Showing 192001 words to 195000 words out of 209297 words
yace "Light Dama baki da lafiya?"
Maimakon ta bashi amsa se cewa tayi "ina wuni"
Yusuf yace "lafiya ƙalau, ya jiki ɗazu Umma ke gayamin ban sani bane"
"Jiki da sauƙi Alhamdilillah" ta faɗa tana rausayar da kanta ƙasa.
"Amma kin daɗe kina rashin lafiyar nan, meke damunki haka?"
Girgiza masa kai tayi tace "bakomai"
"ban yadda bakomai ba, ki gayamin meke faruwa ne?"
Kasa magana tayi, se hawaye da suka shiga zarya a fuskarta, ba tare da ta shirya zubarsu ba, dan tayi duk me yuwuwa ganin basu zuba ba, amma abun ya gagara.
Yusuf ya sakko daga kan kujerar, ya zauna a kan carfet ɗin yana kallonta, a hankali yace "Nurat, dan Allah kiyi magana mana, meyafaru?"
Shiru tayi ta ɗauke kai daga kallon inda yake, dan data kalle shi sonshi ƙara shigarta yake, da kuma kishinsa.
"Nur ko nine nayi miki laifi?"
Ta ɗago idanunta ta kalleshi na wani ɗan lokaci, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsunta, a hankali tace "Nagode sosai kazo ka dubani, nagode ka gaida Umma"
Ta yunƙura ta miƙe zata tafi, cikin zafin nama Yusuf ya miƙe ya riƙo hannunta, ta juyo tana fuskantarsa, ta kalli inda ya riƙe hannunta ta kalli Fuskarsa taji tamkar ta rungumeshi tayi kuka, ita dai a rayuwarta maza dayawa sun nuna suna sonta, amma bata taɓa jin ƙauna da soyayyar wani a ranta kamar Yusuf ba, zata iya cewa akansa ta fara Soyayya.
Yusuf yace "Nurat bana so in zama butulu, bana son zama ɗaya daga cikin masu butulci, ki gayamin me kike so? Meke saki kuka haka?"
Cikin sassanyar muryarta, me cike da karaya tace "bazan samu abunda nake so ɗin ba ai, dan haka babu buƙatar cigaba da ɓata lokaci gurin faɗa"
Yusuf yace "gayamin, ko mene ki faɗamin, me kike so?"
"Yusuf kai nake so, kaine Yusuf, ban taɓa so ba se akanka, ban san haka ake ji ba, sedai nasan bazan sameka ba, kamin nisa na har abada, nasan ko a mafarki Widad bazata yadda ka auri wata bayan ita ba, bayan haka ta fini komai, sannan ga abunda ke tsakaninta da mahaifina, ina ganin ƙiyayyata ƙarara a idonta, ga kuma bazan so ka dinga samun saɓani da mahaifiyarka saboda ni ba, dan haka ina muku fatan Alkhairi a rayuwar Aurenku me cike da alkhairi, Allah ya ƙara tsareku daga sharrin maƙiya, da mahassada nagode sosai Yusuf "
Gaba ɗaya jikinsa yai sanyi, sosai ta bawa Yusuf tausayi, tabbas Nurat ta cancanci a tausaya mata, da tausayi halin da take ciki a yanzu, amma yasan ko wace kalar wiwi yake sha, baze haɗa Widad da wata ba, saboda yasan azabar kishi irin na Widad, Nurat ta zare hannunta daga nasa ta koma ciki da sauri.
Jiki ba ƙwari Yusuf ya fito daga falon, ya nufi waje, Suleiman ya kalleshi yace "lafiya kuwa?"
Yusuf yace "Yallaɓai akwai damuwa"
"meyafaru"?
"Nurat sona take dagaske fa"
Suleiman yace "Au kaida baka san son naka take ba?"
Yusuf ya dafe kai yace "Yallaɓai, dan Allah kamin alfarma ka kaini in ga Widad, dan Allah bazan daɗe ba insha Allah"
Sulaiman yace "Shikenan, bakomai mije ina ne?"
Yusuf yai masa kwatance suka tafi, a bakin gate wani ɗan sanda ya taresu yace "ya akayi?"
Yusuf yace "a gayawa Widad Yusuf ne"
Ɗan sandan yai murmushi yace "Ohhh ashe megidane, ai tun ɗazu take jiranka"
Aka buɗe musu gate, Suleiman ya shiga da motar yana mamakin haɗuwa da tsaruwa gami da girman gidan.
Yai parking Yusuf ya fito daga motar, yace "Yallaɓai zo mu shiga mana"
Suleiman yace "Gurin budurwa ma ban bika ba se gurin matarka, a'a ina nan"
Yusuf kawai yai murmushi ya girgiza kai, ya shiga ya dinga duba falukan dake gidan, Kasancewar ya kirata bata ɗaga ba, can ya hangota a wani falo, tana zaune akan 3 seater, ta haɗe rai sosai, sanye take da dogon wando, da 'yar riga ƙarama, ta gyara gashin kanta ta saka ribbon saki ƙarshensa a bayan ta, hakan ya bawa cikinta damar fitowa sosai, abun mamaki ta saka jambaki da kwalli a idonta, abun da Yusuf be taɓa gani ba, sedai ta haɗe rai.
Yusuf ya ƙaraso inda take yana murmushi yace "farar mace alkyabbar mata, why are you sad? Ba gani nazo ba"
Ta ɗaga kai ta kalle shi, ta mayar ta sunkuyar da kanta tana danna wayarta.
Yusuf ya ƙaraso ya zauna kusa da ita yace "bazaki ɗago in ƙare miki kallo ba?"
Matsawa tayi daga kusa dashi, ya kalleta cike da mamaki yace "lafiya kuwa?"
Ta ɗago tace "Daga ina kake?"
Yusuf yace "naje wani gurine shiyasa..
" Yoseef kasan bana son ƙarya fa, ina kaje? "
Maimakon yai mata magana, seya ƙura mata ido, ta saka idonta a nasa tace " Yoseef gurin Nurat kaje "
" waye ya gayamiki gurinta naje? "
" tunda ka cemin zaka wani guri, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, naji a jikina gurinta zaka je, kuma kana shigowa naji kana ƙamshin turarenta, Yoseef wallahi gurinta kaje"
Yusuf yace "lallai zuciyarki tana tare dani, dan ba tayi miki ƙarya ba, tabbas naje gurin Nurat bisa ga Umarnin Umma, naje na duba Nurat bata da lafiya, Widad, Nurat bata cancanci wulaƙanci ko banzatarwata ba, dukda abunda mahaifinta yayi, amma ta taka mshimmiyar rawa a gurin kuɓutata, kalli ta rasa mahaifiyarta, mahaifinta ya tafi prison, kuma a yau take gayamin tana sona, be cancanci in wulaƙatanta ba"
"Yanzu me kake so ka gayamin? Zaka Auri Nurat ne kokuwa?"
Tai maganar tana tsststare shi da ido, Yusuf yace "ni bahaka nske nufi ba, itama tasan hakan bame yuwuwa bane, amma yakamata itama a dubata, a tausaya mata, ta rasa kowa Widad ko ban Aureta ba bata cancanci wulaƙanci ba, ta temakeni kuma kin.....
Cikin faɗa Widad ta dakatar da shi, ta hanyar cewa " ni ka cikamin kunne da ta temakeka, ni wulaƙanta ka nayi? Ko kana zaton Nurat tana da abunda zata ja da Bukar Bulama ne? Kasan waye Bulama kuwa? Aiko mahaifinta da suke tare da Bulama, wallahi bashi da ƙarfin ja da shi, yana da arziki kuma goyon bayan manyan mutane a duniya ba ƙasa ba kawai, Yoseef Bukar yamin barazana ko inje kotu in bada sheda ko ya kashe Ummanka, ko kasan ba Nurat ce tai sanadin kuɓitarka ba Allah ne ya kuɓutar da kai, amma se da na bada kadarorina na miliyoyin nairori, aka siye mutanen Da Bulama ya siye, nasa aka ninka musu abunda ya basu, na ɗaukar maka babban lawyer wanda shine ya tsara komai? "
Ta ɗanyi shiru sannan ta kalli Yusuf, daya zuba mata ido tace "inda Bulama ya kaini ya ɓoye, akwai wata mata da take kula dani a gidan, wayarta nake karɓa inyi browsing inga yadda shari'arka ke gudana, katsam ta bar wayar a hannuna, ta tafi aikace aikacenta, ni kuma nayi recording a wayar, na cire memory card ɗin bata sani ba, na bata wayarta, na rubuta takadda na bata na nannaɗe memory card ɗin a leda, a cikin takadda, nace ta aramin dubu ɗaya taje ta samu shagon masu saida abubuwa ta basu, na bata ina addu'a Allah yasa saƙona yaje inda na tura shi.
Nayi rubutu ne, nace 'zuwa ga wannan takaddar taje gareshi, dan Allah ina neman Alfarma, ina son duk yadda za' ayi ledar dana aiko da ita, da abunda ke cikin ledar, a kaiwa Barrister Hafiz Mubi, ace masa inji Widad, sannan a karɓi dubu ɗayan hannun matar a bawa wanda ze kai yayi kuɗin mota, itakuma ace maya babu abunda na aikota ta saimin.
Shine aka karɓi saƙon, akace mata babu aiken da na mata, ta dawo ba tare da tasan mena aiketa ba.
Barrister Hafiz, ɗahane daga cikin lawyoyin Daddy, saƙon ya isheshi ya duba, shima na rubuta masa wasiƙa, nace ya duba cikin memory card ɗin, akwai saƙo ya duba.
A cikin audio na gaya masa yadda ze saida wasu daga kadarorina, ya ɗaukar maka lawyer, Kasancewarsa abokin Khalil ɗan uwan Nurat, a nan ya samu dama shima suka haɗu da wasu lawyoyin aka tsaya maka a shari'ar, badan kuɗin da na saki ba, da har yanzu ba'a ƙare shari'ar a haka ba, da kotu bazata wanke ka ba, harse an kammala shari'a dasu Bulama, sedai a bada belinka, amma daka motsa sekace Nurat ta maka halacci, kaje ka ƙarat kai da ita, kaje ka Auri Nurat"
Ta ƙarasa maganar tana kuka, ta tashi zata tafi, Yusuf ya riƙeta gam ya zuba mata idanunsa, taƙi kallonsa ta cigaba da kukanta, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nasa.
"Kinji nace miki zan auri Nurat ne?"
"Idan ma baka faɗa ba alamu sun nuna ai"
"kina so in saɓawa Umma, dukda tarin alkhairinta a gareni saboda ke? Idan nayi haka na kyauta? Kina ganin raguwar auren namu zata yi albarka ne?"
Widad ta girgiza kai alamar a'a.
Yusuf yace "ki bani lokaci, ina son in daidiata komai ne, amma sekin dena wannan koke koken, da tayarmin da hankalin sonake mubi komai a sannu, kinga ni duk ban san wannan ba se yanzu da kika gayamin, kiyi haƙuri kinji"
Ta zumɓura baki taƙi magana, hawaye na cigaba da fita daga idonta.
"bazaki dena kukan bane?"
"Nika ƙyaleni inyi dan haushinka nake ji" tai maganar tana basarwa
Yusuf yace "to shikenan, bari in tashi in tafi"
Sauri tayi ta riƙe shi tace "wallahi ka tafi sena bika"
"to goge hawayen nan maza"
Bata goge hawayen ba, ta kwanta a jikinsa tana sake tura baki gaba, kamar yarinya ƙarama.
Ya shafa gashin kanta yace "dama haka kike sona? Bani da bakin yi miki godiya, nagode sosai Babyna, Allah ya bani abunda zan mayar miki da kadarorinki bazan so ace kin rasa wani abu da kika mallaka saboda ni ba"
Widad tace "Dukiya ɗazu ce, ni kai ne a gabana Yoseef, bana kallon dukiya ni kai nake kallo kawai, zuciyata kai kawai take kallo, ni kai nake so fa, ni banyi dan ka biyani ba, ni tukucin zuciyarka nakeso kawai"
Tai maganar tana sake kwanciya a jikinsa tana kuka.
Ya rungumeta sosai a jikinsa yace "is ok my love, ki dena kuka na fahimce ki, in dai zuciyata ce kin samu I love you my wife"
Tace "I love you too Yoseef"
Ta maƙalƙaleshi tana lumshe ido, tana shaƙar ƙamshin turarensa daya kashe mata jiki sosai.
Yusuf ya shafa gashin kanta yace "kinyi kyau sosai masoyiyata, kamar in sace ki in gudu haka nakeji"
Widad tace "dan Allah mijina ka fahimtar da Umma, mu samu ta yadda mu rayu tare, Yoseef na yadda in rasa komai nawa in kasance da kai har abada, you are my world and happiness Yoseef"
Yusuf kasa magana yayi, se ajiyar zuciya da yake tayi, saboda yadda jikinsa ya mutu gaba ɗaya, ya dinga sauke ajiyar zuciya, can yace "My love ya babyna yake? Fatan baya wahalar min dake dai?"
Ta tura baki tace "gaskiya yana bani wahala, yaita kicking cikina, ko ya hanani cin Abinci"
"ki kwantar da hankalinki, lokacine ze dena insha Allah, zan masa faɗa ya dena wahalar min da babyna, ke dashi duk ina sonku sosai"
Widad ta tashi daga jikin Yusuf, ta kalli cikinta tana murmushi tace "kaji dai Abunda Dad ɗinka yace ko? Ka dena takuramin"
Yusuf ya ƙura mata ido sosai, ta ɗago ta kalle shi tace "lafiya kuwa? Wannan kallon fa? Ga fruit can a dining tashi muje ka bani abaki, nima in baka"
Yusuf ya girgiza mata kai alamar a'a, tace masa "why?"
Yace "that's not what I want"
'So what do you want? " tai maganar tana kallonsa.
" I want to kiss you, lips ɗinki sunyi kyau sosai da kika sa jambaki "
Murmushi kawai tayi ta ɗauke kai daga kallonsa, a hankali ya sunkuyo da fuskarsa dai dai tata yana mata wani irin kallo me wuyar fassara, a hankali yake mata numfashi a fuska, Widad kamar an sassaƙata ta kasa ko motsi daga inda take zaune, tana jin saukar numfashinsa a fuskar ta.
Rungumeta yayi yana kissing ɗinta, to show her how he misses her, and she responds to his message to show him that she also miss him, wayar Yusuf data fara ringing ce ta dakatar dashi daga abunda yake yunƙurin yi.
Sunan Umma ya gani akan screen ɗinsa, yaiwa Widad alama da tayi shiru, ya daidaita nutsuwar sa ya ɗaga wayar yace "hello Umman Yusuf"
Umma tace "kuna inane?"
"muna gidansu Nurat ne"
"bata wayar mu gaisa"
"Umma ai ta koma cikin gida, kin ganni a harabar gidansu, yanzu zamu taho da Yallaɓai"
Umma tace "to shikenan, ka hanzarta ka dawo, bana son ka dinga nisa sosai"
Yusuf yace "to Umma, Insha Allah gani nan dawowa"
Ya kashe wayar yasa a aljihunsa, ya kalli Widad dake kwance, ta ɗauke daga kallonsa yace "sweetheart am sorry, kiyi haƙuri zan tafi kar Umma ta gane nazo gurinki kinji"
Bata ce masa komai ba se binsa da kallo da tayi, ya saita nutsuwarsa ya miƙe ze fita, ya waigo ya kalleta yaga tana hawaye, ya dawo ya durƙusa ya riƙe hannayenta yace "kiyi haƙuri matata, Insha Allah na kusa dawowa gareki kinji, karki damu dan Allah kidena kukan nan haka, nafi ki buƙatar ganinki a kusa dani"
Ya share mata hawayen fuskarta, ya sunkuya ya sumbaci goshinta, sannan ya bar falon cikin hanzari.
Suleiman na ganinsa yace "kai haka mukayi da kai, daga zuwa ka ganta seka shige kayi zamanka kana soyayya ka shanyani, har Umma ta kirani a waya, na mata ƙarya ai muna tare a gidansu Nurat"
Yusuf yace "muje kawai, nima ta kirani karta gane naje gurin Widad"
Sulaiman yace "shikenan muje"
Tunda suka tafi Yusuf hankalinsa baya jikinsa, ya baro shi can a tare da matarsa, gashi yayi mamakin jin itace tayi me yuwuwa, da dukiyarta dan ganin shiya kuɓuta daga halin daya shiga.
Tunani kawai yake yi, Suleiman ya fuskanci hakan, dan haka yaita masa nasiha yana kwantar masa da hankali, amma sam Yusuf baya gane me Suleiman ke cewa.
A waje Suleiman ya ajiye Yusuf, shi kuma ya tafi, Yusuf ya shiga cikin gidan.
Ya shiga tare da sallama, Umma ta amsa masa tace "Yusuf kun daɗe fa, ya jikin Nuratun"?
Yusuf yace "da sauƙi, suna gaisheki?"
Umma tace "to Allah ya ƙara afuwa, amma ya na ganka wani iri? Akwai matsala ne?"
"A'a Umma, bakomai fa"
Umma tace "shikenan, ana daf da shiga sallar magariba, kai alwala ka tafi masallaci"
Yusuf yace "to Umma"
Ya shiga ɗakinsa, cike da tunani fal a zuciyarsa.
Dan kar Umma ta gane yana cikin damuwa, yasa yaje ya ɗauki Abincin dare yaci, Umma nata masa hira amma baya ganewa, se amsa mata yake da ummmm.
Ya tashi ya tafi ɗakinsa, yana zuwa beyi wata wata ba ya ɗakko waya ya kira Widad, sedai muryarta ƙasa ƙasa kamar bata da lafiya.
Yusuf yace "lafiya kuwa wife?"
"bakomai" ta bashi amsa
"Kiranki nayi muyi hira, kuma naji kamar ba lafiya"
"hirar da zata fi kowacce a gurina, itace ganinka a kusa dani, amma kamin nisa, ina ji ina gani ba yadda na iya, dukda son da nake maka"
Nan Yusuf ya kwantar da murya ya shiga aikin rarrashi, harta saki jikinta dashi, ta dena fushin suka koma soyayya, yauma seda suka sha soyayyar su, seda dare yayi sosai sannan suka kwanta bacci cike da begen junansu.
Umma tana monitoring ɗin Yusuf, ya dena zaman tsakar gida ko kuma hira da ita, kullum yana ɗaki riƙe da waya, da tayi zancen Nurat seya dinga basarwa, saboda haka ta zuba masa ido, sedai ta toshe duk wata hanya daze fita yaje yaga Widad, dan bata son ya kuma raɓar Widad yaja musu matsala.
Sosai fa Suke kewar juna shida matarsa, gashi baze iya bijirewa Umma ba, yana matuƙar tausayin Widad sosai, dan yadda suka yi waya yau ya gane bata da lafiya tana jin jiki sosai, ga babu hanyar fita, dan idan harze fita se Umma ta tambayi ina zashi.
Da Yamma Umma ta hanshi zaune yayi jugum, yayi shiru kamar wanda akayiwa mutuwa.
Ta kalle shi tace "Yusuf zo kaje ka siyo kayan miya, zanyi girki naga yamma tayi"
Yace "to"
Ta bashi kuɗi ta lissafa masa abunda ze siyo mata, sannan ta bashi dubu biyu tace "ga wannan ka riƙe a hannunka, kafin ka koma gurin aikin"
Yusuf ya karɓa yace ya gode, ya fita yin cefanen.
Umma tana ta aikinta a tsakar gida, taji anyi sallama, ta amsa tare da waigowa wanda ta gani ne yasata sakin tsintsiyar hannuta ta saki baki, tana kallonsa..
AMANA! AMANA!! AMANACE!!!
IDAN KIKA FITAR BADA IZININA BA, ALLAH YANA KALLONKI, KUMA KINCI AMANA
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
160_161
Umma ta bi mutumin da kallo kamar taga baƙuwar halitta, mutumin yace "Madam a bamu guri mu zauna mana, an tsaya ana bina da ido"
Jin yace a basu gurin zamane yasa Umma leƙa bayansa, taga mutumin tare da Widad a bayansa, take Umma ta ɗan tsuke rai.
Mutumin yace "Jidda wannan kallon fa? Ki bamu gurin zama mana"
Umma tai musu jagora zuwa falonta, taje fridge ta kawo musu ruwa da lemo, Widad tace "Umma ina wuni"
Umma ta amsa sama sama, Mutumin yace "Jidda dama rai kanga rai? Rabona dake tun kina budurwa, ban sake sanin inda kike ba, se kwanan nan naji ashe Bashir Maitama ne mijinki, Allah ya jiƙansa da Rahama"
Umma tace "Ameen ya Allah, kwana ba adadi Alhaji Ahmad, dan yanzu sedai ince Alhaji ka ƙara ƙiba, kamar ba kaiba kamaninka sun canza saboda kuɗi sun zauna"
Alhaji Ahmad yace "bari Jidda, abubuwa duk se godiyar Allah kawai"
Ya juya ya kalli Widad yace "daughter na, wannan ce sirikar taki"
Widad ta jinjina kai, Ya kalli Umma yace "dama kece sirikar tamu kike wahalar min da 'ya?"
Umma tace "kamar yaya kenan?"
Alhaji Ahmad yace "to a al' adar Hausawa dai, namiji ke zuwa biko, to hula taja ɗankwali, munzo