Showing 87001 words to 90000 words out of 209297 words

Chapter 30 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

730

da aka fitar da wannan Sanarwar"

Nurat tace  "Amma Anwar meka fuskanta game da wannan Sanarwar"

"To ni dai abunda nake gani, wata maƙarƙashiyar ce aka shirya domin ɓatawa Yusuf suna, turoshi akayi domin bincike akan maƙiyan Daula, amma kuma daga baya ake nema a ɗora masa sharri, ni yadda naji ma sunce wai babu wanda ya turoshi aiki gidan"

Nurat tayi ajiyar zuciya tace  "Yaya Anwar, wannan abubuwan duk shirine akayi shi domin a ci mutuncin Yusuf, kuma shiryayiya ce aka shirya wannan lamarin, ni ban san yadda za'ayi Yusuf ya ƙuɓuta ba, yana cikin matsala"

Anwar yace  "hakane, nima naje na samu Alhaji Bulama, tunda yana da alfarma a ƙasar nan, ayi bincike yadda yakamata"

Nurat tace "Yaya Anwar, tayasu da Addu'a shine abunda yakamata, amma harkar ƙasar nan se godiyar Allah, gashi haryanzu babu labarin Mahaifin Widad"

Anwar yace "wallahi kuwa, to Allah ya wuce mana gaba, Allah ya kawo mafita gaba ɗaya"

"Ameen ya Allah, nagode sosai Yaya Anwar"

"Bakomai, nima nagode"


Washegari da safe, Widad ta riga Yusuf tashi, yau da kanta ta dafa ruwa tayi wanka, ta gyara tsakar gidan nan fes tayi wanke wanke, ta zuba shinkafa ta fara tsincewa, ta tsince shinkafar nan iya yadda zata iya, amma Yusuf be tashi daga bacci ba,
Taje inda yake kwance ta zauna ya gama ƙare masa kallo, sannan ta shiga tashinsa kamar zata tashi jariri.

A hankali ya buɗe ido, yanayi yana lumshewa alamar bacci be isheshi ba tace  "wai yau da Yunwa zaka barni?"

Murmushi yayi ya sake lumshe idonsa, cikin Shagwaɓa tace "tashi Yunwa nakeji fa"

'Nikuma bacci nakeji "

"to bari inje in dafa da kaina, tunda ba zaka tashi ba"

"No sorry, bari in tashi in dafa miki'

"kaga harna dafa ruwa nayi wanka, na tsince shinkafan ma"

"Haba dai?"

'dagaske nake fa"

Ya miƙe ya duba ta share ko ina, tayi wanka har shinkafa ta gyara ta wanke, murmushi yayi yace   "Alhamdilillah, mutuniyar ta fara zama mace"

"Dama ni namijice?"

"A:a ni bance ba, amma mace ai seda aikin gida, kice zamuyi surprising Daddy '

" Sosai makuwa "

Ya ƙarasa musu girkin, suka zauna sukaci Abincin su.

lokaci lokaci Widad se taji gabanta ya faɗi, amma ta dake da dinga ɓoyewa, dan karya gane tana cikin damuwa.

Widad tace "Yoseef ina kewar su Mama sosai da Hindu, mutum rahama ne"

'Ni Aljani ne kenan? "

" A' a ni ba haka nace ba, na saba ganinsu ne, ina ganin mostinsu da giftawarsu, amma kwana biyun nan shiru bana ganinsu"

Yusuf yace "yanzu kin gane amfanin mutum a rayuwar ɗan adam kenan? Babu yadda za'ayi mutum yayi rayuwa shi kaɗai babu mutane kuma yace hakan yafi daɗi"

'hakane, dan ina gudun a cutar dani ne, shiyasa nake gudun mutane, amma yanzu nasan wannan mutanen da muke tare dasu bazasu cutar dani ba, shiyasa nake kewarsu"

"hakane, naga taku tazo ɗaya dasu sosai, Amma naji anjima zasu dawo ai ko?"

"Eh anjima zasu dawo insha Allah"

"to Allah ya dawo dasu lafiya"

Ta amsa da Ameen.


Anwar sosai yake tunanin samawa kansa mafita, akan lamarin gidansu dan duk se yaji zaman gidan baya kansa ya fita a ransa.

Shiga yayi gidan da nufin gaida mahaifiyar su da safe kamar yadda ya saba, sedai ta window ɗin ɗakinta yaji suna magana ita da Ramlah, seya tsaya be ƙarasa ba.

"Ramlah wannan rayuwar da kika ɗauka ba inda zata kai miki, ki kiyayi kanki da shaye shaye nan, kinga na gwale 'yan uwanki jiya amma tabbas maye kikeyi, dan dai inajin daɗin shawara dake ne da fushi zanyi dake"

'Mummy na dena fa"

"Shikenan, ai dama nasan zaki dena, nace ya kukayi da Fahad ɗinne, ina fatan dai baze tona mana asiri ko gurin babansa ba"?

' Haba Mummy, shiya fara ma tunda abun nan harda shi ake ƙaruwa "

"Yawwa haka nake son ji, yanzu wannan manyan filayen nasa nake so in sa a kasuwa na GRA, dan haka kiyi masa magana, kamar yadda akayiwa Gidajen layout ɗin nan takadda, suma wannan ayi musu takaddu mu siyar, ke ni ko miliyan sha biyar biyar, a siye su"

Ramlah ta ɗan zaro ido tace  "Mummy million sha biyar kima, a filayen miliyan kusan arba'in ɗin za" a siya a haka? "

" Eh to seme? Da gumunmu muka tara? Nifa sonake ayi yadda za'ayi mu ɗan tara daga nan mu san nayi, dan haka ki masa magana, ke har gidan nan ma sena siyar dashi, ai in sun san wata basu san wata ba"

"hakane Mummy, amma gaskiya baza'a siyar da filayen nan a haka ba se an ƙafa, in ba haka ba mume zamu ci?"

"to koma dai yane, kiyi masa magana ayo takaddun daga nan musasu a kasuwa"

"Shikenan zamuyi waya dashi, kokuma inaga anjima ma zezo, se muyi maganar gaba ɗaya"

Hajiya Halima tace  "ainaji daɗin harkar nan da yaron nan, motocin nan na farmhouse ma ai duk shi yayi mana hanya aka siyar dasu, banda sauran abubuwa, aini wannan lamarin ma gaba ta kaimu"

"Wallahi kuwa Mummy, semunci rabon mu tukuna"


Anwar ji yayi kamar ƙasa ta buɗe ya nutse a ciki, dama kadarorin Daula mahaifiyar sa ke siyarwa yana wadaƙa da kuɗin? Lallai ɗan Adam butulu ne, idan ya tambayeta ina motocin gidan se tace tasa an kaisu Farm House, dama abunda take yi kenan? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un'

Jiki a sanyaye yaje ya ɗau motarsa ya tafi gidan gonar Alhaji Daula wanda aka riga aka mallakawa Widad, yaje da niyyar zagaye yake ya biya dan yaga gidan, ya tarar fiye da rabin motocin nan idan ya tambaya se ace Hajiya ta turo a ɗauka, hatta dabbobin Widad tana ta musu ɗuki ɗai ɗai, dan akwai da yawa wanda bana ƙasar nan ba a ciki, dan haka ana siyansu da tsada.

Abun ya bawa Anwar mamaki, ya tuna irin gwagwarmaya da ɗawainiya da Daula yayi dasu, amma mahaifiyar su ta rasa dame zata saka masa se wannan zalunci da tsantsar butulci, lallai ɗan Adam butulu.

Da ƙyar ya kai kansa gida, saboda azabar ɓacin ran da yake ciki, ta haɗa kai da 'ya' yanta suna ta wadaƙa da dukiyar marainiya data mahaifinta, se yanzu yake jin Widad bata da laifi da suke iƙrarin tana Wulaƙantasu.




Da yamma Widad taita zuba ido a hanya taga ta ina su Gwaggo zasu dawo, se bayan ƙarfe biyar se gasu sunyi sallama sun dawo, Widad ta dinga murna, tace  "Sannunku da zuwa na zaci ma kum fasa dawowa yau"

Gwaggo tace  "aiko kowa be dawo hau ba dole in dawo saboda ke, muna can amma hankalina yana nan"

Widad tace "Hindu 'yan biki, a huta azo a bani labarin abunda ya faru"

Hindu tace "ni wallahi muna gurin biki, hankalina yana kan makaranta"

"to aini tunda kuka tafi, nace a bari sekun dawo a cigaba'

Suka baje a tsakar gida, Yusuf ya fito yayi musu sannu da zuwa sannan ya fita.

Saboda ɗaurin Aure, megari ma yaje gurin bikin, da shi da Sunusi Kasancewar Yayar megari ce ta aurar da 'ya, nan ma Yusuf ya shiga yayi musu sannu da zuwa, daga nan megari yaja shi da hira suka shantake a gurin.

Gwaggo ta baje kayan biki da suka zo dasu, ƙulli daban tayiwa Widad na kayan gara kuma fal da yawa, kayan zaƙin nan.

Gasu wainar masa da ƙuli, Widad tana son kayan zaƙi dama, ta zauna ta cicci abunta tana lashe baki.

Ana idar da sallar magariba ta tura yaro ya kira mata Yusuf a waje, Yusuf ya shigo gidan ya shiga ɗaki ya sameta yace

"lafiya kika aika a kirani? Me zaki ban?"

"To ai kaine kaƙi dawowa tun ɗazu"

"to ai bamuyi sallar isha'i ba, kuma zamuyi karatu"

Ta miƙe ta ɗakko masa kayan da Gwaggo ta bata, Yusuf yace "masha Allah, 'yar gatan Gwaggo wannan duk namu ne?"

"Eh mana shiyasa nace kazo kaci naka, gashi nan kaci iya cinka, ni na tafi tsakar gida"
Tana gama maganar ta miƙe ta fita.

Yusuf ya zauna yana cin kayan gara, Widad tayi waje, Hindu tana ta bata labarin yadda bikin ya gudana, Hanne kuwa se cika take tana batsewa, ba wanda yabi ta kanta suka ƙyaleta da ƙuncin ran da take yi.

Bayan Yusuf ya gama ya fito tsakar gida yana alwala, Widad tace "Mama waiya mutum ze gane idan yana da cikine?"

Gwaggo tace "to babbar magana"

Jamila tace "karki damu, ni zan gaya miki in munfi haka yawa"

Widad tace "ai yanzu ma muna da yawa ki gayamin mana"

Hari tace "to bahaushiya, tana nufin se daga ke se ita tukuna"

Widad tace "koma yane, ni dai dan Allah Mama ki dingamin Addu'a, Allah yasa in samu ciki"

Hari tace "Ai himma kawai zaki ƙara, idan kika shiga ɗaki tun magariba, se wata magaribar"

Sam Widad bata gane me Hari ke nufi ba, Yusuf shi kunya cema duk ta kama shi, ya tashi ya fice waje.


Jamila tace "Widad zomu je ɓangarena, in baki tawa tsarabar"

Widad ta tashi ta bita, Jamila tace "Widad nace miki irin wannan tambayoyin, ni zaki dinga yiwa ba Gwaggo ba, kunyace dasu, kinga baki taɓa haihuwa ba balle ace kin san alamomin, dan haka ba lallai alamomin da zan gaya miki su zamana ciki bane, amma mafi akasari dai cikinne ke sawa, Alamomin da zaki gane kina da ciki sun haɗa da, ɗaukewar Jinin al'ada, zazzaɓi, ciwon kai, jiri, Mamanki zasu danyi miki nauyi, koma su dinga zafi, yawan tashin zuciya, koma amai, yawan san ki kasance da mijinki a shimfiɗar Aure, ko jin haushin hakan, yawan som cin wani abu ko ƙin wani kalar Abincin, da sauransu amma alamomin ba lallai kiji su duka ba"


Widad tace "wanne ne babban alama to?"

Jamila tace "Ɗaukewar Al'ada, ko kuma laulayi idan cikin me laulayi ne"

Widad tace "shikenan nagode sosai"

Jamila tace "abubuwan duk da nake gayamiki, kina ganewa kuma kina aikatawa dai ko?"

Widad ta jinjina mata kai.

Suka cigaba da hirarsu, tana ci gaba dayi mata lectures akan Rayuwar Aure.

Da daddare Yusuf ya dawo Widad tayi masa sannu da zuwa, ya lura da ta canza akan abubuwa da dama, wanda da a baya ba tayi.

Ba zato Yusuf yaji Widad tace "Yayan Daddy dan Allah meye maganin mata?"

Yusuf ya kalle ta yace "ke a ina kikaji hakan?"

Tace "A gurin Jamila"

'Sha kika yi kenan? Ya tambaye ta

Widad tayi shiru ba tace komai ba, kawai taga Yusuf ya kwashe da dariya yace "lallai yarinya kina ruwa"

Kamar zata yi kuka tace "wani abu ne ze sameni?'"

"A'a ni bance wani abu ze same ki ba"

Gaba ɗaya bata gane me Yusuf yake nufi ba, taga ya ɗauki kayan shimfiɗarsa yayi wajen kwanan sa.


' Yusuf meye haka wai? "

Yusuf yace " A ina? "

" Naga ka ɗauki kayan shimfiɗarka, yau bazaka kwana a gurina ba?'

"Eh yau a gurin kwanciyata zan kwanta"

Kamar zata yi kuka tace "Amma naga yaushe rabon daka kwana anan gurin, kawai se yau zaka wani ce a can zaka kwanta?'"

Kamar Yusuf zeyi dariya ya maze yace "A'a ni gaskiya sha'awar kwanan kam bargona nake, kowa ya kwanta a inda ya saba kwana"

Kawai ta zauna tana kuka, Yusuf ya sha dariya sosai, dan Widad ta iya gaɓunta wasu lokutan, seda yaga dagaske take sannan ya koma inda suke kwana yana mata dariya.


Da gari ya waye, idan Widad ta tuna abunda tayi jiya kawai se wani irin haushi yakamata taita tsaki, Yusuf yace "uwar kwaɗayi, gobema kije a kuma baki abunda baki sani ba kici"

"Bazan ƙara ba har abada"

Yusuf yaita dariya yace "A'a gaskiya ki ƙara, ni zan bada kuɗi ma ki ƙara"

Ya dinga mata dariya, taga idan ta biyewa dariyar da Yusuf ke mata se tayi kuka, dan haka ta biye masa suka dinga dariyar tare.

Cam tace "Yoseef, dan Allah ka dinga min addu'a, Allah yasa in samu ciki, haihuwa nake so nayi nima"

Maimakon yayi magana, kawai seya janye ta daga jikinsa ya bar mata ɗakin.

Mamaki ne ya cika Widad ta bishi da kallo, tana tunanin me yake nufi da wannan abunda yake yi, duk lokacin da tayi zancen tana son samu ciki, seya canza mata meye Nufinsa nayin haka?......







LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/15/21, 4:52 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

96_97




Widad taje ta samu guri tayi zamanta a tsakar gida tana kuka, saboda tayi mamakin abunda Yusuf yayi, idan wanine yace ze mata haka tabbas zata ƙaryata, amma se gashi Yusuf ke ƙyamar haihuwa ko meye dalilinsa oho, to koma dai wani daliline ai bashi da ƙarfin da zesa ace yana gudun haihuwa haka, idanma tunanin sa yadda zasu yi idan sun koma gida, ai suna da hujjar da zata nuna aure sukayi ba zaman kansu ba, kuma tasan Daddy zeyi farinciki da hakan, abun da yake ta buri yaga 'ya' yan Widad a rayuwarsa.


Kusan kwana biyu babu Anwar, an kai har gurin 'yan sanda amma babu Labari.

Hajiya Halima ta tafi gurin Alhaji Munir, yana ganinta ya ɗan ɓata rai yace "to uwar matsala, ke duk inda aka ganki ba alkhairi se tarin matsala da damuwa"

Haɗe rai tayi sosai tace "nice ma kake gayawa haka? Dole kace ganina ba alkhairi bane, kuma ai ganin naku ba alkhairi bane ba, malam ɗana ya ɓata Anwar, tun jiya ban san inda yake ba, idan wata ƙulla ƙullar kuka haɗa, kowani makircin to kufito min da ɗana, dan babu ruwansa a harƙallar da mukeyi "

Alhaji Munir yace " to akama ɗanki ayi masa me? Har akwai abunda za'ayi aji tsoron gayamiki ne? Kije can kineme shi, idanma a cikin namu ne toni dai bada yawuna ba, dan ban san anyi ba, sedai ko Musa kowani amma ni ban san komai ba kam"

"to bari kaji in gaya maka, idan ma ka sani ka rainamin hankali wallahi duk abunda nayi maka kai ka ja, dan wallahi sena saka mutum dana sani da cizon yatsa"

Alhaji Munir ya taɓe baki yace "a banza ƙiba a kunne, ƙarewa 'yar gidan Daulama duk zare idonta da hura hanci shekaru kusan Goma sha biyu ta kasa gano mu balle ta ɗau mataki, se wata ke zakizo min da wannan ƙaramar barazanar taki dan ki firgitani, kije kiyi duk abunda zakiyi karki fasa, tunda naga alama daga ke har Musa kun fara hauka"

"Shikenan, zakaga hauka ganin idonka, wallahi idan da saka hannunku kika sacemin yaro wallahi se kunyi danasani, zan nuna muku masifa da kaidin mace, shima Musan zanje in kasa masa warning, tun wuri ka kiyaye ni, ku fita daga idona kallon ku kawai nake yi"

Ta juya a fusace ta koma inda motarta take, Alhaji Munir ya bita da ido, yayi tsaki ya koma ciki yana jinjina hauka da rashin hankali na mata.

Daga nan gurin Alhaji Musa taje a Office ɗinsa na neman zaɓe, nan ma suka fafata, sukayiwa juna kaca kaca shi da ita, sannan ta bar gurin rai a ɓace.

Murtalane yake gyarawa Anwar ɗakinsa wasu lokutan, wani lokacin kuma da kansa yake gyara abunsa dan shi babu ruwansa, be ɗau duniyar da zafi ba sam kamar yadda mahaifiyarsa da' yan uwansa suka ɗauka, Nura ya shiga yana gyara ɗakin Anwar, yaga takadda a ƙarƙashin fulon Anwar ya ɗakko tajadar ya buɗe yakaranta ta tsaf sannan ya ɗauka ya nufi cikin gidan.

Suna zazzaune a falo sunyi jugum jugum, suna jimami da tunanin inda za'a ga Anwar Murtalah yayi sallama.

Suna kallonsa amma ba wanda ya amsa masa, a fusace Hajiya Halima tace  "dalla malami meyene, kamar baka san a halin da muke ciki ba, kazo ka samu a gaba da sallama, meyene jarababbu kawai?"

Murtalah yaji haushin abunda Hajiya Halima tayi masa, koda yake imda sabo sun saba, hantara da Wulakan da cin mutunci, sun saba ganinsa dan abunda wanda ya ɗaukesu aikin baya musuma yanzu yi musu ake sedai haƙuri, amma ya dake yace "Dama ba wani abu bane, ina gyara ɗakin Anwar ne na tsinci takadda a ƙarƙashin fulonsa, shine nace bari in kawo miki"

Tasa hannu ta karɓi takaddar sannan tace "to ai seka tafi ko? Ko a gabanka zan duba kaga reaction ɗina, aji daɗin gulma, munafukai kawai 'yan sa ido"

Sum sum Murtalah ya fice yana ƙunƙuni, a ransa yace "Ubangiji Allah ya kawo mana ƙarshenku, jarababbiya dake da wannan matsiyatan' ya'yan naki masu kama da jakuna, da bakinsu kaman na yaran hankaka'

Nurane yaji Murtala na zage zage da tsine tsine, yace   " kai kuma kai dawa? "

Murtalah yace  "nida wannan balamar matar mana, daga zuwa na tsinci takadda a ɗakin ɗanta naje kaimata, ta kama zagina tana cemin munafuki, ni dana san hakane ma da wallahi ban kai mata takaddar ba, inga ta tsiya"

Nura yace "kaima meya kaika? Jiya Daga Isa ya ɗanyi mata tunanin albashi, ta zage shi tsaf taci masa mutunci, hadda wai tunda ba gidan ubanmu bane, wanda ya gaji yaga baze iya ba ƙofa a bude take ya ƙara gaba, kajifa se kace ita nata gidan ubanne, ko daga gidansu tayi gammo tazo dashi, aimu tsakanin mu da wannan matar sedai Allah ya isa wallahi "

Murtalah yace " Allah ya isa me 'yanci makuwa wallahi, dan koni na mata ba adadi banza tana tafiya a karkace, ita ba ɗa' a 'ya' ya babu tarbiyya, se kayan ɗuwawu kamar zata kai kayan tusa birni"

Sosai Nura ya dinga dariya yace "Wallahi idan ta jika seka bar gidan nan, kaima ka sani yaseen, amma fa ka iya ba'a da cin mutunci"

Murtalah yace "to takorenin mana, ai yanzu gidan Daula sunan ne kawai, amma babu komai a ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login