Showing 126001 words to 129000 words out of 209297 words
"Ina Mummy ne?"
"Taje gida zata yi wanka ne, ta canza kaya"
Amal ta jinjina kai, tana sake jin wani irin zafi a hannuta da ƙasanta, ta ɗan rintse ido tana girgiza kai, an mata illar da bazai taɓa gyaruwa ba ta gyara kwanciyarta tana ajiyar zuciya
.
Ramlah ta kalleta tace "Amal meye tsakanin ki da wannan mutumin ne, naga fa kamar akwai damuwa a tare da ke? Meyafaru ne"
Girgiza mata kai tayi tace "bakomai"
Ramlah tace "ki gayamin gaskiya, ko akwai taimakon da zan iyayi miki, naga kamar akwai wani ɓoyaayyen al'amari a tsakaninku ke da shi, naji yana yiwa Mummy wasu maganganu ne marasa kan gafo, wai ai shi ya gani yana so, wai idan zata bashi ke yana so, ni ina tunanin ma wannan hatsarin da akace kinyi, gaba ɗaya na kasa yadda abun kamar wani shirin film ko tatsuniya fa"
Amal taji kamar ta gayawa Ramlah gaskiya, se taga yin hakan tamkar tonawa kanta asiri ne, kuma idan harta nemi taimakon wani, to bata cika mace ba, yakamata ta nunawa Haruna tsantsar kaidi da makirci irin na 'ya mace.
Amal ta dake tace "Idan ma yana nufin sona yake, gaskiya ni bazan auri tsoho kamarshi ba, amma in dai zan fizgi rabona a jikinsa ai shikenan, zan iya biye masa nima in tatsi arziki som raina, Amma dan Allah ki temakamin da ruwan zafi mana, zan gasa jikina, dan duk ciwo yake min"
Ramlah ta jinjina kai, taje samo mata ruwa me zafi ta rakata banɗaki, da ƙyar ta iya kintsa jikinta, saboda karayar hannunta, ga ciwo da kanta keyi, haka ta tsaya tai kuka me isarta a toilet sannan ta fito.
Saleh ya jigata sosai, Alhaji Bukar yaje yaga halin da Saleh yake ciki seda ya ɗan tsorata, dan kar Saleh ya mutu, dan muddin Saleh ya mutu shikenan, abubuwa sun lalace, dan haka yasa aka kira likitansa, ya duba shi yai masa allaurai ya samasa ruwa, da ƙyar Saleh ya farfaɗo koda ya farfaɗo ruwan leda ɗayane se garau garau na shinkafa da aka kawo masa, mutumin daya kwana uku babu abinci, amma ya faraka a bashi bushshsiyar shinkafa da wake, abunka da me jin yunwa ya kama Abincin nan ya dinga turawa, sedai ba'aje ko ina ba yaji kamar yana cin duwatsu ne, dan haka ya dinga aman abincin nan, Saleh ya galabaita sosy, dan kwanakin nan gaba ɗaya a ɗaure yake a igiya kamar rago, dan haka kowace gaɓa tasa ciwo take masa, ga shedar igiya ta fito raɗa raɗa a jikinsa duk fatarsa tayi jajawur, ga ciwon ƙirji saboda dukan da yake sha da katako kamar Ɓarawo.
Bukar ya kalli Saleh yace "wuya koda magani ba daɗi, ina fatan zuwa yanzu ka ɗanɗana kuɗarka kuma zaka bani haɗin kai, ka gayamin abunda na buƙata, ko kuma in sa a ninka maka wannan azabtarwar da ake maka.
Shiru Saleh yayi beyi magana ba, se suka numfashi dayake na wahala, yayi zuru zuri dashi kamar wanda yayi amai da gudawa, maganar duniya Amma Saleh yaƙi cewa uffan.
Me Adda yace "wai ba zakayi magana ba, semun ƙarasa sauke maka allon ƙirjinka?"
Bukar yace "saurara tukuna, wannan idan aka yi ƙwaƙwaran yunƙuri ze iya mutuwa, kuma idan ya mutu ze jamin gagarumar asarane a yanzu haka, dan haka ƙyaleshi tukuna, zuwa anjima idan be faɗa ba, a kamashi kusamin kansa a ƙasa, ƙafafunsa a sama a samo ruwan zafi ku saɓulemin fatarsa dashi, ku barshi anan gurin "
Saleh yabi Bukar da kallo, yana jinjina mugunta da zalunci irin na Bukar, haka Alhaji Bukar ya fice ya barshi a hannun su me Adda yayi tafiyarsa.
Akayiwa Amal aiki a hannunta, aiki yayi kyau an ɗorata, mutane nata tururwar zuwa dubata a Asibiti, kullum a can Hajiya Halima take kwana, kwana uku da yin ɗorin likita ya sallameta, yace su dinga zuwa duk bayan sati biyu ana dubawa harya gama warkewa gaba ɗaya.
Aka basu magunguna da sauran abun buƙata suka tafi gida, ma'aikatan gidan su Nura su Murtalah duk suka shiga suka dubata, suna fitowa Nura yace "Allah ya ƙara, Allah yasa karta warke da wuri hannunma ya ruɓe, jakar matar nan da yake 'yarta ce ta samu matsala, ji yadda ta dinga zarya a Asibiti, amma lokacin da megida yana kwance a Asibiti, sefa ta ga dama take zuwa, ɗantane kawai yaita wahalar jinya, shiba ubansa ba ba komai ba"
Isa yace "karkiya wa Amal wannan muguwar addu'ar, da dai waccan me ƙaton bakin ce Ramlah, ai gara Amal sau dubu da Ramla, dukda itama Amal ɗin ta iya rashin mutunci"
Murtalah dake gefe yace "hakane kam, Allah sarki, Allah ne kaɗai yasan inda megida yake, kaga kaman ma sum rufe babinsa, basa neman inda yake Yusuf kawai suke nema"
Nura yace "Allah sarki, wallahi tsayinsa nakeji, koba komai ba ruwansa wallahi"
Isa yace "kai dai bari, aiko ni da nake jin haushinsa da addua nake masa yanzu, na dinga duba yadda wasu abubuwan suk dinga faruwa amma baya magana, nan ze zauna in ta gayamasa baƙaƙen magana amma ko kallo bam isheshi ba, ima dana sanin wasu abubuwan da nayi masa wallahi "
Nura yace " nima inayi, amma ka fini zaƙewa sosai, kaga nifa da ace wani ne wallahi ko dagaske sace yarinyar nan yayi, wallahi sena hana a kama shi, yasha wahalrta sosai wallahi, ta gara shi san ranta "
Isa yace " Ai wannan akwai sa'a, duk garawar da take masa basu rabu ba, ya dinga mata biyayya, nifa wallahi ban yadda shiya sace ta ba, makirci ne kawai "
Murtalah yace " makairci kamar yaya kenan? "
"Nan Hajiya ta kirani falonta tace min, duk yadda zanyi inyi in nemo mata inda adireshin gidansu Yusuf yake, nayi nayi ya gayamin yaƙi, in ba makirci na Meza tayi da adireshin sa, kuma kun san wani abu, babu ma'aikacin da ake ɗagawa ƙafa a gidan nan kamarsa saboda 'yar masu gida"
Murtalah yace "ƙwarai kuwa, dan ba ƙaramin ci musu mutunci take ba saboda shi, amma dagaske an saka nemo inda yake?"
Isa yace "wallahi dagaske nake, sedai sam kamar yasan an sani fafur yaƙi gayamin, shegen wayone dashi kamar dila"
Nura yace "ba ɗan sanda bane, kai ka isa ka masa wayo nan da nan, ai kaima kasan baka isa ba"
Isa yace "kamar ya ɗan sanda wai?"
"Au kai a labaran da aka sanar ba gani bane, to ɗan sandan farin kaya ne, aikin bincike yake a gidan nan"
Isa yace "la'ilahaillalah illalah, dagaske? Yo aini ban sani ba"
Murtalah yace "to an barka a baya, baka san kanun Labaran ba kam, ɗan sanda ne ai shiyasa hankalin mutan gidan ya sake tashi"
Isa yace "tir ƙashi, amma wannan anyi munafuki, shine be taɓa gayamana ba, muka zauma dashi muyi ta sakin baki"
Nura yace "to mutan gidan ma basu sani ba, balle kai ance maka jami'in sirrine kawai seya zo ya fara gayamaka ai shi ɗansanda ne? Saboda be san aikinsa ba kobe san ciwon kansa ba? Kai dai Isa naga ranar sa zaka waye"
Haka suka cigaba da surutansu dai.
Ita kam Amal ta tsunduma a kogin tunanin me yakamata tayiwa Alhaji Haruna ta huce, da wani makami yakamata ta yaƙeshi ta ɗau fansar budurcinta daya rabata dashi? Sam ta kasa ko da cin Abinci, se uban tunani da koke koke, idan ta kulle kanta a ɗaki se tayi me isar ta, dan sam bata san me yakamata tayi masa bama, ta gama barazanar da zata yi masa amma bata san meye zata yi masan ba ta huce, gashi ta kasa gayawa kowa wannan labarin balle ta samu shawara, gani take zata tinawa kanta asiri ne a banza a wofi, tazo ta kasa samun mafita kuma, ta kalli hannunta dake nan naɗe da bandeji ga goshinta ma, ta lumshe idanunta tana jin zafi a zuciyarta.
Ramlah ta shigo ɗakin tace "Amal kizo ga matan Alhaji Harun nan sunzo dubaki"
Kallon Ramlah tayi kamar bata gane me tace ba, Ramlah tace "ko bakiji bane?"
Amal tace "Ai abunne naji wani iri, sun sanni ne daza suzo dubani?
Ramlah tace "oho muku, sun san Mummy ai, idan ke basu sanki ba"
Amal tayi tsaki tace "ba inda zani"
Ramlah tace "meyasa?"
"haka kawai, bazan zo ba, ki koma ki san abunda zaki gaya musu"
Tai maganar tare da kwanciya, Ramlah ta ɗan taɓe baki ta juya ta fice.
Amal ta sake jinjina rashin kunya, da iskanci irin na Alhaji Haruna, saboda ya gawurta har matansa ya turo su dubata, to suce mata me? Ji tayi kamar taje ta tona masa Asiri a gurinsu, amma meye shedarta? Taja tsaki tai shiru tana ci gaba da tunani.
Kamar wadda aka mintsina ta miƙe da sauri, dan seda ta kusa fama hannunta, ta tako a hankali ta fito, a hanya suka haɗu da Mummy, dan Ramlah ta gaya mata saƙon Amal, Mummy tace "da meyasa kikace bazaki fito ba?"
Amal tace "gaba ɗaya jikina ciwo yake, bana son hayaniya ne, sedai kuma naga babu daɗi, shiyasa nace kawai bari inzo mu gaisa"
Mummy tace "da dai yafi"
Suka fito gaba ɗaya falon, uwargidansace se Amaryarsa wadda take yarinya sosai, Amal ta ƙaraso suka gaisa, sukayi mata ya jiki, Amal ta amsa tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.
Da zasu tafi uwargidan tace "ga mukullin mota yace a baki, gata can yace a baki tunda taki ta lalace, Allah ya ƙara sauƙi"
Amal tai murmushin takaici tace "Amma fa nagode sosai, ai masa godiya ace masa naji daɗin motar nan fa, sannan ina nan tafe karɓar mukullin gida kuma"
Basu kawo komai ba, tunda ce musu yayi 'yace a gurinsa tunda sun san Hajiya Halima, Amal ta karɓi lambar wayarsu, tace sa dinga gaisawa.
Nurat tana zaune suna hira da Mummynta, ta gwada layin Anwar harta gaji amma shiru bata shiga, tun abun baya damunta har ya fara damunta, ta kalli mahaifiyarta tace "Mummy fita nake son yi fa"
"Kije ina?"
"Mummy duk inda ta kama, tunda aka samin doka yau kwana nawa ban fita ko ina ba, gashi ina buƙatar in ɗan fita ɗin in rage zafi, kullum ina cikin gida kamar wata mara gaskiya"
Mummy tace "nidai babu duwana, duk abunda kika jawa ka ki shikenan ba ruwana, kin san yadda kuka ƙareta dashi wancan karon dai"
"Mummy gidan Daula nake son zuwa, ina sin jin ko lafiya, layin Yaya Anwar baya shiga fa Sam"
"gidan Daula ko? Sekin dawo tunda baki da hankali"
"Mummy ba haka bane, ai gaida me gaishe ka ko baze amsa ba, amma tunda hakane, bari in jida zuwan bdk Khalil, idan yazo ya biya ya dubamin ko lafiya"
"Ke wani Khalil ɗin, baki san ranar da yazo ya tarar dashi ba kirana yayi yana masifa ba, wai zaryar me Khalil yake masa a cikin gida ba? Wai in dakatar da shi da zuwa ba"
Nurat tace "to Mummy ke kuma baki ce masa komai ba, sannan me Khalil yayi masa?"
"Oho kin san halinsa na rashin gaskiya ai, shi duk wani motsi seya zata bin diddiginsa ake, shiyasa kullum bashi da nutsuwa ai, shima dole zanyi masa waya, ya rage yawan sintir a gidan nan, ya bari se an kwana biyu yazo"
Nurat ta dafe kai tace "Ohh my God, ba dai gudun tinon Asiri yake ba, Insha Allah ya gamu da shi kenan, in Allah ya yadda se asirinsa ya tonu"
"Ke rufemin baki, kar yazo ya tarar dske kina wannan maganaganun, ya zata wani abun muke shiryawa"
A fusace Nurat ta miƙe ta e "to ya zata iɗn mana Mummy, na gajiya walilahi, am tired"
Ta juya ta bar falon ranta a ɓace, zuciyarta na wani irin tafasa tana tururi.
Yusuf na zaune yana zaune, Widad na kwance akan cin yarsa, yana ta wasa da gashin kanta, tana masa hira sedai gaba ɗaya hankalinsa baya kanta, ya tafi can duniyar tunani, ƙirjinsa nata bugawa haka kurum, yaka sa gank dalikin bugawar ƙirjin nasa, "Yoseef" ta kira sunansa, da sauri ya dawo hayyacinsa yace "Na'am"
"Me kake tunani ne?"
Yace mata 'bakomai "
Ta gyara kwanciyarta tace "Yuzarsef, kwana biyu Saleh bezo na, nifa hankalina yayi gida, gaba ɗaya na ɗan fara damuwa tunda yake zuwa be taɓa cemin komai akan mahaifina ba, zuciyata na son ganin mahaifina, ina yawan mafarkinsa ina son jin abunda ke faruwa gaskiya"
Seda gaban Yusuf ya faɗi, dan Saleh ha tabbatar masa babu wani sahihin kabadi har yanzu akan ɓatan mahaifinta, gashi ita bata sani bama, ya dake yace "tabbas nima ina ta fama da kokwanto a raina, ina son sanin meke faruwa a gida, gashi naga kwana biyu Saleh bezo ba"
Tace "hakane, dukda ni ba shiga sabgarsa nake ba, amma dole zan tambaye shi ya Daddyna yake, in dai lafiya ƙalau ne, baze jure tsawon wannan lokacin be gannj ba, dase yazo har nan kota halin yayane, amma tunda naji shiru something is going wrong somewhere, gidanmu nake son komawa "
" Insha Allah nothing is wrong anywhere, komai yana tafiya dai dai, am yakamata mu koma gida haka kam"
Tace "Allah yasa hakan"
Yace "Ameen, but Baby ta yaya zamu tabattarwa da al'umma Aurenmu, meye shedarmu?"
Widad tace "Allah"
Yace "hakane Allah sheda ne, amma baze yuwu mu gayawa mutane haka ba, dole mu nuna shedar aure mukayi, tunda au can babu wansa yasan hakan"
Widad tace "karka damu, Saleh ya sani, ga al'ummar garin nan da muka zauna tare dasu, suma sun isa sheda ai"
"Hakane, Allah yayi mana jagora"
Tace "Ameen"
Alhaji Musa yana zaune a ɗakinsa yana cin Abinci, ya ɗau waya ya kira Nurat yace yana son ganinta a ɗakinsa, Mamanta ta kalle shi tace "lafiya kuwa? Ina fatan dai ba wani laifin tayi maka ba?"
"ina ruwanki ne? Nida 'yata bazan kirata ba, ki zuba ido kawai"
Tace "Ai gara in dingayi ina bin ba' asai, saboda naga kai abun naka se a hankali gaba ɗaya"
Nurat tayi sallama ta shigo da dogon hijjabinta a jikinta, yace "Bacci kike ne?"
Ta girgiza masa kai tace "A'a salla nayi"
Yace "madalla fatan a nayiwa Daddy addu'a"
Ta jinjina masa kai yace "yawwa 'yar gidan Daddy, dama ba wani abune yasa na kiraki ba, zan sanar dake jn the next couple of weeks zaki koma Karatu"
Nurat tace "A ina kenan?"
Yace "can inda kika baro mana abroad, na nema miki imperial College London, kije kiyi business administration ɗin da kike so a can"
Girgiza masa kai tayi tace "Amma Daddy ai ba haka mukayi da kaiba, ka tambayeni nace maka ni a Nigeria nake son in cigaba, ka amincemin kuma yanzu kace ba haka ba"
Yace "look Nurat, ina nema miki sauƙi ne da kuma safe environment, inda zakije kiyi karatun ki cikin nutsuwa da kwanciyar hankali"
Tace "Nan ma akwai nutsuwa da kwanciyar hankali ai, ni dai kawai ka ƙyaleni a nan, bana son zuwa"
Aikuwa ya harzuƙa yace "ke, nine zance ga yadda za'ayi kice ke ba hakaba? Waye ya haifi wani tsakanin nida ke?"
Nurat tace "kai ka haifeni, amma kaima ka cika Alƙawari mana Daddy, baka gudun yadda tarbiyyata zata kasance, ni ina can ku kuna nan ni gaskiya bazanje ba"
Ya kalli Maman Nurat dake gefe tana jinsu yace "wato ke kike ziga yarinyar nan take rashin mutuncin da taga dama ko? Idan ba hakaba ya za'ayi ina magana tana magana?"
"Malam babu ruwana ni, 'yarka ce yau da gobe ai tafi ƙarfin wasa, ka fiye son kanka da yawa, shiyasa tun yarinyar nan na maka biyayya harta zo ta dena yi maka saboda son zuciyarka, kuma nima gaskiya ban yadda inyi nesa da ita ba, tunda mun baro ƙasar ma meye kuma ita za' a maida ita"
Alhaji Musa yace "lallai ba shakka, na ƙara tabattar da cewa ke kike ziga yarinyar nan, in faɗa ki faɗa tana gani ai dole itama ta fara, to bari kijin in gayamiki tafiya daram, seta tafi dole ta bar ƙasar nan taje inda na nema mata karatu"
Nurat ta fashe da kuka tace "ni gaskiya bazani ba, kuma idan aka takura sena je, wallahi barin gidan nan zanyi, dama naga yanzu ba'a ƙauna ta, tunda har yunƙurin rabani da rayuwata akayi" tai maganar tana ficewa daga falon, tana ji yana ƙwala mata kira amma tai banza dashi tai tafiyarta ko waigowa ba tayi ba.
Yusuf yana kwance har wajen shaɗayan safe, idonsa a lumshe yayi rigingine yana jin yadda gabansa ke cigaba da faɗuwa akai akai, Widad ta shigo ɗakin ta fito daga wanka tace "Yoseef, wai ba zaka tashi bane haryanzu shaɗayan rana, seka sa Hari tazo tana gayamin magana ko? Ina jinta shekaranjiya wai na fiye jaraba goma na safiya ina rufe ƙofa saboda shegen sa ido irin nata"
Yusuf ya kwashe da dariya yace "Ai gaskiya ta faɗa ba ƙarya ba, hakane abunda ta faɗa waike dole sekin samo Baby ba"
Widad ta buɗe baki tace "lallai Yoseef sannu, hakama zakace ko? Kaifa kace in rufe ƙofa sanyi kake ji, shine zakamin sharri"?
"Ba wani sharri malama, ni bance ki rufe ƙofa ba"
Widad tace "Ikon Allah, ni nama rasa me zance maka"
"dole ki rasa mana, kuma yau bazan kwana akan katifarki ba, a ƙasa zan kwana"
"Kaje kaita kwanan mana ina ruwana?"
"A'a dai karkizo kina min kuka, wai kai Yoseef meye haka? Dan Allah kazo ka kwanta" yai maganar yana kwaikwayon muryarta.
Tace "Nikam na shigesu a gurinka, Allah ya shiryeka"
"to kice ba'ayi haka ba mana"
"Aini bazan sake magana ba, nayi shiru"
Yai murmushi ya maida idonsa ya lumshe, ta ɗan ƙura masa ido, ya ɗan faɗa sedai masha Allah Yusuf ba dai kyau ba.
Tai murmushi tace "Mutum da hanci kamar an zana cartoon"
Yace "Kyau yai miki yarinya, shiyasa kike min ba'a"
"Ba wani kyau a nan gurin, wannan zanƙalelen hancin kaman cartoon"
"Kyaji dashi dai, yabawa kika yi"
Tazo tasa hannu ta matse masa hanci, Yusuf yace "ko ki sakarmin hanci, ko kuma yanzu in ɓaro ɗan dake cikin ki"
Da sauri ta cika shi tace 'yi haƙuri "
Yai dariya yace " Yarinya baki da komai a wannan cikin naki "
Ta murguɗa masa baki tace "aini nasan akwai"
Tai maganar tana tura baki, yayin da ya bita da kallo yana jin sonta na ƙara ninkuwa a zuciyarsa, idan ya tuna lokacin da take garashi da izza da rashin mutunci, ga gefe guda azabtuwa da soyayyarta daya dingayi ba tare da ta sani ba, idan akace masa akwai rana da zata