Showing 60001 words to 63000 words out of 209297 words

Chapter 21 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

721

a gidan nan"


Bulama yace "ikon Allah, kalli abunda ake tambayarta daban, abun da take faɗa daban"

Daula ya dafe kai yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ka rufamin Asiri kar Abunda ya ragemin ya kufcemin, Allah ka bawa 'yata lafiya".
Kawai ya fashe da kuka, yana ƙanƙame Widad a ƙirjinsa, aikuwa ta kwanta a jikinsa, tana ajiyar zuciya.

Alhaji Munir yace "dan Allah ka dena kukan nan"

Likitan da suke kira da Hamisu yace "Alhaji ina me sake yi maka ta' aziyyar rashin matarka, sannan kayi haƙuri ka dena kukan nan, ka bani haɗin kai ka amsa tambayoyin da zan maka, saboda alamu sun nuna Ƙwaƙwalwarta ta fara taɓuwa, tana iya bacci, ya yanayin cin Abincin ta?"


Daula yayi masa bayanin duk abunda Widad take yi, nan aka tabattar masa depression ne yake damunta.

"zan mata wata allura guda ɗaya, idan akayi mata insha Allah zata samu sauƙi, za'a samu ƙwaƙwalwarta ta dinga karɓar abunda ake so "


Widad tana zaune, aka haɗa allura aka zuƙa, tana kwance jikin Daula, likitan ya ɗaga hannunta, daidai dantsanta yayi mata allurar, sedai me ko mintuna biyar ba'ayi ba.........






LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

78_79








Take Widad taji duniyar tana juya mata, taga abubuwan dake ƙasa sun koma sama, na sama sun dawo ƙasa, ta kasa gane inda kanta yake, ta dinga jin kamar ta tashi ta zura da gudu, ta riƙe kanta gam, kafin can ta kurma wani uba ihu ta miƙe tsaye tana zazzare idi.

Daula a gigice ya riƙeta yace  "Subhanallah, doctor meke faruwa ne? Kaga abunda take fa, meya sameta ne? Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"

Likitan yace  "wannan shike tabbatar da ta samu taɓin hankali ne, badan haka ba da babu abunda allurar za tayi mata, dole a cigaba da kula da ita, idan ba hakaba kuma zata zama tuburan, amma zan sake mata wata allaurar zata samu relief tayi bacci"

Widad tana ta gunji, tana fizge fizge haka aka kuma yi mata Allura, wadda seda ta ƙara birkitata ga baki ɗaya, ya zamana bata gane a duniya take ko a ina? Ga mutane tana kallonsu, amma bata gane meke faruwa, a haka har wani irin galabaitaccen bacci ya ɗauketa a wahalce.

Seda bacci ya ɗauketa sannan hankalin Daula ya kwanta, ya kalli likitan yace "yanzu doctor, wannan baccin shine samun relief ɗinta? Sannan kuma ya batun yadda za'a cigaba da kula da ita"

Doctor Hamisu yace "Eh shine samun sauƙinta, tunda kace baccin ma bata yinsa sosai, dan haka karka damu, ko yaushe zata kai tana wannan baccin babu wata matsala ba abun damuwa bane"

Daula ya jinjina kai yace  "shikenan, ubangiji Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗunta, Allah ya baki lafiya daughter na"

Alhaji Munir yace  "to tunda hakane baka ganin a cikin taɓin hankalin ne yasa tace kashe mahaifiyarta akayi? Tasa aka kama Bala? Kuma ma ai tayi ƙanƙanta ace ta bada irin wannan shedar an yarda an karɓa"

Daula ya haɗe rai yace "bana yadda in zalunci kowa a rayuwa ta, ina taka tsantsan da duk abunda zan aikata da zesa in ɓatawa wani, ko in zalunci wani dukda tarin dukiyar da nake da ita, amma a wannan karon nima zan ɗana izza da amfani da ƙarfin dukiya da Allah ya bani, in dai hakan ze samarwa da 'yata farinciki, bari in gaya maka wani abu, ko nawane zan kashe a cigaba da tsare Bala, har se ya faɗi abunda yasani game da kisan matata, uwar' yata"

Bulama yace  "Daula karfa soyayyar 'yarka yasa ka aikata abunda zakazo kana danasani, abi komai a sannu har a gano bakin zaren, kaga yarinyar nan ga abunda aka ce yana damunta, ga kuma ita abunda take faɗa, kar ƙaunar da kake mata yasa ka ɓata sunanka a idon duniya"

Daula ya kalli Widad dake kwance a jikinsa, ya shafi gashin kanta yace  "bata taɓa aikata wani abu makamancin haka ba, 'yata ba irin sauran yara bace, Ƙwaƙwalwarta na aiki fiye da shekarunta, tunaninta ya zarta tunani irin na yara, a baya Huda na ɓacin ran irin halayen Widad, tana jin haushin irin kallace kallacen da take yi, sedai me bayan ran Huda wannan hali na Widad yayi rana, saboda ni abunda likita ya faɗa daban abunda kuma ya faru daban, abun da baku sani ba shine, har kitchen inda ta hau kan drower, har garin hawa abunda take ci ya zuba a ƙasa, seda ta nunawa 'yan sanda, kuma ta nuna musu ta ƙofar da Bala ya shiga da mutanen nan, an auna gurin anga zanen yatsunsa a jiki, dan haka bana tantama abunda ta faɗi gaskiya ne"

Munir yace "Amma, baka ganin lokacin da ya shigo duba sune ya kama ƙofar ya shigo, har hoton yatsunsa ya fito"

"Wannan kuma aikin hukuma ne, su zasu tabattar da gaskiyar abunda ya faru, amma wannan karon nima zan ɗana, zanyi Amfani da ƙarfin dukiyata, da kuma alfarma da sanayya da nake da ita a faɗin ƙasar nan, se an nemo wanda suka kashe matata, kuma wallahi ko Arziƙina ze ƙare se na tabattar da anbi mana haƙƙinmu"

Likitan yace "Amma ranka ya daɗe kabi komai a sannu yafi, alamu sun nuna yarinyar ka tun tana ƙarama take da larurar Ƙwaƙwalwa, amma baka ɗau mataki ba"

Daula yace "ni lafiyar 'yata ƙalau, babu abunda ya samu Ƙwaƙwalwarta a wancan lokacin, Allah dai ya bata kaifin basira fiye da shekarunta" yana gama maganar ya miƙe, ya saɓa Widad a kafaɗarsa ya tafi ɗakinsa da ita, yaje ya kwantar da ita, ya koma gefenta ya kwanta ya ƙura mata ido yana jin tausayinta na ratsashi, Widad ta rasa mahaifiya da ƙananan shekaru, yasan rayuwar maraici, yasan yadda take, musamman ga 'ya mace tafi shan wahala, take hawaye suka shiga zarya a fuskarsa yace  "insha Allah zanyi iyayina, ba zakiyi kukan maraici ba Widad"

Wasa wasa tunda aka yiwa Widad Allurar nan bata sake farkawa ba, haka ta dinga wannan baccin kamar wata matacciya, abun ya ɗagawa Daula hankali sosai, Amma likita yace masa bakomai samun relief ɗinta kenan.

Seda Widad tayi kwana biyu cir tana wannan baccin, ko motsi ba tayi rana ta biyu da yamma sannan ta farka, tunda ta fara baccin nan Daula baya matsawa ko nan da can, yana kusa da ita, har Allah yasa ta farka.

Koda ta farka ta farka da wata irin matsananciyar yunwa, amma ta kasa cewa tana jin yunwa, maganar duniya Daula yayi amma taƙi bashi amsa, sedai ta bishi da ido.

Ya haɗo Abinci yazo ya zauna yana bata, tana ci tana kallonsa kamar taga sabon abu a tare da shi, yana cikin cin aka zo aka sanar dashi yayi baƙi yace ayi musu iso nan inda yake baze iya tashi ya bar Widad ba.

Aka musu iso suka shiga har inda Daula yake, sedai Widad na ganinsu se taga kamar wannan mutanen da suka kashe Amminta, seta dinga ganinsu da wannan mask ɗin a fuskarsu, abunda ya faru da Amminta ya shiga dawo mata fes a idonta, taga kamar a lokacin abun ke shirin faruwa, aikuwa ta kurma ihu me razanarwa, haka yasa mutanen suka tsaya suna zuba mata ido, ta riƙe Daula gam tana ihu, ta rintse idanunta alamar bata son ganin kowa gaba ɗaya.

Ƙarshe mutanen nan se barin ɗakin nan sukayi gaba ɗaya, suka koma babban falo suka jira shi, abu kamar wasa sosai Widad take gudun mutane bata son kowa a inda take inba Daddynta ko Bulama ba.

Watarana tana zaune a ɗakin Daddynta, tana wasa da magen Amminta data bari, Alhaji Daula yana son ya ɗan fita, amma yana tunanin yadda zeyi da Widad.

Widad da a rana bata fi tayi magana sau a ƙirga ba amma tace  "Daddy kaje inda kake son zuwa, ba inda zani"

"A'a lovely, ina tsoron barinki anan ke kaɗai, abubuwa sun fara bani tsoro, ina zaton zan sa a ƙara security"

Widad tace  "Daddy har yanzu Bala be magana ba?"

"Eh lovely, Amma a binciken 'yan sanda, security na kan babban titi sunga wucewar mota tsakar darw ta shigo hanyarmu, sedai wai sunyi zaton gurina ko wani suka zo, saboda kin san mukanyi meeting cikin dare, amma har yanzu anata bincike"

Widad ta jinjina kai tace  "Daddy kaje kawai, ina nan ba inda zani"

"Babyna ina tsoron barinki, kinga baki da lafiya"

"Lafiyata ƙalau fa"

"ko kuma mu tafi tare da ke?"

"A'a Bazani ba, ka tafi kawai"

Daula yace  "nayi murna daughter, yau kina magana sosai da kanki".
Tayi murmushi, Daula ya shirya ya fita.

Bayan fitarsa Widad ta fito ta dinga zagaye gidan, kamar bata saba ganin gidan ba.


Kamar gaske ta fara dawowa daidai, amma dukda haka bata son mutane sam, daga Daddynta bata son kowa ya raɓeta, balle a yimata wani abun, haka Daula yake yawo da ita gurin taro ko harkokin kasuwanci, kamar yadda uwa ke yawo da ɗanta, sam ko makaranta bata zuwa saboda rashin son mutane, indai ba'a gida ba ko tana tare da Daddynta bata zama a ko ina.

Daula Shine wankanta, Abincinta, da dukkan buƙatunta, sam baya gazawa.

Wataran zeje taron kasuwanci Africa ta kudu, nanma ya ɗauki Widad ya tafi da ita, ranar da suka dawo kusan ƙarfe ɗaya na dare, direbansa yaje ya ɗakkosu daga airport suna tafe suna hira, kawai aka tare motar tasu.

Widad na ganin mutanen da suka taresu ta gigice, yanayin jikinsu sak wanda suka kashe Ammi, gasu da mask a fuskarsu.

"Kai buɗe motar nan"! Ɗayan yayiwa direban Daddy tsawo

Widad ba zata taɓa mantawa da wannan muryar ba, tabbas sune wanda sukaje har gida suka danne Umminta da pillow, nan da nan jikin Widad ya ɗau rawa, amma ta dake taƙi nuna alamar Hakan.

Suka bubbuɗe murfin motar, Daula ya rungume Widad a jikinsa yana ta nanata Hasbunalahi wani'imal wakil, suka fizgo direban Daula ƙasa suka saita masa bindiga.

Ɗaya daga cikinsu Wanda Widad bazata manta dashi ba, shine wanda taji yana wayar nan ranar da suka kasje mahaifiyarta, har ya ambaci sunan wani mutum, ya kalli Daula yace  "Nasiru Daula, haƙiƙa ina me tabattar maka da zaka bi matarka inda ta tafi idan har ka mana gardama, tambaya ɗaya zan maka kuma amsa nake so ta kai tsaye, ina wannan takaddun da wasiyyar da kayi na cewar akwai wanda yake da kashi bakwai bisa goma na dukiyarka suna ina?"

Daula ya kalleshi cikin mamaki yace
" dama dalilin da yasa kuka taremu kenan? toni babu wannan kayan a hannuna, kamar yadda nayi bayani lokacin da nayi hira da 'yan jarida"

Cikin tsawa yace " kai, karka min wata taƙama da jin kai, babu wani amfani da taurin kai ko tsaurinka ze maka a nan, zan iya fasa maka kaibda harsashen nan"

Ɗauke Daula yayi, yai musu shiru.

"Ina takaddun nan suke?!" sukai masa magana cikin tsawa.

Ko gezau beba balle susa ran ze basu amsa, yunƙurwa sukayi zasu danƙo Daula daga cikin motar, Amma Widad ta buɗe hannayenta ta tare mahaifinta.

Daula yace "lovely, ki bari kar suyi miki wani abun kinji, karsu illatamin ke"

"Am not afraid of anyone, abunda suke nema yana gurina, karsu ƙara yi maka tsawa"

Kallonta suka shigayi, dudu ba zata fi shekaru takwas ba, amma kalli yadda take magana kamar ba yarinya ba.

Hannu babban cikinsu ya saka ze fizgo Widad, amma Daula ya riƙita gam suna janta, shi kuma ya riƙeta gam.

"Idan baka saketa ba zamu fasa kanta da harsashi!"

Daula yace  "idan kuka kasheta kun kasheni, kuma kun rasa abunda kuke nema, kuma koda kun barmu a raye shima duk ɗaya zaku rasa abunda kuke nema, dan wallahi kome zakuyi da kaina bazan baku amana ba, bazan baku kayan da ba nawa ba, sedai idan Widad ɗince ta yarda ta baku bani da matsala da duk wanda ta ɗauka ta bawa"

Zuro hannu ya kuma yi ze danƙo Widad, sedai a wannan karon bisa sa'a, Widad ta nuna musu ita mahaukaciya ce, dan kukan kura tayi ta datse yatsan mutumin nan a bakinta, ta kafa masa haƙora kamar yadda ta yiwa Fahad.

Abun mamaki sega Ƙaton da yake ɗauke da bindiga yana kurma ihu, yasa kan bindiga ya daki kan Widad, wanda hakan yasa ta ƙwala ihu ta sake shi, sega jini na zuba ta hancinta ta sume a gurin, ganin Asirinsu na ƙoƙarin tonuwa yasa suka cika wandunansu da iska suka ɓace daga gurin.

Daula gaba ɗaya ya rikice, ƙarshe direban ne yayi dabarar wucewa dasu Asibiti, aka kai Widad emergency gaba ɗaya Daula ya rasa abunda yake masa daɗi, matsala daga wannan se wancan be maganin wannan ba waccan ta kunno kai.

Yai shiru ya dafe kansa ya zubawa Widad ido, wadda ke kwance ruwa na shiga jikinta, ya kifa kai akan gadon da take yai kuka yai kuka, harya gaji yayi shiru, cikin dare Widad ta farka tayi juyi taji kanta yayi mata nauyi, ta juya taga mahaifinta ya kifa kansa a kan gadonta, ya riƙe hannayenta, da alamu yana cikin matsananciyar damuwa, a hankali tayi juyi ta rungumo kan Daddynta ta kwantar da kanta a kan nasa, a haka bacci ya ɗauketa.

Wayewar gari labari ya cika gari, ga abunda ya sami Daula da 'yarsa nanma akayi ta tururwar zuwa Asibiti dubata.

Daula ya tafi masallaci salla sega wasu mutane sun shigo ɗakin nata, wai sunzo dubata, ta dinga binsu da kallo, suka zazzauna, kallo ɗaya ta gane wanda ya buga mata bindiga jiya, wanda suka kashe Amminta ne, bata taɓa ganin fuskarsa ba se yau, bata ƙara tabattarwa ba seda ta kalli inda ta gasa masa cizo jiya, a hankali yace

  "ina baban naki?"

Shiru tayi ba tace masa komai ba, yazo gaban gadonta ya durƙusa sannan kalleta yace  "Baby girl, tambayarki zanyi kinji ko? Ina abubuwan da Dad ɗinki ya baki ajiya, su nake son ki gayamin inda suke kinji, nima bazan gayawa kowa ba"

Widad ta tsare shi da manya manyan idanunta tana masa wani irin kallo, daya kasa gane na menene?

"Baby ki gayamin kinji"

Still ba amsa, ya ɗakko wata ƙaramar wuƙa yace "idan baki gayamin ba, zan gutsutsura naman jikinki da wuƙar nan, in dafa in cinye, gayamin nace"

Yai maganar yana zare mata ido.

Ya ɗauka Widad irin yaran dazewa barazana ne, amsar data bashi shine  "idan ka kasheni bakomai, nasan dai Daddy zeyi kuka, amma nasan wanda ya kashemin Ammina" tai maganar tana kallonsa

A fusace yace "ina ruwana da wanda ya kashe ta? Kema kashe ki zanyi in kashe babanki idan baki faɗan ba"

Maimakon ta bashi amsa, se tace "Na rubutawa DSP wasiƙa, zan gayamasa wanda ya kashe Ammina, yayimin Alƙawarin ze gano suwaye"

"Ke dan ubanki ba wannan muke tambayarki ba, ina kayan nan suke?"

Widad bata nuna ta ganesu ba, ta sake kallon hannunsa tabbas shine babu ko tantama, ga inda ta cijeshi jiya a tsintsiyar hannu, abun da ya faru ranar da aka yi kisan ya sake dawo mata ranta, gani tayi ya miƙe ya ɗakko handkerchief a aljihunsa ze saka mata a hanci, nan experience ɗinta na kallace kallacen films ya dawo mata, bata san ya akayi ba ta fasa ihu, ta ɗakko kwalbar malt zata buga masa, ai kafin tayi wani yunƙuri, sun bar ɗakin nata da sauri, nan ta cigaba da kurma ihu tana jifa da kwalabe a ɗakin.

Da gudu Daula dasu Bulama, da ɗan sandan Da Widad ta saka ya kama Bala, suka ƙaraso ɗakin, dama suna kan hanyar zuwa ɗakinne, Daula yayiwa ɗansandan waya, yayi masa bayani, shine ya taho Asibitin.

Tayi watsi da kwalabe tana kuka, Daula jiki  a sanyaye ya karaya, tabbas hauka ya tabatta akan Widad, ta haukace.

Daula yana da matuƙar raunin zuciya, dan haka kuka baya bashi wahala, haka ze zauna idan damuwa tayi masa yawa yaita abunsa.

Yazo kan gadon nata ya zauna, aikuwa nan da nan ta rungume shi, tana ta sauke numfashi kamar wadda tayi dambe.

Ɗansandan yace "Alhaji, wannan harin da aka kai muku jiya, ya tabattar da maganar Widad, kashe matarka akayi muma munata tattara abunda bincike ya nuna mana, Insha Allah kamar yadda nayi Alƙawari, se naga abunda ya turewa buzu naɗi"

Daula yace "nagode sosai ranka ya daɗe"

Bulama yace "Nasiru kaga tashi muje a maida yarinyar nan gurin Likitan nan, ya duba ta asan halin da take ciki, abun nata gaba yake fa"

Babu tunanin komai, Daula ya amince, Bulama ya saɓa Widad a kafaɗarsa, suka fito sedai tasa tafukan hannayenta ta rufe idonta, saboda bata san haske kuma bata son koda wasa ta sake ganin mutanen nan.

Asibitin doctor Hamisu suka wuce, ya karɓesu hannu bibiyu, ya sake ɗurkawa Widad allurai wanda suka sake rikita ta gaba ɗaya, sannan ya ɗirka mata allurar bacci.

Gaba ɗaya seda inspector ya kamu da matsanancin tausyin Widad, yarinya ƙarama amma rayuwarta a garari haka, ya kalli Daula yace

"ranka ya daɗe, yakamata ace an sake tsananta matakan tsaro, a hanyar gidanka saboda kariya ga lafiyarka da kuma ta 'yarka, ina jin tausayin yarinyar nan, kuma nayi mata Alƙawari insha Allah bazan mutu ba zan cika mata, tacemin zata yi magana dani rannan, tace maganar tana da mahimmanci sosai, dan haka insha Allah zan sake zuwa, in duba ta sannan inji maganar da zata yi min"

Daula yace "Nagode DSP da wannan ɗawainiya da kake, Allah yasaka maka da alheri"

"Karka damu, aikina ne yin hakan ai, Allah ya bawa Baby lafiya"

Kwana biyu da tafiyar DSP, lokacin Widad ta farfaɗo, a lokacin aka sanar da rasuwar Wannan DAP Na 'yan sanda da yake faɗi tashi akan case ɗin, ranar da ya bar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login