Showing 72001 words to 75000 words out of 209297 words
ɗan taɓa baki tayi ta ɗanyi tsaki sannan tace
"wai dagaske Nurat ma budurwarka ce?"
Yusuf yace "A' a naje gidansu dai, bayan mahaifinta yayi yunƙurin sawa a sace ki, ita na ritsa da bindiga ta gayamin inda kike, bayan nan na koma gidansu, dan inyi mata wasu tambayoyi, da farko ta tsorata daga baya kuma ta saki jiki, muka dinga hira a haka na samu abunda nake son ji daga gare ta, har mukayi exchange na lamba, akwai ranar da muka fita dake, nakw waya nace ina tare da matata ne, ai da ita muke waya, sedai daga baya na fuskanci Nurat ta kamu da sona ne "
Widad tace "kuma kaima kana son ta"?
"To waike meye naki na tambaya ne? Bayan kince bakya sona, ina ruwanki ki ƙyaleni in samo mesona, wanda bazata gujeni ba kota dinga min tsiwa ba"
Ɗan guntun tsaki tayi, tare da jin haushin kanta ko meye na damuwa ma oho, ta janyo kwanon Abinci ta buɗe, kofin an zuba kunun tsamiya, kwanon kuma wainar gero ce an barbaɗeta da ƙuli ƙuli, Widad tace "wannan wane irin Abinci ne kuma, shima wani baƙi dashi??"
Yusuf yace "wainar gero ce"
Tace "Meye kuma wainar gero, mutanen nan suna son yin Abinci baƙi" tai maganar Tare da saka hannu ta fara yashe ƙulin kai tana lashewa, Yusuf ya kalle ta yace "bismillahi, kwaɗayayyiya zaki cinye ƙuli ƙulin ki barmin gaya ko? Dama kin saba"
Hararsa tayi ta cigaba da lasar ƙuli ƙulinta, Yusuf yace "baze fa yuwu ba, se saka yawu kike a jiki, idan muka koma gida sena gayawa Daddy yadda kike bani wahala, duk na rame kekuma ƙibarki kawai kikeyi"
Duk da a fusace take amma murmushi ya suɓucemata tace 'kamar kasan akanka Daddy ze iya zaneni ma inaga, dan yana matuƙar sonka sosai"
Yusuf yace "nima ina sonshi sosai"
Widad ta kalle shi da sauri tace "dagaske? Kana son Daddyna?"
Yusuf yace "sosai makuwa, ai bazan manta alkhairinsa a gareni ba, kuma koba komai ko bama tare, yana da matsayi a gurina saboda na taɓa Auren 'yarsa, dan haka inajinsa kamar mahaifina mussman yadda yake girmamani"
Widad ta jinjina kai, har cikin ranta taji daɗin yadda Yusuf yace yana son mahaifinta harya ya beshi haka.
wainar geron nan ba ƙaramin daɗi tayiwa Widad ba, ta saki jiki taci sosai, sed suka gama faɗansu da Yusuf sannan ya fita.
Widad ta fito tsakar gida, amma bata ga Hindu ba, ta kalli Hansai tace "wai ina Hinduna ne yau ban ganta ba fa"?
"Hindunki a ina?" Hari ta faɗa tana yatsune fuska.
Banza Widad tayi mata, ta kafe Hansai da ido tana jiran amsar tambayarta, Hansai tace "Zazzaɓi take yi, tana ɗakin Gwaggo a kwance"
Widad tace "subhanallah garin yaya?"
Hansai tace "larura daga Allah mana"
Widad ta tafi ɗakin Gwaggo, ta tsaya a bakin ƙofa tayi sallama, Aka amsa ta nemi izinin shiga, sannan ta shiga.
Jamila na zaune a gefe tana shayar da jaririyarta, yayin da Hanne keta ƙoƙarin gyara ɗakin Gwaggo, Gwaggo kuma tana ta rarrashin Hindu taci Abinci amma taƙi.
Gaba ɗaya damuwa ta bayyana a fuskar Widad.
Jamila ta kalli Widad tace "ina kwana?"
Widad ta kalli Jamila ta ɗauke kai, tazo ta nemi guri ta zauna a gaban Gwaggo tace "Mama, meyasa ba'a gayamin Hindu ba lafiya ba?"
Gwaggo tace "ahh haba, ya za'ai a takura miki, amma yanzu ai gashi da kika fito kinji"
Jamila taji haushin sharetan da Widad tayi a karo na biyu, kuma tana ji tana mata magana.
Cike da tausayawa Widad tace "sannu Hindu, Allah ya baki lafiya"
Hindu tayi murmushi tana gyɗa kai, yayin da Hanne se cika take tana batsewa, tana faman jan tsaki kamar wadda akayiwa wani abu, dan data tuna a yadda ta gansu itada Yusuf se taji kamar ta fashe da kuka.
Widad ta kai Hannu ta taɓa Hindu, jikinta zafi sosai Widad tace "Gwaggo, baza'a kaita Asibiti ba? A kaita a duba ta mana"
Gwaggo tace "hmm Amarya kenan, da kinsan azabar tazarar dake tsakaninmu da Asibiti da baki ce a kaita ba, bamu da Asibiti a garin nan, ƙauye uku zuwa huɗune tsakaninmu da Asibitin shaka tafi, yanzu kafin a kaita ma wani wahalar ne, duk seta galabaita"
Widad ta girgiza kai tace "ni wallahi ina mamakin yadda za'ace mutane suna rayuwa babu Asibiti a guri, ai wannan se mutum ya rasa ransa ma ba'a bashi wani agaji ba, haba dan Allah to yanzu ba abunda za'a bata"?
"A'a na ɗan jiƙa kayan magungunanmu na gargajiya, na ɗan bata shima kuma tayi amansa"
Widad tace "Mama nifa bana son wannan kayan jiƙe jiƙen, su ba ƙa'ida ne dashi ba kawai sha akeyi, kuma kayan ciki basa san wannan jiƙe jiƙen, yanzu se wani abun ya taɓu, bari Yoseef ya dawo, in da sauran nasa magungunan se a bata"
Hindu tace "Nagode Amarya"
"Ba godiya tsakaninmu Hindu"
Jamila abun ya bata mamaki taji Widad na hira haka, kuma ta iya hausa amma tayi mata magana taƙi kulata.
Bayan Widad ta gama duba Hindu, ta tashi ta fita, Gwaggo ma ta fito tsakar gida, Jamila tace "wai nikam wacece wannan? Tana ji ana mata magana amma tana wani jin kanta tana share mutane"
Hanne tayi tsaki tace "bar shegiya, haka take wannan wulaƙancin dan tama ganinta a koɗe kamar an wanke karas, taita wa mutane wani iskancin banza da taƙama, se tsabar rashin kunya da rashin tarbiyya, ko magana bata iyaba ga ƙaryar masifa, komai seta dinga nuna bata sanshi ba, saboda gogewa mutane hadda "
Hindu dukda jin jikin da take, ba zata iya jure jin ana cin zarafin Widad ba, Hindu taja tsaki tace " Wallahi Jamila ba bata da mutunci bane, ni baki ga yadda tamin ba, bata da wata matsala, sedai bata sakin jiki da mutane, seta daɗe tukuna, bata fiye son mutane bane, amma Hanne san zuciya ne yasa kike cewa bata da mutunci"
A fusace Hanne tace "dalla malama yiwa mutane shiru, aikin banza uwar shisshigi se wani naniƙe mata kike kina cusa kai ba kwarjini, aikin banza dana wofi kawai"
Jamila tace "ya isa haka, ke Hanne abun faɗa baya miki wuya yaseen, har yanzu kina nan da tijararki baki dena ba"
Hanne ta riƙe ƙugu tana harare harae tace "ƙwarai kuwa, wallahi anamin nake ramawa ehee, babu 'yar masu baƙin jinin da zan saurarawa"
Shiru Hindu tayi, jin Hanne na ƙoƙarin fara ci mata fuska, Jamila tace "Hanne meye hakane? Nace ya isafa"
Hanne ta zumɓura baki tai waje, yinin yau Widad kanta bata da sakewa, ji take kamar itama bata da lafiya, Hindu tana matuƙar birgeta saboda biyayyarta da haƙurinta, shiyasa idan bata nan ko bata walwala Widad ma take shiga damuwa.
Saleh kam kwana biyu yayi ya koma kano, yaje ya tarar abubuwa nata sake rikicewa, dan ya fara karaya ya zubawa sarautar Allah ido, saboda tarakun da'aka kafawa Yusuf, ubangiji Allah ne kaɗai ze iya fidda shi, dan babu imani babu tsoron Allah ko tausayi a tare da su Alhaji Musa.
Saleh yana gidan da yake zaune, yaji ana buga ƙofa yana zuwa ya buɗe yaga Abbas, Saleh yayi murmushi yace "Ahh saukar yaushe haka? Shigo daga ciki mana"
Abbas yabi bayan Saleh suka shiga, har falon Saleh, Abbas yace "ai yau sati na guda a garin nan, nazo in ɗan huta ba inda nake zuwa shiyasa baka ganni ba se yau"
Saleh yace "Allah sarki, to ya Hanya?"
"Hanya Alhamdilillah, dan mun shata kam"
"to masha Allah"
Saleh yace "wai ni kuwa nace ya ake ciki ne? Har yanzu babu wani labari ne? Tun tafiyata banji wani motsi ba har yanzu ba'a samu komai bane?"
Saleh yace "haryanzu ba wani abu fa, ana ta fama ne abun duk se a hankali, shi can ya gudu ba'a san inda suke ba, shima kuma an sace shi, shi Daula babu wanda yasan inda yake haryanzu, anata fama ne"
Abbas yace "Ai naga sanarwar da aka yi akan Yusuf ne ya sace Ita 'yar Daula, hakan yayi ai hakan shine zesa hankalin mutane ya ɗauke daga yin zargi, se a koma sauraren ta inda za' a gano su, ni babban abunda yake damuna ma kar muje ta bashi takaddun mu muna nan, dan wallahi ba kaga alherin da take masa ba"
Saleh kallon Abbas kawai yake harya kai aya, sannan ya numfasa yace "insha Allah, babu abunda ze faru, kota bashi takaddun babu yadda zeyi dasu, su Munir su suka san kan dukiyar, su suka san yadda za'ayi lamarin ya wakana, karka damu komai ze tafi daidai, sedai kamar yadda na gaya maka kansu suma a rarrabe yake yanzu haka, karka yadda wani ɓangare yazo ya nemi wani abu a gurinka, ka yadda ka bayar, karmu ɗau side mu zama a tsakiya, tunda bamu san ɓangaren da zasu yi nasara ba"
Abbas yace "dan wannan, ai karka damu tuntuni kamin wannan kashedin, kuma naji na ɗauka, dan haka ka kwantar da hankalinka, sedai muna biue dasu, zuwa lokacin daza'a samu ɗin"
Saleh yace "hakanma dai dai ne"
Daga nan suka cigaba da hirarrakinsu.
Daga baya kuma suka yi Sallama, Abbas ya shig motarsa sega kiran Suleiman, ya ɗaga yana faɗin "Allah ya temaki Oga, barka da yamma"
Suleiman yace "Yawwa barka Abbas, ya kake ya aikin?"
"Alhamdilillah Oga"
"Good, naji ance ka shigo garin nan, inba damuwa ina son mu haɗu gobe in Allah ya kaimu"
Abbas ya ɗanyi Jim sannan yace "shikenan Oga, yadda kace kaman da ƙarfe nawa?"
"Kamar goma na safe, muhaɗu a office"
"Shikenan, Insha Allah zan shigo"
Yana kashe wayar, Saleh yaja tsaki yace "Aikin banza munafukan banza, da kai aka haɗa baki aka canzamin gurin aiki, aka maida Yusuf kan kujerata, aiga abunda ya sameshi nan, Allah ya ƙara masa saura kaima"
Ya ajiye wayar yana ƙwafa, ya kunna motarsa sannan ya tafi.
Nurat ta rame tayi duhu, gaba ɗaya bata jin daɗin komai, tun mahaifiyarta tana rarrashinta harta haƙura, ita zatonta halayen mahaifinta ne suka sa tashi ga wani hali, bata san me yake damunta ba, ko Abincin kirki bata iyaci, ga wunin ɗaki data tsira, seta wuni cur bata fito ko falo ba tana ɗaki, Abinci in an kaimata ba zata ciba, sedai idan Mahaifiyar tace ta shiga ta sata a gaba shine zata ɗanci kaɗan, fuskar nan tayi fayau bakoma se dogon hancinta da idanuwa saboda damuwa.
Shikuwa mahaifinta sabgar gabansa kawai yake, yana ta faɗi tashi yana kashe kuɗi gurin malamai da 'yan tsibbu, da gurin manyan' yan siyasa domin ya samu ya koma takarar ɗan majalissa da Daula ya tsaya masa yayi, gefe guda kuma sunata cigaba da ƙulle ƙullen yadda ko sun rasa wanccan kuɗin, su samu wani kason ta ɓarauniyar hanya.
Yanzumu shiryawa yayi tsaf, ya tafi gidan Barrister Hafiz da kansa, domin jin inda maganarsu ta kwana akan batun ayi takaddar boge, ayi gwanjon wasu daga kadarorin Daula.
Barrister Hafiz ya karɓi Alhaj Musa hannu biyu, ya masa iso har falo aka gabatar masa da Kayan ciye2, Alhaj Musa ya ture farantin fruit ɗin yace "kafin wannan, dama zuwa nayi inji inda maganar da mukayi ta kwana? Yau kimanin wata guda kenan da yin maganarmu, amma shiru ba amo ba labari bakace mana komai ba, bamu san a ina aka kwana ba"
Barrister Hafiz ya ɗanyi shiru sannan yace "Yallaɓai kamar yadda a wancan lokacin muka rabu akan cewar, zan tattauna da sauran abokan aikin da muka kasance lawyoyin Alhaji Nasir Daula, na bisu ɗaya bayan ɗaya kowa naji ra'ayinsa, na zaɓe wanda nake ganin zasu iya yadda ayi harkar nan dasu, sedai me nazarin da mukayi, da binciken da muka sake yi shine, duk wata kadara da Daula ze siya muna sani, ko ince wasu daga kadarorin daze siya, a gabanmu akeyi da komai da komai, sedai fa takaddun Kadarorinsa babu ɗaya daga cikinmu daya san inda yake ajiye takaddunsa, dukda kasancewar mu lawyoyinsa, 'yar nan tasa dai ita kaɗai ce tasan inda kayansa suke, bakomai muka saniba, munyi tunanin yin takaddar boge kamar yadda kuka ce sedai babu wanda ze iya kwafar sa hannun sa, wataƙila se wannan yarinyar tasa"
Alhaji Musa yai shiru sannan yace, "shikenan ba damuwa, zamuje a bincika dole za'a samu wanda ze iya kwafa, nagode sosai idan akwai buƙatar sake nemanka, zaka jimu nan gaba nagode"
Ya miƙa masa hannu suka gaisa, ya tashi fita.
Nurat ce zaune a bakin gadonta tana ta sharɓe hawaye, wanda ya zamar mata jiki a 'yan kwanakin nan, tayi zurfi sosai a tunani, taji sallama a hankali ta ɗaga kai domin ganin me sallamar barrister Khalil ne, bayansa kuma mahaifiyarta ce, Amsa masa tayi cikin sanyin jiki.
A ɗan razane ya kalleta yace "Subhanallah Anty Sauda dama haka Nurat ta koma?"
"to gata nan dai, shiyasa na kiraka ai, ban sani ba kokai idan kayi mata faɗa taji"
Khalil yace "sistona, meke damunki haka kinga yadda kika rame kuwa?"
Shiru Nurat tayi ba tace komai ba, Khalil yace "gayamin meke faruwa ne?"
Ɗaga kai tayi ta kalli mahaifiyarta ta sunkuyar da kai, Khalil yace "Anty Sauda bamu guri muyi magana"
Ba musu ta juya ta fice ta basu guri, Khalil ya rufe ƙofae, sannan ya ɗakko kujerar gaban dressing mirror ɗinta ya ajiye ya zauna, ya kalleta yace "Nurat, tsakanina dake kin san babu ɓoye ɓoye ko? Bama ɓoyewa juna komai ki gayamin meke faruwa, kin san bazan fallasa sirrinki ba, sirrinki nawane ki gayamin koda taimakon da zan iyayi miki"
Aikuwa ta sake fashewa da kuka, seda tayi me isarta sannan tace "Brother meyasa wayarka bata shiga, na kira layinka babu adadi amma taƙi shiga?"
Khalil yace "wayar aka sa emin a gurin ɗaurin Aure, se yau naje nayi swapping ɗin layin, amma meyasa baki kira ko Mama ba muyi magana?"
Nurat ta goge hawayenta tace "bana son kowa yasan meke faruwa ne, bana son wani yaji shiyasa ban kira kowa ba".
"Shikenan naji, gayamin meke faruwa na ƙagu inji meyasameki haka?"
ɗakko wayarta tayi, ta buɗe labaran da ake yaɗawa akan ɓatan Widad, labarin me ɗauke da hoton Yusuf.
Ta miƙa masa wayar tace "Brother kaga wannan labarin?"
Khalil ya kalli wayar yace "eh naga labarin yana ta zaga gari"
Nurat tace "Allah ya jarrabeni da son wannan bawan Allah brother, kuma wannan shine wanda Daddy na yasaka a gaba, wallahi brother ina tabattar maka da dasa hannun Daddy na aka sacesu, kuma yanzu anyi sanarwa wai shi ya sace Daula da 'yarsa, wallahi baze aikata haka ba brother, dan Allah ka temakeni ka temaki Yusuf "
Khalil yace " yi shiru dena kukan, tsaya yanzu kin zaɓi soyayyarki akan mahaifinki"?
"Brother ba soyayya na zaɓa ba, gaskiya na zaɓa na fifita, na gaya maka komai fa a baya, koka manta?"
Khalil yace "ya za'ayi in manta, ban manta ba kuma indai abunda kika faɗa hakane, to tabbas mahaifinki bashi da imani, yanzu me kike ganin za'ayi? Tukuna ma waishi wannan ɗin waye? "
Nurat tace "direban gidan Daula ne"
"Direba kuma Nurat, to yanzu ya kike son ayi?"
Nurat tace "Sonake a ɓoye, ka bincika waye Yusuf da kuma inda yake, sannan ina son a ɓoye ka cigaba da bin diddigin mahaifina ko zaka samu wani bayanin, wanda ze wanke Yusuf"
Khalil yace "kin haɗani da aiki me hatsarin gaske, amma indai hakan ze sama miki farinciki to zanyi insha Allah"
Ai bata san lokacin da ta faɗa jikin Khalil tana masa godiya ba, kallonta yake yi yana tunani a ransa yace "insha Allah, zan sadaukar da tawa soyayyar dan ganin kin samu taki Nurat"
Zuwa yamma Hindu ta ɗanji sauƙin jikinta, dan harta fito tsakar gidama, Widad tana ta murna, Jamila na jikin ɗakin Hansai, tana wasa da jaririyarta, Widad ta ƙura mata ido kamar tace ta bata jaririyar ta ɗauka, dan ita dai da wayonta bata taɓa ɗaukar jariri ba.
Yusuf yayi Sallama ya shigo, sedai abunda ya ganine yasa ya rikice cikin ɗaga murya yace "Subhanallah......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
86_87
Wato bakomai Yusuf ya gani ba, illa Widad bata taɓa kula Jamila ba, amma taji tana son taje ta ɗau jaririyar nan dako arba'in ba tayi ba, gashi baya tunanin ta taɓa ɗaukar jaririn, Jamila na ƙoƙarin bata 'yar, idan ba'ayi wasa ba tsaf Widad inta ɗauki 'yar nan zata iya jimata rauni saboda yanayin ɗaukar da take shirin yiwa jaririyar.
Yusuf ya ƙaraso da sauri yace "karki bata, bata iya ɗauka ba karta jiwa Babyn ciwo"
Widad ta juyo ta kalleshi, aikuwa ta haɗe rai sosai tace "kamar yaya ban iya ɗauka ba?"
Yusuf yace "eh baki iya ɗauka ba, sekin jima ta ciwo tukuna?"
"wai kai komai ban iya ba, ba a haka zan koya ba, ni gaskiya kabari a bani in ɗauka" tai maganar tana ƙoƙarin cicciɓar ƙafafuwan jaririyar"
Yusuf yace "yi haƙuri tsaya kiga yadda za'ayi, bari in ɗauka ni se in baki"
Yusuf ya karɓi jaririyar, dake ta bacci, yayin da Jamila kuma rigimar Yusuf da Widad suka burgeta matuƙa suka bata dariya.
Yusuf yace "muje ɗaki in baki ki ɗauka"
Yana tafe tana biye dashi har ɗakinsu, suna zuwa ta zauna tace "to zauna ka bani"
"Kedai akwai garaje"
Yusuf ya zauna ya nuna mata yadda zata yi da hannunta, sannan ya ɗora mata Jaririyar a hannu, jaririyar dai baƙace sedai fes da ita, an mata wanka an samata riga me kyau, rigar nata ƙamshin miski, da alama Jamila tana da tsafta.
Widad ta ƙurawa Jaririyar ido, ta