Showing 183001 words to 186000 words out of 209297 words
meyafaru ba.
Isa yace " ranki ya daɗe, Amma kin san an kama Hajiya ko? "
Tace" Eh na sani "
Yace" to dama ya bar gida ai tuntuni, takaddar daya bari ai ita Murtalah ya tsinta, ranar da aka yi zaman ƙarshe a kotu, muna nan 'yan sanda suka zo a motoci suna ta jini ya, na buɗe musu gate sukazo suka shimfiɗe Anwar, an gano shi a wani gida yake rayuwarsa yana kasuwanci a can cikin Jos, aka kawo shi an kasheshi ta hanyar caka masa makami a gefen cikinsa, sedai babu wanda yasan wanda ya kasheshi, amma a ranar kukan da Hajiya Halima take kamar dasa hannun shi Bulaman dai a kisan"
Ai tuni hawaye ya wanke mata fuska, ta dinga jujjuya kai tana maimaita innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Ya Allah, Yaya Anwar ubangiji Allah ya jiƙanka, naso na sameka a raye in maka godiya riƙemin amana da kai, amma zan dawwama yi maka Addu'ar samun salama a kabarinka, kana daga cikin mutanen da bazan manta dasu ba a rayuwata, Allah ya yafe maka Yaya Anwar"
Kuka yaci ƙarfin Widad, yayin da suma duka jikinsu yayi sanyi sukaji mutuwar tamkar yanzu akayi ta.
Widad cikin kuka tace "Murtalah ka sameni a farm House gobe in Allah ya kaimu da yamma, nagode muku Allah yasaka da alkhairi nagode sosai"
Ta kasa ko rufe ƙofar motar, se kuka da take yi, Isa ya rufe mata ƙofar motar, ɗan sandan nan ya ja suka tafi, suna tafe tana kuka, dan Mutuwar Anwar ta da keta fiye da tunani.
Yusuf ya ɗan warware, Suleiman ya kwashe su a mota domin sujewa Nurat gaisuwa, da yake an kwana biyu da rasuwar mutane duk sun watse se tsilla tsilla.
Kahlil yai musu iso har wani katafaren falo, aka kira Nurat, Nurat ta fito cikin Ƙaton hijjabi, tana ganin Yusuf ta kasa magana se hawaye haɗe da murmushi daya ƙwace mata.
Ta durƙusa har ƙasa ta gaida Umman Yusuf, Yusuf yace "Nurat ya ƙarin haƙuri kuma?"
Nurat tace "Alhamdilillah"
"Allah ya jiƙanta yasa ta huta"
Nurat tace "Ameen"
Nan duk sukayi mata gaisuwa, Umma tace "dama munzo muyi miki gaisuwa ne, kuma zamuyi zuwa na mussman muyi miki godiya '
Yusuf yace " Nurat, ban san me zance miki ba, wanda ze nuna irin tarin godiyar dake bakina ba, a sanadiyata ga abubuwa marasa daɗi sun faru dake, Nurat dan Allah kiyi haƙuri, ban san mema zance ba"
Khalil yace "karka damu Yusuf, dama haka Allah ya ƙaddara seya faru, ba kaine sila ba, Allah ya riga ya rubuta hakan dama, sedai kam tabbas tayi faɗi tashi a kanka sosai, tun daga ɓatanku har wannan lokacin"
Umma tace "mungode, mungode Allah ya saka miki da alkhairi, Allah yayi miki Albarka ya jiƙan mahaifiyarki"
Nurat ta dinga jinjina kai, tana tuno Mummynta, ta kalli Yusuf tace "Kasan kuwa an kashe Yaya Anwar?"
A razane Yusuf ya kalleta yace "wane Anwar ɗin wai?"
Ta goge Hawaye tace "Bayan ɓatanku, Daddyn Widad faɗuwa yayi, ya fara rashin lafiya babu kowa a gurinsa babu me zuwa gurinsa , Anwar ne kawai yake gurinsa, ya dinga jinyarsa tsawon lokaci, bayan wani lokaci aka sace Daddyn Widad a Asibiti, aka kama Anwar ya daɗe a tsare ya sha wahala sosai kafin ya kuɓuta, to kwanan nan dai Brother ya cemin ai Ya bar letter a gida, ya bar gidan gaba ɗaya ba'asan inda yake ba, ranar da aka gama shari'arka akace an kashe shi kuma ana zargin Bulama ne yasaka "
. Umma ta dafe kai tana faɗin innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yayin da Nurat ta sake fashewa da kuka.
Khalil yace "se haƙuri, da kuma mu taya su da Addu'a, Wannan me aikin gidan ne Murtalah, ya tsinto takaddar, ban san ya'akayi yai kyan kai ya kaiwa Barrister Hafiz ba, dan abun zamana yayi duk wanda yai wani yinƙuri na temakawa a gano gaskiyar lamarin, se an bishi da mummunar barazana, mutumin nan maƙurane gurin zalunci"
Umma tai shiru tana hawaye, tana jinjinawa zaluncin Bukar, musamman Da taji wai ashe Anwar ɗane a gurinsa.
Nurat ta kira Yayar mahaifiyarta suka gaisa da Umma, sun daɗe suna hira suna jajantawa juna, yayin da Suleiman da Khalil ke hira.
Nurat tai shiru a gefe, tana kuka Yusuf yai ƙasa da muryarsa cike da tausayinta yace "Light am very sorry, kiyi haƙuri da ƙaddarar data same ki a sanadina dan Allah"
'Nifa ba kaine silar faruwar haka a gareni ba, dama Allah ya ƙaddaramin haka zata faru dani ne "
" Bazaki dinga kallona da abunda ya faru ba, koki zargi saboda ni haka ta sameki ba? "
Ta jinjina masa kai alamar eh, Yusuf yace " Nagode sosai, Allah ya jiƙan Mummy ".
Nurat tace " Ameen, naji ance an kaika Asibiti ya jiki kuma? "
Yusuf yace " jiki Alhamdilillah, mungode Allah "
" Allah ya kiyaye gaba, se nazo maka jaje "
Yusuf yace "A'a ni yakamata in sake dawowa in dubaki in sake miki ta'aziyya, Allah ya baki haƙurin jure rashin Mahaifiyarki"
Ta jinjina masa kai tana kuka, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi sosai, ya cigaba da rarrashinta, Umma ta fito ta tarar dasu tace "mu tafi ne ka taho kokuwa?"
Yusuf yace "A'a tare zamu tafi"
Ya miƙe Nurat ta rakosu har bakin mota, Yusuf yana ta sake bata haƙuri yana mata gaisuwa.
Suna tafe a motar, Yusuf yayi shiru yana tausayin Nurat, ga mutuwar Anwar data gigita shi, ga yana son ganin Widad.
Can yaji Umma tace "gaskiya Yarinyar nan tana da nutsuwa da tarbiyya, na yaba da hankalinta gashi ta bani tausayi Yusuf, nikam ko zaka nemi Aurenta idan zasu baka?"
AMANA! AMANA! AMANACE!!! IDAN KIN FITAR ALLAH NA KALLONKI
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
154_155
Gaban Yusuf yai mummunar faɗuwa jin abunda Umma tace, ya kalli Ummansa ta Mirror, amma yai shiru yaƙi cewa komai sema ɗauke kansa da yayi yana kallon waje.
Umma tace "ya Kay shiru ba kace komai ba?"
Ƙin magana yayi, dan bayama son zancen, Umma tace "Suleiman, dan Allah baka yaba da hankalin Nurat ba? Yarinyar tana da nutsuwa da kuma kirki sosai"
Suleiman yace "tabbas hakane Umma, ni kaina na yaba da nutsuwar ta, kuma da alama dai Yusuf akwai dalilin da yasa ta dage ta temake ka"
Umma tace "jimin yaro da wulaƙanci, ana masa magana yayi shiru, kamar ba dashi ake ba"
Yusuf yace "Umma me zance ne? Nifa ina da Aure ya zanyi da Widad kuma?"
"Karka ƙaramin zancen wannan yarinyar, wadda bata san halcci ba bata san abun alkhairi ba, kai ko zuciya baka da ita, duk wannan abunda ya sameka sanadinka baze zame maka darasi ba Yusuf, irin wahalar da ka sha, ba kai kaɗai ba harni kaina da sauran mutane, amma kake ƙara nanata wai kana da Aure, toni ban san da wannan Auren ba, ba wani Aure da kake da shi, ni dai ga yarinyar da ta kwantamin"
Yusuf yace "Umma, Widad bazata bada sheda haka kurum ba, akwai wani dal.....
" Rufemin baki, bana son jin zancen yarinyar nan gaba ɗaya, na gaya maka "
Yusuf yai shiru, ya maida idonsa wajen window, yana tunanin yaze da Umma akan Widad, gashi yana son ya haɗu da ita yana son su gana, amma Umma tana nema ta ɓata komai, kuma yaga alamar idan ya matsa, ze ɓata mata rai, shi kuma babban abunda baya so kenan, ɓacin ranta.
Haka Umma da Suleiman suka cigaba da hira har sukaje gida, ba tare da Yusuf ya tofa ta bakinsa ba, yai shiru dan bema san me suke cewa ba.
Suna zuwa gida Yusuf yaiwa Suleiman sallama ya shige gida abunsa, Umma kuma seda tayi sallama da Suleiman sannan ta shiga gida.
Widad kam sosai take jin mutuwar Anwar, ji take kamar mutuwar Anwar wani babban giɓine a gareta, dukda ba ɗan uwanta ne na jini ba, amma Anwar zuciyarsa ba irin ta mahaifiyarsa bace ba.
Tai kuka, tai kuka ƙarshe taje tai alwala ta tada salla mussman dan taiwa wanda ta rasa addu'a, ƙarshe ta ɗaga hannu zata yi Addu'a, ta kasa roƙar komai kawai ta fashe da kuka, "Allah ka yafemin laifukana, Allah na tuba ka yafeni, Ba Ammina, ba Daddyna, Ba Yaya Anwar, wanda nake sa ran zeji ƙaina maƙiya sun sa na masa abunda bazan sake kima a idonsa ba, ban san dangin mahaifina ba ban san na mahaifiyata ba, bani da wanda zan kalla a rayuwata inji sanyi, babu me raɓata babu wanda zan raɓa, Allah ka kawomin ɗauki "
Ta ƙarasa maganar tana rirriƙe gado da gefenta tana wani irin kuka me raunata zuciya, idanunta sukayi jawur ta fita hayyacin ta, ta rasa abunda yake mata daɗi, gashi har yanzu da tsoron mutane a ranta, tana jin tsoron raɓar wani, bata san meza'a kuma yi mata na cutarwa ba, ta fara tunanin ko ƙauye zata koma gurin Gwaggo?
Wata zuciya tace "suwaye a gareki? Suba danginki ba, wane karɓa zasuyi miki bayan suna zaune an tayar musu da hankali, hadda 'yan sanda ta yaya zasu sake karɓarki? Idanma zasu karɓekin kin san hanyar da za' abi aje a garin? '
Lumshe idinta tayi, hawaye na zuba daga idonta, tana jin yadda take sauke numfashi da ƙyar, alamun zuciyarta bata aiki yadda yakamata.
Ta takure a jikin bango, ta haɗa kai da gwiwarta, tana ci gaba da kuka, sanyin AC dake ratsata taji sanyin da take ji yayi mata yawa, nan da nan jikinta ya ɗau rawa, ta dinga rawar sanyi, kanta na wani irin sarawa amma ta kasa motsawa daga inda takey, ƙarshe ma ta haka ta kwanta a gurin, tana jin cikinta na motsawa, ta tuna Yusuf be san da cikin bama, ta shafa cikin a hankali tana tausayawa abunda ke cikin nata.
Amal ta ɗan farfaɗo, sedai befi tayi magana kaɗan a rana ba, bata magana sam seda ƙyar, gaba ɗaya ta ɗashe ta bushe saboda azabar bleeding da tayi, ga fargaba da tashin hankali da take ciki na kama Mummynsu, ga mutuwar Anwar da damfarar ta kuɗin nan da akayi, gashi har yanzu raɗaɗin fyaɗen da Alhaji Haruna ya mata yakasa barin Ƙwaƙwalwarta, dan haka abun ya mata yawa, ta samu depression, Ramlah ce ke kula da Ita take jinyarta, taga abun nata bana ƙare bane, ta ɗauketa ta kaita Asibiti.
Likita ya dubata, ya rubuta musu teses, ta kaita lap akayimata, suka kaiwa Likitan, ya karɓa ya duba ya kalli Amal yace "ƙanwata, gayamin tsakaninki da Allah ƙanwata meyasameki kike bleeding haka?"
Amal ta kalli Likitan, ta sunkuyar da kai se hawaye, Ramlah tace "doctor, ba lallai tayi maka magana ba, saboda tunda akayi mana rasuwa batavda sukuni, bata magana se kaɗan kaɗan, Fyaɗe akayi mata, harta samu ciki, shine taje ta zubar da cikin jini ya ɓalle mata yaƙi tsayawa"
Likitan yace "waye yayi mata fyaɗen?"
"Wani mutum ne" Ramlaj ta bashi amsa.
Yace "kuma an kai shi gaban hukuma da yayi mata fyaɗen?"
Ramlah tace "doctor, bamu da wannan lokacin yanzu ma baka san da yadda na kawota ba, kawai ai mata abunda ya dace"
"Amma kun san illar dake tattare da ayiwa mace fyaɗe aja baki ayi shiru ba tare da ɗaukaf mataki ba, ba hujja bace a ɓoye irin wannan lamarin dan gudun jin kunyar mutane, ki tsaya ki ƙwaci haƙƙinki shine yakamata, yanzu yaushe abun ya faru? Kuma da ya faru an kaita Asibiti an mata gwaje gwaje ne? "
Ramlah tace " dan Allah ke dena wannan tambayoyin, kawai ka rubuta mata magani a wuce gurin "
Ya ɗan taɓe baki yace " Any way, tunda haka kuka zaɓa zan miki bayanin sakamakon gwaje gwajen da mukayi, wannan abortion ɗin da tayi, an mata amfani da pills me ƙarfi wanda yafi ƙarfinta sosai, musamman duba da yanayin rukunin jininta, hakan ya samar da gagarumin rauni a mahaifarta, wanda yasa take ta zubar da jini, mahaifarta tayi raunin xa abune mawuyaci ta sake ɗaukar ciki, sedai idan an kaita India anyi mata aiki, akwai wani ƙwararren gynecologist dayake aikin, sannan a shawarce yana da kyau a dinga kaita tana ganin Likitan Ƙwaƙwalwa, saboda wannan depression ɗin ze iya zame mata hauka tuburan, duba da yadda matakin depression ɗin nata yayi worst "
Ramlah tace " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yanzu nawane kuɗin aikin zeci? "
Ya kashingiɗa a kan kujerarsa yace " idan kun shirya kumin magana, baya cin fiye da naira miliyan uku haka, ko yanzu idan a shirye kuke, za'a iya booking na jirgi ku tafi"
Ramlah ta dafe kai, dan babu inda zata samo wannan kuɗaɗen, komai ya ƙare musu, basu da komai yanzu a kangon gidan kawai suke, gashi taji labarin Widad na Farm House dan haka a tsorace take, kar Widad tazo ta fatattake su koma tace a kamasu.
Ramlah tace "thank you very much doctor, when we are ready, we will let you know"
Likitan yace "shikenan, ba damuwa Allah ya bata lafiya"
Ramlah ta kama hannun Widad, suka fito suka hau motar da ta rage musu zuwa gida, haka suka koma Ramlah ta saka Amal a gaba tana kallonta, yanzu ita kaɗai ta rage mata, ba Mummy, ba Anwar, ita kanta bata da tabbacin zata tsira, har gara Amal ita ba lallai a sameta da wani laifi ba, gashi itama Amal ɗin ta zama shiri shiri, Ramlah ta rasa abunyi, taje ta ɗakko kayan shaye2 ta ɗurawa cikinta, seda taji tayi dam sannan ta baje tana bacci a gurin.
Kamar yadda Widad tace wa Murtalah tana son ganinsa, haka akayi yaje gidan gona dan ya sameta, amma 'yan sandan da suke gadinta suka hanashi shiga, seda sukaje suka sameta suka gayamata zuwansa, sannan tace a barshi ya shigo tasan da zuwansa.
Har falon ya shiga ya zauna, ta fito cikin dogon hijjabinta, Murtalah a ransa yace "iko se Allah, wai yanzu Widad uwar tsiwa, gadara ganioda izza itace a haka? Itace yanzu take komai sanyi sanyi, harda shigar zumbulelen hijjabi haka, lallai tayi darasi na rayuwa a makarantar duny, me cike da ƙalubale da tarin matsaloli, ya ga yadda ta sake ramewa, se kumburi a fuskarta, duk ƙibar nan babu da da aukinta, amma yanzu kamar sillen kara haka ta koma.
Ta ƙaraso ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon, gaba ɗaya a takude take saboda zazzaɓine ma a jikinta, ga jira dake kwasarta dan tun safe tea ne kawai a cikinta se biscuit, bata da appetite na cin komai sam..
Murtalah ya zube a ƙasa yana "barka da yamma ranki ya daɗe"
Tace "yawwa kana lafiya?"
"lafiya ƙalau Alhamdilillah ranki ya daɗe"
Widad tace "masha Allah, na kiraka ne nan dan muyi magana, zan saka wani aiki ne, amma kafin nan bani labari, wane hali gidan mahaifina ke ciki?"
Murtalah yace "eh to, kamar dai yadda kika sani, an kama matar gidan saboda da haɗin bakinta Alhaji Bulama yake gudanar da wasu abubuwan, ita kuma Amal mamar hankalinta ya gushe, tunda aka kawo gawar Anwar, aka kama mahaifiyarsu ta faɗi shikenan, ko magana bata son yi, kamar dai ta samu matsala a Ƙwaƙwalwarta ne, ita kuma babbar dama tun bayan ɓacewarki take bin wannan ɗan gidan Bulaman, to a yadda muke ganin abubuwa na gudana ma dai, shaye2 take yi dan wataran mankas haka take dawo mana gidan nan, yanzu dai su biyune kawai a gidan ba kowa "
Widad ta jinjina kai tace " Allah sarki, Allah me yadda yaso, anyi ƙoƙarin ƙaƙabamin hauka tuburan ga haauka ya fara bibiyar 'ya' yanta, an haɗa kai an kashemin mahaifiyata, se gashi itama an sa an kashe ɗanta, shi kuma wancan ya kashe matarsa da hannunsa, haƙƙinmu baze taɓa barinsu jin daɗin duniya ba"
Widad tai maganar tana share hawaye, Murtalah yace "ayi haƙuri ranki ya daɗe, ai an gode Allah an auna Arziki sosai, Amma dama ita tasa aka kashe mahaifiyarki?"
"karka shiga hurumin da ba naka ba, ka tsaya iya matsayinka, ina son in dinga sanin duk wani motsinsu, da duk wani abu dayake kaiwa yana komowa a gidan ka dinga sanarmin, tashi ka tafi"
Murtalah ya miƙe yana godiya, harze fita tace "ya batun salary ɗinku? Ana biyanku kuwa?"
Yace "ranki ya daɗe, ai se muyi wata biyu kafin a bamu albashin ma, kuma duk anbi an rarrage mana albashin"
"Kuyi lissafin abunda kuke bi na bashi, zan biya ku ruɓinsu biyu insha Allah"
Murtalah ya zube a gurin yana "Allah ya temakeki, Allah ya baki yawan rai yasa kifi ƙarfin maƙiyanki"
Widad tace "Ameen"
Yana fita itama ta fito, ta kira ɗan sandan nan daya kaita gidansu jiya, ya taho jikinsa na tsuma ya gurfana a gabanta, ta kalleshi tace "kasan gidansu Yoseef?"
Yace "A'a ranki ya daɗe"
Tace "ina son saka ka aikine, kaje ka bincikamin inane gidansu, ina son in dinga sanin duk wani moves ɗinsa ne, ina son dinga sanin halin dayake ciki"
Yace "to ranki ya daɗe, zan ƙoƙari in gano gidan nasu, amma kin san bani da damar da zan bari gidan nan, in koma unguwarsu saboda a nan aka ajiyeni inyi aiki"
"karka damu, akwai tukuici me kyau, sannan babu wanda ze zargeka akan hakan, zan baka kariya ince nine na saka aikin"
Yace "shikenan ranki ya daɗe, amma ki sanar da shugaban mu"
"baka da matsala"
Yusuf jikinsa yayi kyau sosai, ya farfaɗo daga wannan uban baƙin da yayi kamar bashi ba, saboda samun sassauci da yayi daga ƙangin zaman gidan kurkuku, sedai Umma na cigaba da damunsa akan lallai yaje ya nemi Auren Nurat, yace "Umma, kina cewa inje in nemi Auren Nurat, idan fa na nemi Aurenta dole za'azo bincike wataran, bana son abunda ya faru dani akan Salma ya sake faruwa, ga kuma abunda ya faru da iyayenta saboda ni,