Showing 138001 words to 141000 words out of 209297 words
zafim wannan ba, bayan wanda aka mata da bakin bindiga, ta banƙare ta ƙwala ihu, take fatar jikinta ta tashi tai jawur kamar an ƙonata.
Tana zubar da hawaye tana girgiza kai, ji take kamar an saka mata wuta a bayanta, saboda azabar bala'i, ya sake zage ƙarfinsa ya shiga zuba mata, tun tana iya ihu harta kasa, se nishi da take yi yasa ƙafarsa da babu ciwon yai ball da ita, ai dukan da yayi mata be mata ciwo ba, kamar yadda yai ball da ita da ƙafarsa, ya ƙaraso inda take yana huci yace
"zaki gayamin ko bazaki faɗaba"
Ta ɗaga jajayen idanunta tana kallansa, ta shammaceshi ta kafa masa faratanta a inda aka masa ɗinkin nan a cinya, dayake naɗe ƙafar wandon yake, saboda karya sosai masa ciwon yaƙi warkewa.
Aikuwa haka ya buɗe baki ya ƙwala ihu shima, dan har jini gurin ya fara, ta janyo wuƙar nan da ta ji masa ciwo da ita akan taga, tace "wallahi idan baka fita daga gurin nan ba kashe ka zanyi, sena kashe ka wallahi '
Tuna yadda ya sha yanka da wuƙa ne wancan lokacin yasa shi fita da sauri yana faɗin " dawowata ta biyu bazata miki daɗi ba, zaya kasance dawowa me muni a gare ki "
Ya fita hannun sa riƙe da cinyarsa, tana masa wani irin zugi, har yanzu Widad ba tayi laushi ba, halinta be canza ba na baƙar zuciya da taurin kai na jaraba, gashi dukda dukan databsha da rashin lafiyar da take ciki, be hana ta fama masa ciwon nan ba, dan gashi har ya fara tstatsafo da jini, ta fama masa yai ƙwafa ya fita yana tunanin yadda zewa Widad izaya irin wadda ba'a taɓa yi mata ba, wadda zata tirsasata yin abunda yake so.
Ita kuwa Widad zama tayi tana kuka, saboda azabar raɗaɗin da jikinta ke mata saboda dukan da ta sha da tio, jikinta duk yayi tsami, tai kuka tai kuka harta fara tari daga nan kuma se Amai, gashi ba komai a cikin nata, dan baka ta dinga yunƙuri amma babu abunda yake fita, se miyau ga ɗaci da maƙogwaronta yake, se kuma ta shiga aman jini, haka ta dinga kakarin aman nan gwanin ban tausayi, abun da bata saba ba ya sameta, taji ba abunda take so banda ta samu ƙanƙara ta matsa lemon tsami ta sha ba.
Tan nan ta kwanta akan tiles, tana jin yadda sanyin ke ratsata, jikinta kuma yana ɗaukar zafi.
A hankali aka turo ƙofar ɗakin nata, ta tashi zumbur dan zatonta Bulama ne, wannan me aikince ta shigo cikin sanɗa, taga Widad a mawiyacin hali, dan tana jiyo kakarinta tun ɗazu.
Widad zata yi magana tai sauri ta girgiza mata kai, cikin ƙasa da murya tace "karki ɗaga murya mana, kinga Alhaji Bukar yace kar a kuma baki Abinci se sau ɗaya a rana, ya gindaya mugayen sharuɗa akanki, ni kuma ina jin tausayinki zan ɗan temaka mikine, ga Abinci na kawo miki kici"
Widad tace "bana ci, ki bani ruwa me sanyi sosai, ki bani in sha"
"A'a, kici Abinci mana, cikinki bakomai ga jikinki ya ɗau zafi sosai ki daure"
Ta tirsasa Widad yaci Abincin kaɗan, ta bata ruwan sanyi kamar yadda ta buƙata, sannan tai mata sallama ta fita.
Widad ta koma kan tiles ɗin nan tayi kwanciyarta, fatar jikinta duk jini ya kwanta akan fatar ta, ta lumshe idonta ga sanyin A. C gana tiles haka tai kwanciyar ta abunta.
Umma jikinta sauƙi an sallameta daga Asibiti, sedai jikin nata ya kasa ƙwari, saboda tsabar damuwa da tashin hankali da take ciki, ta rame sosai tayi zuru zuru duk ta fita daga hayyacinta, bata iya cin Abinci sam sedai abunda ba'a rasa ba, kullum tana cikin Addu'a ne, dan da kanta taje ganin Yusuf amma aka hanata ganinsa, haka ta dawo gwiwa a saɓule.
Tana zaune ta idar da sallar la'asar, tana lazimi idonta duk yayi ja saboda rashin bacci, sallama taji anyi ta amsa sedai kafin ta bada izinin shigowa Suka shigo ɗakin gaba ɗaya, ta ɗaga kai ta kallesu tace "Sannunku da zuwa Anty Asma'u"
"A'a riƙe sannu da zuwanki, zuwa mukayi muyi kallo sannan mu jajanta, yau dai kinga maganar da muke tayi tun shekarun baya, tsintacciyar mage bata mage, yau dai shege ya ɗakko miki magana, dama ina shege zeyi wani abun arziki, kina ta wahala kika saka ɗan uwanmu yaita wahala daku, ke juya shi kuma shege yau dak gashi ƙarshen Alawa ƙasa, ya zama gagarumin ɗan ta'adda ya sace 'ya yaje yai mata fyaɗe yana neman kuɗin fansa, Allah wadaran naka ya lalace "
Balaraba tace " Ameen dai Anty, alhakinmu ne ya kama su, da tasa ɗan uwanmu ya dinga wahala dasu, yana wulaƙantamu yau gashi kina kuka da idonki, kuka kam yanzu kika farashi, saura ke se sunzo sun haɗa ke dashi tukuna, tunda idan ya samo tare kuke ci"
Suka dinga zazzage mata rashin mutunci iri iri, ta inda suka shiha ba ta nan suke fita ba, Umma ba tace musu komai ba ta sunkuyar da kai kawai, ta cigaba da jan carbinta na tare da ta kulasu ba.
Suka yi suka gama san ransu, sannan suka tafi Umma ta girgiza kai kawai, tana share hawaye.
"Khalil ya ake cikine? Ka samu ganin Widad ɗin kuwa?"
Khalil yace "Nurat, ban samu ganin Widad ba, bata gidan Alhaji Bulama ance wai bata da lafiya an kaita Asibiti, amma ɗan nasa be gayamin ina take ba, wai shima be sani ba, nace masa zan kuma komawa inji abunda ake ciki"
Nurat tace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Yaya Khalil an kusa shiga kotu fa, Allah yasa dai a gano ta, na damu sosai dan Allah ka koma da wuri kaji"
"Shikenan insha Allah, karki damu zan koma inga yadda zamu yi dashi"
Alhaji Haruna ya kira layin Amal ba adadi amma taƙi shiga, ya rasa me yarinyar nan tayi masa ranar da tazo, ta barshi a yashe, yana ta tunanin ne kiran Alhaji Musa ya shigo wayarsa ji a sanyaye ya ɗaga.
Alhaji Musa yace "Haruna ina ka shiga ne? An kira layin ka ba adadi amma taƙi shiga, gashi baka bawa Bukar takaddar nan ba gashi za'a shiga kotu, kasan fa idan wani ya ɗau takaddar nan tsaf zamu shiga matsala, har saƙo aka turo maka na zamuyi taro amma baka ɗaga ba"
Alhaji Haruna yace "bani da lafiya ne, banga saƙon ba"
Alhaji Musa yace "ban yadda ba, akwai wani abu a ƙasa, ka gayamin ko menene mana? Kasan halin Bukar wallahi ze iyayi maka Akuya kasani sarai"
Alhaji Haruna yace "a bar zancen kawai, zanzo in same ka zamuyi magana"
"Shikenan, seka zo amma kasan yarinyar nan ta gano Bukar kuwa"
"Ahh haba dai garin yaya kuma?"
"oho masa dai, wallahi tayi masa sheda da wuƙa, ta yanke shiba fuskarsa da cinyarsa, kai baka ga yadda ya sha ɗinki ba, gaba ɗaya halittun fuskarsa sun sauya"
Alhaji Haruna yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Taɓɗijan dara taci gida kenan, to wani mataki ya ɗauka"
Alhaji Musa yace "eh to, yace tunda ga riga ta gano shi yasan yadda ze da ita, sedai kawai idan mun haɗu da kai tukuna, mayi magana mu tattauna maganar bazata yi ta waya ba, zan shiga meeting ne yanzu"
"Shikenan, sena zo tukuna"
Ramadan ne yai sallama ya shiga falon mahaifinsa, yana zaune yana kallon labarai, Ramadan yace "Daddy barka da hutawa"
Bulama yace "Yawwa barka, sannunka wai ni ina ɗan uwanka Fahad ne, yaushe rabon da in sashi a idona"
Ramadan yace "Daddy kasan halinsa fa, wallahi yau kwanansa huɗu baya gidan nan, nima ban san inda yake ba, babu wanda yayiwa sallama, dama hana yin haka fa, yakan kwana biyu ma baya gidan nan"
Bulama yace "da kyau, ze gauraya dani kuwa, dan ubansa"
Ramadan yace "Yawwa Daddy, nace a wane Asibitin Widad take ne, Nurat ta aiko a gayamata imsa take, tana son ganin tane kasan ƙawarta ce"
Bulama yai shiru yana nazarim Ramadan sannan yace "wata aiko?"
"Wani ne, nima ban sanshi ba, wai ko Khalil ne kowaye, ya cemin ɗan uwanta ne shi, yana so zeyi magana da Widad ne, Nurat na son sanin halin da take ciki"
Bulama ya jinjina kai yace "rabu dasu kawai"
"Daddy saboda me? Aikowa yasan tana hannunka, yakamata ka faɗi Asibitin da take, saboda masu dubiya sannan wataƙila 'yan sanda zasu samu wani rahoton daga gareta"
"Kai Ramadan ka kiyaayeni, ka fiye shisshigin tsiya wallahi, to ban saniba tunda nace maka tana Asibiti amma kama cigaba damin tambaya"
"Allah ya baka haƙuri, amma Daddy wannan yakan fa dake fuskarka da ƙafarka? Tun shekaranjiya nake son in tambayeka amma se inga kana bacci, na tambayi Mummy tace itama bata sani ba"
Bulama yace "Accident ne na samu, tashi ka bani guri tafi maza ka bani guri in huta"
Haka ya fatattaki Ramadan, ya kulle ƙofarsa ya ɗakko wayarsa ya kira Alhaji Musa, ya ɗaga yace "Allah ya temaki Bukar Bulama"
Alhaji Bulama yace "Musa kasan da ana shirin samun ɓaraka daga gidanka kuwa?"
"kamar yaya kenan?"
Bulama yace "Waye Khalil a family ɗinka kona matarka?"
Alhaji Musa yace "ɗan yayar Babar Nurat ne, cousins ne shida ita"
"Shine ta turoshi gidana wai azo agane mata ya Widad take? Wai aga halin da take ciki, da sanin ka akayi haka?"
Alhaji Musa yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wallahi ban sani ba saboda haka fa na kirsheta a gida, ko nan da cam bata zuwa, na hanata zuwa ko ina Sam, ban san yadda akayi tayi hakan ba, amma ka ƙyaleta zanyi maganin ta, zan ƙwace wayoyinta sannan in turata ƙasar waje, bakomai zan ɗau mataki a kai, hakan bazata sake faruwa ba"
"gara dai kayiwa tufkar hanci tun kafin inyi abunda yakamata da kaina, karka ƙara turomin wani yazo yana neman Widad, ka jawa 'yarka kunne"
"Insha Allah, hakan bazata sake faruwa ba, zanyi abunda ya dace base ka ɗau mataki da kanka ba"
Bulama yace "da dai yafi"
Litinin, tushen aiki kotu ta cika maƙil, domin ji da ganin yadda shari'a zata kaya, musamman shari'ar da mutane suke cike da sonji da ganin yadda zata kaya, wato shari'ar Yusuf Bashir Maitama, ɗaga jajirtaccen ɗansanda wato Bashir Maitama.
Umma ya halarci zaman kotun nan, dan shine kaɗai hanyar da zata ga Ɗanta Yusuf, 'ya' yan Bulama su Alhaji Munir, da Hajiya Halima da 'ya' yanta duk sun halarra a kotun.
Umma tana nan zune tana waige waige aka shigo da Yusuf, hannunsa ɗauke da sarƙa, 'yan sanda sun taso shi a gaba, yadda yake jan ƙafa da ƙyara da yadda jaabiyarsa tai baƙiƙirin saboda datti, ga fuskarsa duk a kumbure, kai da gani base an faɗa ba kasan Yusuf a wahala yake, Umma ta ƙunshe fuskarta a mayafinta ta fashe da kuka.
Haka akaje aka tsayar da Yusuf, 'yan sanda suka kewaye inda yake, Yusuf ya ɗaga kai yaga yadda kotu ta cika maƙil, masu masa kallon banza nayu, masu na tausayi suna yi, idonsa ya sauka akan ummansa wadda idonta yayi fururu saboda kuka, ya sunkuyar da kansa yana danne hawayen dake shirin zubo masa Allah kaɗai yasan me Umma takeji a rantava yanzu haka.
Aka karantowa Yusuf ƙunshin tuhumar da ake masa, amma Yusuf ya musanta yace "shi bashi ya sace Widad ba"
Barrister Saminu ya miƙe, ya gabatar da kansa a matsayin lawyoyin gwamnati masu gabatar da ƙara sannan yace "duba da yadda wanda ake zargi ya musanta abunda ake tubumarsa dashi, muna neman wannan kotu me Alfarma data bamu dama muje mu tattara hujjojinmu da zamu gabatar a gabanta, wanda zs tabattar da abunda ake zargin wanda ake ƙara ya aikata"
Me shari'a Justice Abdallah A dutse yace "duba da yadda lawayan gwamnati ya nemi a basu dama domin kawo shedunsu, wannan kotu ta ɗage sauraran wannan ƙara zuwa goma ga wata me kamawa, sannan wannan kotu tayi umarni da akai wanda ake zargi gidan gyaran hali zuwa lokacin da za'a sake wannan zama"
Haka aka tashi a shria'r yau, aka taho da Yusuf za'a sashi a motar 'yan sanda,' yan jarida sukayi dandazo amma aka hansu magana da shi, Umma ta taho da gudu Suleiman ma cikin hanzari ya nufi inda su Yusuf suke, Umma tana kuka tana "dan Allah ku barni in ganshi ko sau ɗayane, ɗana ne watana kusan biyar rabona dashi, ganinsa kawai zanyi Suleiman dan Allah kace su bari in ganshi"
Suleiman yace "Dan girman Allah ku bar baiwar Allah nan taga ɗanta, ko sau ɗayane uwace kunsan ba zata iya jurewa ba, dan Allah ku bari ta ganshi"
"Ba a bamu wannan damar ba, seta bari idan mun kaishi prison taje can idan sun batta seta ganshi"
Ayshercool
07063065680
11/23/21, 8:06 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
130_131
Haka aka ja mota aka tafi da Yusuf, umma tana ta zabga kuka, Yusuf ma ya sunkuyar da kansa yana kuka a cikin motar nan, shiba kaishi gidan yarin bane damuwarsa, kukan da Ummansa take shine ya tsaya masa a ransa.
Dan abun takaici, 'yan jarida sukazo suka kangawa Umman Abubuwan magana sun antaya mata tambayoyi, Suleiman ya janyeta suka hau mota suka tafi, ba tare da tace uffan ba, amma a haka suka naɗi muryarta tana kuka tana ambaton Allah dan suji daɗin yayatawa a duniya.
Haka aka watse a zaman kotu, kowa da abunda yake faɗa, wasu su faɗi alkhairi wasu kuma su faɗi som zuciyarsu.
Aka wuce da Yusuf gidan gyaran hali, aka bashi kayan fursunoni, aka shigar da bayanan sa, sannan aka kaishi ɗakin daze zauna, mutane masu laifi sunyi su sittin a ɗaki ɗaya, ga rashin isashshen vantilation, ga cunkoso ga tsamin dauɗa da wasu suke yi, gaba ɗaya abun se godiyar Allah haka akaje aka gwamutsa Yusuf a cikinsu.
Bayan an tashi daga zaman kotune, Bulama yabi Justice Abdullah gidansa, aka masa iso ya shiga, yana ganinsa A dutse ya faɗaɗa murmushinsa yace "kaine da kanka haka baa aike ba?"
Bulama yace "Ai saƙonne, yafi da cewa in isar dashi da kaine ba aike ba"
"to barka sa zuwa, ya kaga zaman shari'ar tamu na yau?"
"To Aini dutse banyi zaton haka ba, muda muke da shedu tuni mun tanada, na gaskiya dana boge amma kace wai ka ɗage sauraren ƙarara, ina laifin a fara gabatar da shedun, nifa da wuri nake son ayita ta ƙare fa, ayi a yanke masa hukunci in rufe babainsa, saboda in dai yana nan ze hanani rawar gaban hantsi, dan gaba ɗayansa matsalane a gare ni wallahi "
A dutse yayi murmushi sannan yace " hmmm Bukar Bulama, ai ita shari'a saɓanin hankkalice, bar ganin ka saye ni ka saye lawyoyi da hukunar 'yan sanda, karka manta akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu, na kare haƙƙin ɗan Adam, akwai lawyoyi masu zaman kansu, dukda wasu abubuwa da akayi da suke fito da laifin shi yaron ƙarara, amma duk da haka zasu saka ido akan shari'ar, za' a samu wanda zasu bibiyi shari'ar, dan haka muje a sannu, ina sane nayi hakan komai a sannu akeyinsa cikin hikima da ƙwarewa irin ta aiki "
Bulama yace " Aini gaba ɗaya hankalina baze kwanta ba muddin ba a gama shari'ar nan ba, yaron nan fa ba ƙaramin bincike yayi akaina ba, kuma bana son Daula ya bayyana ba'a gama shari'ar nan ba"
"Calm down mana, waini haryanzu babu labarinsa, babu wanda yasan inda yake ne? Abunfa da mamaki"
"to waye ya sani, anneme shi am rasa kamar wani kuɗi, duk iya bincike na saka anyi amma babu labarinsa, ni dai kayi kayi ayi gaggawa a ƙarƙarw shari'ar nan da wuri, ka yanke masa hukunci, kuma hukunima me tsanani wanda ze ƙare a prison"
Justice Abdullah yai murmushi yace "Bukar Bulama, ai komai akan doka akeyinsa, dukda munawa dokar karen tsaye wasu lokutan, saboda irinku da mukewa alfarma, amma karka damu insha Allah zanyi duk yadda zanyi in ƙarƙare shari'ar nan, ba da daɗewa ba yanzu se Allah ya kaimu bayan sati uku zamu sake zama "
"Gara dai ayi a sake zaman, dan Allah karka zake jan lokaci dayawa, bazan iya jira ba, sonake a ƙare komai"
"Shikenan, kaje ka kwantar da hankalinka, nan kusa zan ƙarƙare shari'ar hankalinka ya kwanta"
Bulama yace "da dai yafi ai"
A dutse yace "Amma, wai ya akayi kaji wannan raunin haka? Gaba ɗaya kamaninka sun sauya kayi wani iri, fuskarka ko ina ɗinki"
Bulama ya miƙe yace "karka damu da wannan, ƙyaleni kawai daga nan wani guri zanje, ina nan ina sauraren yadda zata kaya"
A dutse yace "shikenan, nagode sosai ka gaida gida"
Sukayi musabaha sannan Bulama ya tafi.
Nurat! Nurat!! Alhaji Musa ya shigo yana ƙwalawa Nurat kira, ta fito falo tace "Gani"
"Ubanwaye yace ki aika wai aje a duba miki Widad?"
Ta kalle shi tai shiru, ba tace komai ba.
"Ba magana nake miki ba? Ubanwaye yace ki aika wai a dubo miki ita babarkice ita meye haɗinki da ita?"
Yai maganar yana zazzaro ido kamar ze daketa.
Nurat ta girgiza kai tace "A'a Daddy nifa ba da wani abu na aika ba, kawai naga ƙawata ce kuma ga abunda ya sameta, ni kuma ka hanani figa, shine nace aje a dubamin"
"Ƙawarki ɗin banza da ta wofi, kuma wallahi ki kiyayeni da wannan yaron Khalil, idan kika bari na sake ganinsa a gidan nan sena ci mutumcinsa, sannan kije ki kwaso min wayoyinki ki kawomin su nan, kuma ko kina so ko bakya so sati me zuwa zaki bar ƙasar nan "
Mahaifiyar Nurta ta fito tana cewa," Kwanan nsm bam san meyasa kake wannan abubuwan haka ba, meye laifi dan kawai tace aje a duba mata ya take? "
" Idan ina magana kika ƙara sakamin baki wallahi sena ci mutuncinki, na gayamiki kin sani