai akan aikinka, sannan kana taka tsan tsan dan kar in san ko kai waye"
Ta ɗanyi shiru tana nazarinsa sannan tace "Sannu Yoseef amma meyasa kasa hannu akan contract ɗina, bayan na gaya maka bana yafewa maƙaryaci?, saboda tsabar taurin kai, son aiki da rashin nuna gazawa ka saka hannu, dukda baka san wane irin hukunci zan ɗauka akanka ba idan na ganoka, idan ban manta ba a lokacin nace if you know you are here to spy don't sign the contract, but you feel like to sign it, saboda ba zaka iya komawa Office ba tare da kayi aikin da'aka turoka ba right? Yoseef meyasa kayimin ƙarya? "
Jiki a sanyaye Yusuf yace " ai kin bawa kanki wannan amsar Widad, bazan iya komawa ince ba zanyi aikin ba, saboda Alƙawari nayi kafin in fara aiki zan kare rayuka da dukiyoyin jama'a, kuma tunda na fara aikin, dagaske har cikin zuciyata naji ina son in baki kariya, musamman ranar da mukaje gurin birthday Nurat akayi yunƙurin saceki, tun anan na fara karaya, na ƙara tabattarwa lallai rayuwarki a hatsari take, dan haka nayi ɗamarar baki kariya iya iyawata, amma dan Allah ya akayi kika san wannan abubuwan haka?"
Ta ɗan jinjina kai tace " lallai biri yayi kama da mutum, ranar ba yadda banyi da kai ka gayamin meyafaru ba, amma kaƙi ka gayamin, nima nasan nayi ganganci a wannan ranar, na zuwa gidan Alhaji Musa, sedai ina ƙoƙarin cire kaina a cikin rigimarsa da mahaifina, shine dalilina na zuwa gidans, amma shima ka ɓoyemin baka gayamin meyafaru ba ranar, meyasa? "
Yusuf yace " saboda muddin na gaya miki zakiyi yunƙurin ɗaukar mataki ne, da kinyi yinƙurin yin haka nikuma Asiri naa ze iya tonuwa, kuma zaki ɓata komai ne, Amma dan Allah ya akayi kika sani? "
Cikin isa tace "Lallai ka raina Wacece Widad da kuma AƘIDARTA, in dai nice har yanzu bakaga komai ba, Tunda kazo gidanmu, jikina ya bani akwai something different with you, either good or bad, na kasa nutsuwa, na dinga ɓullo da abubuwa daban daban amma na kasa gane komai na cutarwa a tare da kai, ranar da 'yan sanda suka kama ka da bindiga, ni na fara ganin bindigar a jikinka kafin mu fita daga gida, kazo shiga mota ka ɗaga rigarka naga bindigar, nai shiru ban nuna na gani ba, dan ina son sanin da wacce kazo, sannan inga wani hukunci ne ya dace da kai, bayan mun fita a ranar aka kamaka da bindiga ka bawa 'yan sanda id card, sukayi ƙoƙarin saluting ɗinka amma ka hanasu, tun daga nan nabi diddigi da ƙwaƙƙwafinka na gane waye kai, har headquarter ɗinku naje aka bincikomin waye kai, sedai abu ɗaya ne ban gano ba har yanzu, waye yasa a baka aikin nan?!"
Yusuf yayi ajiyar zuciya, cikin damuwa yace " Nima ban sani ba, da bani za'a bawa aikin ba, amma abokin aikina yace a bani na fishi haƙuri, ban san waye ya bada aikinba nima"
Widad tace "Abokin aikinka Sani me zuwa gurin Isa megadi ko? Wato Abbas"
Gaba ɗaya Yusuf ya rasa meze ce saboda tsananin mamaki.
"Ni na saka aka ɗauke shi daga kano, aka kai shi kudancin Nigeria saboda ban yadda dashi ba, yayi ruwan Azzalumai da yawa"
Yusuf yace "Dama kece kika saka aka ɗauke shi? Ba mugu bane aminina ne, bani da aboki sama dashi"
"Yana ɗaya daga abunda yake cutar da mutane, shine saurin yadda, waye ya gaya maka duk memaka dariya sonka yake yi? Kayi kuskure ni bemin ba, shiyasa nasa aka rabashi da garin nan, sannan ina cike da son sanin waye ya bada wannan aikin"
Yusuf kam rasa bakin magana yayi, se kallonta kawai da yake yi.
Widad tace "shikenan" ta miƙe tsaye ta ɗau kwanukanta, yaji taja sumar kansa tace "matsoraci kawai, ashe haka kake da tsoro, i wish kaga idonka yadda suka sauya, kaine mutum na farko da na yafewa wanda yai min laifi mafi muni, saboda kaima hanyar da akabi aka baka aikin dan a cutar da kaine"
Yusuf yace "kamar yaya?"
"Bazan faɗa ba, ban yadda da kai ba" tai waje abunta tana dariya.
Mamaki ya cika Yusuf tatil, yanzu dama kallon biri yake mata take masa na Ayaba, tasan waye shi tsawon lokacin nan, be taɓa zaton zata gane ba yadda ya dinga taka tsan tsan, lallai Widad ba ƙaramin wayone da ita ba, amma kuma yana da tarin tambayoyi daze mata, amma taƙi bashi damar yin hakan.
Anwar ne ya shigo falon mahaifiyarsa yace "Mummy zanje kiran da Babansu Fahad yake min ne"
Ta kalle shi tace "Naji amma tare da Amal zaku tafi"
Anwar yace "Amma Mummy meyasa?"
"Saboda haka naga dama" ta bashi amsa, ta ɗau wayarta ta kira Amal tace tazo.
Befi mintuna biyar ba sega Amal ta shigo tace "Mummy gani"
"Jeki shirya maza kizo kuje gidan Bulsma keda yayanku"
Amal tace to, Hajiya Halima ta kalle shi tace "jeka mota ka jira ta"
Anwar ya fita kamar yadda aka bashi umarni, Amal ta shirya ta koma ɗakin mahaifiyarta, tace "Mummy gani na shirya"
"Yawwa ki