Showing 141001 words to 144000 words out of 209297 words

Chapter 48 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

752

sarai abunda ke tsakanina da uban yarinyar, amma take shisshige mata"

"Amma larura ai tafi ƙarfim wasa, abun jaje ya samu mutum kace baza'a jajanta masa ba?"

Yace  "eh baza'a jajanta ɗin ba, wuce kije ki kawomin wayoyinki, daga yau har ranar da zaki bar ƙasar nan, bake ba fita ko ina, kuma kar wani ya sake yazomin gida, ɗakkomin wayoyinki gabaɗaya, har System ɗinki"

Nurat ta shiga ɗakinta, ta ɗauki wayarta ta ɓoye, ta ɗakko sauran ya kai masa, ya karɓi wayoyin da system ɗin yace  "ina ɗaya wayar taki take"?

Yai maganar yana kallon ta, Nurat tace  "Na bawa Khalil ya kaimin gurin gyara"

"to ki gaya masa maza maza ya kawota, ki aika direba maza ya karɓomin wayar nan, maza fice daga nan ki bani guri"

Nurat ta wuce ɗakinta, tana tunanin meye abunyi, koda tsiya koda tsiya tsiya dai bazata bar ƙasar nan ba, se taga abunda ya turewa buzu naɗi"





Wasa wasa fa fiye da wata guda babu Anwar babu labarinsa, duk neman dazaa'yi anyi amma ba'a samu Anwar ba, hankalin Hajiya Halima gaba ɗaya a tashe yake, da tana iya basarwa amma yanzu ta kasa jurewa, ga Shu'aibu ya sata gaba yana ta tatsarta kota ko ina, ta zauna tayi shiru a falo ta rasa abunda yake mata daɗi.

Sallamar Alhaji Haruna ce tasa ta ɗaga kai ta kalle shi, mamakine yakamata ganinsa da tai kamar korarre, tace  "lafiya kuwa?"

"Ina fa lafiya, ina' yarki take?"

"wace 'yar tawa kake nufi?"

"Yarinyar da kika aiko ta kawon takadda"

"Wai Amal kake nufi?"

"Eh ita, wadda ta karye"

Hajiya Halima tace  "to meye yasa kake nemanta? Wani abun tayi makane ko kuwa?"

"Eh nemanta nake"

Amal tace "gani nan, lafiya kake nemana haka? Ko kuma naci ban biys bane?"

Suka juya, suka bita da kallo, tace  "meye kake nemana?"

Sekuma ya diririce, ya rasa me zece ganin ga Hajiya Halima ta tsatstsare shi da ido.

Amal tace  "faɗi mana, ina jinka"

Hajiya Halima tace "nifa gaba ɗaya kaina ya kulle, kumin bayanin abunda yake faruwa"

Amal tace  "Mummy, ki kwantar da hankalinki babu wani abu fa, Alhaji muje farfajiya muyi magana"

Amal ta janye shi zuwa farfajiyar gidan ta kalle shi tace "lallai kaci ksi, baka da hankali da nasani nz tona maka Asirin abunda kayimin a gabanta, tunda kanka baya js yadda yakamata"

"wace maganar banza kikeyi hakane? Me kika aikatamin?"

"ba wani abu na aikata maka ba, illa na saka maye na ɗauki wayarka na bayar anyi abunda yakamata na turi kuɗi daga Account ɗinka, na raba kuɗin gida biyu na ɗau rabi, shine fansar budurcina daka ɗauka, kuma bari in gaya maka wani abu, akwai mahimmin saƙo da na ajiye na rarrabawa mutane, wallahi duk abunda ya sameni kaine, seka ƙara wannan akan kaidim mata da kace mim ba wanda baka sani ba, wawa kawai kuma wallahi ka kuma zuwa gidan nan duk abunda nayi maka kaika siya da kuɗinka ba wani ya sai maka ba, kuma a taƙaice takadda dai babu ita dan nima ban san inda take ba"

Ta ƙarasa maganar tana masa wani irin mugun kallo, ta shigevta barshi a gurin kaman gunkin mutanen farko.

Har ta shiga zata wuce ɗakinta, Hajiya Halima ta kira sunanta   "Amal"

Ba tare da ta juyo ba ta tsaya cak , "meye haɗinki da wannan mutumin?"

"Babu komai"

"Karkimin ƙarya, meye haɗinki dashi?"

Yace "yana so nane, nikuma nace bana sonshi, ya takuramin nikuma na zage shi, shine zezo ya ɗagamin hankali"

"to dan ba kya sonsa meye na zagin masa kuma? Ai bekamata ki zage shi ba"

"to Mummy ni kalarsa ce? Ko da ƙuriciyata zan Auri wannan dattijon mutumin ne? Ai uba na ɗauke shi, amma tunda bega hakan ba shine nai masa abunda ya dace dashi"

"koma dai meye karki kuma zaginsa, dan ya haifeki kuma koba komaiakwai mutunci, da alaƙa tsakanina dashi"

"karki ji komai Mummy, hakan bazata sake faruwa ba"  ta wuce ɗakinta.


Bulama ya fito ze fita, yaga motar Fahad a harabar gidan, dan haka ya fasa fitar ya nufi BQ inda suke, a falo ya tarar da Fahad, yana ƙoƙarin kunna TV, ya kalli Fahad yace  "kai daga ina kake? Na samu labarin seka kwanaki baka gidan nan, gidan ubanwa kake zuwa haka?"

Fahad ya sosa kai yace  "Daddy gurin abokaina nake zuwa, shiyasa"

"wasu irin abokaine zakaje ka kwana huɗu a gurin su? Kai baku da gidane?"

"muna dashi"

"to ya akayi kake zuwa kwana wani guri?"

Fahad yai shiru, Bulama yace  "Shikenan ka kiyaye idan na sake ji sena hukunta ka na gaya maka"

Fahad yace 'to, amma Dad what's wrong with you in your face, naga ɗinki a fuskarka"

"Da ka damu dani ai da baka fita ba, kaje kayi kwanaki haka ba, ban sani ba"

"Sweet heart, wai har yanzu me kake a falon ne?"

Wata yarinya ce ta fito da Towel ɗaure a ƙirjinta daga bedroom ɗin Fahad, Fahad ya shiga zazzare ido, Bulama yace  what, mezam gani haka? Fahad wacece wannan? "

Fahad ya sunkuyara da kai yana sosa kai," ba magana nake maka ba? Wacece wannan ɗin me take a nan ".

" Daddy dan Allah kayi haƙuri "

" Sallameta tazo ta barmin gida maza maza "

" wallahi ka bani kunya Fahad, neman mata? Akanme kuma a cikin gida na dan asara"

Fahad yace "wallahi Daddy ni Aure nakeso, kuma har yanzu kaƙi ka auramin Widad shiyasa, ni gaskiya shiyasa kawai nake bi ta ɓarauniyar hanya"

Bulama ya dinga masa bala'i, ya kori karuwar nan, ya taho cikin gida yana zazzaga bala'i,  "Sarah, kina gidan nan amma yaron nan yake neman mata, kai Ramadan ga ɗakinka ga nasa, amma yake kawo mata gidan nan baka taɓa faɗa ba?"

Ramadan yace "ai Daddy kafi sonsa, kuma kona faɗa ba yadda zakayi ba Shiyasa"

"Nika ke gayawa haka Ramadan?ke Sarah kina kallo amma baki ɗau mataki ba, ko ki gayamin ba?"

"Barewa bata gudu, ɗanta yai rarrafe"  shine amsar kawai data bashi, ya tsaya sororo yana kallonta.



Nurat taje ta ɗauki wayarta, ta ɓoye ta shiga tunanin yadda zata bawa Khalil wayar nan, ba tare da mahaifinta ya sani ba, tunda an hanata fita, kuma Mahaifiyarta na ja maata kunne sosai akan shisshigi akan lamarin mahaifinta.


A hankali ta lallaɓa ta sato wayar Mum ɗinta, ta dawo ɗakinta ta kira Khalil, yana ɗagawa tace "Brother a gurguje, dan Allah karka sake zuwa gidan Bulama neman Widad, akwai wata ƙulallaiya a ƙasa, akwai wani abu ds suke ƙullawa shi da Daddy na, ya gaya masa kaje gidansa neman Widad, amma Daddy yazo yana ta faman min faɗa, ya ksrɓs wayoyina saura ɗaya kawai, ya za'ayi kazo ka karɓa? "

" Nima na fuskanci akwai wani abu a ƙasa a tsakanin mahaifinki da Bulaman nan, ina da wani plan ne a ƙasa, amma karki damu zanzo in karɓi wayar "

" karka soma zuwa Brother, akwai matsala, zan san yadda zanyi idan ina so muyi magana zan kiraka a wayar Mum, se anjima "

Tai sauri ta kashe wayar, ta lallaɓa ta mayar mata da wayar.





Bulama ya kalli Fahad dake zaune ya sunkuyar da kai yace " kai dama Aure kake so amma ka tsaya kana bin wannan sakarkarun matan? Bayan zan aura maka cikakkiyar mace "

" Daddy wane cikakkiyar mace, bayan har ciki gareta?"

"ina ruwanka da cikinta? Nayi wani planning akanta, yanzu haka tama gidana na can hanyar ƙuyukan nan ma bayan gari, in da nake noman albasa, wannan gidan can na kaita na ajiye, kuma ko tana so ko bata so, za'a zubar da cikin nan ka Aureta, amma wannan da kake kawowa aiba mata bsne, idan aka kamanta su da ita "

Fahad ya washe baki yace " to Daddy nagode sosai, wallahi idan na Aureta sema rama dukan da tayi min, bazan manta marin nan ba"

Bulama yace "kai dai ka bari, aure kamar anyi an gama ne ai"


Fahad ya dinga washe baki, kamar wani sakarai.



Widad duk ta ƙare saboda larura da rashin kula, gashi cikin nan ya sakata gaba da Amai komai taci baya zama in dai ba Ruwan sanyin nan ba da lemon tsami, a ɓoye take zuwa ta turasasa Widad taci Abinci, sam bata kwanan kan katifar nan sedai kan tiles, duk ƙibarta seda ta ƙare ta rame sosai, duk tayi wani iri.

Yauma meaikin me suna Sabuwa tazo tana bata ƙosai da kunu, tana ci ds kyar, can Widad tace "Dan Allah ina labarin mijina kuwa? An fara shari'arsa ko?"

Sabuwa tace "gaskiya an fara, dan har Alƙali ya kaishi prison se bayan sati uku za'a cigaba da shari'ar"

Widad ta girgiza kai cikin ƙunar zuciya tace "Allah sarki mijina, Allah ya kawo maka mafita ta inda baka zata ba, babu abunda zan iya yi a kai, Allah ya fitarmin da kai Yoseef"

Sabuwa tace "Addu'ar dai da kike masa ita yakamata ki cigaba amma ba wannan kukan ba"

Widad dai nata shiru ba tace komai ba, dan tayi nisa bata jin kira, can tace "zan kwanta, ina son inyi bacci"

Sabuwa tace "to shikenan"
Ta tashi ta bawa Widad guri, ta rufe mata ƙofa, Widad yau taji bata san kwanciyar tiles ɗin ta koma kan ƙatuwar katifar dake baje a ɗakin, ta rage kayan jikinta ta kwanta tayi shiru, ko yaya Yusuf zeyi a prison, tana kwance akan katifa, amma bata ds tabbacin a inda Yusuf yake kwance a prison, ta tashi da sauri, taje ta leƙa tagar dake ɗakin.

Ko ina da haske, ga wasu ƙarti ne ke sintiri a harabar gidan, babu hanyar guduwa, gashi dama hanyar gurin gaba ɗaya babu gidaje, se kangwaye da gonaki, da manya manyan filaye fetal a gurin, dan haka babu hanyar guduwa.

Ta koma kan katifar nan, ta kwanta wani irin ƙaunar Yusuf da tausayinsa na ratsa jinin jikinta, ga wani irin mugun kewarsa da take yi, tana buƙatarsa a kusa da ita, ta tabattar da yana kusa da ita yasan da cikin nan, zata sha kulawa sosai.
Ta ƙanƙame filon nan a ƙirjinta, tana hawaye, a hankali tace "i miss you Yoseef, ina kewarka sosai, Allah yasa abunda ya faru karyasa ka dena sona, ina sonka Yoseef ka yafemin please, dalilina ka shiga wannan halin Yoseef, ina sonka Yoseef dan Allah ka dawo gare ni" a hankali take furta maganar tana zubar da hawaye.



Kwana uku da kai Yusuf prison Umma ta damu ta ɗaga hankalinta, akan lallai seta je ta ganshi, dan haka Suleiman yaje har gida ya ɗakko ta suka tafi gidan yarin tare.

Kasancewar Suleman ɗansanda ne yasa har gurin shugabn gandirobobi na gidan suka shiga, suka gaisa Suleiman yace  "wannan mahaifiyar Yusuf ce, da aka kawo gidan nan, dan Allah munzo a bamu dama dan Allah muganshi"

Shugaban gandirobobin yace "a gaskiya ba'a bamu wannan damar ba, daga sama akace karmu bar kowa ya kawo masa ziyara"

Suleiman yace "saboda shi ba mutum bane? Ko kuma ba ɗan ƙasa bane ba? Haba dan Allah, wallahi kwata kwata babu adalci a shria'r da za'ayiwa Yusuf, dan Allah ka dubi girman Allah ka bari mu ganshi"

Umma cikin kuka tace  "dan Allah dan Annabi ɗan nan kabari in ganshi, kusan watanni biyar zuwa shida, tynda akayi garkuwa dashi, ban sashiba idona ba ka temakamin"

"Wannan ce mahaifiyarsa?"

Suleiman yace "eh mahaifiyarsa ce"

Yace "kaman ba ita ta haife shi ba, kamar yayarsa, anyway gaskiya na lura da yanayinsa, tunda aka kawo mana shi gidan nan, ba sawa ba fitarwa, ko magana ba ruwansa da kowa, bashi da Hayaniya sam hakan yasa na fara tausayinsa, kuma nake jin ina shakku akan laifin da akace yayi, sedai baya iya cin Abincin gidan nan kunsan yanayin yadda Abincin namu yake, kuma gashi ance ba'a yadda kowa yazo gurinsa ba, nayi nayi inyi interview dashi amma yaƙi magana Sam "

Sulaiman yace " ai ba lallai yai maka ba, kaima Allah ya saka maka da alkhairi, shima abokin aikinmune ɗan sanda sakamakon wannan abunda ya faru, naji an sanar da an kore shi daga aikin, amma ita gaskiya ai zata yi halinta, nidai fatana ka mana wannan alfarmar dan Allah, ka bari mu ganshi"

Yace " Shikenan, kuyi zamanku bari aje azo dashi"

Suna nan zaune yai umarnin, aje azo da Yusuf suka cigaba da tattaunawa da gandiroban nan.

Aka shigo da Yusuf sanye da kayan prison, yana jan ƙafarsa da ƙyar da alama ƙafar ciwo take masa, da Gudu Umma ta tashi taje ta rungume shi tana kuka, Yusuf yasa hannayensa ya rungumeta shima, hawaye na gangarowa daga idonsa.

Tana so tayi masa magana amma takasa, se kuka da take Yusuf ya share nasa hawayen sannan ya ɗago Umman ya kalleta ya ƙaƙalo murmushi yace  "Umman Yusuf, baki da lafiya ne? Kinyi baƙi kin rame sosai"

Girgiza kai take tace  "Yusuf ka ganka kuwa? Gaba ɗaya ka fita hayyacinka kamsr ba kai ba, fuskarka duk ciwo Yusuf garin yaya haka ta faru?"

Yusuf bece komai ba, se cigaba da share mata hawaye da yayi, ya samu guri ya zauna, suka gaisa da Suleiman, Suleiman yace "nayi iya ƙoƙarin da zanyi, akan a barni inzo inda kake amma abu ya gagara, se yanzu da aka mana alfarma"

Yusuf yace "Aini bani data cewa, na barwa Allah shine ze fidda ni"

Suleiman yace  "waini ina Saleh nema, Saleh yasan komai fa"

Yusuf yace "Anyiwa Saleh illafa saboda duka, inaga wani abu ya taɓu a cikin sa, yana kwance a Asibiti"

Umma tace  "Yusuf wai ya akayi haka ta faru ne? Ya akayi aka kamaka kaida ita? Ance kai kayi garkuwa da ita harda fyaɗe, garin Yaya Yusuf"

"Umma kin yadda zanyi haka?"

"Kasan bazan taɓa yadda ba ai, ina son jin dahir ne"

"Umma, na shiga wannan halin ne dan kawai na temki Widad, ita kaɗai zata iya bada sheda akan abunda ya faru, se kuma Saleh, kinga bansan ma inda Widad ɗin take ba"

Suleiman yace "tana hannun abokin babanta Bulama"

Yusuf yace "Bulama kuma?"

"Eh tana hannunsa"

Yusuf yai ajiyar zuciya, Umma tace  "wai ya akayi aka kamaka da ita a ƙauye? Garin yaya Yusuf?"

"Umma Aure mukayi da Widad"

Ta kalle shi tace  "Aure kamar yaya?"

Gandiroban nan yace  "Hajiya lokaci yayi, yakamata ku tafi haka"

Umma tace  "to hakanma nagode sosai Allah yasaka da alkhairi"

Suleiman ya bawa Yusuf siyayar da suka yi masa, suka tafi yakasa waigawa ya kuma kallon Umma saboda yasan kuka take.


Suka juya suka bar Yusuf a gidan yari.


Bayan tafiyar su Umma, wannan gandiroban yasa aka canzawa Yusuf ɗaki, zuwa me mutum Ashirin, yana nsn kwance yana tunanin rayuwa, mussman Widad ya damu da yaji Widad wai tana hannun Bulama, shifa tun farkon saninta da yayi ya tsani Bulama, mussman da yayi bincike a kansa, sosai yake kewar matarsa, yana son sanin halin da take ciki, yana missing ɗinta sosai, kawai Fahad ya faɗo masa a rai, take yaji gabansa ya faɗi ya miƙe tsaye da sauri.



Cikin dare bacci da ƙyar ya ɗauki Widad, baccin beje ko ina b taji an motsa ƙofar ɗakin da take kwance, a hankali an buɗe ƙofar.



Banyi editing ba amin afuwa


A siya kafin a karanta dan Allah
Ayshercool
0009450228
11/23/21, 8:45 AM - Buhainat: Ki tura document din nan anjima takwara🙏🏻🙏🏻
11/23/21, 8:48 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

132_133




Widad ta buɗe idonta a hankali, tana son ganin waye wannan ya shigo mata haka a wannan daren, Kasancewar ɗakin da duhu shi baya ganinta se ita ke ganinsa, ya ɗakko ƙaramar wayarsa ya kunna ya haskata, tana kwance ta lumshe ido kamar me bacci, ya tako ya ƙaraso a hankali inda take, ya ƙara hasketa da fitila ya kai hannu a hankali ze taɓata ta miƙe zaune da sauri.

Tace "waye wannan? Ɗan dena haskani mana, waye wannan zaka shigomin ɗaki babu izini ko baka san ni matar Aure bace"?

"Aurenki na banza dana wofi, nazo in rama marin da kikamin ne, yadda gobe in ance ki kuma yiwa wani abunda kikamin, bazaki ba"

Se yanzu ta ɗau muryarsa, Fahad ne ba wani ba dan haka tai zumbur ta miƙe tsaye, shima kuwa ya miƙe, ya kai hannu ya riƙota ze gwada mata ƙarfi, sedai tarihi ya maimaita kansa, kamar yadda ta taɓayi masa shekarun baya, ta saka masa haƙora a hannunsa, wata irin azaba yaji ta ratsa shi tun daga yatsunsa har kansa, ya danƙi kanta yai jifa da ita a ƙasa, ai kuwa kanta ya gwaru da bango, hancinta ya fashe, ta saki wani marayan kuka, saboda zafi da taji, ya kuma yo kanta amma cikin sauri da zafin nama, ta tashi tai waje da gudu tana ihu, sedai duk wannan ihun da take babu wanda yayi yunƙurin kawo mata ɗauki, nan suka shiga guje guje dashi, Allah ya bata sa'a ta samu wani ƙarfe ta buga masa ya gigice, ta koma ɗakinta da sauri ta rufe ƙofa, gigicewar da yayi tasa yakasa komai ya shiga tangaɗi a gurin, duk ta bashi wahala sosai.

Ta shige banɗakin dake ɗakin ta rufe, ta dinga rusa kuka, gaba ɗaya ta rasa mema zata yi? Ta ding kuka me sauti.

Haka nan Yusuf ya dinga jin faɗuwar gaba a wannan daren, yakasa bacci sam, ƙirjinsa ya dinga bugawa da sauri, yakasa zaune ya kasa tsaye kawai yake jin kamar wani abu yana faruwa da Widad ɗin, ya dinga addu'a a haka har gari ya waye ba tare da ya rintsa ba.

Alhaji Haruna ya rasa me zeyi wa Amal ya huce, kuɗin data kwasa a account ɗinsa ba ƙananan kuɗaɗe bane, ya rasa meze mata wanda ze huce.
Yana zaune yana wannan tunanin Salma ta shigo ɗakinsa a fusace, ya ɗaga kai ya kalleta yace "lafiya kuwa?"

"dole ka tambayeni lafiya mana, munafuki macuci, to bari kaji in gaya maka, barin gidanka zanyi bazan zauna ba da kai ba Wallahi, dama can ba sonka nake ba aka ƙaƙabamin kai"

"Ni se wasu maganganu kike wanda ban gane inda kika dosa ba, kimin bayani yadda zan gane mana"

Jefo masa wayarta tayi, ya ɗauka ya duba, message ne aka turo mata da wata baƙuwar lamba  "Ki saka ido akan mijinki, in bahaka ba watarn

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login