Showing 129001 words to 132000 words out of 209297 words

Chapter 44 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

733

zo su kasance a haka baze yadda ba, amma shine zaune da ita a ƙarƙashin inuwa ɗaya ta Aure, suke zaune ba tare da ya ɗaga masa hankali ba, wani farinciki ne ke ratsa zuciyarsa, tabbas da Widad ta rayu da masoya na gaskiya, mussman tare da mahaifiyar ta ba zata yi wannan izzar da jin kai ba, sedai rashin masoya, da kuma tsantstsar zalunci da butulci da aka gwada mata yasa tayi wa mutane gaba ɗaya kuɗin goro mussman talakawa.

Saleh gaba ɗaya ya sadaƙar, jira yake kawai suzo su fara gana masa azabar da Bukar yayi umarni, sedai basu yi masa komai ba sedai ɗaɗɗaureshi da suka kuma yi.

Yana zaune a inda yake aka buɗe ƙofar ɗakin da yake kwance a ciki, ya ɗaga kai seya ga 'yan sanda sun shigo, tare da Alhaji Bukar, ya nuna musu shi yace "gashi nan, ku tuhume shi yasan inda suke, kuyi masa duk wata izaya da duk wani abubda zesa ya faɗi gaskiya, karku saurara masa dan Allah"

Ɗaya ɗan sandan yace "karka wani damu, zamuyi abunda ya dace"  suka kwancewa Saleh wannan igiyoyin suka ɗauke shi suka sashi a mota suka tafi dashi.

LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/21/21, 7:45 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

114_115

Saleh dai ne ce komai ba, yana jin yadda ake tafiya dashi a mota 'yan sanda, a galabaice yake dan haka be san inda suke tafiya ba, harabar police station akayi parking, aka fito da Saleh, yana tangaɗi haka aka tankaɗa shi cikin cell aka ƙulle.

Duk da yamma ce amma sauro har ya fara shagali a gurin nan, ga zafi a gurin kamar oven, haka Saleh ya baje a ƙasa ƙirjinsa da cikinsa na masa ciwo kamar zasu tsage, saboda duk daya sha da katako.

Yana jin wani ɗan sanda yayi sallama, sauram suka dinga sara masa, ɗaya daga 'yan sandan da suka ɗakko Saleh yace "Oga gashi nan a cell, munje mun ɗakko shi"

Ɗan sandan yace  "ok shikenan, ku rubuta statement ɗinsa"

"Yallaɓai tome zamu rubuta?"

"Kai baka san me zaka rubuta ba, ku rubuta bayani akan an same shi da laifin haɗa kai da Yusuf, sun sace 'yar gidan Nasir Daula, sun ɓoye su, ka dai rubuta abunda yakamata"

Ɗan sandan ya sara masa yace "ok sir, za' ayi yadda kace"

"Yawwa that's very good, and a matsa shi yadda yakamata ya faɗi abunda ake nema a gurinsa"

"Yes sir, za'ayi abunda kace"

Yace "good"

Daga nan ya wuce ya shige office ɗinsa.

Hankalin Nurat ya tashi sosai, ganin cewar dagaske mahaifinta yake ze raba ta da ƙasar, itama tayi ɗamarar wannan karon zata bijire masa, kome ze faru se taga ƙwal uwar daka, se taga ƙarshen abunda mahaifinta yake yi, dan barin mutum irinsa suna cigaba da abunda suke so a doron ƙasa hatsari ne ga al'umma, wataran za'a iya wayar gari mutanen kirki su ƙare, ta ɗau wayarta ta kira Khalil, Khalil ya ɗaga yace 

"Hello my dear, ya akayine any news?"

Nurat tai ajiyar zuciya tace "bad news brother, Daddy ya dage akan cewar wai sena tafi imperial U. K Inyi karatau a can, me Daddy yake nufi dani ne?"

"Calm down dear, make your statement clear please, kamar yaya imperial Collage, ke kaɗai zaki koma UK ɗin kiyi karatu, wanda kika yi a baya be isa ba"

"Nima shi na gani brother, shifa yayi min alƙawarin zanyi school a Nigeria, a Nigeria zanyi high institution, Amma kawai yazomin da wannan maganar, da alama yana zargina ne da fara bin diddiginsa, ni kuma gaskiya i won't tolerate it dear, gaskiya zan bijire"

Khalil yace "subhanallah, Nurat don't say that again, haba Nurat na sanki da biyayya da haƙuri, me zesa ki fara faɗar haka kuma? Haba Sister na"

Kuka Nurat ta fashe dashi tace  "Broz Khalil, iya biyayya da haƙuri kasan nayi, nayiwa Daddy biyayya yadda yakamata, nayi ƙoƙarin kasancewa a cikin 'ya' ya nagari masu haƙuri, tun taso wata fa kullum cikin tsangwama da kyarar mahaifiyata yake, amma ban taɓa kulashi akan hakan ba, Brother babu ɗan daze dinga ganin mutuncin duk mutumin daze dinga cin zarafin mahaifiyarsa, komai kusanci da soyayyar dake tsakaninsu kuwa, amma na share na ɗauke kai, nake masa biyayya, ni da mahaifiyata mun masa biyayya, amma baya gani Khalil, baya gani kullum cikin zagi da cin zarafin mu yake, har gara ni yana ɗagamin ƙafa, akan mahaifiyata lokaci yayi da zan nuna masa nima 'yar halak ce, zan nuna masa ni ma' yace, wallahi bazan sake masa biyayya ba nagaji Khalil "

Khalil yace " Calm down, calm down my dear, i feel your pain Baby, kiyi haƙuri dan Allah, nasan me kike ji a zuciyarki, amma dan Allah karki bijirewa mahaifinki, hakan ba halinki bane ba"

"Yanzu na koya, kuma shine ya koyamin, kuma zega canji tabbas, na masa biyayya har akan abunda be dace ba, haka kake so in cigaba da binsa yana jan rayuwata data mahaifiyata a ƙasa?"

Barrister Khalil yace  "kamar yaya ya saki abunda be dace ba?"

Cikin kuka tace  "Khalil, Daddy da farko ni yasa in hilaci Widad, aka sumar da ita za'a sace ta, Yusuf ya ceceta, wani abunma baze faɗu ba ni kawai ka ƙyaleni, idan kuma ya dage sena bar ƙasar nan wallahi sena kawo masa ɗan shege ya raina a cikin gidansa na rantse da Allah "

" Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Nurat kin san me kike faɗa kuwa? Ko kin fara shaye2 ne ban sani ba"

Ta ƙara sautin kukan ta tace "idan ma ban fara ba ina daf da farawa, dan wallahi ya takuramin zan bar masa gidansa in shiga duniya, ko in tafi England inyi irin rayuwar da yake ganin gara inyi irinta da ya kasa cinma nasa burin"

Khalil ya kwantar da muryarsa yace "kina jina Nurat, am sorry kinji, nasan a irin matsala da damuwar da kike ciki, amma kin san zukata nawa ne zasu shiga garari idan kika lalace? Mummynki da kike wannan damuwar saboda ita, ya kike gank idan taga tilon 'yarta ta faɗa mummunar rayuwa? Ya kike tunanin shi masoyin naki ze kalle ki idan kika koma mutuniyar banza? Family duk zasu shiga damuwa idan suka ji labarin yarinyar da suke so, suke ji da ita ta shiga wata rayuwa daban, dan Allah kiyi haƙuri ki bar wannan maganar "

" Brother idan na bar wannan maganar wacce zanyi? Am tired wallahi na gaji dayi masa biyayya, Khalil abun ba sauƙi fa, dama mutumin kirki ne da sauƙi"

"Nasani Nurat, ki kwantar da hankalinki kinji, Insha Allah zan shigo gidan naku, zanzo muyi magana amma ki dena kukan nan please, kuma karki sake faɗin wannan maganar kinji Light" gabata ne ya faɗi jin yace mata Light, sunan da Yusuf ke gayamata, ajiyar zuciya tayi tayi jifa da wayar, tana ci gaba da rushewa da kuka.

A hankali hannun Amal yana warkewa, an kwance mata bandejin kanta ma, se hannun da haryanzu akayi hangin ɗinsa a wuyanta, yanzzhma ta fito daga wanka tana tsaye a gaban madubi, daga ita se towel kanta a tsefe, ta baje gashin kanta, ba laifi gashinta yana da tsawo, ga hannuta sagale a wuyanta, ga goshinta inda yayi tabon ciwon da Alhaji Haruna yaji mata, ta dinga ƙarewa kanta kallo a mudubi.

A hankali tace "dubeni, mace har mace, bani da makusa sedai an gurguntamin rayuwa, an rabani da mutuncina saboda zalunci, kuma ya biyoni da wasu tarkacen banza saboda ya rainamin hankali, bayan tabo na sarari da yayi min, ya barmin na zuciya me matuƙar ɗaci da baze goge ba, me zanyiwa mutumin nan in huxe, wace irin illa zan masa daze dasa masa baƙin ciki a rayuwar sa ne? Me zanyi ne Amal kiyi tunani ƙwaƙwalwarki bata ja Sam "

Ta dafe kanta ta fashe da kuka, tana tuna yadda ya suka dinga kokawa, da muguntar da yayi mata yacinma burinsa, zubewa tayi a gurin tana wani irin kuka, me tsuma zuciya
" Duk laifinki ne Mummy, laifin kine, nace ba zani ba kika ce se naje, Mummy why? "
Jikinta har rawa yake saboda kuka, dukda daga wanka ta fito amma ta haɗa gumi, ga hawaye ga majina se shesheƙa take.

Ramlah ta shigo ɗakin, ta tarar da ita a zaune a ƙasa, idonta yai ja tana kuka.

Ramlah ta ƙaraso da sauri tace " ke Amal lafiya kuwa? Meye haka? Meye ya same ki"

"Bakomai"

"bakomai kamar yaya? Kalle ki fa"

Tsaki Amal Tayi tace  "excuse me please, dan Allah ki bani guri, ina son kaɗaicine"

"wane irin kaɗaici kuma? Anya kina hayyacinki kuwa?"

"Na miki kama da Widad ne, balle kice na haukace? Kawai ki fita ki bani guri"

"Amma Amal"

"Dan Allah ki fita ki ƙyaleni, kad in haɗiyi zuciya in mutu, dan Allah ki fita!"

Tai maganar cikin kuka, Ramlah na fita taje ta dstse ƙofarta ta kwanta akan gadonta ta cigaba da rera kukanta, tana jin Ramlah ta kira Mummy, suka dinga buga ƙofar amma tayi musu banza kamar ba taji ba.

Bukar ya kira Alhaji Haruna, Ya ɗaga wayar suka gaisa, Bukar yace "kunyi waya da Musa ne?"

Alhaji Haruna yace "A'a gaskiya, na kwana biyu bamuyi waya ba"

Alhaji Bukar yace "ok, na zaci kunyi wayane, haryanzu be ce mana komai ba akan batun wanda ze saka mana hannun, kuma yace mu saurareshi zuwa Laraba, anjima zamuyi meeting kota zoom ne, sannan ya batun takaddar da aka ce wannan yaron ya bari? Ka karɓo mana ɗinne kokuwa?"

Alhaji Haruna yace  "eh na karɓo, naje har gidan da kaina naje na karɓo takaddar"

Alhaji Bukar yace  "good, kasan duk wata sheda da zesa a ganemu, dole mu ɓatar da ita kar wani ya samu, dan haka ka kawomin takaddar nan"

Yace "shikenan, Insha Allah zan kawo maka ita, sannan zan sanar dasu batun meeting ɗin nan da kace"

Alhaji Bukar yace  "to shikenan, se kazo"

Alhaji Bukar ya ajiye wayar, ya miƙe ya bar ɗakin dayake, dan ya manta da ya karɓi tajaddar yazo da ita nan gidan ko kuma a can ya barta gurin da ta bashi?.

Hindu tana tsakar gida, suna ta aiki a tsakar gida, Hanne tana gefe tana gyaran wake zasuyi alala.

Hari tace  "sannu da aiki Hanne, Allah ya kaimu bikinki mu kira masu kiɗan ƙwarya muyi ta juyi a gidan nan"
Hanne ta taɓe baki, dan ita sama gaba ɗaya haushin Auren nan ma take ji, dan Yanzu haushin mijin da zata aura takeji, dan gani take bashi da komai idan ta kalli Yusuf, ita dai tana son Yusuf sosai, tana jin ina ma ya aure ta, da tafi kowacce mace dace a ƙauyen nan, da yana ɗan kulata amma yanzu ya dena, saboda wannan koɗaɗɗiyar matar tasa me kama da Yahudawa.

Hindu tace  "Allah dai ya kaimu bikin nan ds rai da lafiya, ban san wane irin shagali zanyi ba, nima sena gyagije nayi shagali, idan kika tattara kika tafi in gaje gurin kwanciyar ki da nawa, Abinci ma zan haɗe nawa da naki ne, dama yanzu ba ƙoshi nake ba" Hindu Tayi maganar cikin sigar wasa da zolaya.

Amma Hanne ta karkace ta kyaɓe baki, ta kalli Hindu tace  "aifa dama ina zaki ƙoshi tunda mayya na gidan? Ai gara in tattara in bar miki gidan ki cigaba da haɗa kafaɗunki dana iyayen mu, tunda dai ke kinfi kowa baƙin jini, babu wanda yake sonki balle kisa ran zakiyi aure ki bar gidan nan, ai se kiyi ta zaman gidan ki ƙare ki tsufa a gida, mujiyar garin nan, shikenan mutum ba zuciya balle ya samo wanda ze rufa masa Asiri ".

Ai tuni idon Hindu ya ciko da hawaye, ita har ga Allah wasa tayi wa Hanne, amma harta fara yan kamata baƙaƙen maganganu da cin zarafi, Hanne na ɗagowa suka yi ido huɗu da Yusuf, da alama duk yaji abunda ta faɗa, sekuma ta shiga kame kame, dan wata irin kunyace ta kamata, bece komai ba ya sa kai ya fice, dan be fiye son shiga sabgar iyalan gidan ba.

Yana fita Widad ta fito tsakar gidan nan, taga yadda Hindu ta nutsu tayi shiru, ido duk ya tara hawaye saboda zafin maganganun Hanne.

Widad tace "ke Hindu, wai ita wannan banzar 'yar uwar taƙi haifarki tayi? Haifarki Tayi da zata dinga gaya miki magana kina jinta? Wai wane ɗan matsiyatan zata aura a garin nan da har take miki wannan gorin haka? Wanda zata aura ɗin ma ya kai a kira shi namiji da take miki gori a kansa "?

Hanne tana hura hanci, cike da ƙauyanci da jahilci tace " Wallahi, tallahi nafi ƙarfin auren matsiyaci, niba matsiyaci zan aura ba"

"wallahi kika bari nazo inda kike, na shaƙeki se na jefa ki a rijiyar nan, saboda me zaki takurawa yarinya dan bata magana, dan kinga tana da haƙuri, wallahi ki kiyayeni akan ɓata mata rai"

Hanne tace "idan anƙi fa?"

Wata irin zuciya ce ta kwashi Widad, sedai Hindu tai saurin riƙeta tace  "A'a Amarya yi haƙuri ƙyaleta kawai"

Widad ta harzuƙa matuƙar gaske, ji take tamkar ta jefa Hanne a rijiya, mussman idan ta tuna yadda take juya manyan attajirai masu ji da kansu, amma wata kucakar 'yar ƙauye na gayamata magana, ƙwafa kawai tayi tace  "ba alfahari ba amma Wallahi da kin san wacece Widad, da baki isa ki yadda in haɗa ido dake ba, dan wallahi ko masu gyaran gadon baccina sun fiki kyan gani, ki zuba ido zakiga mijin da Hindu zata aura, Jahila kawai"

Ta wuce ɗakinta tana huci, duk wannan budurin Gwaggo da Hari basa nan akayi shi, amma abun yana damun Widad taji an taɓa Hindu, setaji kamar ita aka taɓa, danma ita Hindun ce shashasha take tsayawa ana mata wulaƙanci.

Amal kam wani tunani tayi a ranta, dan haka ta miƙe da ɗan sauri, ta fita falo, Mummy ta kalleta tace "kinga damar buɗewa yanzu?"

Amal tace  "Mummy Ramlah ta kasa fahimta tane, wani lokacin idan ina cikin jin zafin ciwo, bana son kowa a inda nake, nafison kaɗaici amma se a takuramin, kun kasa ganewa"

Mummy tace "madalla, shine nake ta magana kika ƙi buɗewa"

"Am sorry, bazan sake ba insha Allah"

"Hmm ai shikenan, ya hannun naki yanzu?"

Tace "da sauƙi, Mummy dan Allah aramin wayarki zan transfer ɗin kuɗi, ni banki sun hanani wai ba network"

Ba musu ta miƙawa Amal wayar, Amal ta karɓa ta koma gefe, ta tura lambar Alhaji Haruna wayarta, ta bata wayar tace "Mummy, ga wayar nagode"
Ta koam ɗakinta, tana zuwa ta kulle ƙofa ta zauna akam gadonta ta kira Alhaji Haruna.

Lokacin yana tsaka da bulayin neman takadda, ya ɗaga suka gaisa dashi, sannan tace  "Naga saƙonka, amma meyasa kwana biyu ba kazo ka dubani ba"

Se ynzu ya ɗau muryar ta, yai murmushi yace  "nima naji saƙonki, ance bayan mota zakizo karɓar gids ma"

Tace "eh hakane, ko idan na dawo bazan samu ba"
. Yace "idan kika dawo ina?"

"zuciya ta, ta fara rayamin kawai idan na warke zan bazama in nemi arziki, in more ƙuruciya ta, idan ka shirya nima a shirye naake zan dawo gareka, tunda aikim gama ya gama tunda fari"

Yai wata shegiyar dariya sannan yace "ni zaki yaudara, ko har kin manta abunda kika gayamin a Asibiti, kaina yana ja sosai dan haka abune mawuyaci kiyi galaba a kaina, tabbas naji daɗin kasancewa dake sedai bazan sake amincewa dake ba, tunda kikayi wannan fueucin, ki sake shawara kinji 'yan mata, idan da gaske kike ki bazama ki kama wasu alhazan, nikam na gama muma na biya tunda na bada motar miliyoyi"

Bata sanma yadda akayi ta ajiye wayar ba, tana jera ajiyar zuciya kamar wadda tai gudu, duk yadda take tunanin abun ya wuce tunaninta, ashema matan suna suka tara, ba kowaccece ke iya kaidin ba, shi kansa shirya makircin ba abune me sauƙi ba, tai sharkaf da gumi tana sake tunanin wata hanyar.

Yusuf na dawowa Widad ta manta da damuwar da take ciki, sedai duk da hakan seda ya gane, yace "Maman Baby, ya akayi ne naga kamar ranki a ɗan ɓace yake"

Tace "A'a ni ba abunda akayi min, Ina ɗan tunani akan Hindu ne, ina ma Megari ze bani ita idan mun koma gida"

Yusuf yace "gaskiya abune me wahala, ya ɗau 'ya ya bamu alhalin bamu da wata dangantaka a tsakaninmu"

Ta jinjina kai tace "hakane, Gaskiya nifa na damu Saleh yazo ayi wacce za' ayi, na fara gajiya hankalina yayi gida sosai fa"

Yusuf yace "ki kwantar da hankalinki, nima shi nake jira yazo, muji abunda yakamata ayi"

Tace "shikenan, Allah ya kawo shi"

Yace  "Ameen"

A gurin 'yan sandan ma babu sassauci, baƙar wahala Saleh yake sha, dan yana kyautata zaton an masa illa saboda duka, dan a nan ɗinma' yan sanda ke sa kulki, suyi ta dukansa izaya daban daban wai lallai seya faɗi inda su Yusuf suke, ga rashin Abinci gashi ko Najasa ne sedai yayi a nan, nan da nan Saleh ya fita daga hayyacinsa, ya canza kamanni fuska duk ta kumbura, ko ina rauni me yake zubda jini, sun doddoke masa ƙafafuwa da ƙyar yake iya miƙewa.

Da Safe Yusuf yana kwance akan cinyar Widad, ta samu comb se jagwalgwala masa sumar kansa take yi, shi kuma yana lumshe ido, can yace  "gaskiya ki ƙyalemin gashina mana, haba se izaya kikemin a kaina"

Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login