Showing 3001 words to 6000 words out of 209297 words

Chapter 2 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

703

gida tana ta kokawar yin tatar gasara, se barna take”

Yusuf yayi dariya yace “danma baka ga yadda take tankaɗe ba, bakaga asarar garin da tayiwa Gwaggo ba, ai Gwaggo ba karamin mutunci take man aba, se fatan Allah ya sakamata da alkairi”

Saleh yace “ai abunma da takaici ace yarinya kamar wanna bata iya aikin gida ba,abun da kunya ai”

“yakamata kiyi mata uzuri da an koya mata da zata iya ai”

Saleh yace “waye ze koya mata, ta dinga hantarar mutum tana masa wulakanci”

Yusu yace “adinga kara mana matata ce fa Saleh”

Sale yai murmushi yace “masu mata manya,to Allah ya bada hakuri, na manta ne, Allah yasa in an tashi komawa a tafiwa da Daula jika”

Shiru Yusuf yayi bece komai ba yana tunani, Saleh yace “lafiya kuwa?”

Yusuf yace “Saleh akwai matsala ina cikn damuwa sosai, har yanzu bata san waye niba, bana son taji a wani gurin tayimin kallon makaryaci, yanzu ban san ta in zan faraba bansa n ya zata kalli abunba, zata iyayimin bore ina tsoron darunta”

Saleh yace “hakane amma ai kai namijine, kuma zuwa yanzu duk ta rage wasu abubuwan ai, ba lallai ta maka wulakanci tunda yanzu ba wanda ta sani se kai”

“Saleh anya ba ka manta wacece Widad ba? Jiya ta gama jadaddamin bata yafiya ga wanda yayi mata karya ko yaci amanarta”

Saleh yace  "ƙwarai na san wacece ita, yadda ta gaya maka hakane bata yafiya ga wanda yayi mata ƙarya ko yaci amanarta, duk yadda suke da shi kuwa, amma ai kai akwai alaƙa me matuƙar ƙarfi a tsakaninku, zata iya ɗaga maka ƙafa kuma kamata yayi ace kai da kanka ka gaya mata, karka bari taji a waje, idan kuwa ka kuskura ta samu labari a gurin wani akwai matsala, dan bata ƙi ka tafi prison ba kaima, tace an haɗa baki da kai za'a cuce ta, abun da nake ganin dai yafi shine ka sanar da ita kawai, hakan zefi "

"tabbas nasan bata yafiya ga wanda yaci amanarta, nikam Saleh me kayi mata wanda yasa ta kasa duba alkhairin ka se laifukanka? "

Saleh yayi murmushi yace " labari ne me tsawo Yusuf, kuma gaya maka labarin tamkar ƙara wani laifin ne akan laifi, amma ka bari idan tayi niyya zata iya gaya maka komai, nidai shawarata da kai, tun kuna nan ka gayamata waye kai"

Yusuf yaja ajiyar zuciya yace " Inajin tsoro Saleh, harga Allah ni fa ina son Widad ne tsakani da Allah, yanzu idan na gaya mata zata iya ƙina, a yanzu mu tana ƙasa tana dabo ne, dan itafa bata yadda akwai so ba, dan haka bani da tabbacin tana sona, kuma inzo in gaya mata wannan magana, abun ze lalace gaba ɗaya ne fa"

Saleh yace "haba namijin duniya, ai kai kana da jarumrtar da ka cancanci a sara maka, haka nan duka butulcin me butulci dole ya sarawa namijin ƙoƙarin da kayi akan Widad, ni kaina na fuskanci sonta kake, amma dole zata ɗaga maka ƙafa dan baka cancanci ta wulaƙanta ka ba, be cancanci ta manta da alkhairin da kayi maka ba, dukda yarinyar wata irin muguwar bahaguwa ce, amma kayi ƙoƙari kafin ku bar garin nan tasan abunda ake ciki "

Yusuf ya dafe kai yace " Subhanallah, ban san ta ina zan fara ba Saleh, ina tsoron abunda ze biyo baya, ni kome zata yi baze dameni ba, ni fargaba ta karta rabu dani ko tayi min wata mummunar fahimta "

" Yusuf kenan, da alama wannan ne karonka na farko na shiga soyayya ko?"

Yusuf ya girgiza kai yace " Na taɓa soyayya Saleh, har na sawa kaina bazan sake soyayya ba, katsam Widad ta shigo cikin rayuwata ba tare da na warke daga wancan ciwon dake zuciyata ba, kuma har nake jin cewa a yanzu inawa Widad son da banyi wa waccan yarinyar ba"

Saleh yace "lallai kana cikin Jarrabawa Yusuf, ina maka fatan Alkhairi tare da fatan Allah ya fitar da kai"

Sallamar Widad ce a ɗakin ta katsesu, suka amsa mata gaba ɗaya, fuskarta duk bushashiyar gasara, kanta babu ɗankwali goshinta duk gumi.

Ta kalli Saleh ha haɗe rai tace "Excuse us please"

Saleh yace "to" ya tashi ya fita ya bar ɗakin.

Ta kalli Yusuf tace "ka zauna kana ta surutu, baka san lokacin salla yayi bane, har an fara aikowa ana tuna maka, kaje kaja salla"

Yusuf yace  "aini yanzu gaba ɗaya kunyar mutanen nake ji".

Widad tace "me kayi musu na kunya?"

Yusuf yace "tunda kika rungume ni a gabansu, indai suka ganni se inga suna wani sunkuyar da kai"

Ɗan guntun tsaki Widad tayi tace "to dana rungumeka a gaban su is it an abomination? Saɓo nayi kome?"

"to ai su basu saba ganin irin haka ba, is against their norms"

Widad tace "to su suka sani, ni wanka zanje inyi, kaje kayi sallar"

Yusuf yace "to bari inje in dawo in rama dukan da kika yi min da Asuba"

"ina nan ina jiranka kuwa, kasan dai na fika ƙarfi yanzu, kai sauro ya zuƙe maka ƙarfi".

"dole kice haka mana, tunda na baki jinina, dole kiyi ƙarfi ai"

Ta kalle shi tace "ji wata magana, jinin naka ma da bashi da kyau, duk ba wasu sinadarai a cikinsa, shine duk ka dameni da ka bani jini, to zan biya ka abunka"

Yusuf yayi dariya yace "kamar gaske"
Yai waje, yana fita ta kintsa ta ɗau bokiti ta tafi taje tayi wanka.

Tana zaune tana shafa man zaitun a jikinta Yusuf ya dawo, ta bawa ƙofa baya, farar fatarta se ƙyalli take da ɗaukar ido, ga baƙin gashinta ya kwanta sosai a bayan ta, ƙasansa ya jiƙe da ruwan wanka, ba taji dawowar Yusuf ba se jinsa tayi zaune a kusa da ita, numfashinsa na sauka a jikinta.

Da sauri ta ɗago ta kalle shi tace "meye haka? Ya zaka zo ba ko sallama, ka zauna kana shinshinani"

Seda tasa Yusuf yayi dariyar dabe shirya yinta ba, yace "niba shinshinaki nake ba, se kace wani kare"

"to baga numfashinka nan inaji a jikina ba"

Beyi magana ba, ya kalli hannun ta data tsiyayo zaitun, ya zura nasa hannun akan nata, zaitun ɗin wani duk ya zube, ya shiga shafa mata a jikinta.

Ji tayi tsaigar jikinta na tashi, ɗan yamutse fuska tayi tace "Yoseef bana so, ka bari in shafa da kaina"

"Ni kuma ina so, ki bari in shafa miki"

Tsaki tayi ta ɗan ɗaga murya tace "nace maka bana so" tai maganar tana ƙoƙarin miƙewa, Amma Yusuf ya riƙeta ya hanata tashi, a hankali yace "yi haƙuri Widad, magana nake so muyi" yai maganar yana sauke numfashi.



Littafin kuɗi ne, kuyi magana ta wannan lambar domin siyan littafin
Nagode
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 48_49

Littafin kuɗi ne pay before you read please 🙏 🙏 🙏



Haɗe rai tayi tace "dan za muyi magana shine zaka dinga yimin wannan abun haka, ni bana so gaskiya karka sake yimin"

Maimakon yayi magana Shiru yayi ya sake ƙanƙameta sosai a jikinsa, ya kwantar da kansa a jikinta, ita kuwa mutsu mustu kawai take, so take taga ta ƙwace daga jikinsa, amma abu ya gagara, ya riƙeta sosai ga ƙarfinsu ba ɗaya ba.

A hasale Widad tace "Wai dan Allah Yoseef meye hakane?, ka cikani towel ɗin jikina ze kwance fa? Nace maka bana so ka cikani dan Allah, wallahi gaba ɗaya ka canza hali, kwanan nan sekai tayi min wasu abubuwa wanda bana so, kuma kana sane"

A hankali ya cika ta, ya kwanta akan katifar yayi shiru tare da lumshe idonsa.

Se kuma ta juya tana kallonsa tace "meye kuma?" ba tare da ya buɗe idonsa ba ya girgiza mata kai.

"to me zaka gayamin?"

"bakomai" ya bata amsa

"wani irin bakomai bayan kace magana zamuyi?"

Gabansa ne ya faɗi, yaga be kyautu yayi mata wannan zancen a wannan gaɓar ba data ɗau zafi, dan haka ya buɗe idonsa ya ɗan tsare ta da ido yace dama ba wata magana bace, ina son in sake gayamiki Ina sonki Widad "

Ha ɗe rai tayi tace " kaga tasarmin daga kan katifa ta, tunda ba zaka dena wannan shirmen ba, kuma daga yau in ka san wannan shiritar zaka gayamin, karka sake cewa zakayi magana dani na gaya maka, dan bazan saurareka ba"

Yusuf yace "Maganar tawace shiririta? Queen ba shirita bace i mean it, kalmar so ba abun wasa bane ko imagination ba, please my Queen ki yarda ina sonki mana"

Banza tayi masa, ta ɗakko kayanta tana ƙoƙarin sakawa, ya juya mata baya don ta sa kayanta.
tayi ƙasa da muryarta cikin ƙunƙuni tace 'kaji da shi dai, kai ta mun wasu abubuwa amma idan zansa kaya seka wani juya, wai kai gaka na Allah, inma baka juya ba niba abunda ya dameni sa ka yana zanyi'

Bece mata komai ba se dai murmushi da yayi, se data gama sa kayan, ta yunƙura zata miƙe ya sake riƙeta, a fusace tayi niyyar yi masa rashin mutunci, amma ya rungumota ta kasa cewa komai jin ya haɗe bakin su.

Gaba ɗaya Yusuf yafi ƙarfinta, ta kasa gane kansa kwata kwata, kwanan nan se wasu ɗabi'u yake mata wanda bata gane kansu, tana ji tana gani seda yayi me isarsa sannan ya cika ta, ba zata iya ƙwace kanta ba.

Yana cikata bata kuma kallonsa ba, ba tace komai ba rai a matuƙar ɓace tayi waje, kallo ɗaya zaka yiwa fuskar ta kasan a fusace take, ta fita tsakar gida rana ta take, kowa yana ɗaki ta fita ta samu guri a ƙasan bishiya tayi zamanta.

Hakanan Yusuf ya dinga jin be kyauta ba abunda yayi, amma ya zeyi shima bayin kansa bane, mutum ne shima kuma me cikakkiyar lafiya, shi kansa yanzu ya fara ɗar ɗar na zama da Widad a guri ɗaya, komai ze iya faruwa.

Barrister Khalil kam tunda yakoma gida yake tunanin hirar da sukayi da Nurat game da mahaifinta, tabbas mahaifin Nurat ba karamin hatsabibi bane ,ze iya aikata komai muddin burinsa ze cika ,amma yayi mamakin yadda Nurat tace masa da saka hannunsa a sace Daula da akayi,abun da mamaki matuka, nan ya shiga nazarin ta ina yakamata yayi wani abu? Amm muddin ya kuskura Alhaji Musa yasan yana wani yunkuri,ko kuma ya gane ya san wani abu akan abunda yake aiktawa,to tabbas ba abunda ze hanashi daukar mataki akansa,dan bashi da Imani sam.

Barrister Hafiz ma tunda ya koma gida yake tunanin batun da aka bijiro masa da shi akan dukiyar Daula,tabbas kudi abun sone,amma meze biyo baya idan suka amince akayi wann aika aika? Idan sukayi aikin nan tabbas zasu samu kudi,amma hatsarin dake cikin hakan shine abun dubawa, watakila idan shi nya amince ba lallai sauran lawyoyin su yadd ba,amm tabbas yana son kudi shima.

Ya yanke shawarar zefara tuntubarsu daya bayan daya yaji opinion din sauran akan lamarin abunda suka yanke shikenan.
  Ya tashi ya dau mukullin motarsa ya fice.

Anwar kuwa gaba daya yayi baki,ya rame saboda zaman gurin nan babu sauki sam, ga sauro ga rahsin kula, ga azabar wahala da ake gana musu akan lallai se sun fadi inda Daula yake, amsar sa dai dayace be san inda yake ba.

Yana zaune a inda suke ajiye yayi shiru yana tunani,s hi babban abunda yake damunsa shine waye ya sace Daula? Wanda ya sace shin yana iya kula dashi?maganinsa ma ko ana kula dashi a bashi oho? Yayi zurfi a duniyar tunani yaji an kira sunansa, a hankali ya daga kai, dan sandan yace

“ka taso kana da bako”

Anwar ya taso ya taho a hankali yana jan kafa,yabiyo bayan dan sandan.

wanda aka nuna masan akace shine me nemansa sam be sanshi ba, dan ko ganinsa be taɓayi ba.

Mutumin ya kalli Anwar yace “kaine Anwar?”

Anwarv yace “Eh nine”

Mutumin ya kalli Anwar yace “ naji ance ranar sha biyar ga wata za a kaiku kotu ko?”

Anwar ya jinjina kai yacec “ eh hakane”

Dukda ban gabatar maka da kaina ba baka san koni waye ba,nima turoni akayi gurinka,kuma ancemin babu bukatar seka san waye ya turoni, yanzua abunda nake so nbda kai shine ina son ka gayamin tsakani da Allah meka sani game da batan Alhaji Nasir”

Anwar ya gaya masa iya abunda ya sani,Mutumin yace  "shikenan karka damu ka kwantar da hankalinka,insha Allah komai zezo da sauki”

Anwar yace  “shikenan nagode sosai”

Mutumin yace “sannan kuma, bana bukatar kowa yasan nazo gurinka ciki harda mahaifiyarka’

Anwar yace “shikenan,Insha Allah babu meji”

Daga nana sukayi sallama mutumin yatafi.


Widad na zaune a gindin bishiya, tana tunanin abunda ya shiga tsakaninta da Yusuf, tai shiru sosai tana tunani, tama rasa me yakamata tayi, haushi zataji kome?, Ganin Widad zaune ita kaɗai a gindin bishiya yasa Hindu tazo ta Zauna a gurin Widad, tace "Amarya me kike anan ke ka ɗai haka?"

"ina shan iska ne kawai" Widad ta bata amsa

Hindu tace "tunda ba abunda kike, ɗan koyamin turancin mana"

Murmushi Widad tayi tace "to ta ina zamu fara, bansan a inda kika tsaya a turancin ba"

Hindu tace "ni dai kota ina ne mu fara"

Nan Widad ta shiga koya Mata daga ƙananan abubuwa wanda zata iya riƙewa.

Yusuf ya fito ze tafi Sallar la'asar, ya ya kalli su Widad yace  "karatu ake ne?"

Widad bata amsa ba, Hindu ce tace "eh  wallahi turanci ake koyamin"

Yusuf yace "Masha Allah, Allah ya temaka"

"Ameen" Hindu ta amsa banda Widad data haɗe rai.

Daya dawo ma a gurin bishiyar ya tarar da ita, tana cin Abinci.

Yusuf ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita yace  "Shine kike cin Abincin babu ko gayyata? Bari inzo muci tare, kin san cin Abinci tsakanin ma'aurata yana ƙara danƙon soyayya, nikuma ina son Soyayyarmu ta wuce ɗanƙo ta zama kamar ƙarfe"

Banza tayi masa taƙi kula shi.

Ya wanke hannu yazo yasa hannu suna cin Abincin, amma Widad taƙi ce masa komai.

Se yanzu Yusuf ya fuskanci fushi take dashi.

Yusuf yayi ƙasa da muryarsa yace "My Queen me nayi miki ne? Se magana nake am kin basar dani, bana jin daɗin hakan fa"

Ƙara haɗe rai tayi, ba tare da tace masa komai ba.

Yusuf yace "Abunda  nayi miki a ɗaki ne yasa kike fushi dani ni ko?"

Cire hannunta tayi daga Abincin, taje ta wanko hannunta ta dawo tai zamanta, shiru yayi yana sake binta da kallo.

Hanne ce ta fito, tana ganin Yusuf ta wangale baki tace  "Sannu"

Jiki a sanyaye Yusuf yace "Yawwa Sannunki Hannatu"

Ba ƙaramin daɗi Hanne taji ba jin Yusuf ya kira sunata da Hannatu.

Ta ƙara wani rausayar da kai tana murmushi, ta ƙaraso inda yake zaune kusa da Widad a kan tabarma, tace "bari in ɗauke kwanon, naga kamar ka gama cin Abincin"

Bece mata komai ba, taje ta ɗauke kwanon ta kai gurin wanke wanke, ta kawo masa ruwa a buta tace "ga wannan ka wanke hannu"

Yusuf yace "God bless you, Nagode sosai"

Ta jinjina masa kai tana murmushi, Widad ko kallon inda suke ba tayi ba, ta cigaba da kaɗa ƙafarta.

Tana jin yadda Hanne keta wata kwarkwasa, Hindu  dake banɗaki ji take kamar ta fito ta shaƙe Hanne, ta wani ɓangaren kuma tana ganin baiken Widad, data zuba mata ido ta ƙyaleta.

Yusuf ya tashi ya tafi ɗakin su, Hindu na fitowa daga banɗaki a fusace tace  "Hanne gaskiya abunda kike bakya kyautawa, ya zaki dinga shigewa mijin mace a gabanta, dan kawai kinga tana ɗaga miki ƙafa, haba Hanne dan Allah ki dimga tunani mana"

Hanne tace "ba zanyi tunanin ba ɗin, ina ruwanki dani? Tunda ita ba zata iya kula dashi ba ai shikenan, mace ba abunda ta iya se girman kai, sam bata da tarbiyya, bata san darajar miji ba"

Widad ta miƙe zata koma ɗaki, sedai babu zato Hanne taji Widad ta shaƙeta da rigar jikin ta, seda idanunta suka yo waje dan azaba, cikin zare ido da ɗaga murya Widad tace

"Am tired, ban taɓa ɗagawa wani mahaluki ƙafar dana ɗaga miki ba, ina ƙyaleki ne saboda Karamcin iyayenki a gare ni, kin san wacece ni? Babu ruwana da alaƙar dake tsakaninki da Yoseef, amma karki sake sakani a irin wannan haukan naki, banda ƙaddara ko a mafarki aka ce ni Widad zan zauna a wannan ƙasƙantaccen gurin zance ƙaryane, saboda kawai ina zaune a cikin wannan jar ƙasar shine zaki dinga gayamin baƙaƙen maganganu? Kin san wace ni, idan kin san wace Widad ko hanya muka haɗa sekin kauce, banda dalilin ƙaddara babu abunda ze haɗanj da daƙiƙiyar baƙauyiya kamarki, hanyar dana sa ƙafata na wuce ma baki isa ki biyo ta ba"

Hanne se kakari takeyi, Su Hari sukazo da gudu amma suka kasa ƙwatar Hanne a hannun Widad, fitowar Yusuf ne yayi daidai da shigowar Saleh, da sauri Yusuf ya ƙarasa inda dramar ke faruwa, idanun  Widad sunyi jawur, fuskarta sharkaf hawaye tana masifa.

Yusuf ya ƙarasa yasa hannu ya cire hannun Widad daga wuyan Hanne, Hanne ta shiƙi iskar 'yanci, ta koma gefe tana ta haki tana zare ido, kamar an karɓeta daga hannun zaki.

Saleh yace "Wallahi da ta kasheki ta kashe banza, dan babu wanda ya isa ya ɗaukarr miki mataki, kin san wacece kuwa? Kin san' yar waye ita? Ko dan kawai kin ganta a cikin gidan nan a zaune, ina lura da yadda kike mata wasu abubuwan tana ƙyaleki, tunda kika ga nima tana mun abunda taga dama ina ƙyaleta to tabbas kin san ba a banza ba, ƙaddara ce ta kawota zama daku, amma ke a gidan su ko me goge mata takalmi baza'a ɗauke ki ba"

Gwaggo tana jin duk dramar da'ake yi, amma tai shiru a ɗaki bata ko fito tsakar gidan ba, saboda tasan abunda ke faruwa, tasan yadda Hanne ne ke wuce gona da iri a wasu lokutan.

Shikan sa Yusuf yasan ba ƙaramin ɗaga ƙafa Widad kewa Hanne ba, a yadda Widad keda izza bata ɗauka raini, amma take sharewa idan ta mata wani abun, lallai haƙurinta ne ya ƙare.

Suka shiga ɗaki, Widad se kuka take jikinta na tsuma, ga gumi data haɗa.

Yusuf ya shiga share mata hawayen fuskarta  tare da faɗin "is ok, kiyi haƙuri nasan kina haƙuri, Amma ki ƙara insha Allah mun kusa mu koma gida"

Kamar wadda aka mintsina, ta miƙe daga jikinsa a fusace tace  "dalla ma ni ƙyaleni, ba kaine kake mata dariya ba, yasa ta rainani takemin wani kallo na daban ba, harni wannan baƙauyiyar yarinyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login