Showing 93001 words to 96000 words out of 209297 words

Chapter 32 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

749

lafiyar ta jarabtace Allah ya jarrabesu dan ya gwada imaninsu.

Nan ma dangi suka kuma kwaroroto, suna yamaɗiɗi dashi, waiya fifita matarsa akan danginsa, abun takaicin hadda maza ake wannan sakarcin, ba abunda yake ƙona masa rai irin hadda ƙannensa da suke uwa ɗaya uba ɗaya suke ƙin abunda yake so, ya tabattar a zuciyar tausayi da imani na mahaifiyarsu, da tana da rai duk bazata bari ayi masa haka ba, shikam Bashir ya musu banza dasu da surutun da suke yi, yayi kamar besan sunayi ba.

Daga baya ma ya koma, indai zeyi tafiya ta 'yan kwanaki wani garin harkar aiki, da ita yake tafiya suje su dawo, dan karma wani daga danginsa su bita gida su ɗaga mata hankali Wataran tafiya ta kama shi, yace ta shirya su tafi Tare, haka kuwa akayi suka tafi tare, seda sukayi wata guda sannan suka shirya dawowa Kano, sedai dare yafa yi musu a hanya, Bashir yace  'Jidda, dole idan muka shiga gari mu samu Hotel mu kwana, kin san ƙasar nan ba security "

Jidda tace " dama abunda nake son in gaya maka kenan, dan a tsorace nake "

" to sarkin tsoro, karki damu muna samun guri zamu tsagaita da tafiyar "

Da yake daga kudu suke, wani dajin idan sukabi, sesu shafe tafiyar awa guda basu ga ko giftawar me keke ba, balle abun hawa.

Daga nesa suka dinga hango hayaƙi, gaba ɗaya Jidda ta tsurw tace "Anya bazamu juya ba? Nifa tsoro nakeji hayaƙin meye wancan?" '

"idan mun juya mu koma ina? Aiba inda zamu se naga meke faruwa a gurin"

Jidda ta cigaba da salati, dan tunda yasa kansa seya ƙarasa, saboda Bashir Jarumi ne sosai, bashi da tsoro.

Suna suka ga wata motace tayi hatsari a gurin, sun daki bishiya motar ta kama da wuta, ma'aurata ne a ciki sun kasa buɗe murfin motar su fita, se matar ta daki glass ɗin motar da yayi saura be ƙarasa rugurgujewa ba, ya fashe, tana ta ihu Wuta na cin jikinta tana Yusuf ɗana, ɗana Yusuf ta jefo jariri daga Widow, hannun ta duk ya ƙone se salati take, da alama shi mijin nata dama tuni ya mutu.

Ta wurgo jaririm ta wannan tagar, sedai jikinsa lafiya ƙalau beji ciwo ba, amma gefen wuyansa ya yanke, saboda glass ɗin motar daya fashe, yaron yasha hayaƙin gobara, baya numfashi sosai ga jini na zuba a wuyansa, Jidda tai Wuf ta ɗauki kyakkyawan jaririn a towel, se ƙamshim turare da ƙaurin hayaƙi yake yi, suna ji suna gani haka Wuta ta ƙone motar da iyayen wannan jariri yake.

Jidda tai kuka tai kuka, tunda take bata taɓa ganin bala'i da tashin hankali irin wannan ba, Bashir ya rarrasheta, suka shiga mota ya dinga tsala gudu, har suka fita gari suka sami Asibiti suka shiga, kasancewarsa ɗan sanda id card kawai ya nuna akayi admiting ɗin jaririn.

Bashir ya ɗakko waya daga aljihunsa, Jidda tace  "wa zaka kira?"

Bashir yace "zanyi wayane, in gayawa abokan aikina incident ɗin ɗaya faru, azo a san yadda za'ayi muyi mus handing ove jaririn mutafi gida"

Girgiza kai ta shigayi tace  "dan Allah Yaya Bashir ina son yarom nan ka barmin shi, karma ka gayawa 'yan sanda mun samu yaro, kabarmin ina so tunda ban taɓa haihuwa ba"

"to yanzu ai danginsu zasuji daɗi idan suka ga yaron ya kuɓuta"

"Yaya Bashir, komai nasu fa ya ƙone, ta ina za' a fara neman dangin nasa, dan Allah ka barmin inajin ƙauna da tausayin Yaron nan a raina, dan Allah ka bsr maganar nan, zan raini yaron nan in dai kamin izinin hakan, dan Allah"

Bashir yayi shiru, ganin yadda take kuka, bilhaƙƙi son ɗan nan take dagaske, yasa yace "shikenan is ok, Allah ya tayaki riƙo maman Yusuf, Allah ya raya mana Yusuf bisa tafarki madaidaici, ya bashi haƙuri da juriya irin na me sunan"

Nan ta dinga murna, ta rungume Bashir tana zuba masa godiya da Addu'a, ita da Bashir sukaje yayo siyayyar kayan jarirai kala kala, da duk abunda zasu buƙata, seda suka kwana uku a Asibitin daba'a garinsu ba, dan jaririn ya samu sauƙi.

Bashir kuma yayi waya, akaje aka kwashe gawarwakin nan a inda aka yi hatsarin.

A kwana ukun nan madara take haɗawa ta bashi, Jaririn sam bashi da rigima, harta ɗan fara damuwa ko jikin nasa ne be gama warwarewa ba, daga baya kuma ta fuskanci haka halinsa yake, bashi da rigima sam, bayan an sallamosu suka kamo hanyar gida, amma tun a hanya ta fara tunanin me zata cewa dangin mijinta idan suka ganta da ɗa? Bashir ya lura da yadda tayi shiru, yace  "Maman Yusuf, ya kuma naga damuwa a fuskarki?"

Ta ɗan yi ajiyar zuciya tace  "Yaya Bashir, ina fargabar amsar da zamu bawa mutane, idan suka ganni da jariri, mussman su Yaya Asma'u"

Bashir yace "ba dai kina son ɗanki ba?" ta jinjina masa kai alamar eh.

"to karka damu da abunda mutane zasu faɗa, kisa a ranki ba rainon kariri kawai zakiyi ba, harda na ƙalubale ki manta da wani ƙalubake da abunda mutane zasu faɗa, mu rungumi jaririnmu, Allah ne ya bamu"

Ta kallesh tace  "dagasake kaima kana son jaririn nan?"

Yace "meze hana, muda muke nema Allah ya bamu, ai ina son duk abunda kike so, ina son Yusuf nima bari kiga mu koma gida, hakika zan kuma yanka masa, muyi shagalin suna dan Jaririn naki befi watanni biyu ba, gashi me kyau masha Allah kamar ke"

Jidda tayi murmushi tace  'mijina ɗan Aljanna, Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira "

" Ameen tare da ke matata"

Se fargabar da take ta ɗan ragu, suka nufi gida.

Bayan la' asar suka isa gida, bayan sun yi salla sun huta, ta dafa ruwa ta yiwa jaririnta wanka, ta canza masa kaya, ta goya abunta tana jin ƙaunarsa a ranta.

Bashir da kansa ya sai cingam, ya dinga aikawa mutane cewar za suyi taron sunan jariri, mutane suka dinga mamaki dan su dai basu san tana da ciki ba.

Nan 'yan uwansa sukazo domin ganin ba' asi, aikuwa suka tarar da ita da Jariri.

Wani Yayansa ya sashi a gaba da tambayoyi, akan sun san matarsa ba haihuwa take ba, ina suka samo ɗa Bashir yaƙi gayamusu, suka haɗashi da wani ƙanin babarsu, ya kira shi ya tambayeshi,
Bashir yace  "gidan marayu sukaje suka ɗakko yaro, jaririn iyayensa ne suka yi hatsari suka mutu, kuma ba'a san daga inda suke ba, shine sukaje gidan suka karɓo shi.

Nan ma 'yan uwa suka samu nayi, wai ya biyewa matarsa sunje gidan marayu sun ɗakko shege, babu wani iyayen yaron sun mutu, duk yaran dake gidan shegune.

Jidda ta dinga kuka tana ɗanta ba shege bane, Bashir yaita rarrashinta, ya gayyaci mutane akayi sunan Yusuf, akayi shagali sosai aka watse.

Jidda ta rungumi jaririmta da mijinta, sedai wani abun mamaki da iko na ubangiji, tunda Allah yasa suka fara rainon ɗan nan, Jidda ta dena wannan rashin lafiyar da take yawan yi, ta warke sarai ta dena kwanciyar Asibiti, idan ba an faɗa maka ba bazaka ce tayi fama da jinya ba a baya, sosai suke rainon Yusuf, bazaka taɓa cewa ba ɗansu bane, idan har kana son farincikin Jidda da Bashir to kaso ɗansu Yusuf.

Sedai fa dangin mijinta suka kuma sata a gaba, suka tsani yaron nan ƙarara suke nuna masa ƙyama, suke ce masa shege, Sedai Jidda tayi kuka, ita dai tasan Yusuf ba shege bane da iyayensa, amma haka take sharesu ta cigaba da kulawa da shi ita da mijinta Bashir.

Jidda ta kauda kai daga duk wani ƙalubale da take fuskanta, akan rainon Yusuf ta kowane ɓangare, Bashir yana iya ƙoƙrinsa akan Yusuf, daya isa shiga makaranta ya sashi a makarantar kuɗi, wanda a wannan lokacin se 'ya' yan wane da wani ake kaiwa private school, amma yasa shi a private school, yasa shi a makarantar islamiyya, ga tahfeez sannan aka ɗaukar masa malamin lesson, idan Bashir na gari shike kai Yusuf makaranta ya ɗakko shi, idan baya nan kuma Jidda ke kaishi, Yusuf ya taso cikin gata da kulawa, yayin da gefe guda dangin babansa suka sake ɗora masa karan tsana shida iyayensa, mussman Jidda waita asirce musu ɗan uwa tasa sun ɗakko shege yana masa bauta, ya taɓe a gindinta dana wannan shegen yaron.

Babban abun mamakin be wuce yadda suma yana wahalta musu dai dai gwargwado yadda ze iya amma basa gani.

Yusuf ya tashi da tarbiyya da ilimin addini dana zamani, gashi da matuƙar haƙuri, da wuya kaga yayi fushi, be fiye shiga faɗace faɗacen yara ba, karatunsa ya fiye masa komai.

A tsakanin maƙwabta ma ana samun hassada da ƙyashi, ganin kaf tsukinsu babu me gatan Yusuf, komai ana masa sam bashi da wata damuwa, hakan yasa maƙwabta suma suka fara jin haushinsa, abun wasa duk tsadarsa zakaga Yusuf dashi, shi kaɗai amma keken hawa uku ne dashi na hawa, shekararsa takwas a duniya, amma har system yake da ita saboda karatun Al'qur'ani da sauran litattafan addini dana zamani, dan haka Ƙwaƙwalwar Yusuf na kawo wuta sosai.

Nanma maƙota suka fara jin haushinsa, saboda wannan gata da tarairaya a cewarsu dama gashi shege kuma ana ƙara sangarta shi, Yusuf tunda ƙuruciyarsa yake jin kalmar shegen nandm daga bakin mutane, besan ma'anar kalmar ba, amma yasan kalmace me muni, da wasu lokutan maƙotan ko yaransu kan gaya masa, ko kuma dangin Abbansa, Yusuf yana da matuƙar haƙuri da kawaici, ko wasa ya fito cikin yara idan yaga za'ayi faɗa ko rigima, seya bar gurin ya koma gida, wasu lokutan har haushin haƙurinsa Bashir ya kanji, yaita masa faɗa ya dena yadda yara suna masa rashin mutunci yana ƙyalesu, se yace ai malaminsu yace  "Allah yace yana son bayinsa masu haƙuri"

Katsam ranar suka yi faɗa da wani yaron maƙwabcinsu, akan kayan wasan Yusuf ɗin, yaron ya dinga zaginsa, uwar ɗan ta fito ta shigarwa Ɗanta, Yusuf ya juya ze koma gida, yaron ya biyo shi ya dake shi, Jidda ta fito jin Hayaniya, Jidda tace  "Maman Salim bekamata ki dinga shiga faɗan yara ba, ɗa na kowane kamata yayi ki haɗasu ki musu nasiha, in da kara ɗana da ɗanki ai duk naki ne, idan zaman tsakani da Allah akeyi, Yusuf da Salim duk namune'

" Ke saurara karki ƙara haɗa ɗan sunna da shege, tsintacciyar mage wadda bata mage, akan me? Kedai da kika ɗakkoshi kikaga zaki iya se kije kiyi, kekaɗai ne ɗanki amma ni wannan yaron ba ɗana bane"

Nan da nan ran Jidda ya ɓaci, kawai ta durƙusa a gurin fashe da kuka, da yake ita bata da baki sosai, Yusuf yazo ya rungumeta yai shiru yana sake juya kalmar shege a ransa.

Salim ya ɗau dutse da nufin ya jefi Yusuf, amma ya samu Jidda a gadon baya, karo na farko da Yusuf ya harziƙa, beyi wata wata ba yai sama da Salim ya sake shi a kwata.

Nan babar Yusuf ta gigice ta biyo Yusuf zata daka, dai dai lokacin motar Bashir ta shigo layin, take yayi parking ya fito yace  "ke lafiya zaki dakarmin ɗa? Ke kuma Umman Yusuf meya sameki haka kike kuka?"

Aikuwa ba tayi nauyin baki ba ta gaya masa komai, nan ya fara sirfa bala'i, yace  "na lura mutanen nan bakwasan zaman lafiya, wallahi duk wanda ya kuma kiran ɗana da shege sena ɗaure mutum, kai kuma Yusuf duk yaran da ya kuma gayamaka haka, ko ya dakeka baka zanemin shi ba, ni zan zaneka da kaina, ba babarka zaka dinga shigarwa faɗa ba, duk wanda yayi maka ka masa duka ka lallasan mon yaro, in yaso akawomin ƙararaka zan bada haƙuri "

Tun daga nan Yara suka ɗan saurarawa Yusuf, saboda babansa mutum ne me raha da barkwanci amma be iya fushi ba da tashin hankali, Yusuf ya cigaba da tasowa, tun be gane kalmar da ake gaya masa ba harya gane ma'anarta, baze manta ranar wata Juma'a ba, wadda itace ranar da ya gane mariƙansa basu suja haife shi ba, ya ɗauka ana gayamasa shegene kawai dan a zageshi, amma ya gane basu suka haife shiba.

Ƙanwar Bashir, me suna Balaraba ta haihu, saboda gudun magana yasa Jidda ta shirya, ta shirya ɗanta tsaf dasu, kai kace wata matar hamshaƙin attajirice, saboda Bashir baya wasa gurin kula da gidansa, daga ci har sha da sutura, baya wasa gurin basu, shiyasa kullum iyalinsa suke tsaf dasu.

Suka shirya tun safe Bashir ya tafi kaisu gidan suna, a ƙofar gidan yayi parking ya kalli Jidda yace  "kin san Allah, ba dan kin matsa ba da bazakuzo sunan nan ba, ke kin damu Yusuf yasan 'yan uwana, saboda halin Rayuwa ni kuma nasan babu wani amfani da hakan zeyi, dan haka idan kimga ba hali ki samu abun hawa kukoma gida, idan kinga zasuyi muku cin mutunci ki kirani a waya ko ku koma gida kinji ko? "

Jidda ta jinjina kai, Bashir yace "ki kularmin da kanki da Yarona, ya kalli Yusuf yace   " My boy, zaka shiga cikin yara, bance ka saurarawa duk wanda ya taɓamin kai ba kaji ko? "

Yusuf yayi murmushi ya sunkuyar da kai, Bashir ya sumbaci goshinsa, sannan suka shiga gidan, suna shiga basu samu wata karɓar arziki ba, sema bimta da aka dingayi da kallo a nayiwa zanin jikinta kuɗi, da kayan jikin Yusuf.

Suka dinga zage zagen su, suna faɗar baƙaƙen maganganu, Jidda ta tashi da nufin ta taya su aiki, suka dinga caccakarta kamar zasu cinye ta ɗanya, suna mata gori suna zaginta.


Ta tashi ta koma gefe, ta ɗau Yusuf ta ɗora akan cinyarta, tana share hawaye, Yusuf ya kwanta a jikinta yayi lamo yana jin yadda take kuka, har kusan ƙarfe ɗaya ana ta rabon Abinci, amma aka hanata ita da Yusuf, ga lokacin da shabiyu na rana tayi, take bawa Yusuf abinci, se can wata mata daga maƙotan Balaraba ce ta kawo musu Abinci, dambun shinkafa aka kawo musu, sedai Yusuf baya cin dambu, se Jidda ta aiki wani yaro tace

"Dan Allah jeka gurin da ake rabon Abinci, kace a baka waina zan bawa yarone, in basu baka ba kazo ka karɓi kuɗi ka siyomin wani abun in bashi"


Yaron yana zuwa yace a bashi waina, wata ta kalle shi tace "waye yace a baka"?

Ya nuno Umman Yusuf yace "gata can, ita ce tace a bata zata bawa yaronta, wai baya cin dambu"

Asma'u tace "iyeee ina abun yake inji Mayya, saboda samun guri har wani zaɓen Abinci yaron yake yi, lallai abunda mamaki samun guri, dama ɗan uwanmu ne ya haife shi da sauƙi, amma kin sashi a gaba anje gidan marayu an ɗakko shege se wahala yake akanku, ke gaki juya shi gashi shege ba dangin iya babu na baba an samu guri se iskanci ake, kina ci kina ƙiba kina narka kashi, gefe shegen daba'a san asalinsa ba ma yana cin nasa rabon, kin kanainaye mana ɗan uwa kin hanashi yayi mana komai "


Balaraba tace " wai lafiya kike wannan kwarmaton haka? "


" inafa lafiya, za'amin iyayi da feleƙe wai wannan shegen yaron sun samun an basu Abinci, hadda turowa wai a canza masa bayacin dambu, saboda samun guri wai Abincin ma seya zaɓa, dan ubanka da a gidan Marayun ka taso, naga uban da zakawa sanaben baka cin kaza, kai kaza kake ci"


Jidda ta toshe baki ta fashe da kuka, a nan Yusuf ya fara fuskantar ashe ba Babansa ne ya haifeshi ba, idan be manta ba a makarantar su sun taɓa zuwa gidan marayu, akace musu wanda iyayensu suka yadda sune, kokuma wanda iyayen suka rasu, wato kenan shima yadda shi akayi, ko iyayensa na asali sun mutu.


Jidda ta tashi, ta kama hannun Yusuf ta baro gidan nan, kafin ta fito ma shaddarta milk ta sha aiki, suka watsa mata dagwalon kayan miya, haka suka tafi tana tafe a hanya tana kuka,

Yusuf yace "Umman Yusuf kiyi haƙuri, kidena kuka Allah yana son masu haƙuri, haka ya sayyadina yake gayamin"

Amma ta kasa dena kukan nan, ta rasa wani abu tayiwa dangin Bashir suka tsaneta haka, banda hauka ina laifin Yusuf a wannan al'amarin? Me yayi musu? Shida yake yaro ƙarami, take tayi wani tunani ita yanzu daba cikakkiyar lafiya ba, idan ta mutu waye ze kular mata dashi, ita dai Allah ya jarrabeta da son Yaron nan, tasan babu matar da zata kulamata da ɗanta tsakani da Allah haka.


Gaba ɗaya wunin ranar haka suka yi shi babu daɗi.

Bashir na dawowa ta dake ta maze, ta ɓoye duk wata damuwa da take ciki, ta saki fuskarta, suka ci Abinci ya rungume Yusuf yana faɗin

"ɗan Babansa, meyafaru ne? You look somehow disturbed, meyafaru ne gayamin"

Yusuf yace "am ko Abba, ba abunda yake damuna, munje gurin suna amma ba'ani Babyn na ɗauka ba"
Bashir yace "Subhanallah, to shikenan rabu dasu, da kaina zan kaika a baka ka ɗauka tunda kana so"

Yusuf yace "to Abba nagode, nima Allah yasa Ummana ta haifi Baby, in dinga kular mata da ita ina goya ta"

Bashir yace "Ameen ya Allah yarona, waini idan ka girma me kake son ka zama ne?"

"Daddy doctor nake son zama, surgeon doctor"

"Wow that's good my Boy, Allah ya bani rai da lafiya inga burinka ya cika Yusufana, kenan baza'abi sahun Abba ba a kare dukiya da rayukan al'umma ba?"


"Ina so Daddy, amma bana son in dinga cin hanci, ustaz ya cemin ba kyau"

Bashir yayi murmushi yace "babu aikin daba'a cin hanci Mu Son, nima na gashi police bane, kaga ina irin wannan?"


Yusuf yace "A'a".

"To ko duk 'yan sanda zasu lalace, amma kai ka tsaya kai da fata akan gaskiya idan wasu basu yi nasara ba, wasu zasu samu sassauci a sanadin ka, dan haka' yan sanda ba 'yan rashawa bane kaji Masoyina"


Jidda tace "Abba, ko kunya ba kaji kake cewa ɗan fari masoyinka ko? Allah yasa tsofaffi su jika, kasha zazzaga"

Bashir yace "sedai suyi su gaji, amma ina son masoyin nan nawa, inajinsa a zuciyata, idan na kalle shi ina samun farinciki da nutsuwa, nasan ko bayan raina akwai amfanin da zewa al'umma, ɗan waliyin Allah me halin sufaye"

Jidda tace "ina ganin ikon Allah, kabari a faɗa mana kawai kasa shi a gaba kana ta koɗashi, Taso muje in maka addu'a in kwantar da kai"

Bashir yace "ke yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login