Showing 195001 words to 198000 words out of 209297 words

Chapter 66 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

741

muyi bikone, dan Allah a temake mu a bamu mijin mu mana, ayi mana afuwa"

Umma tace  "wai ya akayi ta zama 'yarka kuma? Kuma ni gaskiya ina tsoron abunda ze biyo bayane, ni inajin tsoron ɗana ya sake shiga matsala gaskiya"

Alhaji Ahmad yace "labarin dogone, amma dan Allah ayi haƙuri a bamu mijinmu, zamuyi miki bayanin komai, amma waini ina sirikin nawa yake nema? A nunamin shi in ganshi, inga ya yake a yanƙwanamu akansa haka?"

Umma tace  "A'a ba wani na musamman bane, kawai ni bana son ɗana ya sake shiga matsala saboda itane, ya wahala fiye da tunaninka, duk saboda ita, wahalar da akayi a baya Allah ya amfana"

Yusuf ne yayi sallama, hannunsa ɗauke da ledar aiken da Umma tayi masa, ya shigo falon cikin nutsuwa da sallama, sedai yana ganin Widad a zaune gabansa ya faɗi, ya ɗan tsaya yana kallonta, ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta.

Yusuf ya durƙusa ya gaida Alhaji Ahmad, Alhaji Ahmad ya amsa yana ƙarewa Yusuf kallo, yace  "iko se Allah, lallai dole a mana jan aji akan wannan zuƙeƙen matashin, Widad banga laifinki ba da kikabi kika ɗaga hankalinki akan mijinki, dan an ganshi kyakkyawa shine ake wani jamana Aji"

Yusuf ya ɗanyi murmushi, yana son sanin waye wannan mutumin da suka zo tare da Widad?

Yusuf ya maida kallonsa ga Widad, ya ɗan kashe mata ido, amma ta haɗe rai tana ƙoƙarin maida ƙwallar idonta, girgiza mata kai Yusuf yayi, ya ɗakko handkerchief ɗinsa, ya faki idon Umma, ya miƙawa Widad, Alhaji Ahmad suna magana da Umma, amma hankalinsa yana kansu Yusuf.

Yusuf ya miƙe ze bar falon, Widad tabi Yusuf da kallo, kamar zata cinye shi.
Alhaji Ahmad ya kalleta yace  "Widad ɗan bamu guri, maza tashi ki bishi, ai tunda Allah yasa munzo se Jidda ta bamu mijinmu, an dena wahalar min da 'ya dan anga yana da kyau, nasan dai' yata tafi shi kyau"

Umma tayi murmushi, Widad kam cikin hanzari ba kara ba kunya, ta miƙe yabi bayan Yusuf, yayin da Umma ta jinjina rashin ta ido irin na Widad "

Suna fita Yusuf ya janyota gefe yace " sweetheart, waye wannan mutumin ne? "

" Nima ban sanshi ba"

"Are you serious?"

"dagaske nake" ta bashi amsa

"Amma ya akayi kuka zo tare?"

"Nifa ban sanshi ba, ya cemin yasan Ummane, nazo mu bada haƙuri"

Yai murmushi yace  "shikenan naji, zomuje ɗakina muyi hira kafin su gama maganar"

Widad ta zaro ido tace  "haka kurum, Umma tace bani da kunya, ni a nan zan zauna"

Ya shimfiɗa musu dadduma, suka zauna hirarsu suke kawai kamar babu abunda yake damunsu, Umma ta fito ita da Alhaji Ahmad, Alhaji Ahmad yace "Widad taso mutafi, se Allah ya kaimu weekends ɗin"

Widad ta tsaya tana kallonsa, kamar bata gane me yake faɗa ba.

Ya sake maimaita masa maganar, amma Widad taƙi motsawa.

Yusuf yace  "ki tashi ku tafi mana"

Aiba kunya Widad ta noƙe kafaɗa, alamar ba inda zata je.

Alhaji Ahmad yace  "iko se Allah, kiyi haƙuri kizo mutafi, idan Allah ya kaimu Weekend zamuyi tafiyar nan, kuma ina lallaɓa sirikata mu, dan haka kiyi haƙuri za'a baki mijinki"

Widad tace  "dan Allah ni ka ƙyaleni a nan, wallahi bana son zaman gidan nan nika ɗai, damuwa damuna take, dan Allah ka barni a nan zuwa weekends ɗin mu tafi ta nan gaba ɗaya"

Alhaji Ahmad yace "Ikon Allah to sirkarmu kinji abunda tace, bakomai ta zauna ɗin a nan, zuwa Allah ya kaimu weekends ɗin?"

Umma tace  "toni me zance, in dai gidane gashi nan ta zauna, sedai mu bamu da Arziki ba lallai muna da abubuwan da take buƙata ba"

Yusuf a ransa yace  "Umma da kin san a ƙungurmin ƙauyen da muka zauna, da baki faɗi haka ba"

Widad kam cewa tayi  "Ni dai zan zauna a nan"

Alhaji Ahmad yace  "toke yanzu gashi baki ɗakko kayanki ba, a haka zaki zauna ɗin?"

Widad tace  "zamuje da Yoseef in ɗakko"

Alhaji Ahmad yace  "ina ganin ƙauna, ikon Allah dan Allah Jidda ayi haƙuri idan muka dawo daga tafiya Yusuf ya koma ɗakinsa"

Seda Umma tayi dariya, jin abunda Alhaji Ahmad ya faɗa, gaba ɗaya suka raka shi har bakin mota ya tafi, sedai tafiyarsa babu wuya aka girke 'yan sanda a bakin layin su Yusuf dan basu tsaro.

Mutanen layin sunata gulma dan sunga an kawo' yan sanda layin, wataƙila Yusuf aka kuma zuwa kamawa, tunda yai wannan laifin unguwarsu bata rabo da 'yan sanda.

Yusuf yana son ya keɓe da Widad suyi hira sosai, amma kunyar Umma yake ji sosai, Umma kam basar dasu tayi kamar bata san da zamansu ba, sabgogin gabanta kawai take yi.

Bayan sallar magariba Yusuf ya dawo daga masallaci, Widad tace  "Yoseef nayi waya gida, Nura zezo da mota muje farm House mu ɗakko kayan.

Yusuf ya kalli Umma, amma yaga basu take kallo ba.

Ba daɗewa sega Nura direban Daddy ya ƙaraso, Yusuf yaje ya samu Umma yace " Umma zan raka Widad ta ɗakko kayan ta "

Umma tace  "sekun dawo"

Sam Yusuf baya jin daɗin yadda Umman keyi, duk se yaji ya damu ya tsargu sosai, baya jin daɗin hakan sam.

Widad ta saka takalmanta tayi waje, Yusuf yabi bayan ta, suna zuwa Nura ya buɗe mota ya fito yana, jinjinawa Yusuf hadda duƙawa yana   "Allah ya temaki me gida, Allah ya tsare gabanka da bayanka mijin Hajiya Widad, siriki ga Alhaji Nasir Daula"

Yusuf yai murmushi yace  "Nura karka bani kunya mana dan Allah, ni nayi laifi ma, tunda aka sakeni, ban samu nazo mun gaisa na muku godiya ba, saboda bana son sake zuwa gidan nan ne, amma ina godiya Nura"

Yai maganar yana miƙawa Nura hannu su gaisa, Nura ya zare ido yace  "wane talaka haɗa hannu da kai yanzu? Ai sedai ai muku gaisuwa irin taku ta manya"

Yusuf yace  "dan Allah Nura ka bari, bazanji daɗin haka ba, ka barni a Yusuf direba na kawai"

Widad tace  "aikuwa naga wanda ze kiramin miji da direba, yaga yadda zanyi dashi, koda yake ni kaɗai zan dinga ce masa direbana"

Sukayi dariya gaba ɗaya, Widad ta ɗakko ƙaramar jakarta, ta ɗebo kuɗi ta miƙawa Nura tace  "gashi nan, ka hau mota ka koma gida, bawa Direbana mukullin, zamuje yawo tare"

Yusuf yai murmushi yace  "Yarinya ki cigaba da cemin direba, idan na kaiki bazan dawo dake ba"

"kai ka isa"? Tai maganar tana kaimasa dukan wasa a ƙirjinsa, Yusuf ya karɓi mukullin motar suka shiga suka tafi.

Nura kuma yai ram da kuɗin da Widad ta bashi, dan kuɗin yafi ƙarfin dubu Ashirin, yana tafe yana mamakin yadda Widad ta canza gaba ɗaya, ga kuma ga dukkan alamu ba ƙaramin so takewa Yusuf ba.

Haka ya isa gida yana wannan mamakin da tunani, Isa yace  "ha na ganka kao kaɗai? Ina motar da kuma gimbiyar Daula?"

Nura yace  "barni inyi mamaki Isa, gaskiya gimbiyar Daula ta canza, kaga wasa da dariya?"

Isa yace  "na gani ranar data zo nan kam"

Nura yace  "mhmmm, na yadda dare ɗaya Allah kanyi bature, nikam dama can Gimbiya bata son Yusuf kuwa, tunani nake yadda ko a baya da yana direbanta, tana masa wulaƙanci son ranta amma bata yadda wani ya taɓashi ba, kai kaga soyayya, motar suka karɓa wai zasu unguwa, Allah sarki dafa a cikinmu yake, amma Allah ya tsame shi ya auri 'yar masu gida, shikenan Allah ya masa sitirar arziki, dan ynzu yayi hannun riga shida talauci, da Daula yana da wata' yar nima se ince inama inama"

Isa yace  "Inama me? Kana ganin baƙar azabar da ya sha, kafin ya kuɓuta, ni mamakin da nake ya akayi sukayi auren ne?"

Nura yace "kanaji ana gayamaka, Saleh ne ya kuɓutara dasu, ya kaisu wani ƙauye aka ɓoyesu, kasan ta bata da yadda sam, taƙi yadda da kowa seshi, kuma ance lokacin bata da lafiya sosai, tace bame kula da ita seshi, shine fa sukayi Aure a can, daga nan kuma abu ya zame masa silar Arziki, dan nasan yanzu ita da abunda ta mallaka yana da iko dasu, dama ka santa ga kyauta, gaskiya ze warwasa, inama inama nima ace in samu dama haka ko bata kai kamar tasa ba"

Isa yace  "ga Amal, ka lallaɓa da ita mana"
  Nura ya haɗe rai yace  "Agolar? Uwar me taci balle ta bani, suma yanzu suna fama da kansu, sun saida koma, komai ya ƙare musu, an kashe babban ɗa, uwa ta tafi hannun hukuma, ita wannan ga rashin lafiya, waccan ga shaye2, komai ya ƙare, ni nayi mamaki ma da Gimbiya ta ƙyalesu har yanzu zaune a cikin gidan nan, ai dama shi ramin mugunta idan zaka ginashi, seka gina shi gajere, dan wataƙila kai zaka faɗa "

Isa yace " babu wanda yafi bani mamaki, se Alhaji Bulama ubangiji Allah yayi mana tsari da azzalumai kamarsa, yanzu duk yada yake da Daula, da soyayyar da yake nunawa Daula, ashe azzalumi ne mufuki, na ƙaryane zagon ƙasa yake masa, gaskiya mun shiga haƙƙin Widad na ganin aibunta, ashe tana da dalili akan ƙin mutane, ji wannan asara fisabilillahi "

Nura yace " bari kawai Isa, duniya babu gaskiya, mutane mun lalace se fatan shiriya, amma tabbas gaba ɗaya mutanen nan sunyi tarayya a cikin ƙaddarorinsu, Alhaji Daula, 'yarsa da kuma Yusuf daya shiga rayuwarsu daga baya, sedai fatan Allah yasa bakin wahalrsu kenan, kuma Allah ya bayyana Alhaji Daula "

Isa yace " Ameen ya Allah "

Yusuf da Widad kuwa, seda suka sha yawonsu a gari, sannan ya kaita suka ɗakko kayanta suka dawo gida.

Ɗakin Umma ya kai akwatin kayan nata ya ajiye, ita dai UMMA bata tanka musu ba, tana ganin Yadda suke rawar kai akan junansu, da nan nan da juna cike da tsantsar kulawa da soyayya.

Yusuf yace  "Umma kinci Abincin dare ne?"

Umma tace  "eh naci, ga naku can a flask"

Yusuf ya ɗakko flask ɗinAbinci ya kawo, tuwon Alkama ne miyar kuɓewa Umma dafa, Yusuf yana zubawa Widad kamar zata shiga cikin kwanon, saboda yadda yawunta ya tsinke.

"Yoseef dan Allah ka zuba da sauri mana, kana yi a hankali fa, kuma ni sonake inci"

Tai maganar a ɗan Shagwaɓe, Yusuf ya kalli Umma, amma yaga hankalinta baya kansu, kuma tana jin taɓarar da Widad ɗin keyi.

Yusuf a hankali yace  "bazanyi saurin ba"

Ta harari Yusuf tana tura baki, ya zuba mata tuwon nan, miyar ta sha kifi, ya samat man shanu, yadda Widad ta duƙa tana zuba tuwon nan yafi komai bawa Yusuf mamaki, ci take kawai ko magana ba tayi.

Yusuf yace  "wai baki ƙoshi bane har yanzu?"

Widad tace  "wallahi ban ƙoshi ba, rabona da Abinci inci cikakken Abinci cikin kwanciyar hankali, tun ranar da muka baro ƙauyen nan, bana samun Abinci inci, ga Abincin yayi daɗi Sosai"


Yusuf yace "ikon Allah, yanzu ke tunda kike gurin Bulaman bakya cin Abinci?"

Widad tai murmushi me ciwo tace "Yoseef, bana son tuna abunda ya riga ya wuce, ban zaci zan kuɓuta ba, na sha wahala fiye da tunaninka, banda duka da baƙar azabtarwa ba abunda nake sha a hannunsa, ga ɗansa kuma Fahad, daya dinga nema yaci zarafina, bana samun abunda nake so inci, komai bayamin daɗi, shiyasa na masa wannan tabon da wuƙa a fuskarsa, ko zan rage raɗaɗin abunda yayi min"
Gaba ɗaya jikin Widad yai sanyi tace "ƙaramin tuwon nan, yunwa nakeji ban ƙoshi ba"
Ya sake zuba mata, ta dinga cin abunta, ba wata kunya ko kara seda taji tayi ƙyat babu sauran gurin zubawa sannan ta haƙura, ta tashi taje fridge ta samo ruwa me sanyin gaske, ta zauna ta sha abunta ta wanko hannunta tazo ta zauna tana hutawa.

Yusuf yace "Sannu da aiki"

Widad tai murmushi ba tace komai ba.

Abincin data cine ya fara taso mata, tai shiru ta kasa magana, Yusuf ya zuba abunda ta rage yana ci.

Cikin hanzari Widad ta tashi ta fita, ta dinga amai, seda ta amayar da duk abunda taci, Yusuf yabi bayan ta da sauri.

Tayi amai sosai, Yusuf ya temaka mata, ta gyara jikinta ta kuskure bakinta.

Umma ta fito daga ɗaki tace "garin yaya take amai haka? Ko bata da lafiya ne?"

Widad tace "A'a Umma, lafiyata ƙalau"

Yusuf yace "inaga ko over feeding ne da tayi"

Umma tace "in ba hali, ko Asibiti zaka kaita saboda dare"

Widad tace "A'a, base munje Asibiti ba, ya lafamin ma"


Umma tace "shikenan, kije kwanta ki huta"

Widad taje ta canza kayanta, zuwa na bacci ta sake burma ƙaton hijjabinta, ta nemi guri ta kwanta a ƙasan carfet.


Umma ta shigo ɗakin ta ga Widad a kwance a ƙasa tace "tashi ki hau kan gadon mana"

Widad tace "A'a Umma, bana jin daɗin kwanciyar kan katifa, bayana ciwo yake nafison kwanan ƙasa"

Umma tace "shikenan"

Widad dukda basar da ita da Umma take, amma taji daɗin ganin yadda Umman, ta nuna mata kulawa.

Umma taje ɗakin Yusuf tace "bani bargonka guda ɗaya, a shimfiɗa nata tace bata son kwanciyar kan gado"

Yusuf yace "yawwa Umma, naji ana cewa za" ayi tafiya da weekend, amma ina za'aje ne? "

" ban sani ba, meya hana ka tambayi matarka? Bani bargo ni"

Yusuf ya miƙa mata bargon, ya ja bakinsa ya tsuke.

Umma ta gyarwa Widad gurin kwanciya, ta kwanta.





Nurat kam gaba ɗaya damuwa ta addabeta sosai da sosai, bata jin daɗin zaman gidan gaba ɗaya, gashi ta saka duk mutan gidan a damuwa, ganin yadda taƙi sakin jikinta, Nurat tai tunani taga damuwa bazata maganta mata abunda ke damunta ba, ta tashi ta fito falon gidan.
Ba kowa a gidan, duk ma'aikata ne sun tafi gurin aiki, ƙannen Khalil kuma duk suna kudancin Nigeria suna karatu.

Nurat ta gyara ko'ina na gidan, tayi girki yaje tai wanka ta dawo falo tana kallo, duk a ƙoƙarin ta na kauda damuwar dake ranta.

Wajen ƙarfe biyu Khalil ya dawo gida, ganin Nurat a falo tana kallo yasa yaji daɗi, ba kamar da ba da kullum tana ɗaki, ya ƙaraso yana mata murmushi yace "Sisyna, masha Allah, wannan kyau haka"

Tai murmushi taje ta karɓo kayan hannunsa, tana masa sannu da zuwa tana masa murmushin nan nata me ɗaukar hankali.
Yaji inama ace matarsa ce.

Nurat tace "Sannu da zuwa, kaje kai wanka kazo yau nina yi girki kaci Abinci"

Khalil yace "ashe yau da shagali, zanci Abincin 'yar auta"

Nurat tai murmushi, taje ta kai masa kayan ɗakinsa, dake kusa da falon.

Bayan yayi wanka yai salla, ya fito ya zauna a falo yana jiranta, ta shigo da sallama hannunta ɗauke da kulolin Abinci, ta tarar da Khalil ya zubawa wayarsa ido.

Nurat tace "inyee, da alama wannan matashin barrister ya shiga soyayya, hoton wa ake kallo haka?"

Ya ɗago ya kalleta yace "kalleki, wai hoton wa nake kallo, niwa zan kalla"

"Nifa dama baka taɓa nunamin budurwarka ba, gaskiya yakamata kayi aure haka, haba seka zama tuzuru tukuna, dan kaga Mama ta shagwaɓaka ne, da Abincin ta, ta koraka bakin gate a maka ɗaki, sannan a dena baka abinci zakayi aure"

Khalil yace "kice azabtar dani za'ayi kenan? Hmm ni tsoron matan yanzu nake Nurat, soyayyar gaskiya tana wahala, shiyasa ni ban taɓa budurwa ba"

Nurat tace "No akwai soyayyar gaskiya mana, kai dai kawai kace tsoron 'yan mata kake yi, you can't toast a lady"

Tai maganar tana dariya, Khalil ya girgiza kai yace "Eh naji ɗin, yanzu dai in kin matsu inyi Aure ki samo min budurwa, sannan ki dinga rakani zance"

Nurat tai murmushi, seda fararen haƙoranta suka bayyana tace "ba budurwar da zata aureka kuwa a haka, in dai sena raka ka zance"

Ta zuba masa Abinci, yanaci yana kallonta, yana jin kamar ya gayamata yana Sonta, sedai yasan zuciyarta tana tare da Yusuf.



Da Safe Widad ta tashi, Umma tana bacci ta tafi ɗakin Yusuf, yana kwance yayi ɗai ɗai akan gado, yana baccinsa.
Ta kalli ɗakinsa, ɗakin tsaf dashi, kamar ɗakin wata matar ga Mirror, da gado wardrobe komai tsaf dashi.

Ta ƙarasa kan gadon nasa, ta zauna ta ƙura masa ido, Wani murmushi take ganin yadda yake baccinsa hankali kwance, kamar wani jariri ya ɗan ciko daga ramar da yayi, sedai shima jikinsa duk tabon duka daya sha a prison.

Hannu ta kai tana shafa gefen fuskarsa, tai ƙasa sa muryarta tace "Hubbyna ka tashi muna jin yunwa fa"

A hankali ya buɗe ido ya kalleta yace "ke kin fiye takura, haba Babyna wace irin yunwa ƙarfe shida na safe?"

Cikin shagwaɓa tace "ni dagaske yunwa nakeji, ka tashi yunwa nakeji"

Yusuf ya noƙe kafaɗa, yana ɗora kansa akan cinyarta yana lumshe ido.

"Wallahi idan baka tashi ba, zan zauna se Umma tazo ta gamu a nan tare"

Ba shiri Yusuf ya miƙe zaune, yace "rufamin Asiri, tashi muje"

Widad ta dinga dariya, har sunje bakin ƙofa, ya juyo ya kalleta ya rungumota jikinsa yai kissing ɗinta yace "good morning"

"Morning, ka tashi lafiya?"

"Alhamdilillah, ya babyna?"

Tace "yana nan yana jinka"

Yai murmushi, suka fito tare suka shiga kitchen.

Suka feraye dankalin hausa tare, suka dafa tea, suka shiga suya Tare, hirarsu kawai suke kamar suka ɗaine a gidan.

Yusuf so yake ya saki layi, amma Widad na kakkarewa tana hanashi.

Umma kuwa tuni motsinsu ya tashe ta, amma bata fito ba karta takurasu, suka gama sukayi wanke wanke suka gyara komai tsaf.

Widad na shiga ɗakin ta tarar Umma ta tashi, Widad tace "Umma ina kwana"

Umma tace "lafiya ƙalau, ya jikin naki?"

Widad tace "naji sauƙi"

Umma tace "Allah ya ƙara sauƙi"

Duk yadda Umma take basar da Widad, Widad bata nuna mata taji haushi ba sam, tana girmamata sosai, sedai bata iya kara ta ɓoye soyayyarta ga Yusuf ko a gaban Umma ne

Wajen ƙarfe goma na safe, ciwon ciki ya kama Widad, tun tana mazewa seds Umma ta gane.

Lokacin Umma ta aiki Yusuf, baya gidan amma ganin Yadda Widad ke murƙusus yasa Umma ta kira shi a waya.

Da hanzari ya dawo gida, ya tarar Da Widad ta durƙusa tana kuka, se numfashi take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login