Showing 168001 words to 171000 words out of 209297 words

Chapter 57 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

747

saboda rashin nasaba ba, sedai cikin hukuncin Allah ya auri yarinyar da zuciyarsa ta mato a sonta, dukda nisa da ratar dake tsakanin su, yarinyar da manyan wanda suka isa ma basa gabanta, soyayyar ma bata yadda da ita ba, amma Allah ya ƙaddara Aurensu, har suka yi zama cikin farin ciki, ya dinga tuna irin Shagwaɓarta wauta da yarinta wasu lokutan, ya tuna lokacin da take koyar tankaɗe, da sanda take wa Abincin garin kallon banza, da yadda ta dage ita seta samu ciki, da irin kallon da take masa idan ya tsokane ta.
A hankali ya sake lumshe ido yana murmushi, sekuma ya tuna yadda ta shiga damuwa daya bata labarinsa, da yadda ta dinga kururuwa tana kuka tana gaya masa tana sonsa lokacin da aka kama shi a garin, da yadda taje kotu ta bada sheda akansa, ga shekarun da aka yanke masa a gidan yari, ga abunda ta rubuta masa kawai se yaji ya karaya hawaye ya shiga bin gefen idonsa, baya tunanin ze sake wata rayuwa me daɗi a nan gaba, mussman kasancewa da Widad a inuwar Aure.

Da ƙyar likitoci suka samu Nurat ta dawo hayyacinta ta samu bacci, aka sa mata ruwa, sedai harta farfaɗo ɗin numfashinta da vital signs ɗinta suka daidaita bata gane mutane sosai, saboda ta galabaita an samu dai bacci ya ɗauketa cike da fatan idan ta tashi zata iya dawowa hayyacinta gaba ɗaya, mahaifiyarta kuwa gaba ɗaya har yanzu ba'a gano kanta ba, tana kwance ne kawai, numfashi ne kawai a ƙijinta, banda haka babu abunda yake aiki a jikinta, sam bata san abunda ke faruwa ba, shi kansa numfashin nata da ƙyar take yinsa wasu lokutan, saboda ta zubar da jini sosai, kuma ana kyautata zaton ta samu rauni a cikin kanta, sakamakon buguwa da tayi, likitoci sun rubuta mata hoton Ƙwaƙwalwa dan tabattar da abunda yake damunta.

Abu kamar wasa, jini yaƙi tsayawa Amal, se aikin zaryar banɗaki take, jini se zuba yake babu ƙaƙƙautawa, ta rarrafa ta haɗa Abinci tana ci kota samu sauƙin wannan wahalar haka, zuciyarta tana ƙuna akan yadda Alhaji Haruna ya cuce ta, Hajiya Halima ta fito falon ta zauna ta dafe kai ta kalli Amal tace

"wai kuwa lafiyarki ƙalau kuwa? Gaba ɗaya kin wani ɗashe kinyi fari ƙal, kamar baki da jini a jiki, ko baki da lafiya ne?"

Amal tace "lafiyata ƙalau, period kawai nake shiyasa"

Hajiya Halima tai ajiyar zuciya tace "Amal kin kuwa san abunda Bulama yaimin?"

"A'a sekin faɗa"

"wai an gano inda Anwar yake, amma yace wai a kasheshi saboda karya tona Asiri"

Da sauri Amal ta kalleta tace "A kasheshi kuma? Me me kikace masa?"

"Naje har gidansa jiya da daddare, na ƙare masa tatas, nace wallahi aka kashe min ɗana seya fanshi ransa da nasa ran kona 'ya' yansa"

Amal tabi mahaifiyarsu da kallo, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, duk mahaifiyarsu ta ɗaiɗaita rayuwarsu da kanta, kowa yana karɓar nasa kason ɗaya bayan ɗaya.

Ramlah ce ta fito tana tangaɗi, tana magana cike da maye ta tsaya a tsakiyar falon tace  "Wai ni.... Waini Fahad baze Aureni bane... Bazaki ce ya aureni ba ko? Wa.. W.. Wallahi kuwa bazan dena shaye2 ba tunda ya lalatani, ku.... Kuma... Kumaaa ai shikenan tunda nasan Na sakawa Bulama cutar tunda shima ya sakamin... Wallahi idan baka Aureni ba sena sakawa Wannan yaron Ramadan ma, idan yaso kow... Ko..... Kowama ya samu ni za'ayiwa hauka? Ya.. Ya ɗauka bani da wayo hmm baka san Rmalha bane"  kawai ta faɗi a gurin tana juyi tana ci gaba da sambatu marasa kan gado sam.

Hajiya Halima ta kalleta tace "Ramlah wai wace cutar kike magana akai ne? Wace irin cuta?"
Ramlah bata san me take ba, juyi kawai take yi tana wasu surutan irin na marasa kan gado, Amal kam tasan babu mamaki idan akace Fahad yana ɗauke da wannan cutar me karya garkuwar jiki, amma sedai dagaske Ramlah take tana mu'amala da Bulama ma kenan, gaban Amal ne ya faɗi kardai ace itama tana da wannan cutar, miƙewa tayi da sauri zata tafi ɗakinta, Hajiya Halima tace  "Amal ina zaki? Kina jin maganar da gake faɗa? Ko dai duk a cikin maye take ne?"

Amal tace "tunda ki kaji ta faɗa a maye, to ko ba'a mayen bama ya faru, sedai fatan Allah ya kyauta"

Amal ta tafi ɗakinta, dan itama fama take da kanta, wannan azabar ciwon marar da zubar jinin sun isheta haka.

Anty Saddiƙa ƙanwar Maman Nurat itace a gurin Nurat, itakuma maman Nurat ba'a barin kowa ya shiga inda take in ba likitoci ba, saboda tana ƙarƙashin kulawa ta musamman, Anty Saddiƙa taje salla Khalil na zaune a gurin Nurat, ai kuwa ta farka ta zaci zata ganta a ɗakin Dad ɗinta ya kulle ta, sedai tana buɗe ido tai arba da wani gurin daban, ta yunƙura zata tashi zaune, Khalil ya taho da sauri ya riƙeta yace  "yi haƙuri, ki kwanta kinji, karki gaggawa jikinki babu ƙwari"

A Shagwaɓe Nurat tace  "Brother ruwa zan sha"

Yace "ok bari in baki"

Ya ɗakko ruwam roba, ya buɗe ya bata ta sha, har ze gyara mata kwanciyarta ta kwanta, ta riƙe shi gam tana kallonsa, tana ƙoƙarin tuna meyafaru ihun Mummynta ta tuna, nan da nan ta razana tace masa "Mummy, Khalil Mummy na tana ina?"

Khalil yace "kwantar da hankalinki tana nan lafiya"

"A'a ban yadda ba, naji ihunta fa ranar, ban san meye ya sameta ba, tunda Daddy ya kulleni ban sake ganinta ba, waini ya akayi ma nazo nan ne?"

Khalil ya kalleta yace "kamar yaya ya kulle ki? Ya kulleki a ina?"

Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta gaya masa, yai shiru yana nazarin maganganun Nurat, cikin kuka tace  "ina Mummy take? Dan Allah ka kaini in ganta dan Allah"

Khalil yace "ki kwantar da hankalinki, likitoci na can na kula da ita, idan ta farka zata zo ki ganta"

"to wai meyasa meta ne?"

"Bakomai, ta faɗi ne kawai saboda Dad ɗinki ya rufeki, bari Anty Saddiƙa tazo ta temaka miki kiyi wanka"

Bayan Saddiƙa ta shigone, Khalil ya tashi ya fita, a reception yaje ya samu Alhaji Musa a zaune, dan idan yazo Asibitin ya duba su Nurat nan yake dawowa ya zauna, dan gaba ɗaya haushinsa suke ji.

Ya zauna kusa da Alhaji Musa ya kalle shi yace  "garin yaya ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene?"

Alhaji Musa yace  "wace irin magana ce wannan? Ba a gabanka nayi wannan bayanin ba?"

Khalil ya kalle shi yace  "to ya akayi ka kulle Nurat? Laifin me tayi maka"

Da sauri Alhaji Musa yace  "tana ina? Nurat ɗin ta farkane?"

Yai maganar yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, amma Khalil ya tareshi yace "na tambayeka kana ƙoƙarin tashi ina zaka?"

Yace  "wai ita Nurat ɗince tace maka kulleta nayi?"

Khalil yace "labari na samu, daga majiya me ƙarfin gaske, dan haka nake tambayarka garin yaya ka kulleta"

"wai Khalil yaushe ka koma haka? Yaushe ka koma mara kunyane?"

"ba rashin kunya bane, gaskiya ce dama ina da ayar tambaya akanka, wallahi muddin na ganoka da wani abu ba dai dai ba, naga wani abun kayiwa ƙanwar mahaifiyata ta faɗo daga bene, wallahi se nayi shari'a da kai, yanzun ma ba ƙyaleka zan ba, dan ba ƙaramin haushinka nakeji ba"

Alhaji Musa zeyi magana, amma Khalil ya dakatar dashi yace "ba abunda zaka gayamin, bana buƙatar jin komai daga gareka, amma tabbas ina nan ina bincike akanka, kuma wallahi ina daf da tsayawa a kotu a gaban alƙali da kai"

"Da nayi maka me?"

"in mun haɗu a kotu kaji"

Ya miƙe ya bar gurin, Alhaji Musa ya bi shi da kallo, yana tunanin me Khalil yake nufine?

Bayan Ramlah ta tashi daga mayen da take ne, Hajiya Halima tazo ta sata a gaba tana tambayarta   "Ramlah wata magana naji kina yi ɗazu cikin maye, wai Fahad yasa miki cuta, kekuma kin sakawa Bulama, wacce magana ce haka?"

Ramlah tace  "Eh to, dukda kince a maye nayi maganar kamar yadda kiji maganar haka take, Bulama shiya fara lalatamin rayuwa ta, na kamu da son ɗansa wanda hakan yasa na biye masa, sedai Bulama yaƙi goyon bayan ya aureni, yake ta cusa masa 'yar Daula ya aura saboda ya cika burinsa, soyayyar da nakewa ɗansa tasa na dinga biye masa ya koyamin shaye2, ya koyamin rayuwar banza nida shi ba abunda bama yi, nace ya Aureni amma yaƙi, kuma na gano yana da cuta me karya garkuwar jiki, dan haka na ƙuduri aniyar ramawa na komawa mahaifinsa, kuma da yake ɗan Akuyane ya karɓeni, ba tare da yasan ina mu'amala da ɗansa ba, dan haka shima ya kwasa, zuwa yanzu nasan uwarsa ma ta ɗauka, hakan yasa na ɗan rage abunda ke zuciyata gara muyi jinyar tare hadda ubansa"

Hajiya Halima ta ɗora hannu a ka tace "yanzu Ramlah abunda kikayi kenan? Ramlah gaba ɗaya kika biyewa namiji kika barbaɗar da rayuwarki da mutuncinki? Kin kyautawa kanki kenan?"

Ramlah tace "Mummy, bafa laifina bane wannan lamarin, duk wanda yazo neman Aurena se ki nunamin ai shi ba sa'an aurena bane, ina gidan Attajiri kamar Daula bekamata in Auri wane ba, ƙarewa ɗan uwanki ya biyoni ya lalata, na kamu da son ɗansa amma yai biris dani, kuma akan idinki nake fita ai, kin taɓa tuhumata ina muke zuwa nida Fahad idan mun fita? Me yasa? saboda idonki ya rufe ke burinki ya kawo miki masu siyan kadarori ki tara kuɗi, don't blame me for this please "

Ta tashi tai tafiyar ta ɗaki ta bar mata falon, Hajiya Halima ta dafe kai ta fashe da kuka, Bulama ya riga ya gama cutarta a rayuwa, ba ta san mema za tace a game da shi ba, ya lalata mata rayuwar 'ya, kuma wai yanzu Ramlah na ɗuke da cuta me karya garkuwar jiki, wanda ta samune a sanadin ɗansa, kuma ya dawo yace a kashe mata ɗa, ta rushe da kuka harda sheshsheƙa, gaba ɗaya komai ya rikice mata, tama rasa meye abunyi, wannan wace irin masiface haka take bibiyar ta? Daga wannan se waccan gaba ɗaya 'ya' yanta sun barbaɗe, haka ta dinga gunjin kuka ita ɗaya a falo, Amal ta ƙarawa ƙofar ɗakinta key, dan bata son tashin hankali.


Da safe Fahad ya shiga cikin gida, domin gaida iyayensa, sedai yan zaune a falon Iman nata masa surutu amma sam hankalinsa baya kanta, yayi zurfi a tunani can ya ɗago kai yace "ke wai ina Mummy ne?"

Iman tace "tana sama ɗakin Daddy"

Ji yayi kamar ta watsa masa wuta, ta ina ze fara gayamata hakinda ake ciki? Koma ya gayamata ai yasan aikin gama ya riga ya gana zuwa yanzu.

Yana nan zaune Sega Bulama yana Sakkowa, hannunsa ɗauke da jakarsa, Mummy sanye da doguwar rigar baccinta, ta riƙo masa wayarsa suna hira, Fahad yaji kamar yaje ya make Bulama saboda tsabar baƙin ciki da takaici, ga wani irin tausayin mahaifiyarsa ya kama shi.

Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace  "yau Allah ya nufe ka da shigowa cikin gidan kenan? Yaushe rabonka da shigowa"

Bulama yace "wai gidan ubanwa kake shigewa ne? Ko haryanzu yawon kake baka kwana a gida?" ga mamakinsa seya ga Fahad ya maka masa wata uwar harara, abun da be taɓa yi masa ba, ya kalli mahaifiyarsa yace  "Mummy ina kwana?"

"Lafiya ƙalau, ka tashi lafiya?"

"Lafiya ƙalau, dama na shigo mu gaisa ne zan karya"

Tace "shi Daddyn naka bazaka gaishe shi ba?"

"Ai na gama gaidashi, ni da sake gaisheshi har abada"

Kallonsa sukayi gaba ɗaya, Hajiya Sarah tace  "Fahad, daga kan kayan shaye2 naka ka taso ka shigomin falo ko? Shine har kake gayawa mahaifinka wannan maganar?"

Alhaji Bukar yace "ƙyaleshi, ina daf da maganinsa akan wannan mummunar ɗabi'a ta shaye2, dank yake zancen, ban agogona zan fita ina da ayyuka da yawa a Office "

Yasa hannu ya karɓi agogonsa, yai waje bayan fitarsa Hajiya Sarah ta kalli Fahad tace " Fahad, meyasa ka gayawa mahaifinka wannan maganar haka? Kai lalacewar taka harta kai kayiaa mahaifinka haka? Me yayi maka? "

Yace " bakomai "

" Bakomai amma ka faɗa masa wannan maganar? Abunda kayi ya dace kenan?"

Ya girgiza kai alamar a'a

"to meyasa kayi, salon mutane suji suce ni nake saku a turbar banza, na ku Wulaƙanta mahaifinku?"

"Nifa Mummy bakomai, kema da kin san me yayi da baki faɗi wannan maganar ba, kawai dai Allah ya kyauta"

Ya mike a fusace ya baf falon, tabi bayansa da kallo, Iman tace  "Mummy"

"Na'am"

"wai kuwa idonki biyu, jiya da Maman su Amal tazo gidan nan?"

"haba dai? Gidan nan tazo? Ai ban sani ba"

Iman tace "wallahi tazo, bayan ƙarfe goma se bala'i take tana neman Daddy"

"subhanallah, Allah yasa ba'a akan Ramlah tazo ba, saboda kin san halin ɗan uwanku sarai, ina kyautata zaton akwai alaƙar banza a tsakanin sa da Ramlah"
. "Mummy ya akayi kika sani?"

"last week na ganta ta fito daga sashinsa, na tambaye ta amma bata gayamin komai ba, sema baƙar magana da tayi min"

Iman tace "Umma kiyi ta haƙuri, Yaya Fahad se Addu'a gaba ɗaya zamansa a ƙasar waje ba abunda yasa masa se koyar mugayen halaye"

Hajiya Sarah tace  "idan da zaman ƙasar waje dai to harda halinsa, meyasa shi Anwar be lalace ba se shi? Bani da abunyi se dai yi masa addu'a, baya jin faɗa baya jin rarrashi, babu wanda banyi ba, amma duk baya ɗauka"

"Mummy kiyi haƙuri, wataran se labari ze dena insha Allah"

"Mhmm Iman kenan, yaushene watarn ɗin? Mutum ya girma amma kullum ba hankali, Allah ya kyauta dai kawai".

Yanzu ma Bulama yana zaune a Office, kiran wayar Me Adda kawai yaje amma taƙi shiga, yai shiru can wayar ta fara ringing, cikin hanzari ya ɗauka ya zata me Adda ne, sedai yaga baƙuwar lambace, ya ɗaga yai sallama

"justice A dutse ne ke magana '

Bulama yace " ok nagane, ya kake ya aiki? "

" Alhamdilillah, dama na bugo in sanar makane da cewar tawagar lawyoyi da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ɗaukaka ƙarar shari'ar Yusuf da nayi, kuma ina kyautata zaton ƙarƙashin jagorancin shahararren lawayrn nan ɗan gwagwarmaya wato Barrister Adam A Adam, dan haka tun wuri kasan abunyi!!!





(Alhamdilillah masha Allah, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, da addu'oinku da na samu bisa rashin da akayi mana, nagode sosai Allah ya bar zumunci)

AMANA! AMANA! AMANACE!!!
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN  ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin  wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_)

IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _






146_147




Cikin Bulama yai wata irin ƙara yace  "A dutse garin yaya haka ta faru? Ina tarin kuɗin dana baka kaida lawyoyi, ya za'amin haka?"

'Aini kuɗin daka bani, nayi aikin daya dace da su, na rufe yaron nam amma doka ta bashi damar ɗaukaka ƙara, kuma ya ɗaukaka ni yanzu shawara ɗaya zan baka, karka sake a gane kana da hannu cikin wannan badaƙala dake faruwa, idan da hali ma ka halarci zaman kotu da za'ayi, karka bari wani ya gane da saka hannunka"

Bulama yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, ko dai ƙasar zan bari gaba ɗaya ne? '

" baza' a gane da saka hannunka ba, tunda manyan ƙasar nan da 'aya siyasa dama jam'ian tsaro suna tare da kai, karkaji komai I will give you the necessary support i can, ka kwantar da hankalinka fa"

Bulama kawai ya ajiye wayar, ya dafe kansa Fahad ne ya bankaɗo office ɗin kamar wanda aka jefo, Bulama ya ɗaga kai ya kalleshi, ya mayar ya sunkuyar, Fahad ya ƙaraso gabansa ya tsaya yace "wallahi Daddy ka bani kunya, ka zubar mana da mutunci a idom duniya, ka cucemu ka zaluncemu kuma se Allah ya sakawa Mummy"

Kasa vane inda maganganun Fahad ɗin suka dosa yayi, dan haka yace "kai me kame faɗane haka? Meye hakan?"

"dole ka tambayeni mana, dama Daddy kana alaƙar banza tsakaninka da Ramlah?"

"kai wace irin maganar banzace wannan? Ƙwayar taka bata sakeka a gidan ba shine ka biyoni har nan za kamin hauka? Wacece kuma Ramlah"

Cikin shouting Fahad yace "niba hauka nake ba, dagaske nake, akwai haramtacciyar alaƙa a tsakaninka da Fahad, kuma Asirinka ya tonu"

"wane banzan ne ya gaya maka wannan maganar banzar, mara tushe balle makama? Waye wannan waima wace Ramlah kake nufi ne?"

"Ramlah dai, 'yar gidan Hajiya Halima kumabita ta gayamin, da bakinta ta gayamin"

A fusace Bulama yace "zaka fitarmin daga Office ko sena ci ubanka na tattaka ka, dama akan tsini nake, saboda mahaukaci ne kai kamar ni, ni zan nemi wannan yarinyar? Inyi uwarme da ita? Fitarmin daga Office kobin saka security su casamin kai, kai ko kunya bakajiba, ina ubanka ka tunkareni da wannan maganar ba kai ba ma'ana, kai data gayamaka meyasa baka yi bincike a kai ba? Kawai ta gayamaka maganar banza ka hau kai ka yadda, fitarmin daga Office shashasha kawai "

Sekuma Jikin Fahad yai sanyi, dan ƙarya batawa Ramlab wahala, a ransa ya dinga fatan Allah yasa ƙarya takeyi, yana fita Bulama ya share gumi ya zauna yace
" Jimin tsinanniyar yarinya, ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login