Showing 45001 words to 48000 words out of 209297 words
wayarsa, yana jin wani sanyi a ransa, dan da ba ƙaramin ɗurar ruwa cikinsa yayi ba.
Nura direba ne a cikin lambun Widad yana ta gyarawa, yana cire ciyayin ciki yana gyara flowers ɗin tare da sharewa, yace "Allah sarki, lambun nan kansa yayi babban rashi, da meshi tana nan babu yadda za'ayi a barshi a haka, kai rayuwa ba tabbas"
Kukan mage ya dingaji a tsakanin flowers, har ya tsorata ze ruga da gudu, sekuma yayi ta maza ya dake, leƙawa ya shigayi a hankali, yana duba ciyayin.
Roux ce magen Widad a kwance, gaba ɗaya tayi wani iri abun tsoro, da ƙatuwace magen nan, gata da kyau gwanin ban sha'awa da yake bata Nigeria bace, amma yanzu kamar an jiƙata a ruwan zafi, gaba ɗaya gashin jikinta yayi wani iri, gashi duk ya zube ta koma wata iri abun tsoro.
Nura yasa hannu ya ɗakkota, ya nufi bakin gate da ita, yana zuwa ya ajiye ta, Isa ya kalleshi ya yamutsa fuska yace "meye wannan haka?"
Nura yace "Magem 'yar masu gidace"
Murtalah yace "itace ta koma haka?"
Nura yace "kaima dai ka faɗa, ai maraici yakama magen nan, abun tausayi"
Isa yace "wannan matsiyatan basu kula da mutum bama balle wata mage, duk halin nan da ake ciki na rashin me gidan nan da' yarsa ko a jikin su, sabgarsu kawai suke har gara ma Anwar ɗin nan, shikam akwai kirki sosai"
Nura yace "bari Isa, Allah abun tsoro duniya abun tsoro, kalli da yadda gidan nan kullum cikin shige da ficen mutane ake, amma yanzu tsit kake ji"
Murtalah yace "kai dai bari, bari in jarraba bawa magem nan Abinci ko zata ci"
Isa yace "kaga fa baka da abunda zaka bata, dan Wani Abincin da fake ci kai kanka baka taɓa ciba, ka ƙyaleta kawai ta ƙarasa ta hutawa rayuwarta"
Murtalah yace "A'a ba'ayi haka ba, Yanzu a dalilin taimakon dabbar nan se kaga Allah nima yaji ƙaina, kuma dame ita tana nan kasan bata yarda abar wani da yunwa a gidan nan ba, dan haka zan jarraba bata Abinci ko zata ci"
Isa yace "ai se kai tayi ɗan wahala, ga hanyoyin neman lada nan ba adadi, amma ka tsaya wahalar da kanka akan abar data kusa mutuwa"
Murtalah be kuma kula shi ba, yaje ya siyo biscuit katako, da madara 'yar talatin yazo ya haɗa ya bata, ai nan da nan magen nam ta lamushe, saboda azabar Yunwa da take ji, abunka da dabba da sabo, tana jin ƙwarin jikinta ta koma ɗakin Widad, tana kuka ta hau kan gadonta ta sauka, ta fito falonta zuwa babban falo.
Ramlah tace "wai dama wannan shegiyar halittar tana raye bata mutu ba?"
Amal tace "ni kaina na zata ta mutu fa"
Ramlah tace "aikuwa ƙarasata zanyi, sena kasheta"
Amal tace "ke Ramlah, ina ruwanki da ita? Me tayi miki?"
"ke nifa duk wani abu daya shafi waccan banzar ba sonsa nake ba, tunda Allah yasa ta bar gidan nan mukayi 'yanci, muke warwasawa son ranmu, babu tsawa balle hantara, shiyasa bana son ganin duk wani abu daya shafeta balle raina ya ɓaci"
Amal tace "dukda haka dai karki huce akan magen nan danni tausayinta nake ji, itama magen wata kinibabbiya kamar uwarɗakinta, bata zuwa ko ina se tare da ita, ai gashi yanzu tana wahala"
Ramlah tace "tunda uwaɗakin nata bata nan, ai itama seta ƙara mai"
Da ƙyar Yusuf ya iya tashi sallar Asuba saboda daɗewar da suka yi basu yi bacci ba jiya, hadari yana ta cida, da akama ruwan sama za'ayi.
Ya tashi Widad sannan yaje yayi alwala ya fita salla, sedai harya dawo bata tashi ba, hannunsa yaje ya wanke yazo yana shafa mata ruwan a fuskarta.
A hankali tayi miƙa, ta koma ta kuma lumshe idonta, ɗagota yayi daga kwanciyar gaba ɗaya ya ɗan ƙura mata ido sannan yace "wai wani darem za'a kuma yi miki ne?"
Kasa buɗe idon tayi saboda baccin da take ji, hannayenta ya shiga matsawa yace "kalli gari ya wayefa, buɗe idonki ki gani"
. A hankali ta buɗe idonta, tabbas gari ya fara hasks duhun Asuba ya yaye, ta kalle shi tace "meyasa baka tasheni ba"?
"na tasheki baki tashi bane" a hankali ta zauna sosai, sannan ta miƙe taje tayi alwala tazo ta tada salla, Yusuf yana gefe yana cigaba da lazumi, ya kwaɗaitu da son jin ƙarshen labarin Widad, sedai yasan halinta da rikicin tsiya, idan bata ga dama ba haka zatai ta ja masa rai ba zata gaya masa ba, idan ya takura ta se yaji kuma suyi faɗa.
Data idar da sallar ta fara lazimi ta kife a gurin, yana kallonta da alama bacci ne sosai a kanta, ya tashi a hankali ya ɗagata ya maida ita kan katifar, still yana jin tausayinta yana ratsa ruhinsa da ganganr jikinsa.
Ya kwanta a bayanta cike da fargabar kar ta tashi ta kama masifa, tunda ba ita tace ya kwanta ba, sedai ta ɗanyi juyi taji shi a bayanta, a hankali ta juyo tana fuskantarsa, ba tare da ta buɗe idonta ba, ta zura hannunta ta rungumeshi, ta kwantar da kanta a jikinsa, a haka bacci ya sake yin awon gaba dasu.
Har shaɗaya da rabi na Safe basu farka ba, Hari sunata aikace aikacen su a tsakar gida, ta kalli Gwaggo tace "Yaya, har yanzu fa Wudas basu fito ba, lafiya kuwa?"
Gwaggo tace "lafiya ƙalau insha Allah, ai da Asuba shi yaja salla, dan haka lafiya ƙalau"
"Yaya sha ɗaya da rabi fa"
Hansai tace "A'a haba Yaya Hari, abu na mata da miji ina ruwanki? Ba suyi niyyar fitowa yanzu bane"
Hanne ji tayi kamar ta faɗi ƙasa dan haushi da takaici.
Widad ce ta fara farkawa, ta buɗe idonta taga yadda rana tayi, a hankali ta bar jikin Yusuf ta tashi zaune, garin ta tashin ne shima ya farka, ya kalli garin yadda rana ta buɗe, yace "Subhanallah, rana tayi ma"
Widad tace "Aikam dai, kasan bamuyi bacci da wuri ba, shiyasa"
Yusuf yace "hakane, gashi ko breakfast bakiyi ba, bari in tashi idan akwai Abinci a gurin Gwaggo shikenan, in babu se inzo in dafa"
Widad tace "karka damu ni bana jin Yunwa, wanka nake son inyi amma ina son Ka temakamin in wanke kaina, gani nake kamar baha fita yana damuna sosai saboda babu gyara"
Yusuf yace "to aini ban san yadda ake yi ba, ban san yadda ake wanke gashi ba"
Widad ta kalleshi tace "eh amma ka iya taɓawa ai"
Yusuf yayi murmushi yace "wannan ai me sauƙi ne, dan bana gajiya da taɓawa, amma wankewa ni ban san yadda ake yi ba"
"Yau zaka koya kuwa, zan karɓo ruwa a gurin Gwaggo seka tayani mu wanke"
Yusuf yace "wait, waima a ina zamu wanke kan? Ba dai banɗaki ba"
"Koma a inane" ta bashi amsa
Yusuf yace "kawai se aga mun shiga banɗaki tare? No banda wannan, sannan da kunya aga na taƙarƙare ina tayaki wankin kai a tsakar gida, ki bari seda daddare, muje toilet mu wanke gashin, yadda ba wanda ze ganmu"
Hararar Yusuf tayi tace "ni yanzu nake so, idan aka wanke kafin dare ya sha iska, in aka wanke daddarw na kwanta ai wari zeyi tunda babu shampoo"
Yusuf yace "ni ya zanyi, kawai aga mun shiga banɗaki tare? Da kunya fa"
"Au wai nan kunya kake ji, amma ai baka jin kunyata tunda..
" tunda me? "
" ban sani ba"
Murmushi yayi yace "Allah ya barni da abar sona, ina sonki Habibty na, kura kike ga tsoro ga ban tsoro"
Suleiman ne tafe yana driving a motarsa, yana sauraren radio yana jiran ƙarfe huɗu ta cika ya saurari labaran yamma, kanin labaran ne suka ɗauki hankalinsa, hakan yasa shi maida hankali don jin cikakkun labaran.
Labarin farko da aka sanarne ya ɗau hankalinsa, ya kaɗashi matuƙa ya tayar masa da hankali, be gama tsinkewa da lamarin ba, seda ya ƙarasa traffic ta tsaida hannun da yake, wani yaro yazo ya tsaya a window motarsa yana masa tallan jarida, shafin farko ya kalla yaji gabansa yayi mummunar faɗuwa.
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
MASU FITARMIN DA LITTAFI KUMA, IN DAI DAI KUKE KUN SANI IDAN AKASIN HAKANE MA KUN SANI
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
70_71
Da rawar jiki Suleiman ya sayi jaridar nan yayi parking a gefen titi, hoton Yusuf ne a bangon jaridar an rubuta wanted, ya buɗe cikin jaridar ya shiga duba shafin da labarin yake, wai 'yan sanda sun fitar da sakamakon binciken da suka yi akan ɓatan 'yar gidan Daula, bincike ya tabattar musu da direban Widad Nasir Daula wanda aka sani da Yusuf, shine ya sace Widad yayi garkuwa da ita, ba sace su akayi tare ba, dan haka jam'ian tsaro suna nan suna binciken inda suke, sannan duk wanda ya gano inda suke ya faɗa akwai kyauta me tsoka.
Gaba ɗaya jikin Sulaiman yayi sanyi, akanme za'a fitar da wannan sakamakon binciken? Meye dalili? Cikin hanzari ya juya sitiyarin motarsa zuwa wani gurin, tuƙin kawai yake amma hankalinsa sam baya kan abunda yake yi, Allah ne ya kaishi inda yake son zuwa.
Harabar headquarter 'yan sanda yaje yayi parking ɗin motarsa, ya fita da sauri daga cikin motar, yana shiga harabar gurin ƙananan' yan sanda sunata sara masa, cikin gaggawa ya nufi wani office, ya buɗe ya shiga suka gaisa da ma mallakin Office ɗin, Suleiman ya zauna ya miƙa masa jaridar hannunsa sannan yace "SP waye ya fitar da sakamakon wannan binciken haka? Har aka sanar da 'yan jarida?"
SP yace "kamar yaya kenan? Sakamakon binciken da akayi kenan, kuma aka bada umarni mu sanar"
Suleiman yace "haba SP, wannan yaron fa jami' inmu ne, ta yaya kake tunanin ze iya aikata wannan mummunan aikin haka, sam ba haka abun ya faru ba, ta yaya za'ace Yusuf ne yayi garkuwa da 'yar gidan Daula? Ta yaya?"
"Kaga karka zo ka ɗagamin hankali mana, nima umarni aka bani inyi wannan Sanarwar kuma nayi, meye nawa a ciki?"
"An gabatar maka da sakamakon binciken da akayi kafin kayi wannan Sanarwar, wannan fa tamkar ɓatawa hukumar' yan sanda sunane, ta yaya wasu tsirarin mutane zasu sa ku saɓa dokar aikinmu saboda biyan buƙatarsu?"
SP ya kalli Suleiman yace "ya akayi kasan wasu tsirarin mutane ne suka sa ayi hakan?"
Nan da nan Suleiman ya dawo hayyacinsa ya daidaita nutsuwarsa yace "to koma dai a cikinmu ne mukayi hakan ai munsan mun saɓa dokar aiki, yaron nan abokin aikinmu ne, jajirtaccen ma'aikaci ne mara ƙyuya, ga gaskiya a harkar aikinsa, ya dace ayi masa haka, zan iya rantse maka ko a wasa Yusuf baze aikata haka ba"
SP yace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, kai kake zaune dashi kasan halinsa, ni babu ruwana sakamakon da aka gabatarmin shi zan bayyanawa al'umma, dan haka in baka da abunyi zaka iya bani guri, ina da baƙi"
Cike da baƙin ciki da ɓacin rai, Suleiman ya baro office ɗin nan, gaba ɗaya tausayin Yusuf da mamaki suka cika zuciyarsa, tabbas idan akayiwa Yusuf haka an zalunce shi, kuma an zubar da kimar aikin ɗan sanda a idon duniya.
Saleh ne yayi jifa da jaridar hannunsa yace "Impossible, Alhaji Musa anya kanaso mu gama da duniya lafiya kuwa? Ta yaya za'ace anyi masa wannan ƙazafin haka? Abun yayi yawa, yakamata mudinga yi muna jin tsoron Allah"
Alhaji Musa yace "kai dakata! Meyasa ba zamu nemawa kanmu mafita ba? Ina ruwanmu da koma wani hali ze shiga, ai ba ƙarya akayi masa ba, in ba hakaba meyasa da suka gudu basu dawo ba, waye yasan inda suke? Dan haka shiya saceta yayi garkuwa da ita, kuma ya koma yayi garkuwa da mahaifinta, ai mafita muke nemawa kanmu, ɗan sanda nefa, yanzu idan ya dawo asirinmu ne ze tonu, dan haka gara da mukayi masa haka, idan kuma baka cikinmu ne zaka iya ƙarawa gaba"
Saleh yayi shiru cike da takaici da baƙin ciki, ya rasa mema yakamata yayi, idan aka yi haka an cutar da rayuwar Yusuf ba kaɗan ba, rasa abunyi yayi kawai ya juya ya fice a matuƙar fusace.
Hari tana ta fifitar Wuta, ta kuma kallon ƙofar ɗakinsu Widad tace "taɓ amma wannan abu yayi yawa haka, ai kome suke yaci ace sun fito haka, sha biyun rana fa wane irin abune haka?"
Banza Gwaggo tayi da ita, yayin da Hansai tace "ke kuma sa idonki yayi yawa, ina ruwanki da koma me suke yi ina ruwanki? Kedai bakya rasa abun faɗa shiyasa duk tabi ta raina ki"
"to naga abun magana bazan magana ba? Ai abun da damu ace garin Allah ya waye, har wannan lokaci suna ƙule a ɗaka, idan wani abun ya samesu fa"
Widad ce ta fito hannunta ɗauke da bokiti, ta ƙaraso inda Gwaggo take ta gaisheta, tace "A temakamin da ruwa, ina so da ɗan yawa zan wanke gashina ne"
Gwaggo ta karɓi bokitin, taje rumfar da suke girki ta Ɗebo mata ruwan, Yusuf a kunyace ya fito suka gaisa da mutanen gidan, yaje ya Ɗebo ruwa a rijiya ya sirka ya kai banɗaki.
Widad ta ɗakko abun wanka, tazo ta shige banɗaki, Yusuf ya rasa yadda zeyi ya bita toilet ɗin nan saboda kunya, leƙowa tayi tace "Yoseef ka shigo mana, kose ruwan yayi sanyi?"
Hari ta tsaya tana kallon ikon Allah, haka Yusuf ya shiga banɗakin nan, ta cire hijjabin jikinta daga ita se towel, ta cire ribbon ɗinta, ta zauna akan kujera, Nan Yusuf ya shiga tayata wanke gashin nan me matuƙar tsawo da yawa.
Hansai kam burgeta sukayi, yayin da Hari ta taɓe baki tace "ni tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin baɗalar da nake gani a gurin bayin Allah nan ba"
Hansai tace "taɓ wallahi nikam birgeni sukeyi, yanzu kai anan ka isa miji ya wani ta yaka wanke kai, yadda yake ɗawainiya da ita ba ƙaramin birgeni yake ba"
Hari tace "mhmm, ai ko sharar ɗaki baki isa miji anan ya tayaki ba, balle wani wanke kai, ai maza suna birni, mu nan se godiyar Allah kawai"
Hansai tace "me kike nufi to?"
"Ni ba abunda nake nufi, karki ƙullamin sharri"
Haka suka cigaba da maganganunsu.
Yusuf dai bega wani datti da kan Widad yayi ba, ta dai damune kawai ta wanke kan nata, tunda ta saba wanke shi akai akai.
Seda ta gama ya bata guri tayi wanka, duk ya jiƙa kayansa da ruwa, Widad tayi wankanta ta kammala sannan ta fito, Towel ɗin nan kawai ta ɗauro ta fito, gashin nan ya baje a bayanta se ɗigar da ruwa yake.
Ai gaba ɗaya sukabi Widad da kallo, tubarkallah Allah yayi mata kyau da halitta me ɗaukar hankali, ta kama ƙasan gashinta tana yarfewa, ga towel ɗin iyakacinsa gwiwarta, fatarta se sheƙi take.
Hanne tabi Widad da kallo, tana tunanin me zata yi mata ta huce wannan baƙincikin, Widad kamar da gayya take juya jikinta har ta shiga ɗakinsu.
Hindu ta lura da irin kallon da Hanne ke yiwa Widad, dan haka tace "Masha Allah, Allah me halitta duk mutumin da yake da mace kamar Amarya, wallahi babu me kama da bayan tukunyar daze kalla balle yayi sha" War Aurenta, kamar ita tayi kanta masha Allah "
Hanne ta kalli Hindu, taja tsaki tayi tafiyar ta abunta.
Yusuf ya kalli Widad yace " Masoyiyya ba dai a haka kika fito ba? "
" A haka na fito menene? Ai dai naga ba maza"
"Anya kin san irin kyawun halittar da Allah yayi miki, koda ba maza baki abun gudu ne, dan Allah karki kuma fita a haka"
"Kaga nifa na fara jin yunwa"
Yusuf yace "maganar tawa ce bata da amfani ko? Shine kike sharewa"
Shiru tayi masa ta nemi guri tayi zamanta.
Hindu tayi sallama ƙofar ɗakinsu, ta kawo musu Abinci, Yusuf ne yaje ya karɓo ya dawo ya zauna, Widad bata da niyyar saka kaya, a haka take zaune abunta, Yusuf kam se ƙureta yake da ido, gaba ɗaya ya rasa sukuni har suka kammala cin Abincin idonsa a kanta.
Bayan sun gama yace "yau kuma baza'a sa kaya bane?"
"zan saka ban shafa mai bane"
Yace "Kawo in shafa miki"
Ɗakko zaitun tayi ta miƙa masa, ta koma ta zauna tana cin jiƙaƙiyar aya da Hindu ta koya mata ci.
Yana shafa mata man yanajin fatarta kamar ze ji mata rauni idan beyi a hankali ba, Yusuf yace "me kike cine haka?"
Tace "Hindu ce ta bani, ina son wannan abubuwan da Aya, da wata baƙar aba mulmulmulalliya, da yama sunanta wani abu baƙa cikinsa ja ƙanana me ɗan tsami tsami"
Yusuf ya jinjina kai yace sannu bagwariya, ɗinya da tsamiyar biri dai ko? "
Widad tai murmushi tace " what ever dai "
Haka ya kammala shafa mata mai, se sheƙi fatar take saboda man zaitun daya shafa mata, yaje ya buɗe Akwatinta ya ɗakko mata kaya, Ya kalleta yace " bari in samiki "
Tura baki tayi tace "A'a bana so"
Yusuf yace "Meyasa ba kyaso? Ai tunda na shafa miki mai saura sa kaya kuma"
Tace "A'a ni gaskiya bana so, ka ƙyaleni kawai in saka abuna"
Kokawa suka shigayi ita da Yusuf, aikuwa ta buɗe baki ta shiga kiran sunan Gwaggo da ƙarfi, ba shiri ya cikata ya ƙyaleta, dan a wautar Widad ba taƙi azo a tarar dasu a haka ba in be ƙyaleta ba, ta koma gefe tana harararsa hadda murguɗa baki.
Yusuf yace "Ni kikewa wannan ihun Masoyiyya?"
"An maka ɗin, waye yace kamin abunda zanyi ihun?"
Murmushi yayi yace "Shikenan Allah ya baki haƙuri"
Zumɓura masa baki tayi, ba tare da tace komai ba.
Labari ya game gari a game da Yusuf, Nurat tana kwance tana kallon labaran dare a TV aka nuno zancen Yusuf, ta kaɗu matuƙa da ganin labarin da gudu ta tafi ɗakin mahaifiyarta tana ƙwala mata kira.
"Ke lafiya kike ƙwalamin kira hak?"
"Mummy kinga abunda na gani kuwa?"