Showing 201001 words to 204000 words out of 209297 words

Chapter 68 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

735

bata ƙaunata yanzu haka, Yusuf yana son matarsa sosai cigaba da musu shisshigi a rayuwar su ze iya basu matsala, musamman da Ummansa da take son lallai ya aureni, Yusuf mutum ne me nagarta da haƙuri ba dan Widad ba ze iya aurena, amma ga laifin da mahaifina yai musu, ga Widad nasan dukda a baya bata soyayya amma yanzu na fuskanci akan Yusuf ba abunda bazata iya ba, gara in ƙyalesu bana som zama silar rasa farincikin kowa a rayuwa, ina wa Widad murnar samin nagartaccen abokin rayuwa, nima Allah ya bani miji nagari wanda ze soni, me kyawawan halaye kamar Yusuf "

Ta ƙarasa maganar, tana zubar da hawaye sosai, Khalil ya ƙarasa gabanat, wani irin matsanancin tausayinta ya kama shi, he feels her pain, yasan yadda raɗaɗin son maso wani yake, Nurat ta so Yusuf sosai yana zuwa inda take tsaye, ta faɗa jikinsa tana kuka, ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta, da alama abun yana cim zuciyarta bata samu damar yin kukan bane ba.

"kiyi haƙuri, Allah ze miki musaya mafi Alkhairi, kin san da yawa a rayuwa, mu kanso abunda ba alkhairi bane a rayuwarmu, Allah ya zaɓa miki mafi Alkhairi Ƙanwata"

Ta dinga jinjina masa kai, amma ta kasa magana, saitin kunneta yace "koda kuwa nine, idan Allah ya musanya miki kina so?"

Tashi tayi daga jikinsa ta goge hawauenta tace "cake ɗina ze ƙone, bani guri in duba"

Tai maganar tana basar da abunda yace kamar bata ji ba, ya dinga bimta da kallo yana tunanin she didn't accept his proposals.





Su Widad sun shirya tsaf, domin zuwa ƙauye, Widad se murna take, Amma daga baya se jikinta yai sanyi tace "Daddy, wai ina Saleh ne? Zamuje garin su gurin 'yan uwansa, me zamuce musu idan suka tambayemu shi?"

Daula yace "ai kema kin san Daula baya manta alkhairi, Saleh yayi sintiri a Asibiti saboda ni, kuma shiyafara gayamin kuna hannunsa, sannan kunyi Aure, saboda alkhairin da yayi muku nakejin zan iya yafe masa, na karɓeshi a hannun 'yan sanda, an kai shi Egypt saboda anma rauni da duka a hantarsa, za' a masa aiki "

Widad tace" Daddy hanta kuma? "

Daula yace "Eh, saboda dukansa da aka dingayi a ciki ya samu matsala"

Widad tace "Allah ya bashi lafiya, amma yayi ɗawainiya damu sosai"

Yusuf ne ya fito Umma da Alhaji Ahmad suna bayansa, seda suka fara shirin shiga motar sannan Yusuf yace "nifa Umma har yanzu banji yadda akayi kika san Alhaji Ahmad ba?"

Daula yai murmushi yace "Budurwarsa ce ta farko tun zamanin ƙuruciya, a gidansu akaga be shirya ba Abbanka ya aureta ya barshi'

Kunya ta kama Umma, kamar ta nitse a ƙasa dan kunya, Widad da Yusuf suka shiga yimata dariya.

Alhaji Ahmad yace" kuma har yanzu ina so ba, amma tace min se ɗanta ya yadda, dan haka Yusuf nidai ina so har yanzu "

Yusuf yai dariya ya buɗe mota yana faɗin, ni dai ba ruwana".

Suka shiga mota suka ɗau hanyar garin Bauchi, bisa rakiyar 'yan sanda.


Tun su Alhaji Daula suna sa ran ƙarewar tafiyar, har suka zuba ido nausawa kawai ake cikin ƙauyuka, sannan aka bar kan titi aka saki hanya aka nausa wani surƙuƙin ƙaiye, tun daga nan Daula yake tasibihi, da mamakin azabar surƙuƙin gurin nan.


Nanam sukayi tafiya me nisa akan burji, babu kwalta ba zaka taɓa cewa zaka tarar da gida ba, se sama da ƙasa sukeyi danma a manyan motoci suke, amma hakan be hanasu jin jiki ba, idan aka shiga wani ramin, se Yusuf ya riƙe Widad gam saboda kar abunda ke cikinta ya wahala, a haka suka ƙaraso ƙauyen nan.

Suka fir fito yayinda 'yan garin sukayi dandazo suna kallon motocin, yayin da wasu suke gudu saboda ganin motar' yan sanda.

Daula ya kalli ƙauyen, ya sake kallo yace "yanzu Baby, a nan kuka rayu?"

Widad tace "ƙwarai kuwa Daddy"

Ita kanta Umma daba wani kuɗine da itaba, tunani take ta yadda zata yi rayuwa a wannan ƙauyen.

Widad ta raɗawa Yusuf a kunne "Allah sarki, yau zanje inga ɗakin amarcinmu"

Suka ƙunshe baki suna dariya

Tuni labari yajewa megari, ga wasu nan sunzo a jibga jibgan motoci irin na masi sace mutane, da 'yan sanda, ya fito a ruɗe, dan baya son abunda ze tayarwa da mutanensa hankali.


Sam be gane Yusuf ba balle Widad, Yusuf ya ƙarasa gaban sa ya zube yana gaisheshi, seda ya tsurawa Yusuf ido sannan ya gane shi, yace "innalillahi, Malam Yusuf kaine? Dama zan sake ganinka Yusufa?"

Yusuf yace "Alhamdilillah, gani ai tare muke da iyayen namu ai"

Widad ta ƙaraso itama tana gaida megari, yace "Allahu Akbar, Amarya 'yar gwaggonta"

Widad tace "aikam bari in ƙarasa in ganta kuwa"


Ta shiga da sallama, Hindu na zaune tana tankaɗen garin dawa, taji wani irin ƙamshin turare ya gaauraye gidan, ta ɗaga kai zata amsa sallama tayi tozali da Widad, aiba shiri tayi wani uban tsalle tai fatali da ƙwaryar garin, tai gurin Widad tace "Allah yasa ba mafarki nake ba?"

Widad tace "idonki biyu Hindu, nice Widad ce"

Suka rungume juna suna kuka, Gwaggo ta fito da sauri jin kamar muryar Widad, aikuwa itace ba wata ba, nan gida ya hargitse da murna da koke koke, Widad tace "ina aminiyata abikiyar faɗana Hari"


Hansai tace "taje barka bayan layi ita da Hanne, amma yanzu zasu shigo"

Tana gama rufe bakinta, sega Hari da gudu kamar ƙaramar yarinya "wayyo Allah na, jama'a dagaske Wudas ce? Wai Wudas ce tazo garin nan?"

Widad tace "nice Hari"

Widad ta rungume Hari, Hari ta shiga kuka tace "ban taɓa zaton na saba dake haka ba, seda kuka bar garin nan"

Umma tai sallama itama ta shigo, nan aka shimfiɗa musu tabarma, suka karɓsu hannu bibbiyu Widad tace "Mama ga Wannan itace Umma mamanmu nida Yoseef"

Hari tace "kamar yaya kenan? Ya za'ayi ku zama uwa ɗaya? '

Widad tace " zaki fara ko? Tunda na gayamiki ki barshi a haka mana"

Hari tace "naji an barshi a hakan"


Hanne tai sallama ta shigo, ta kalli inda Widad take, ta ganta a balarabiyarta, fatarta ta sake ja tayi kyau sosai, Kallo ɗaya Widad tayi mata ta ɗauke kai daga kanta.


Tuni aka fara kiciniyar ɗora girki, Widad tace base an ɗora komai ba, sunabda abinci a mota, amma ita dai idan an gama tuwo a bata zata ci.

Aka karɓo mukulli aka buɗe ɗakinsu da suka zauna, Widad cikin hawaye tace Allah sarki ɗakin mijina, wayyo rayuwa, a lokacin da nake shan baƙar azaba a hannun Bulama ji nake tamkar in dawo ƙauyen nan da zama in huta"

Ita kanta Umma tayi mamakin yadda suka rayu a gurin nan, megari yayiwa Su Daddy jagora har ɗakinsu Widad, nan suka tsaya suma suna mamaki.

Hindu har ƙasa ta durƙusa ta gaishesu, Yusuf yace "Hindu amma dake zamu tafi kano ko?"

Hindu tai murmushi tace "waceni"

"yakamata, kinga yayartaki ta kusa haihuwa, seki tayata zama"

Hindu tai murmushi tace "Allah ya sauketa lafiya"

Yace "Ameen"

Daddy ya kalli ɗakin nan nasu yace "yanzu Widad ce ta rayu a ɗakin nan? Allah me yadda yaso sannu Yusuf nasan ka sha gwagwarmaya"
Yusuf sedai yai murmushi.


Hari yazo kusa da Widad ta zauna tace "abun mamaki, Wudas da ciki ana shan taɓara nasan"

Widad tace "ko in kira miki Yusuf ki tambaye shi idan ina taɓarar ko ba nayi?"

"kefa matsala ce dake, baki san wasa ba"

Hari ta shiga halin nata na ɓare ɓaren zance, aka shiga shigo da kayan Abinci gidan nan kamar ba gobe, wanima basu san meye ba.

Nan jikinsu ya hau rawa, suka tabattar da lallai Widad 'yaf ga tace gaba da baya.

Widad taja hannun Hindu gefe, tace "Hindu kinga babana?"

Tace "Na ganshi mana"

Widad tace "tsoho ne sosai ko?"

"A' a wallahi ba tshoho bane, gashi me kyau wallahi yana kama da mijinki sosai, dake dashi da Yusuf duk kuna kama, irin idanunku ɗaya sak"

Widad tai murmushi tace "zaki iya auren Babana?"

A razane Hindu ta kalleta tace "Kamar yaya, ta yaya babanki ze auri 'yar ƙauye kamarni, gashi babban mutum"

"Hindu ki dena duba wannan, dan Allah ki aure shi, nasan zaki kulamin dashi dan Allah Hindu ki auri babana"

Jikin Hindu ya hau rawa, zata yi magana amma Widad tace "yi shiru, karkice komai ina zuwa, kuma karki gayawa kowa wannan maganar"

Widad taje ɗakinsu, inda su Daddy ke zazzaune tace "Daddy, i want to talk to you"

Ba musu ya miƙe ya biyo bayan ta, ta ja shi can waje a wani soro tace "Daddy nifa nayi maka mata a garin nan"

"mata kuma kamar yaya?"

"Daddy, matar Aure dai nayi maka, dan Allah karka bani kunya kaji Daddy"

"Widad, nifa na haƙura da Auren nan"

"A'a Daddy, dan Allah ka tsaya ka ganta mana"

Yace "shikenan"

Ta shiga cikin gidan da sauri, ta tarar da Hindu a inda ta barta, jikinta a sanyaye tace "saka hijjabinki kizo muje"

Hindu ta saka hijjabi, ta biyo bayan Widad, ta mata jagora zuwa inda Daddy yake zaune, gaba ɗaya yaiwa Hindu wani irin kwarjini, da bata taɓa gani a gurin wani ba.

Suka ƙarasa Widad tace "Daddy, ga amaryar da nayi maka, ina fatan bazaka ƙi karɓa ba"

Daddy ya kalli Hindj, yarinya ce ƙarama, yace "Amma daughter, naganta yarinya ce sosai fa, kamar zaki girme mata ma"

Cikin harshen larabci Widad tace "Daddy aiba haramun bane, wallahi yarinyace tagari me nutsuwa, zakayi alfahari da ita"

Yace "to ita kin tabatta tana sona? Karki ƙwareta dan son kai kinga na girma dayawa"

"Daddy Hindu bazata ƙika bafa" tai magana kamar zata yi kuka.

Daddy ya kalli Hindu yace "ya sunan ki ne?"

Hindu dake gefe ta takure kamar bokanya tace "Sunana Hindu"

"masha Allah, Hindu kinji rigimar da wannan matar ta tattago, ban miki tsufa ba?"

Hindu ta kasa cewa komai, se jikinta dake ta tsuma, tana rarraba ido.


Widad tace "Daddy ai mun gama magana da ita, yanzu megari zakayi wa magana, kaga se a bada kuɗin aure ma kafin mutafi.








AMANACE!!!
Ayshercool
07063065680
12/10/21, 1:36 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

168_169

Daula yace 'Widad mubi komai a sannu, ki bari muji ta bakinta, karki mata dole mana, kuma maganar aure ai ba' a gaggawa "

Widad tace " Daddy, nasan irin zaɓen da na maka ne, ni dai ka amince kawai please "

Daula ya lura da yadda jikin Hindu keta tsuma, ko idonta bata iya ɗagawa ta kalle shi, ta sunkuyar da kai tanata cimimiyewa a hijjabinta.

Daula yace " Hindatu, tashi ki koma gida, Widad zata sa ki auri tsoho "

Cikin hanzari Hindu ta miƙe, ta shige cikin gida tana haɗa hanya, Daula ya kalli Widad yace  "Widad, wannan haɗin naki beyi ba, kowa zega kamar an ƙwareta ne, tayi yarinta dayawa kuma kinga ba ita tace miki tana sona ba, gashi ni na riga na fidda rai da Aure"

Widad tace "Daddy, na zauna a garin nan na zauna dasu, nasan halin yarinyar nan, Daddy karka duba ƙauyanci ko ƙuruciyarta, ni dai tukuicin dazakamin shine ka Auri Hindu, sannan akawo musu cigaba a garin nan, shine zaka biyani ɗawainiyar sa sukayi damu, dan Allah Daddyna "

Daula yace " Naji, zanyi shawara kafin mutafi "

Da ƙyar ya lallaɓa Widad ta tafi, ta koma gurin Alhaji Ahmad da Yusuf ta dinga musu magiya akan lallai su saka baki, Daddynta ya auri Hindu, Alhaji Ahmad yace "to muyi musaay, kice mijinki ya bani ummansa nima"

Widad tai dariya tace  "ka samu, nidai fatana Daddy ya amince da Auren Hindu, sonake kafin mutafi ya bada kuɗin Aurenta"

Umma tace "Widad, ba'a gaggawa a harkar Aure, karki takuramasa ko ita yarinyar ki takura ta fa"

Yusuf yace "Umma Hindu bata da matsala, and she deserves to marry a descent person like him, idan harya yarda ya aureta ze sha biyayya"

Widad tace  "Yoseef, dan Allah zomuje ka gayawa Megari, bana son Daddy yayi missing wannan opportunity ɗin"

Daula yai shiru yana tunanin maganar da Widad tazo masa da ita, yadda yaga suna nan nan da su Widad, da yadda suka sake dasu, suma hira ama wasa ana dariya, da yadda mutane keta shiga suna fita a gidan, ya tabattar masa da cewa sun riƙe su Yusuf da Amana, dan haka duk wanda ya shigo gidan seya fita da kuɗi ko Abinci, Daula ya dinga basu kyautar kuɗi da Abinci, da wannan ya shigo se Widad tace Daddy ga wane a bashi kaza, ko kuma ai masa kyautar kaza.

Widad sun sha hira da Gwaggo, seda aka tuƙa tuwon nan taci, suna ta faɗa ita Hari, Hari tace  "Ohh ni Hari, wai Wudas ce sa ciki, ranar haihuwa akwai kallo"

Widad tace "me za'a kalla?"

"raki da rashin haƙuri mana"

"Hari kema fa Allah kaɗai yasan abunda kika yi haihuwar fari"

Umma sunyi hira sosai da Gwaggo, ta dinga bata labarin yanayin zaman da suka yi dasu Yusuf a gidan, Hanne kam ta kasa yadda ace wannan ne mahaifin Widad, iya motocin da suka cika ƙofar gidansu ma 'yan rakiya kawai abun kallone, banda rakiyar motar' yan sanda, wai ashe dagaske dai Daula ne baban Widad, lallai yaci sunansa Daula.

Ɗaliban Widad suka dinga zarya suma, suma zuwa gaishe ta da ɗaliban Yusuf, magidantan da yai ta koyarwa, sedai dukda wannan tarin kaɓakin kayan Abincin da aka rarrabawa 'yan ƙauyen, wannan yazo ya bawa Widad kyautar kuka, wannan ya kawo tsintsiya, wannan ya kawo Nono, ƙwan zabi zuma, haka suka dinga kawo musu wai suyi tsaraba, Daddy yai farinciki da karamcin mutanen garin, da yadda suka riƙe' ya'yansa suka zauna lafiya, gefe guda kuma ya tausaya musu yadda suke rayuwa ba makaranta, ba wutar lantarki ba kwalta bare Asibiti.

Kafin su bar garin, Daddy ya sanar da me gari cewa za'azo a gina musu makaranta ta boko da islamiyya a saka gwamnati ta kawo musu malamai, Widad kuma tace zata gina musu Asibiti, a kawo musu ma'aikatan lafiya, Daddy yace  "Alhaji Yusuf baka yi magana ba"

Yusuf yai murmushi yace  "Aini tunda aka musu makaranta da Asibiti, an gama min komai, fatana kuma ai musu boreholes na ruwan sha, saboda babu ruwa a garin nan, a saka gwamnati ta samar musu da wutar lantarki, saboda Asibiti baze yuwu babu wuta ba.

Nan jama'ar suka dinga murna suna Allah ya Sanya alkhairi, suna saka musu albarka.

Hindu kam ta ƙuke a ɗaki, tana tunanin abunda Widad ke shirin yi, banda abun Widad ina ita ina wannan hamshaƙin attajiri, ɗan gayu me ilimi ga kyau da dukiya, ita kuwa ga ƙauyanci da rashin wayewa, amma ta dage seta aure shi, ita gani take kawai ze aureta ne saboda 'yarsa, amma tabbas ba sa' ar Aurensa bace.

Tana cikin tunanin taji ana guɗa da shela a tsakar gida
"Alhaji Daula, yaga 'yarmu yana so, kuma harya bada kuɗin Aurenta naira dubu ɗari biyar, mudai zaman Yusuf da matarsa a garin nan namu alkhairi ne, yace ya gani yana so, kuma me gari ya amsa, yace ya bashi, watan arzikinmu a ƙauyen nan ya tsaya,' yarmu zata auri attajiri, ko iya Asibiti da makarnta da akace za' a mana aimu am biyamu, 'yarmu Hindu Tayi goshi, zungureren goshima kuwa "

Gaban Hindu ya faɗi, kenan dagaske dai ta tabatta Widad za tayiwa Babanta Auren dole da' yar ƙauye?

Hanne kuwa gigicewa tayi, dan a ganinta tafi Hindu komai, dan meyasa ba'ace itaba se wata Hindu, Hindun daba wani kyaune da ita ba ga baƙin jimi, amma ace zata auri attajiri haka.

Da zasu tafi Widad ji tayi kamar karsu tafi, dan sosai takejin kewa da ƙaunar mutanen garin, saboda karamcinsu da girmamawa, Ta shiga ɗakin Gwaggo ta sami Hindu a ƙarshen gado  tayi shiru tana tunani.

Widad tace  "Hindu, karki ɗaga hankalin ki, babana bashi da matsala ko damuwa, mutumin kirki ne zaku zauna lafiya ƙalau dashi, sannan an saka wata biyu, saboda kafin ɗaurin Aure a kawo muku cigaba garin nan, saboda manyan mutane ne zasu garin nan, munyi magana za'a aiko da mota tun saura sati biyu biki a ɗauke ki a kaimin ke can kano, mu fara shirye shirye "

Hindu kawai jinjina mata kai tayi, daga nan suka yi sallama suka tafi, a hanya sunata jinjina karamci da mutuntawa na wannan al'ummar gari.

Gaba ɗaya ƙauyen nan ya ɗauka, Daula ze auri Hindu, ga kuma kaɓakin arzikin da aka sauke musj, sunata rawa da murna ga alƙawarurrukan da aka musu na kawo musu cigaba a garin.

Su Widad kuwa garin kanon dabo suka wuce kai tsaye, suka sauka a farmhouse, Bayan sun huta Alhaji Ahmad ya wuce gidansa, Umma tace ba zata zauna a nan gidan ba, gidanta zata tafi, shi kuma Yusuf nauyi yake ji, koba komai Daddy sirikinsa ne, ace suna gida ɗaya su kwana ɗaki ɗaya da Widad, haka ya basar Widad kuma ta dage se Umma ta kwana a gidan ba zata tafi can gidanta ba, da ƙyar Umma ta yadda ta amince.

Wasa2 Seda suka kwana biyu da dawowa, amma suna farmhouse tare da Umma, kullum se Alhaji Ahmad yazo, Umma ta takura akan cewa lallai seta bar gidan, dan ita gaba ɗaya jinta take a takure.

Daddy yace zasu rakata gida, kafin nan ze kaisu gidan daya saiwa su Yusuf, kuma ranar nan da sati biyu Yusuf ze tafi Lagos, inda babban kamfanin shige da ficen ƙarafa yake, wanda yake mallakinsane, shi dai Yusuf jin abun yake banbarakwai, kamar bashi ba.

Koda suka fita seda suka fara zuwa ainihin gidansu da suke zaune, suna zuwa ma'aikatan nan suka dinga rige rige zuwa gurin Daula, ganin ya bayyana ashe yana raye, sedai gidan kamar kango, ba shige da ficen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login