Showing 27001 words to 30000 words out of 209297 words
da tayimin, amma bari in gaya maka yadda akayi tasan waye shi, wataran da yamma na kammala abunda nake zan bar office ɗin nan, kawai sega wata mota ta shigo gurin nan a guje, kamar zata tashi sama,
ma' aikatanmu sukayi kanta don son ganin wane mara ɗa'ar ne haka? Ko a jikin me tuƙin, Ta buɗe motar ta fito, wata matashiyar budurwa ce jikinta sanye da abaya, ta saka face mask, sannan ta rufe fuskarta da glass.
Kai tsaye inda nake ta shiga tunkarowa, da ma'aikatanmu sunyi kanta zasu hanata ƙarasowa, nace su barta ta ƙaraso.
Ko kallonsu batayi ba tazo inda nake ta tsaya ta kalleni tace "kaine Suleiman?"
Nace mata "Eh nine"
Tace "ina son muyi maganane"
Nace mata shikenan, nai mata jagora har office ɗina, muka shiga muka zauna, ta kalleni ta cire glashin fuskarta da face mask tace "kasanni?"
"Nace mata a'a"
Tace "Amma kasan Nasir Daula?"
Nace "ai duk Nigeria babu wanda be sanshi ba"
tace "sunana Widad Nasir Daula, nazo me zan maka wasu tambayoyi, kuma idan ka amsamin ba dai dai ba, ka shirya karɓar abunda ze biyo baya, bana sassauci ga mutane maƙaryata, waye Yusuf?"
Suleiman yayi ajiyar zuciya yace "wane Yusuf ɗin?"
"Direbana" ta bashi amsa
Suleiman yace "Yusuf jami'inmun ne, ɗan sanda ne na farin kaya" Suleiman ya bata amsa
"danme zaku turoshi? Me yasa kuka turoshi,? wato an haɗa kai daku a cuceni"
Suleiman yace "Yusuf bashi da laifi, jajirtaccen ma'aikacine me kishin ƙasa, umarni aka bamu daga sama akan cewar, a baki kariya sannan kuma ayi bincike akan wanda suke bibiyar rayuwar ki, amma bayan haka Yusuf be san komai ba"
Cikin isa da izza tace "akan me? Sannan kuma waye ya bada umarnin hakan? Ko kuma ni nace ina buƙatar hakanne? An haɗa kai daku za'a cutar dani, in ba hakaba meyasa Yusuf yasa hannu akan takardar zeyi aiki dani, dukda na gaya masa hakan tamkar saka hannu akan kwangilar mutuwarsane? Na kama Yusuf da bindiga"
Tun anan Suleiman ya jinjinawa Yusuf, ya yabawa ƙoƙarin sa na jure zama tare da yin aiki da Widad, saboda yadda take magana cike da izza da isa.
Suleiman yace " kamar yadda na gaya miki, Yusuf jajirtaccen ɗan sandane, kuma ba abun mamaki bane samun ɗan sanda da bindiga, sannan Yusuf baza'a taɓa bashi aiki ya dawo dashi yace ya karaya ko baze iyaba, amma sam bashi da laifi, kuma da farko bashi mukayi niyyar bawa aikinba, abokin aikinsane yace a bashi saboda jajircewarsa da haƙurinsa"
Ajiyar zuciya Widad tayi tana huci, inda Allah ya temaki Sulaiman gaskiyar data buƙata ita yake gaya mata, ta kalle shi tace "Ina buƙatar sanin waye yasa a dinga bin diddigi na?"
Suleiman yace "kamar yadda na gaya miki ne, ban saniba nima umarni aka bani daga sama, ban san komai akai ba"
Widad tace "shikenan, ni zanje in bincika da kaina, amma zan maka gargaɗi da jan kunne, Yusuf be san na ganshi da bindiga ba, kada ka kuskura Yusuf yasan nasan waye shi, idan har ka gaya masa nasan waye shi zan gane, and you know what am capable of doing"
Suleiman yace "karki damu, Insha Allah baze sani ba, bazan gaya masa ba"
Tace "and Mark you, bana son kowa yasan da nice nazo gurin nan, and zan cigaba da bibiyarka, duk lokacin da Yusuf yayi misbehaving ko wani abu na yunƙurin cin amana ta, to dasa hannunka a ciki"
Suleiman yace "ina me tabattar miki da babu abunda zeyi na cin amanarki"
Ta miƙe a gadarance, ta maida face mask ɗinta, ta saka glass ɗinta ta fito, sedai tana fitowa Abbas ya kawo kai yana shigowa, ta tsaya ta ƙura masa ido, harya shige wani office, sam Abbas be lura da kallon da take masa ba, ba tace komai ba tayi gaba da sauri ta hau motarta ta bar gurin.
Bayan wasu 'yan kwanaki da yin hakan, Widad ta kira Suleiman tace tana son ya gayamata full name na Abbas da rank ɗinsa, amma Suleiman yace hakan ya saɓa da ƙa' idar aikinsu, sedai ta gaya masa meyasa take neman hakan, bata kuma bi takansa ba bayan kwana uku, aka kawo transfer later na Abbas aka maye gurbinsa da Yusuf.
Saleh ya jinjina kai yace "wato duk inda mutum yake tunanin hatsabibancin yarinyar nan ta wuce haka, yana cam yana ta zullumi akan yadda ze gayamata, ashe tuni ta sani"
Sulaiman yace "tabbas tasan waye Yusuf, kallonsa kawai take sannan kamar yadda naimata Alƙawari ban gaya masa ba"
Saleh yace "Allah sarki, ni gaba ɗaya tausayi yake bani wallahi, bejiba be gani ba yana ta ɗawainiya da yarinyar ta bata san kimar mutane ba, duk naga ta rage wannan zafin kan nata, ta kwantar da mai tana rayuwa a ƙauyen da babu wuta, babu ruwa babu abubuwan more rayuwa, abun gaanin ban tausayi"
Suleiman yace "Allah sarki Yusuf, samun mutum me irin zuciyarsa se an tona, ina masa fatan ubangiji Allah ya kuɓutaf dashi, daga sharrin Azzaluman nan"
Saleh yace "Ameen ya Allah, amma tabbas Yusuf yana cikin jarrabawa, dan ina tunanin matakin da zasu ɗauka akansa, basu da imani sam"
Suleiman yace "Allah ya fisu kam, amma indai batun sadaukarwa ne, to tabbas Yusuf yayita"
Haka suka cigaba da tattaunawa a tsakanin su.
Se bayan la'asar, lokacin kayansu sun bushe sannan Yusuf ya tattaresu ya ninke, suka kamo hanyar gida, suna tafe suna hira gwanin ban sha'awa, Widad nata takura masa da tambayoyi dan duk abunda ta gani bata sani ba seta tambaya.
Suna zuwa gida Gwaggo tai murmushi tace "Amarya yau gidan nan ba daɗi ba kya nan, duk naji ba daɗi"
Widad tai murmushi tace "nima haka naji ba daɗi yau Mama"
Hindu tace "wallahi kuwa Gwaggo, gaba ɗaya yau gidan se a hankali ba daɗi da bakya nan"
Hari tace "Nikam naji daɗi, bakin mutane shiru yau ba neman magana"
'
Widad tace "in mutane na magana ki dena saka baki, danke ba mutum bace"
Gwaggo tace "Amarya yau wake muka dafa, ban sani ba ko zaki iyaci, dan haka na dama miki kunu gashi can da zafinsa"
Widad tace "wayyo Allah Mamana ta kaina, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, wakenma duk zan iyaci nagode sosai Mama"
Gwaggo tace "Babu godiya a tsakaninmu ai"
Yusuf kam bayan sun gama gaisawa, ɗakinsu ya wuce, ya bar Widad tana cigaba da neman maganarta.
Hari tana ta ƙulla gyaɗarta ta siyarwa, Widad tazo ta cika hannu ta zuba a hijjabi tayi ɗaki, Hari ta buɗe baki tace "Wudas yaseen sekin biyani kuɗin gyaɗar nan"
Gwaggo tace "yi haƙuri, zan baki kuɗin"
Seda tayi me isarta sannan ta koma ɗakin, Yusuf tun yana mamakin halin Widad har ya dena, ta kwaso kwanukan wanke wanke tayi, gaba ɗaya yau wani irin nishaɗi take ji, taji daɗin fitar da suka yi sosai, wani irin farinciki ya dinga ratsata.
Ta karɓo musu Abincin gurin Gwaggo, suka zauna suka ci, bayan sun gama ne ta ɗanyi shiru sannan tace "Naji daɗin fitar nan sosai Yoseef, ban taɓa tunanin ana samun farinciki haka ba koda babu dukiya"
Yusuf yace "aishi farinciki da jin daɗi base ka tara dukiya ba, indai zakayi tawakkali da yadda Allah ya ajiyeka, zakayi rayuwarka cikin farin ciki da jin daɗi, kuma har kafi me Dukiya walwala ma".
Widad tace "ƙwarai kuwa yau na gani, rabon da inyi farinciki haka tun Ammi na nada rai, shekara goma baya kenan"
Yusuf yace "kina nufin duk tsawon wannan shekarun, bakya farinciki?"
"tun bayan rasuwar Ammi, ban kuma samun farinciki haka ba, babu club ɗin da bana zuwa a waje, dan inyi nishaɗi, nice club ɗim wrestling stadiums na ball da sauran wasanni, amma babu sauyi, na kanji nishaɗi ne kawai idan nai wasan doki, kona kasance da dabbobi kuma idan ina Tare da Alhaji Nasir Daula "
'yar Wulaƙanci yau kuma saunan baban nata take faɗa gatsal"
Ta cigaba da cewa "nasan Daddy zeyi murna sosai, idan ya ganni cikin walwala haka, danya fidda ran faruwar hakan a rayuwata" ta ƙarasa maganar muryarta na rawa alamun zata yi kuka.
Rungumota Yusuf yayi yace "haba Jarumata, kuma Gimbiya ta, karkiyi kuka please kiyi haƙuri kinji babyna, nifa jarumtar nan taki burgeni take yi, dan haka idan muka koma gida, zan saki a aikin ɗan sanda kema"
Kwashewa tayi da dariya, tace 'kai dai kaje kaita aikin ɗan sandan, nikam a kai kasuwa "
" Zaki iya kama' yan fashi fa da ɓarayi da wannan dakakkiyar zuciyar taki Baby"
Shiru ta ɗanyi tace "da wanda suka kashemin Ammi ma ko?"
Yusuf yace "am just kidding, idan wanda suka kashe mahaifiyarki ne, Insha Allah ni zan ɗau nauyin yin wannan binciken"
Girgiza masa kai tayi tace "this the most dangerous case, don't take the risk of it, ni suke bibiya suke son ganin bayana, dan haka koni ko su, karka sa kanka a ciki, a yanzu ma kalli yadda kake wahala"
Yusuf yace "Amma suwaye suka kashe ta, kuma meyasa? '
Widad tace " nima ban sani ba"
Yusuf yace "i have to know even a little bit of your life"
"bazan faɗa ba, ban yadda da kai ba" tai maganar tana dariya.
Yusuf yace "ai yadda ta ƙare, tunda muka zama abu ɗaya, har muka kasance a inuwa ɗaya"
Hararsa tayi tace "wace irin inuwa ɗaya"
"Inuwar Aure mana Baby na, kuma gashi.... Sekuma yayi shiru
Widad tace " Kuma gashi me? Ƙarasa mana, kai ko kunyata na baka ji ko? Allah ya shiryeka, ni cikani"
Ƙara rungumeta yayi yana murmushi yace "Kunyarwa zanji? Mutum da matarsa"
"Matar ƙauye ba, dan iya nan ne, kafin mu koma gida zamu rabu'
Murmushi kawai Yusuf yayi bece mata komai ba, a hankali yace " ki gayamin mana "
" wai mai meyasa ka damu se kaji tarihin rayuwata? Ko nima binciken ake a kaina? "
Yusuf yayi dariya yace " wane ni?"
"idan kana son in baka labarin, kwanta in kwanta akan ƙirjinka"
Yusuf yace "dan dai wannan, ai shi yafi komai sauƙi"
Yusuf ya kwanta, ta kalle shi tace "kuma wallahi idan kamin wani abu, se munyi faɗa na gaya maka"
Yusuf yace "idan nai miki me?"
"Bansani ba"
"Allah ya baki haƙuri, niba abunda zanyi miki"
A hankali ta kwanta akan ƙirjinsa, tayi shiru na wani ɗan lokaci
WACECE WIDAD NASIR DAULA.....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
60_61
Kallonsa ta ɗanyi tace "ina fatan Allah ya rabaka da son abunda ba zaka samu ba, na gaya maka babu Aure a tsarin rayuwata, bazan ji daɗi ba ace wani abu ya sameka saboda ni ba, amma ina fatan zumuncinmu ya ɗore nida kai"
Yusuf yayi Ajiyar zuciya yace "naga jarrabawa daban daban a rayuwata, ciki harda Jarrabawa a kan Soyayya, sam bani da sa'a a wannan ɓangaren, dukda tarin gargaɗi da kashedin da kikemin akan Sonki da nake, nakasa jin zan iya dena sonki, a kowane lokaci ina sake jin sonki a raina"
Shiru tayi suka cigaba da tafiya, ba tare da sun sake cewa komai ba.
Ta kalli Yusuf tace "ko mu tsaya ka huta ne? Saboda ƙafarka"
Yusuf yayi murmushin yaƙe yace "waye yace miki nagaji ne? Ko ance miki nima ragone irinki?"
"Nice ma raguwar?"
"Eh kece, me tsoron rago da spider ba"
Dariya tayi tace "kaikam baka mantuwa ko? Saura mu koma gida kace ga abunda nayi ka jamin raini"
"Ni na isa in faɗi abunda Gimbiya tayi, ai wannan sirrine kuma tarihi ne me matuƙar girman gaske daze zauna a zukatanmu nida ke"
Widad tai murmushi tace "gaskiya ne, wannan rayuwar ba zata taɓa gogewa a zuciyata ba"
Yusuf yace "dukda ragoncin nan naki, akwai inda na jinjina miki Gimbiya, ban taɓa tunanin samun jarumar mace kamarki ba, yadda kika sa hannu kika rama dukan da kidnappers ɗin nan sukayi miki, na jinjina miki ta wannan fannin"
Murmushi tayi tace "hakan ya samo asaline tun daga ƙuruciya ta, Allah Sarki, Allah ya jiƙan Ammi na da Baban Yoseef"
Da sauri ya kalle ta yace "Kaman Babana kikayi wa Addu'a"
Tace "Eh iyayenmu da muka rasa nayiwa Addu'a, ko baka so"
"Ni na isa imce bana so, Ameen ya Allah, ubangiji Allah yayi musu Rahama"
"Ameen"
Sunyi tafiya me nisa sannan suka iso rafin, ba kowa a gurin, gurin shiru se kukan tsintsaye, da kaɗawar bishiyu.
Widad tace "Wow masha Allah, ɗan uwa gurin nan yayi kyau sosai"
"enjoy yourself"
Yusuf ya shiga aikin yi musu wanki, yayin da Widad keta kalle Kallen tsuntsaye.
"Ɗan uwa da ruwan nan yana da kyau sosai, da swimming zanyi"
"kin iya ruwane?"
"Taɓ sosai ma, na iya ruwa sosai fa, ina shiga"
"Ai da alama kina da rashin ji, ba wanda ze gane hakan se wanda yake zaune dake"
"Wanda yake zaune da ni ɗin ma ba kowa ne ze gane hakan ba, kaima ban san yadda akayi na sake da kai haka ba, haka kurum naji kamar in yadda da kai"
"Aikin gama ya gama ai, kinma yarda dani ni ɗin"
Cigaba tayi da wasanninta a gurin, tayi nan tayi can ta Leƙa nan ta leƙa can, Yusuf yana ta wanki har ya kammala, yai shanya ya zura ƙafafinsa a cikin ruwan, kusa da Yusuf tazo zauna itama ta zura ƙafafunta a ruwan tana kallonsa.
"Meye kuma kike kallona?"
"Me zan kalla?"
"Muni mana" ya bata amsa
Murmushi tayi tace "kaine mummunan? Ai baka da muni sam"
Murmushi kawai yayi, yana jefa dutse a cikin ruwan.
Widad tace "kasan wani abu?"
"A'a sekin faɗa"
"Ban taɓa sanin a duniya akwai mutane nagari kamarka ba, da ina yiwa talakawa kallon mayun kuɗi, maciya amana, amma gaba ɗaya you proves me wrong"
Yusuf yace "dama bekamata ka yankewa mutane hukunci da laifin tsirari daga cikinsu ba, duk lalacewar zamani akwai na kirki"
Widad tace "Aikama nagani, dan yadda nake treating ɗinka a gida ban taɓa zaton zaka iya taimakona ba, nayi mamakin ganin hawaye a idonka lokacin da ni kaina na yanke tsammani da cigaba da rayuwa"
Ta ƙarasa maganar tana kwanciya a jikin Yusuf.
"Habibty, a wannan lokacin da kin mutu ban san ya zanyi ba, Nagode Allah da ya nunamin na Aure ki, dukda ba kya sona"
Shiru tayi ba tace komai ba, can Yusuf yace "Widad, yanzu idan na mutu zaki damu?"
Tsaki tayi tace "wace irin tambaya ce wannan?"
"Tambayarki kawai nayi"
"To wannan wace irin tambaya ce mara amfani, kawai muna hira ka kama wannan zancen ni bana so"
Ɗagota Yusuf yayi ya kalli idonta, ƙwallace kwance a idonta, se wani tura baki take, murmushi yayi ya maida ita jikinsa ya kwantar da ita, ya shiga shafa bayanta.
Ɗagowa tayi ta kalle shi tace "Ɗan uwa"
Yusuf yace "Yaushe na zama ɗan uwane, naji kin canza min suna'
" Gwaggo ta hanani faɗar sunan ka, kuma kaga ni bani da ɗan uwa, se gaka ka bani jini, kaga mun zama 'yan uwa tunda an samun jininka, mun zama' yan uwa kenan"
Dariya Yusuf yayi yace "wannan philosophy ɗinfa,? Lallai kam shikenan nima nayi ƙanwa tunda bani da ƙanwa mace"
Ta gyara kwanciyarta a jikinsa tace "Yoseef, idan muka koma gida zaka dawo gidanmu ka zauna kaida ummanka?"
"Ai muma muna gida" ya bata amsa
"Dan Allah ka dawo gidanmu, nasan bazaka cigaba da tuƙani a mota ba, nasan maybe ma in koma ƙasar waje, amma dan Allah ka dawo gidanmu kaji"
Girgiza mata kai yayi yace "so kike Mamansu Amal ta dinga wulaƙanta Ummana? Kuma zaman me zanzo inyi a gidanku, bayan bamu da wata alaƙa, kafin nan fa mun rabu"
"Dan mun rabu shine zaka ce bazaka dawo gidanmu ba, sannan idan na koma gida dole ta bar mana gida"
Yusuf yace "meyasa?"
"Saboda wani dalili me girman gaske, amma yanzu ba wannan maganar muke ba, dan Allah idan mun koma gida ka dawo gidanmu da zama,"
"Nida bakya sona, me zan zo gidanku inyi? Idan dai har ina ganinki zan cigaba da sonki ne, kuma ni bakya sona"
"Nifa ba tsanarka nayi ba, kawai ni bana son soyayya ne, ban santa ba kuma ban iya ba, dan bata birgeni, ƙarya ce da tarin damuwa a cikinta, amma ni bana son ko mun koma gida kayi nesa dani, na saba da kai sosai, kana iya haƙuri da dukkanin halayena, kuma kai garkuwa ne a gareni, dan Allah Yoseef ka yadda kaji ɗan uwa"
Yusuf kam murmushi yayi, a ransa yace 'sarkin taurin kai, kina sona amma kina garani'
A fili ya maze yace "Idan muka koma gidanku ace munje kwaɗayi, ni nafison in zauna a gidanmu nida Ummana"
"dan Allah, ba wanda zece muku haka, Dan Allah Yoseef kaji"
Juyowa yayi yana kallonta, har cikin ranta take maganar.
Wani abune ya dinga fizgar Yusuf game da Widad, yana jin wani irin farinciki a tare da shi, abunda bata son dai yayi mata, sedai wannan karon bata hana shi ba, sema biye masa da tayi.
A hankali ya cire bakinsa daga nata ya riƙe hannunta yace "ina sonki Habibty"
Ajiyar zuciya tayi ba tace masa komai ba.
Kawai ya tsaya ya zuba mata ido, a hankali tace "yakamata muje muci Abinci"
Yusuf ya cikata, suka miƙe ya shimfiɗa musu abu suka zauna, ya buɗe shinkafa da wake, da manja ya ɗakko tumatir da gurji ya yayyanka, ya juya suka fara ci.
Suna ci yana kallon Widad, ta kwantar da hankalinta, ta rugumi ƙaddarar rayuwarta, da farkom zuwansu ne se yayi fama kafin taci Abincin, amma yanzu hankali kwance ta dinga cin Abincinta.
"Wai meye kake kallona haka?"
"Gani nayi kina loma fiye da tawa, zaki cinye Abincin ki barni"
"Cigaba da kallona, cinyewa zan in barka"
Ya dinga jin farinciki, ganin yadda Widad ɗinsa ke nishaɗi tana fara'a, saɓanin Widad ɗin daya sani a baya, me shegen haɗe ran tsiya da koke koke, mara afuwa da tausayi.
Juyawa yayi gefensa ya tsinko wata 'yar ciwa, ya miƙo mata yana cewa