Showing 198001 words to 201000 words out of 209297 words

Chapter 67 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

764

da ƙyar.

Yusuf ya ɗagota yace "Widad, lafiya kuwa?"

"Yoseef cikina, ciwo yakemin"

"Wai anya ma kina zuwa Asibiti awo?"

Umma tace "Awon me kuma?"

Ɗan dirircewa Yusuf yayi, dan Umma bata san da ciki a jikin Widad ba, saboda kullum cikin zumbulelen hijjabi take.

Yusuf yace "ina nufin, taje likita ya ganta"

Umma ta tashi, taje ta ɗaga Widad daga jikin Yusuf, ta kwantar da ita akan pillow, tace "naga da mota a hannun ka, jeka ɗakko kazo a kaita Asibiti ko ɓarine"

Yusuf yace "Umma ba ɓari bane"

Umma tace "kamar yaya?"

Widad cikin kuka take cewa "Umma cikina, zan mutu"

Widad ta haɗa gumi sosai Umma tace "kiyi ta ambaton Allah, kidena kuka"

Widad ta kwanta rigingine, tana jujjuya kai, hakan ya bawa cikin nata damar fitowa sosai, Umma tayi mamakin ganin cikn nan, kenan dama da cikin aka kamosu?

Umma tace "to ko haihuwa ce?"

Widad ta girgiza kai tace "beyi wata shida ba, Allah yasa ba zubewa zeyi ba"

Yusuf dai haka ya ɗakko mota, suka sa Widad a ciki zuwa Asibiti.

Ta sha wahala sosai, seda suka wuni a Asibiti, likita ya tabattar musu da cewa allurar zubar da ciki da aka dinga mata ce take bata wahala haka.

Yusuf yace "Widad meye ya haɗaki da allurar zubar da ciki?"

Widad tace "Bulama, shine yasa aka dingayi min tunda akace masa ina da ciki, Amma dai cikin yana nan ko likita? Bana son in rasa shi dan Allah"

Likitan yace "ki kwantar da hankalinki, bakomai cikinki yana nan lafiya"

Haka nan Umma taji Widad tana bata tausayi sosai, mussman da taji tace allurar zubar da ciki aka dinga mata.

Se bayan ƙarfe goma na dare suka koma gida.



Bulama yasha matsa sosai, dan gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, a hankali yake ta faɗar da wanda yake haɗa baki ana cutar Daula, ga HIV ta fara nunawa a jikinsa, gudawa yake ba ƙaƙƙautawa, ga zazzaɓi me zafin gaske da yake fama.

Ya kalli 'yan sandan dayake hannunsu yace "Ranka ya daɗe, yakamata fa ace an barni naga lawayerna, dan har yanzu ba' a tabattar da laifin da ake zargina dashi ba"

Ɗan sandan yace "ka makara, dan baka da wannan damar kaima, kamar yadda ka siye wasu daga cikin hukumomin tsaro akayi maka yadda kake so a wancan karon, to yanzu an siyesu, ninkin yadda ka siyesu, kuma anace kar a sake a baka duk wata dama ko kwatankwacin ƙofar Allura ce, dan haka karka yi zaton zakayi free, kaida 'yanci har abada daga kai har muƙarrabanka!!!




AMANA! AMANA!! AMANACE!!!

DUK WANDA YA FITARMIN YACI AMANA

AYSHERCOOL
07063065680
12/9/21, 2:40 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

166__167



Gaba ɗaya a razane suka kalli Bulama, ya cigaba da cewa  "bayan ya kashe Huda, shine ya ambaci sunana har Widad taji, da niyyata har ita a kashe, bayan ya kasheta ne, a gurin zaman makoki Widad ta tonawa Bala asiri a gaban Wannan ɗan sandan, shima na faɗi na tashi na saka aka kashe shi!"

Yusuf ya rintse ido, yana jin kamar Bulama yana rura wuta a zuciyarsa.

Bulama ya cigaba da cewa," daga nan na lallaɓ Saleh, akan ya saki Halima, akwai kaso me tsoka daze samu idan harya sake ta ta aureka, dama ba iya kula dasu yake ba, dan haka ya amince dan yaji batun kuɗi, ya sake ta ko idda batayi ba, na dinga tura ta a gurinka, har seda ka amince da Aurenta, ka kuma ɗauki ɗawainiyar yaranta, ta aureka dan ta dinga tatsar mana kuɗi a gurinka.
Da kuma saka ido, domin mu samu ta karɓo mana wannan dukiyar daga hannunka, na saka aka dingayi wa 'yarka Allurar mahaaukata, saboda kar ta tona min Asiri, kuma inyi amfani da damar idan ta haukace ko Allah zesa in samu inda dumiyar nan taje, amma a banza, na dinga tura maka saƙonni kala kala, na razanarwa akan dukiyar nan, na dinga farmakar ka kaida' yarka da barazanar kisan kai, sannan duk wanda yai yunƙurin raɓarku koku raɓeshi, se shime in farmake shi, na taka rawar gani akan AƘIDAR 'yarka, dana ga hakan bzata yuwu ba, na koma ma baka shawarar ka aurar da ita ga ɗana Fahad, hakan zesa ta canza halaye, amma a zuciyata ina son ta auri Fahad ne dan idan bamu samu waccan dukiyarba, mu gane zunzurutun dukiyar da ka malllaka mata, duk wani meeting da yadda za'a karɓi dukiyarka da matarka mukeyi, watarnma se cikin dare a hotel haka muke meetings ɗin, bazan ɓoye maka ba Daula, tunda komai yazo ƙarshe wallahi ban taɓa sonka ba, na tsaneka ko ganinka nayi cikin walwala se inji kamar in kasheka in huta, kafini komai bana appreciating duk wani goodness ɗinka, burina kawai inga bayanka hankalina ya kwanta, saboda ganinka a raye ma bana ƙaunar yi "

Daula ya sunkuyar da kai, hawaye na bin idonsa, Alhaji Ahmad yace" kaiconka Bulama, kayi asara Nasir da dukiyarsa, da ƙarfinsa haka ya dinga maka wahala kai da iyalinka, ka kawo wasu ma cin arziki, kuma ya musu, amma ƙarshe ga inda ciwon hassada ya kawoka, to ina maka Albishir dukiyar da kake hari, ga me ita nan"

Ya nuna Yusuf, sannan ya ci gaba da cewa "dukiyarsa ce, shine ɗan Yusuf yayan Nasir, wanda kasa rai akan lallai seka karɓi dukiyar, ka azabtar dashi da ahalinsa saboda abun duniya, yadda kazo a banza haka zaka koma a wofi, sannan duk wata kadara indai ta Nasir ce, zamu karɓeta har gidan da kake ciki da motoci, da kamfanin daya ɗora kka akai ka maida shi naka, sannan kema Halima da kika dinga siyar da kadarorinsa, bayan wanda kika ci a baya, da wanda kika dinga sata, duk wanda kika siyarwa da wani abu ya sai aikin banza, zasu iya yin shari'a daku ku biyasu dukiyarsu, sannan bisa ga adalci na Nasir, yace  "ze baku duk wata dama a shari'a, baze amfani da dukiya ba ai muku hukuncin daya dace daku akan kisan kai na matarsa, da kuma garkuwa da kuka yi masa da yaransa"

Widad fuskarta sharkaf hawaye tace  "Nikuma zanyi Amfani da ƙarfin dukiya, ayi masa irin shari'ar da yai amfani da kuɗi akayiwa mijina, kaiconka Bulama daga kai har 'yar uwarka da sauran mutanen da suka zaluncemu, kuda Allah"

Ana cikin haka aka tankaɗo Abbas ma, Ya kalli Yusuf, Yusuf ya kalle shi, Abbas ya fashe da kuka yana faɗin "dan Allah Yusuf ka yafemin, na biyewa Zuciya da son abun duniya na aka haɗa kai dani aka cutar da kai, dan Allah Yusuf ka yafemin"

Yusuf ko kallonsa beyi ba, yai waje da sauri, yana tuna shima irin yadda ya amince da Abbas, be taɓa aboki kamarsa ba, amma yai masa wannan muguntar.

Su Alhaji Ahmad ma sukayi waje, daga gurin, su Alhaji Musa suna ta salalami dan sun san tasu ta ƙare, ga jikin girma dama kuɗine yasa ba'a gane tsufan nasu sosai, yanzu kuwa kam se cituttukane ke kunno musu kai kala kala.

Wani ɗan sanda ya biyo bayansu Daula yana musu bayani "To yallaɓai har yanzu muna nan munata tattara bayanai, da bincike akan wannan baƙin azzalumi da duk wanda ya haɗa kai dasu, kama daga yadda suka haɗa baki da megadinka, wani Bala zuwa yadda yasa aka kashe shi a gidan yari, da duk wani wanda yake da hannu muna ta kama mutane ɗaya bayan ɗaya, kuma ba da daɗewa ba zamu gurfanar dasu a gaban kotu insha Allah "

Alhaji Ahmad yace " Masha Allah, yayi kyau sosai wannan shine wanda aka bawa aikin dana bayar, Bulama sukayi amfani da wannan damar wajen cinma burinsu"

Widad ta kalli Alhaji Ahmad tace "wane aiki kenan?"

Alhaji Ahmad yace  "Aini koda bama tare da Daula, ina bibiyar al'amarunsa, kuma haka nan nake zargin Bulama zata iya kasancewa da hannunsa a masu yiwa Daula barazana, dan tuni ns gane dukiyarsa yakewa, sedai a lokacin son Bulama ya rufewa Daula ido, baya ganewa, ina jin duk labarin yadda kike bakya sakewa da mutane, da larurar taɓin hankali da kuma bibiyarki da ake akan wannan dukiyar, ni kuma na saka ayi bincike akan me bibiyar taku, sannan a baki tsaro ba tare dake ko mahaifinki wani ya sani ba, sedai ban san yadda akayi Bulama yasan an bada wannan aikin ba, har ya shiga ƙoƙarin karɓar file ɗin idan an gama binciken, dan ɓatar da duk wata hujja da zata saka a gane shi "

Widad ta sauke ajiyar zuciya tace " kowa yayi nagari kansa, a duniya babu abunda za ayiwa Bulama wanda zesa mu huce takaicin abunda yai mana, sedai ai masa hukuncin daya dace duniya sauran a barshi se a lahira "

Haka suka shiga mota suka tafi gida, suna jinjinawa azabara zalunci da baƙar mugunta na Bulama, tunda ya kashe ɗan 'yar uwarsa waye baze kashe ba, duk saboda abun duniya.

Da suka koma gida, fuskonkinsu kawai Umma ta kalla tasan wani abun takaicin suka kuma zuwa suka jiyo, a gurin' yan sanda shiyasa tun farko tace bazata bisu ba.

Umma tai musu sannu da zuwa, Daula ya wuce ɗakin hutawarsa, saboda yana buƙatar ya ɗan huta yayi tunani.
Widad ma ta janye mijinta, zuwa wani ɗakin daban, Alhaji Ahmad ya zauna a kujerar dake kusa da ta Umma yace  "Hajiya Jidda"

Umma tace "Jiddan dai banda Hajiyar"

"Dole ace miki Hajiya mana, tunda kika riƙe ɗan Daula, kika riƙe babban attajiri haka"

Umma tace 'mhmm, ni tsoro nake ma kar yace ze ƙwacemin ɗana, bana son sunana ya canza daga Umman Yusuf, dan bana tunanin ko da Allah ya bani haihuwa, zanso ɗan nan kamar yadda nake son Yusuf'

'tabbas nima nagani, kuma Wallahi Daula ua jinjinawa ƙoƙarin ki, yace idan ya kalli abunda Bulama ya masa, se yace "Anya kuwa akwai ragowar mutanen kirki a duniya? Idan ya duba irin riƙo da wahalar da kika sha da Yusuf se yace duk lalacewar zamani akwai na Allah, wallahi kin ciri tuta Jidda, kuma abunda kikayi Jihadi ne, riƙon maraya da zuciya ɗaya tamkar ɗan da kika haifa "

Jidda tace " gashi nan ina morarsa, wataƙila da ban riƙe Yusuf ba haka tsufa ze riskeni babu me jin ƙaina, 'yan uwana bama su ƙarfi bane, hasalima a gurina suke nema, bani da wanda muke uwa ɗaya uba ɗaya sedai' yan uba, amma Yusuf ya riƙeni Uwa, yanamin biyayya fiye da yadda kake zato, ƙare magana ko ɗan dana haifa banajin zemin biyayyar da Yusuf yayi min, koda ban taɓa haihuwa ba, amma ni riƙon Yusuf yamin rana, ko be zama komai ba, tausayinsa da jin ƙansa ya gamamin komai "

Alhaji Ahmad yace" hakane, tabbas yana da haƙuri da biyayya, kuma bayan wannan dukiyar dai Allah yayi tasa ce, da ba lallai ya iya jure wannan tsananin da wahlar ba, amma da yake tasace kuma Jininsa ne Daula, kinga ya jure duk gwagwarmaya, an gaisheki Jidda kin cika Uwa tagari "

Jidda tai murmushi tace  'Nikam Ahmad, ina naka iyalin ne?"

"Meyasa kike tambayata?"

"gani nayi tunda mu kazo banga ka koma gidanka ba, ko ka yi zancen su ba"

Yai murmushi yace "iyali suna nan a kano, da ina nan zaune tare dasu ne a nan Abuja, tace ita dai tafison zaman kano, shine suka koma suka barni sedai in dinga zuwar musu"

Umma tace "Allah sarki, Allah ya raya zuriya"

Yace "ameen ya Allah, Jidda nayi mamaki har yanzu kina nan da kyanki baki canza ba gs gayu"

"kajika da wani zance, ina wani kyau da gayu bayan na tsufa"

"wallahi baki tsufa ba, kalleki fa ras dske, amma meyasa baki sake aure ba bayan mijinki ya rasu?"

Umma tai ajiyar zuciya tace "saboda ina son in kula da yarona, idan na auri wani waze yadda ya riƙemin shi, mussman da bani na haife shi ba, shiyasa na zaɓi in zauna ba Aure in riƙeshi"


Alhaji Ahmad yace "to amma ai yanzu ya girma, shima me riƙe wasu ne mussman wannan sitira da Allah yayi masa yanzu, saboda haka yakamata kiyi aure ai"

Umma tace "tsofaitsofai dani se in kama yin wani aure, a'a ai na girma Aure mun barwa yara"

"kece kika tsufan kokuma wa?"

"Eh mana, na tsufa"

"yanzu fa da wanine ya gaya miki seki ji haushi ko?"

Umma tace "akanme zanji haushi, ai nasan na tsufan ne"

Alhaji Ahmad yace "ba wani nan, ni dai ina zawarci har yanzu, ina so"

Umma ta kalli Alhaji Ahmad tace "dan Allah ka dena wannan zamcen haka, haba Ahmad"

"kinga dole inyi wannan zancen, haba Jidda me zesa ki haramtawa kanki Abunda Allah ya halatta, haka zaki cigaba da zama babu Aure kenan?"

Tace "eh mana, har zuwa lokacin da Allah ze karɓi rayuwata"

Alhaji Ahmad yace "No, gaskiya bazaki zauna haka ba, kawai ki tsaya mu sasanta"

Umma ta miƙe tace "kai dai bazaka canza hali ba, ka girma kana abun yara"

Yai murmushi yace "Au hakama zakice? Aini bazaki girman a idona ba, tunda.. Bari dai in shiru"


Umma ta bar falon tana dariya.


Yusuf kam salla yayi a ɗakin da suke, Widad tasa aka kawo fruit da madara me sanyi, amma Yusuf yaƙi sha.

Widad tace "haba my Fluid of life, wai baka murna da kasancewat ƙanwa a gareka ne? Naga baka walwala sam duk kana cikin damuwa"

Yusuf yai murmushin ƙarfin hali yace "yama za'ayi ince bana farinciki da Kasancewar ki ƙanwata, na daɗe ina miki so mai tsanani da takurawa ruhi, se yanzu na tabattar da ashe son ne ya haɗemin dana 'yan uwantaka, tsabar farinciki ne yasa na rasa ta ina zan nuna tsantsan farinciki danake ciki, ashe tun tuni da' yar uwata nake tare, shiyasa nake jin zan iya yin komai ko in bada komai nawa, gurin baki kariya koda kuwa raina ne, nayi farinciki da haka, kuma gefe guda ina jimanta irin wahalar da muka sha, da mamakin cin amanar yadda na mutanen wannan zamani, dukda abunda akayimin be kai na Daddy ba, Amma Widad ko a tatsuniya akacemin Abbas zemin haka bazan yadda ba, ashe haɗa baki akayi dashi akamin gadar zare, yazo ya lallaɓani aka bani aiki, shi yayi dan cutar dani, ashe hakan Silar taradda farinciki nane, kai Widad mutane abun tsorone, banga laifin AƘIDARKI ba baby, kaso mutum dan Allah shikuma bashi da maƙiyi kamarka"

Ya ƙarasa maganar muryarsa na rawa, alamun karaya Widad ta rungume Yusuf tana shafa sumar kansa ta sigar rarrashi tace "tabbas haɗuwarmu da wasu mutanen a rayuwarmu darasi yake bamu, da mutane sunyiwa AƘIDATA mummunara fahimta, amma ba haka kurum nake abubuwan da nake ba a baya, dukda daga baya na gane a AƘIDATA akwai wadda bata kamaceni ba, amma a hankali duniya ta ladabtar dani ns gane rayuwa sosai, sannan nayi farinciki na kasancewarka ɗaya daga ahalina managarcin mutum me matuƙar kamala, ina sonka Yusuf "

Yusuf ya kalleta dukda gefen idonsa hawayene ke zuba, amma yai murmushi har seda haƙoransa suka fito yace " waye ya koya miki yadda ake faɗar sunana? In kikace Yoseef yafimin daɗi, saboda nasan ba wanda yake faɗar sunana a haka se Gimbiyar Yusuf "

Widad tai murmushi tana sake rungume Yusuf a jikinta, Widad tace "Alhaji Yoseef Nasir Daula, seka dena bearing wancan sunan, tunda har gida akazo ama kashedi akan ka dena amfani da sunan saboda tsabar jaraba irin ta mutanen nan"

Yusuf yace "am sorry to say, Baby bazan iya dena amfani da sunan Bashir maitama ba, saboda shina saniba ubana, shina buɗe ido dashi yana ɗawainiya dani"

Widad tace "hakane, babu laifi Mijina"

Yace "Amma ni gaskiya, wannan kuɗin da ake shirin bani, nifa ban san yadda zanyi dasu ba"

"Yoseef, wannan kuɗinfa na mahaifinka ne da mahaifiyarka, wakake so a bawa idan ba kaai ba?"

Yusuf yai shiru yana zancen zuci, Widad tace "mu bar maganar nan, zamuje ƙauye a satin nan yaushe zamu tare ne, nina gaji gaskiya"

"to mara kunya, kije ki tambayi Daddy, wace tarewa kike nema, banda wannan tarewar na cikinki"

Sosai Yusuf ya bata dariya tace "ai shikenan, bama semun wani tare ba, ɗaki ɗaya zamu koma kwana, ai akwai ɗakuna dayawa a gidan nan"

Yusuf yace "Allah ya baki haƙuri, kiyi haƙuri mu koma kano kinji ƙanwata"

Tai murmushi tace "naji, tashi muci Abinci ko?"


Haka suka wanzu suna farinciki da annashuwa a tsakaninsu.





Nuray kama tunda ta gano Khalil sonta yake, take jin tausayinsa, be taɓa gayamata ba, amma idan tana tuna kyautatawarsa, da kulawarsa a gareta, tabbas idan ba so babu abunda ze kawo hakan.

Tana kitchen tana aikace aikace tana tunanin yai sallama ya shigo, ta amsa masa tana binsa da kallo.

Yace "Nurun, me kike soya mana ne?"

Tai murmushi tace "kwaɗayi nake ji, ma rasa me zanci na tsiri yin cake"

"kwaɗayayyiya kawai, amma dai ɗan sanmun"

Tai dariya tace "mun zama kwaɗayayyu kenan"

Ya ɗauka yana ci yana faɗin, "kai Komai naki na dabanne, ban taɓa cin Abinci me daɗin wannan ba fa, Allah ya bani mace tagari wadda ta iya girki kamarki"

Nurat ta kasa ce masa komai se kallonsa kawai da take yi, jiki a sanyaye yace "lafiya kuwa?"

"Lafiya ƙalau Yayana"

"to ai gani nai kamar jikinka ba ƙwari fa, ko akwai matsala ne?"

Ta girgiza masa kai alamar aa' "ko Yusuf ɗinne dai ya kuma yi miki wani abu?"

"Brother, Yusuf yafi ƙarfina na haƙura dashi"

Cikin damuwa yace "saboda me? Ya da karaya haka Nurat"

"Khalil, Ka sani an tabattar da Widad matarsa ce, aure sukayi Dan harda tsohon ciki ma, kasan a ynzu na shiga sahun maƙiyan Widad, nasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login