Showing 150001 words to 153000 words out of 209297 words

Chapter 51 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

729

bayan raina, idan ya gano ajiyar dana bashi ze danƙa amana ga masu ita "
Tai maganar tana tsura masa ido, nata cikin nasa.

" me kike nufi, suna gurinwa? "

" Gurin masoyina mana, da kake so ya ƙare rayuwarsa a prison, seka bari ranar daya fito seya baka "

Ya wanketa da mari da wannan Ƙaton hannun nasa, idan ya mareta har wani jirine yake kwasarta, amma ta dake tace "idan ka kasheni, ka kashe dukiyar da kake nema, ka huta, shedar tana gurinsa, mabuɗin yana gurina, dan haka dabara ta rage game shiga rijiya"




IDAN KIN SIYA AMANACE, IDAN KIKA FITAR KUMA KINCI AMANA!!!
Ayshercool
07063065680
11/24/21, 10:26 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

136_137

Bulama ji yayi kamar ya shaƙeta ya huta da wannan baƙincikin, daga wannan se wannan, daga wancan se wancan se wasa take masa da hankali, ya miƙe kamar ze fita ya juyo ya kalleta, yasa ƙafarsa ya dinga dukanta yana taka ta, tasa hannu tana tare cikinta saboda karya dakar mata ciki, danshi ya sakankance cikin nan babu shi ya fita tuni.
Haka ya dinga Takata da ƙafarsa, ko kukan bata iyawa sedai hawaye dake zuba kawai kamar an kunna famfo, yai me isarsa ya dinga zaginta ita da Daula, yai ya gama yasa kai ya fice.

Widad tai kuka har hawayen suka gagara zuba se ƙunar rai da take, tana jin abunda ke cikinta yana motsawa kaɗan kaɗan, ta tuna yadda Yusuf ya dinga binta da kallo, kana ganinsa kasan a tsatsanr wahala yake, fuskarsa duk tabo da raunuka na ciwo.
idanunta sukayi jawur, kamar wadda aka zubawa barkono saboda kuka, ta sunkuyar da kanta ta shafi cikin ta, da take jin motsinsa kaɗan kaɗan a can ƙasar mararta, cikin zubda hawaye tace "wace amsa zan bawa abunda yake cikina, idan har ya girma ya samu labarin mahaifiyarsa taje kotu ta bada sheda akan mahaifinsa an kai shi prison? Shedarma ta ƙarya, nasan duniya zata zageni ga duka wanda yasan ainihin abunda ya faru, sedai ba yadda na iya, nayi hakanne da ceton rayuwarsa, kaicona haɗuwa ta da Yusuf ta zame masa babbar ƙaddara a rayuwarsa, ya sadaukar da rayuwarsa don inganta tawa, amma maƙiyana suna ƙoƙarin cin galaba akanmu, abun da basu sani ba shine, tun ran gini tun ran zane, ita gaskiya duk daren daɗewa zata yi halinta"

Tai maganar ranat yana mata wani irin zafi da raɗaɗi.

Yusuf kam ya sha mamaki da Widad taje ta bada sheda a kotu, akan cewar saceta yayi sedai yanayin daya gantabya tabattar masa akwai lauje cikin naɗi, akwai abunda yake damunta, da gani duk inda take ba'a kwanciyar hankali take ba, amma duk da haka ya zaci zuwanta kotu ze zama sassauci a gareshi, sedai zuwanta kotu ya zama ƙarin tsanani a gareshi, yanzu kam ya haƙura yasan idan ba ikon Allah ba, bashi da wata hanyar kuɓuta sam.

Alhaji Haruna kwana biyu ya samu sauƙi, Amal ta dena bibiyar sa, sedai ba ƙaramar kassarawa tayi masa ba, kwashe masa kuɗin Account da tayi, gashi ba damar kai rahoto yaje ya ɗaure kansa da kansa, gashi gaba ɗaya yanzu wanda zs nemi shawarar tasu hankinsu na kan wannan shari'a da'ake fafatawa.
Bulama gaba ɗaya yakasa nutsuwa, dukda wannan shirin da wannan shirin da yake yi, slide mistake Asirinsa ze iya tonuwa, kuma yasan koda tsiya, koda Arziki Yusuf baze bada abun nan ba, yayi signing ma a tabattar wannan signing ɗin nasane, me shige dana Daula amma yaƙi, babu irin dukan da baa'yi masa a gidan yarin nan ba amma fafur Yusuf yaƙi sakawa, wane ma tabbaci yake dashi akan cewar Recording ɗin yana gurin Yusuf, dan rainin hankali ba wani abun wahala bane a gurin Widad, zata iya raina masa hankali tace yana gurin Yusuf amma baya gurin nasa, nan ya dinga takura Ƙwaƙwalwarsa, akan lallai seya gano mafita.

Umma kuwa tun daga ranar da Widad ta bada wannan shedar taji ta tsane ta, bata sonta duk wannan halin wahalar sanadiyyarta ya shiga amma taje ta bada shedar zirr, gashi a maganar da Yusuf yai mata ranar da sukaje ganinsa a prison ya gayamata wai Widad ɗin matarsa ce, ko ta yaya oho? Umma gaba ɗaya tunaninta ya tsaya, bata da yadda zata yi wanda zata temaki Yusuf dashi.
Ta kira Suleman tace "dan Allah idan baya komai yaje tana son ganinsa"

Bayan awa ɗaya da rabi, sega Suleiman yazo suka gaisa sannan tace  "Suleiman, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi da ƙoƙarin da kake ta min, amma ina neman wata alfarma ne a gurinka"

Suleiman yace "To Umma ina jinki"

Tace "dama cewa nayi, ko zaka samo me siyan gidan nan, ai masa kuɗi a siyar, a saida Babur ɗin Yusuf, da gurin furnitures ɗinsa, a ɗauki lawyer me zaman kansa yaje kotu ya tsayawa Yusuf , ko Allah zesa a dace"

Suleiman yace "Umma da hakan ze yuwu, da tuni nayi wallahi base an siyar da gidan nan ba, har Office akamin aike daga sama, akace muddin nace zan saka kaina a cikin case ɗin nan, to tabbas zan rasa aikina, kuma nima za'ace dani aka haɗa baki, sannan a hanya aka kuma tsareni, akace idan nai involving kaina a case ɗin nan, to za'a kasheni da iyalina, kuma irin wannan barazana akewa duk wanda yai yunƙurin taimakon Yusuf, shiyasa kikaga an kasa komai a kai, bakiga inaji ina gani akace wai ba hukumar 'yan sanda ce ta bashi aiki ba, bayan kuma nasan ƙaryane ba, da hannuna na bawa Yusuf aikin nan, amma ina yunƙurin yin wani abu, komai ze kwaɓe "

Umma tai ajiyar zuciya tace" babu wanda ya bani mamaki irin Abbas, har gida yake zuwa ya ɗaukeshi su tafi gidansu yarinyar nan, amma saboda rashin imani, yace wai be san zancen ba"

Suleiman yace "kiyi haƙuri, ki dena kuka haka, dama ai si mutane kullum ƙara koya maka hankali suke, amma ina tabattar miki Yusuf baze zauna a gidan yari ba, gaskiya zata yi halin ta"

Umma tace "Allah yasa, ina fatan haka nima"

Nurat kam kamar ta ɗora hannu aka tai ihu, ta rasa abunda yake mata daɗi, wai ace Widad ya bada wannan shedar aka Yusuf, dukda irin yaddar da tayi dashi, tabbas da Yusuf yana neman wani abu a gurin Widad dabe dinga bata kariya ba, yanzu shikenan saboda shedar Widad, ta tabatta Yusuf yayi abunda ake zarginsa dashi, kamar wadda mintsina, ta tashi da sauri don taje ta sato wayar Mummy tai waya, sedai tana fitowa falo ta tarar daddynta yana kallon labarai, 'yan jarida na bayyana abunda ya faru a kotu, Alhaji Musa yace  "Maman Nurat, kinga shari'ar yaron nan ko? Dama na faɗa miki, irinsa ba abun tausayi bane, gashi nan ita kanta yarinyar ta tabattar da abunda ake zarginsa dashi, bari in kira Bulama"

Ya ɗakko wayarsa ya kira Bulama, "Allah ya baka yawan rai, ai yau naga yadda shari'ar nan ta kasance, komai ya tafi daidai, kayi ƙoƙari gaskiya, haka ake son Amini, gashi baya nan amma ka tsaya tsayin daka akan sha'anin iyalinsa, gaskiya kayi namijin ƙoƙari, Allah dai yasaka da alkhairi"

Nurat bata iya jin abunda ake cewa daga ɗaya ɓangaren, amma tana ganin yadda Daddynta ke ƙyaƙyata dariyar mugunta a waya.

A hankali ta juya ta koma ɗakinta, tana hawaye tace "Allah sarki Yusuf, ya za'ayi in fita in gayawa duniya cewar ba kai kayi garkuwa da Widad ba, da saka hannun mahaifina a sace su Yusuf? Ta yaya? Tabbas idan aka rufe Yusuf ba'a masa adalci ba, definitely tasan akwai yadda akayi har suka kuɓuta aka kamasu a ƙauye, amma Yusuf baze garkuwa da Widad ba, ta zauna tai shiru tana tunani, bata san ta ina zata fara temakawa Yusuf ba, amma tabbas ƙarshen zalunci an masa.




Ramlah ce tsaye akan Fahad tana zazzaga masa masifa, "Wallahi Amal baka isa ba, tun wuri ka maida hankalinka, nafi ƙarfin ka wulaƙantani, wato ka gama dani ka kama wasu, to baka isa ba tun wuri kaje ka turo azo ayi maganar Auren nan"

Fahad yai wata irin dariya sannan yace "Ramlah kenan, waye yake yaudarar wani tsakanin nida ke, dama a rashin wannan yarinyar ne, tuntuni tun ina ƙasar waje kin san ita zan aura, kuma gata ta dawo, dan haka me kike so inyi miki kuma? Kawai ki rungumi sorry, in kin samu wani wanda zaku daidaita se ku haɗe, dukda dai bance ke mummuna bacd but gaskiya ga balarabiya ina kallo bazan aureki ba, sorry kawai "

" Ni kake kallo kake gayawa haka? Lallai baka san Ramlah ba, kai ƙaramin ɗan isaka ne, wallahi baka isa ba, zaka ga abunda zan maka "

Fahad ya busa hayaƙin shisha sama sannan yai murmushi yace " Hmm keme baki san waye Fahad ba, karki bari ki gane waye Fahad tabbas "

" Ni kake gayawa haka ko? "

"Na gayamiki ɗin, dama haka bariki ta gada, kuma ki shiga hankalinki tunda wuri, tun ban saɓa miki ba"


Ramlah ta kalleshi tai ƙwafa, tai waje a matuƙar fusace, tana fitowa tai karo da Hajiya Sarah ta fito zata fita, mamaki yakamata ganin Ramlah daga part ɗin Fahad, ta tsaya Ramlah ta ƙaraso, tana ƙoƙarin buɗe motarta, Hajiya Sarah tace "Ramlah, lafiya kuwa? Me kika je yi ɗakin Fahad? Ina fatan lafiya?"

Ramlah ta kalleta tace "ba lafiya ba, kuma wallahi ki gayawa ɗanki ya saurari abunda ze biyo baya"

Hajiya Sarah tace "lafiya kuwa? Meya haɗaki da Fahad ɗinne? Me yayi miki ne?"


"Ki tambaye shi, shi yasan me yayi, kuma ya jira sakamakon abunda yayi min"

Ta bankaɗa ƙofar motarta ta shige ta jata a guje, mamakine ya cika Hajiya Sarah, ta shiga part ɗin Fahad, tana zuwa ta tarar yana shan shisha ta kalle shi tace "Fahad, wato har yanzu baka dena shaye shayen banzan nan bako, kana kawo mana matan banza har cikin gidan nan, kasa ubanka yazo ya kamani da faɗa da masifa, wallahi kaji tsoron Allah, ita kuma Ramlah meye ya haɗaka da ita?"

"wani abun tace miki na mata?"

"Ban sani ba, me take a part ɗinka? Ko itama shashancin kuke yi?"

"Mum dan Allah ki bar wannan maganar, kawai wasu suratanta ne na banza, marasa tushe balle makama, tazo ta nawa mutane Hayaniya a ka"

"wane irin Hayaniya ce? Gayamin kasan halin uwatta sarai, daga ita har yaranta ba mutunci suka cika ba, har gara Anwar ma, amma wannan me soyayyen idon, idan ka sake wani abu mara daɗi ya haɗaku dasu, wallahi duk abunda suka maka kai ka janyowa kanka, kaje ka ƙarata kai da uwarsu, idan yaso ubanka yasan yadda zeyi dasu, tunda 'yan uwansa ne, na gaya maka, tunda wannan rayuwar ka zaɓawa kanka Fahad, gaka nam ga duniyar kaje kayi Allah ya temaka "

Ba ce mata komai ba, ta fito ta baro ɗakin nasa, zuciyarta sam babu daɗi, ace yaronta na farine ke irin wannan mummunar rayuwa haka, ranat baya mata daɗi Sam.



Amal ta rasa yadda zata yi da uban kuɗin data damfari Alhaji Haruna, gashi sam Mummy bata san abunda ya faru da ita ba, balle tasan da wannan uban kuɗin data damfari Alhaji Haruna, sedai Amal ta kasa gane abunda yake damunta, gaba ɗaya yanzu kullum cikin ciwo take, nan ciwo can ciwo, abun ya fara damunta, ta yanke shawarar zata je ganin likita zata je taji meye yake damunta haka.

Ramlah kuwa data bar gidan Bulama kamfaninsa ta tafi, yana tsaka da aiki yana shirin shiga meeting se gata, babu sallama babu komai ta tsaya ta tstsareshi da ido.

"Ke lafiya kuwa? Ni na rasa waye yafi hanki tsakanin ke da babarki, ya zaki zo ki tsaya a kaina haka kina ƙaremin kallo babu ko sallama"
"kaga suararamin kawai, tsason shekaru kana juya mahaifiyarmu, muna abunda kake so, wancan satin har kotu kasa naje na bada sheda akan wannan sharia'r, to nazo da buƙatata guda ɗaya tam, da nake so kamin"
"wace irin buƙatace haka? Bayan seda aka baki wani percentage kema, kuma idan kuɗin nan suka samu hadda ke za'a ci"
"Niba kuɗi zaka bani ba, shekaruna sun na ina zaune a gida na gama karatu bana aimin fari, balle na baƙi, kuma ɗanka Fahad ya taɓa min Alƙawarin Aure, dan haka tunda wuri azo ayi maganar da za'ayi a wuce gurin"
"Nifa ban gane maganar da kike ba"
"Kamar yaya baka gane me nake nufi ba? Wane yaren nakeyi maka? Ɗanka Fahad ya Aureni"

"Haba Ramlah, wacs irin kwaɗon magana ce wannan haka mara daɗin ji? Baki san Widad ze aura ba?"

"ban saniba, kuma matsalar kuce ba ta Ramlah ba, kawai ayi maganar da za'ayi"

Bulama yace "ni kike wa magana a haka? Ƙwarai kuwa waye kai a gudina da bazan maka magana a haka ba, ina ƙarewa 'yar gidan Daula shekaru ta kwashe tana maka wulaƙancin data ga dama, balle kuma ni da kake wa kallon biri ina maka ta ayaba, kawai kayi abunda ya dace, ko kuma komai ya faru "

Bulama yace " Ramlah, ban san meyasa kike haka ba? Kema kin san aurenki da Fahad ba abune me yuwuwa ba ko? "

" Aurena da Fahad, ba abune me yuwuwa ba, ka gayamin shima ya gayamin, nagode nima ku jira matakin da zan iya ɗauka "

Ta bar office ɗin Bulama, zuciyarta na ƙuna da raɗaɗin abunda sukayi mata, Amal na zaune a falo tana kallo, cikinta ss ciwo yake mata, ga wani irin ciwon baya da take fama dashi, gashi lokaci lokaci inda ta karye yana motsa mata.


Ramlah tana parking ta fito, ta buga ƙofar motar da ƙarfin gaske, tai ciki fuuuuu, kamar guguwa, Nura yace "Allah dai ya kwashe ma wannan baiwa Albarka, da ita da duk wanda suka je kotu suka bada shedar ƙarya akan Yusuf"

Murtalah yace "bari Nura, wallahi abun ya bani mamaki sosai, Amma nan aka zo aka taramu aka mana kashedi akan duk wanda yai wani yunƙuri, ze fallasa wani abu se an kasheshi, wayaga ta bakin magana, amma da tabbas nima sena bada sheda"

Isa yace "dan Allah Murtalah kaje ka bada shedar nan a saki Yusuf, wallahi zaluntarsa kawai ake yi"

Nura yace "Allah sarki duniya, kalli Isa wai kaine ke cewa ayi abunda za'a temaki Yusuf, abun da mamaki"

Isa yace "bari Nura, wallahi duk baƙin cikin mutum da iya ƙiyayyarsa, idan dai har mutum ya zauna da wannan bawan Allah, wallahi idan kaji za'a masa haka dole ka tausaya masa, kalli duk irin abunda muka dinga masa baya tanka mana, se azabar miskilancin tsiya a cikinsa kamar Uwarɗakinsa"

Nura yace "kai dai bari Isa"

Isa yace "kun san abunda ya ɗauremin kai kuwa?"

Sukace A'a

"Wai ashe Sani me yankan farce shima ɗan sanda ne, shine fa ya haɗani da Yusuf yace ɗan uwansa ne, dana gayamasa ana neman direba, amma naji wannan lawyern yace wai Abbas be san zancen ba, Amma duniya babu gaskiya, tabbas yanzu nake ganin gimbiyar Daula bata da laifi na ƙin mutane, ka yadda da mutum ya cuce ka a banza, yanzu duk wanda suke jikin Daula suna morarsa sune suke zalintarsa, kalli matar gidan nan ko sau ɗaya ba taje kotun nan ba"

Murtalah yace "iko se Allah, wallahi Isa da zamu samu dama ko iya wannan shedun muka riƙa, aka shiga kotu dasu zasu temakawa Yusuf, amma wallahi ina jin tsoro, kuma wallahi dani akan matar gidan nan zan bada shedata"

Nura yace "kai ita ta dameka, a samu a Yusuf ya kuɓuta, wallahi dukda nima inajin haushinsa yadda ƙirƙiri ya samu fada fiye damu a gidan nan, musamman ni daya nemi ya ƙwacemin aiki na, Amma gaskiya Yusuf baze aikata haka ba, kalli fa ko magana ake, idan aka sakota ko aka zageta seya haɗe rai yana ɓata fuska yana kare ta, wallahi da yayi niyyar sace ta da tuni ya saceta, akwai dai yadda akayi "

Nan suka cigaba da tattaaunawa suna hirar a tsakaninsu.

Ramlah kuwa tana shiga falo, Amal ta kira sunanta, Ramlah ta waigo a fusace tace " lafiya kuwa? "

" Ashe kema kim bada sheda a kotu akan Yusuf "?

" Eh na bayar se yaya? "

" Yakamata kiyiwa kanki adalci Ramlah, a bar bawan Allah nan da wahalar da aka jefa shi a ciki, bakya ganin saboda Alhakinsa ne muma namu ɗan uwan yana nan kwana da kwanaki ba'a ganshi ba, ga mahaifiyarmu se fama take da marurar hawan jini saboda damuwane da ɓacin rai? "

'Ke dalla sauraramin, an bada shedad kiyi abunda zakiyi, da aga Anwar da kar a ganshi be dameni ba, abunda yake gabana shi zanyi, kuma karki ƙara yimin wannan maganar"

Ta nufi ɗakinta, tana jin yadda zuciyarta take tafasa.

Tana zuwa ta jefar da Jakarta akan gado, ta buɗe wardrobe ɗinta ta ɗakko kwalaben syrup, kawai ta kafa kai ta kama tittilawa cikin ta, Hakan yai dai dai da buɗe ƙofar ɗakin da Hajiya Halima tayi, ta tarar Ramlah ya shanye kwalaben syrup ta faɗi a gurin, cikin fitar hayyaci.


"Na shiga uku, Ramlah me zan gani haka? Ramlah dama dagaske shaye2 kike? Me yasa zaki cuci kanki"

Sam Ramlah bata san me ake ba, tuni ta fara maye ta lula gajimare.

"Amal! Amal!" ta shiga ƙwalawa Amal kira.

Amal tazo tace "gani"

"Amal kinga, shaye2 Ramlah take yi, meke damunta haka zata faɗa wannan mummunar hanyar haka?"

Amal ta ɗan taɓe baki, tare da naɗe hannunta tace "Allah ya jiƙan Yaya Anwar, ba dan ya mutu ba, nan ya hukunta ta ya gayamiki ga abunda take yi, amma baki yadda ba, tuntuni take shaye shayenta, kuma wannan Fahad ɗinne ya koyamata, amma ba yau ta fara ba"

Hajiya Halima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login