Showing 12001 words to 15000 words out of 209297 words

Chapter 5 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

706

buɗe kunnenki ki jini, wannan yayan naku wani lokacin sakaraine, ba hankali ya cika ba, ina son ki saka min ido akansa, duk abunda ya faru ko abunda Bulama yace idan kun dawo ki gayamin"

Amal tace "shikenan Mummy, Insha Allah zan gaya miki"

Ta juya ta fita, ta samu Anwar a mota suka tafi.

Suna zuwa gidan Bulama, Ramadan da Iman suka shiga murna  Ramadan yace  "Sannu Anwar, barka da Arziki Allah ya kiyaye gaba ya bayyana Daddy"

Anwar yace  "Ameen Ramadan"

Iman tace "Sannu Yaya Anwar, Allah ya tsare"

Nan suka tsaya suna hira, Hajiya Sarah ta fito daga ɓangaren ta, itama tana ganin Anwar ta faɗaɗa murmushinta tace  "Anwar, sannu Anwar ashe ka fito da yau naso inzo har gida in maka jaje, Amma naji alamun hawan jinina ya tashi, shiyasa na fasa fitar"

"Allah sarki, bakomai Mummy Allah ya baki lafiya"

"Ameen Anwar, Amal sarkin zumunci ya Maman naku? '

Amal tayi murmushi tace " Mummy kenan tana lafiya "

Bulama ne ya sakko daga kan benensa, bayan ya sakko Anwar cikin girmamawa ya rusina yace  " barka da Yamma Daddy "

Bulama yace " Yawwa barka Anwar, ya kake ashe ka fito?"

"Eh Daddy Alhamdilillah, Allah yayi na fito"

Amal cike da basarwa tace "Ina wuni"

Bulama yace "lafiya ƙalau Autar mamanta, ya gidan naku?"

"Lafiya ƙalau" ta bashi amsa.

Yazo ya zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun falon.

Ya kalli Anwar yace "barka da Arziki Anwar, ba irin sintiri da shiga ficen da ba'ayi ba akan aga an samu ka kuɓuta amma Allah be nufa ba, amma ya akayi suka sakoka ne suka bar Sufyan?"

Anwar yace "to nima dai wani mutum ne yazo ya taho dani, bemin wani gamshashen bayani akai ba, ya cemin shima wanine ya turoshi"

"Allah sarki, haka lamarin ubangiji yake ai, kaga mu ba yadda bamuyi ba amma abu ya gagara, mahaifiyarka ta ɗaga hankalinta ta dinga ganin kamar bama wani ƙoƙari akai, se gashi Allah yayi an sako ka, to ubangiji Allah ya kiyaye gaba"

"Ameen ya Allah Daddy, Daddy nace to har yanzu babu wani labari akan ɓatan Daddy, har yanzu ba'a san inda yake ba?"

Bulama cikin damuwa yace  "Anwar da akwai wani labari ai da kaji, babu wani labari har yanzu, binciken ake amma kamar ba'ayi"

"ubangiji Allah ya bayyana shi, ni fatana Allah yasa yana hannu nagari, tunda bashi da lafiya"

Hajiya Sarah tace "sha'anin ƙasarmu ai se Addu'a, banda haka ace an sace mutum kamar Alhaji Daula, abun da mamaki kuma har yanzu ko a jita jita babu wanda yaji inda yake, bawan Allah nan ba lafiya ba, yana fama da kansa ga tashin hankalin an sace masa 'ya, Amma a bishi har gadon Asibiti a sace, ga' yar tasa har yanzu babu wanda yasan inda take, abun akwai ban tausayi, Daula yana ganin Jarrabawa "

Bulama yace " tabbas, yana ganin jarrabawa, na rasa wani irin abune wannan ita kanta Widad wata na biyu zuwa uku kenan da ɓatan tal, amma babu labarin inda take, ni abun har tsoro yake bani"

Anwar yace "gaskiya ne, abun da tsoro kam, kamar Widad tasan meze faru ranar da zasu tafi farm house, tana kuka tacemin ga Amanar Daddy nan in kula dashi, nace mata zanyi iya ƙoƙarina, Amma ga abunda ya faru, i don't even know how to explain this incident to her when she's back "

Ramadan dake gefe yace " Allah sarki, karka damu ai duk wanda yaji abunda ya faru yasan ƙaddara ce, Amma ni wani lokacin har mamakin Widad nake, yarinyar nan 'yar baiwace akwai ta da kai"

Anwar yace  "sosai makuwa, ina fatan Allah ya bayyana mana su gaba ɗaya"

Suka amsa da Ameen.

Haka suka cigaba da hira, sannan suka fito zasu tafi.

A harabar gidan suka haɗu da Fahad, Fahad yana ganinsa cike da borin kumya ya rungume Anwar yana faɗin  "Ohh God, so you are free now, Alhamdilillah na ta yaka murna, Allah ya kiyaye gaba, nace zanje in duba ka akace ba'a bari a ganku"

Anwar yace "Haba kamar kai kaje inda nake ace bazaka ganni ba, da kazo da zamu iya haɗuwa ai"

Fahad yace "kasan bana son disgracing, and those people are good in that, but da naji ance court za'a kaiku ya akayi ka fito?"

Anwar yace "Al'amarin ubangiji ne kawai, shiya dubeni ya fitar dani"

Fahad yace "hakane, that's good ubangiji Allah ya ƙara karewa" ya kalli Amal yace  "ke bakya kula mutane ne?"

Tsaki tayi tai masa wani irin kallon banza, ta buɗe mota ta shige.

Anwar ya girgiza kai yace "Fahad bari inje, akwai inda nake son zuwa daga nan".

"Ok, shikenan my regards to Mummy and lovely Ramla please"

Anwar yayi murmushin yaƙe yace  "Fahad kenan, za suji insha Allah"

Daga nan shima ya juya ya shiga motar.

Suna cikin tafiya Anwar yace  "wai Amal meyasa kuke yawan faɗa da Fahad ne? Banji daɗin abun kikayi masa ba, ya yanki ne fa"

Amal ta kwaɓe baki tace "nifa wallahi Yaya Anwar na tsani Fahad ɗin nan, nifa tun asali bemin ba, mugun maƙaryaci ne munafuki duk yadda kuke dashi ya kasa zuwa ya jajanta maka abunda ya same ka"

Anwar yace  "to meye a ciki? Koma menene ba gashi Allah ya fito dani ba, idan kace zaka dinga biye wa mutane ranka ne kawai ze ta ɓaci"

Amal tace "taɓ ai kai zuciyar ka daban Yaya, ba kowa ze iya wannan abun naka ba"

Da suka je gida a waje yayi parking, ya kalli Amal yace "sauka ki shiga gida, ina son zani wani guri ne"

Ba musu ta sauka daga motar ta shige gida, shi kuma Anwar ya tafi.


Shiru shiru Yusuf be fito daga ɗaki ba, har Widad taje tayi wanke wanke ta dawo yana zaune a inda ta barshi, ta kalle shi tace  "wai yau bazaka fitan bane?"

Jiki a sanyaye yace  "zan fita mana"

"to ai naga ko wanka ba kayi ba, ko har yanzu tunanin kake ne?"

Ɗan murmushin yaƙe yayi, yana sake mamakin Widad, ya miƙe yaje yayi wanka ya shirya, yana yi yana kallonta yaga ko zata canza masa, amma yaga babu wata alama ta damuwa a tare da ita.

"zan tafi"

"Wai naga se wani sunkuyar da kai kake, kana komai a sanyaye meyafaru ne"

Cikin damuwa ya kalleta yace  "bakomai"

"to seka dawo" yasa kai ya fita.

A hankali Widad tana ta koyon abubuwa, dan yanzu ta fara iya saƙa mafici da Hindu ke koya mata, tana gane abubuwa duk aikin da zasuyi seta shiga cikin su tana ƙoƙari.

Yanzu indai Widad zasu gaisa da Hindu da turanci suke yi, Hindu na da matuƙar ƙoƙarin riƙe abubuwa, gashi ta sawa zuciyar ta zata iya, tana son karatun sosai, Widad ta koya mata na boko sannan tana mata bayani akan litattafan addini, sega Hindu ta iya gaisuwa da turanci, tasan sunan abubuwa, Widad tana yawan yi mata magana da turanci dan wasu lokutan hausar ma wahala take mata, dan haka Hindu take kama wasu abubuwan.
Nan fa Hindu ta fara birge wasu daga cikin ƙawayenta, suke cewa itama ta koya musu.

Hindu suna ɗaki tana yiwa Gwaggo tsifa tace "Gwaggo, kinga laraban gidan me tabarma, da su Ishalle ne wai suma suke son a dinga koya musu karatu, nace zan tambayi Amarya amma nauyinta nake ji, kar taga kamar na takura mata"

Gwaggo tace  "kunfi kusa keda ita ai, Amma na lura kamar bata son mutane fa, kina ganin ko baƙi akayi ɗaki take komawa bata son mutane, amma ki tambaye ta idan zata dinga yi muku taren"

Hindu tace "to shikenan zan tambayeta insha Allah, Amma nikam Gwaggo Amarya ba ƙaramin mamaki take bani ba, wai bata son meye kishi ba, kuma wai ita gani take Soyayya ƙaryace da ɓata lokaci, na tambayeta to bata son mijin nata? Wai wallahi itama bata sani ba ko tana sonshi ko bata sonshi "

Gwaggo tayi murmushi tace " Amarya 'yata ta kaina, yarinyar kam tabbas yarinta ce ke damunta, kuma kinga karta kamar shagwaɓaɓiya ce, bata san abubuwa da dama na rayuwa ba, shi kansa zaman Auren da alama bata san meye ba, Amma insha Allah ina son in zauna da ita, in dinga yi mata nasiha, naga tana jin faɗa, dan Hindu ina jin takaicin Abunda Hanne ke aikatawa a gidan nan, yadda take shigewa Yaron nan, dan ina daf da kai ƙararta gurin mahaifinku"

Hindu tace  "A'a Gwaggo dan Allah kiyi hakuri, idan kika gaya masa ze ɓata mata rai sosai, ni mamakin da ta ke bani da kuɗin Aurenta a ka fa, amma take haka, ki dai cigaba da ja mata kunne zata dena"

"Ai banga alamar hakan ba"

Har Yusuf ya dawo a cikin damuwa yake, saboda ya fuskanci kwata kwata gane kan Widad se Allah, yanzu zaku zauna lafiya ana jimawa ta canza gaba ɗaya.
Widad bata san ya dawo ba, ta fito daga wanka tana zuwa ta tarar da Yusuf ya kwanta a ƙasa, ya lumshe ido.

Widad tace "ya dai harka dawo ne? Ya naga ka kwanta haka a ƙasa, ko jikinne?"

Ya buɗe idonsa ya kalleta yace "Eh na dawo, na gajine sosai bayana da ƙafafuna ciwo suke min"

Ajiye bokitin tayi ta zauna kusa dashi tace "me kaje kayi a wajen bayanka yake ciwo sekace tsoho?"

"Faskare nayi" ya bata amsa

'meye kuma Faskare? " ta tambaye shi, kallonta yayi yace  " Faskaren ne baki sani ba? "

" Wallahi ban sani ba, kaima kana ganin wani abun idam nace ban sani ba ƙarya nake ko? "

" A' a ni bance ƙarya kike ba, nasan baki sani bane, kuma daɗina dake idan baki sani ba kina tambaya"

Widad tace "to ai ba wani abu bane, idan mutum be sani ba gara ya tambaya, ka tashi kaci Abinci seka yi wanka mana"

"bari in huta tukuna"

"Shikenan bari in sa kaya" har taje ta shirya Yusuf yana kwance, a hankali yaji tana danna masa bayan tace  "wajen inane yake maka ciwon?"

"duka bayan Queen"

"bance bana son Queen ɗin nan ba?"

"Ai sunan naki ne bana son faɗa, kuma Daddy ma Gimbiya yake ce miki, ko in koma ce miki lovely kamar yadda yake faɗa?"

Dundu tayi masa tace "A'a Widad zaka dinga cemin, niba lovely kowa bace ta Daddy ce"

Yusuf yace "so kike Gwaggo tayi min faɗa? Tace ina faɗar sunan ki"?

Dariya Widad tayi tace "Hajiya Mama manya, tace in dena kiran sunan ka fa ko?"

"Eh amma baki dena ba kuma, ga sunan nawa ma baki iya faɗa ba, ana Yusuf kina Yoseef amma fa suman yana min daɗi in kin faɗa"

Murmushi tayi tana danna masa baya tace  "shikenan zan dinga cewa Yayana, kamar yadda Daddy yake ce maka"

Yusuf yace "A'a nifa mijinki ne ba Yayan ki ba, call me with romantic names mana, haba ke kuwa"

"Kaine romantic ɗin ai, kai ka sansu ni ban sansu ba"

"Tabbas na sansu, kuma ni zan dinga kiranki dasu"

Shiru tayi masa, a hankali ya juyo daga ruf da cikin da yayi yace  "Nagode sosai My wife, Allah yasa ki a Aljanna, naji daɗin tausar nan kamar karki dena, dama kin iya kula da miji haka?"

"A'a zomaye na iya kulawa da, ai koma meye kaika koyamin, idan bani da lafiya kayimin ina jin daɗi, shiyasa nayi maka"

Shiru ya ɗanyi sannan yace  "Widad, meyasa kika ƙyaleni dukda girman laifin da nayi miki, baki hukunta ni ba?"

Widad tace "Saboda Widad ba azzaluma bace, babu zalunci a AƘIDATA, duk wanda na kasa yafewa abunda yayi min to tabbas girman laifinsa ya wuce tunani, ya wuce laifin da zan iya yafewane"

"Yanzu ni laifina be kai a hukuntani ba?" ya tambayeta

"tabbas laifinka ya kai girman a hukunta ka, sedai kash akwai wani dalili me ƙarfin gaske daze hana ka karɓi hukunci, akwai wata ƙaddara da ta ratsa, ita ce zata hana ka karɓi hukunci, sannan idan nace zan hukunta ka Yoseef banwa kaina adalci ba, dan ka bani kariya ka bawa rayuwata kariya sosai, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana ai, matsoraci kaga gumin da ka dingayi ɗazu kamar ba kaine Jarumin ɗan sanda ba me gwagwarmaya kamar yadda aka bani labari, amma se gashi ina baka tsoro"

"Wudas babu Jarumi a soyayya, ba hukuncin da za kimin ne damuwata ba, kice zaki rabu dani shine damuwata"

Haɗe rai tayi tace  "me kace?"

"A ina?"

"da wani sunan ka kirani?"

Dariya Yusuf yayi yace  "wai Wudas"?

"kaima ko? Zanyi maganinka da kai da Harin da kuke ɓatamin suna, ni ba haka aka samin ba"

"niba ruwana, ɗanawa kawai nayi ai, kuma sunan naki ne na Larabawa, ba kowa ze iya faɗa ba"

Jikinta ne ya ɗanyi sanyi, tai shiru, Yusuf yace  "meyafaru kuma?"

"Yoseef ina missing ɗin Daddy sosai, zuciya ta na kwaɗayin in ganshi, i missed a lot from him, ina kewar babana, dashi na rayu na buɗi ido, amma yanzu muna duniya ɗaya amma munyiwa juna nisan gaske, a dalilin wasu tsirarin mutane da suka saka rayuwarmu a gaba "

Hawaye ne ya fara bin idonta, janyota jikinsa yayi ya shiga share mata hawayen cikin tausayawa yace " tabbas yin nesa da wanda muke so ba abune me sauƙi ba, kin ganni nima ban taɓa nisa da mahaifiyata haka ba, amma mu ɗau wannan a matsayin wata ƙaddara ta darasin rayuwa, kiyi hakuri insha Allah zamu koma kiga Daddy, nasan zaman ƙauyen nan tamakar zaman prison ne a gurinki amma ki daure mu cinye jarrabawar mu"

Ajiyar zuciya ta sauke, ta sake kwanciya a jikinsa tace  "zamana a ƙauyen nan baya damuna, na ɗau hakan tamkar wani darasine na rayuwa, Allah ya na nunamin ishara, na koyi abubuwa da dama na rayuwa wanda bam sansu ba da, kuma a nan ina zaune hankalina a kwance babu tashin hankali, babu fargabar komai saɓanin a gida, ga dukiyar ga komai hankalina kullum a tashe ina tunanin ta inda maƙiya zasu farmin, nidai tun taso wata rayuwata a cikin ƙaddara take, ina fatan Allah ya kawomin ƙarshen abun nan haka, ya kawo kwanciyar hankali a gareni da mahaifina"
Tai maganar tana ci gaba da zubar da hawaye, sosai tausayinta ke ratsa ilahirin jikin Yusuf, ya dinga shfa gashin kanta cikin sigar rarrashi zuwa gefen fuskarta,  yana tunanin anya duk ƙaddarar da Widad ta tashi a ciki takai a misalta ta dashi wadda ya tashi a cikinta?......


LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH
NA ƊAYA KYAUTA NE, WANNAN NA SIYARWA NE
₦300 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 54_55

LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

Shiri ne ya wanzu a tsakaninsu, na wani ɗan lokaci, har bacci yayi awon gaba da Widad, Yusuf ya ƙurawa fuskarta ido, yana jin wani abu na fizgarsa game da ita, wani irin sonta na ƙara ratsa ilahirin jikinsa.
Wai yau Widad ce kwance a hannunsa, har take masa kuka yana rarrashinta, kamar ba itace wannan me tsawa da muzuran ba, ya kwaɗaitu da son jin meyafaru da ita a rayuwa, meyafaru a rayuwarta haka? Amma yasan idan ya takura seya sani, to tsaf ze rusa duk wata alaƙa da yadda da take tsakaninsu

Anwar kuwa gidan su Nurat ya tafi, seda yaje ƙofar gidansu sannan ya ɗakko wayarsa ya kirata, tana kwance tana kallon TV sedai idonta ce kawai akan tv, yayinda zuciyar ta tana can tana fama da tunani, se da wayar ta katse ya kuma kira sannan ta faraga, tasa hannu ta ɗaga wayar sedai tayi mamakin ganin sunan wanda yake kan wayar, Sunan Anwar ne a jiki.

Da hanzari ta miƙe zaune ta ɗaga wayar tasa a kunnen ta.

Anwar yace  "ko bacci kike ne na tashe ki"

Zumbur ta miƙe zaune tace  "muryar wa nakeji ne haka?"

"Muryar Anwar mana"

Cikin farin ciki Nurat tace  "innalillahi, i don't even know what to say, I pray that am not dreaming"

Anwar yayi murmushi yace "you are not dreaming dear, ina harabar gidanku"

"dan Allah dagaske?" ta faɗa cikin tsananin farinciki

Anwar yace  "leƙo ki gani"

Mayafin doguwar rigar jikinta ta ɗauka ta yafa, ta ruga da gudu tayi waje, aikuwa tana zuwa ta tarar da Anwar zaune a cikin mota, da sauri ta ƙarasa gaban motar, tana ganin Anwar ɗinne kuwa kawai ta tsaya tana murmushi a lokaci ɗaya hawayen tausayinsa da farinciki ya shiga bin fuskarta.

Ya rame sosai, se dogon hanci da manyan idanunsa da suka sake yin zuru zuru, ga duhu da yaya, koba a gaya maka ba akasan inda yaje babu komai se zunzurutun wahala.

Ya kalleta fuskarsa ɗauke da damuwa yace  "ya da kuka kuma?"

"Yaya Anwar dole inyi kuka, baka ji ba baka gani ba daga abun alkhairi aka kama ka, kaje kasha wahala ba yadda banyi ba a ɓoye a samu a sakeka amma abu ya gagara, ƙarewa ma akace kotu za'a kaika na shiga damuwa sosai hankalina ya tashi, se gashi Allah yasa ka fito Alhamdilillah, ban taɓa zaton zaka fito ba"

Anwar yayi murmushi yace  "hakane, amma yanzu dena kukan mana"

Murmushi tayi tace  "ƙyaleni na farinciki ne, taso muje Mummy ma na ciki seku gaisa, amma dan Allah karka nuna muna wani abu tarene, kawai dai ka nuna ka biyo a gaisa ne please"

Anwar yace  "karki damu, ba abunda zan nuna insha Allah"

Ya miƙe ya bita zuwa cikin gidan, a falo ya zauna yayin da Nurat ta shiga ɗakin mahaifiyarta   "Mummy kizo ga Anwar yazo ku gaisa"

Da ɗan mamaki ta kalli Nurat tace  "Wane Anwar ɗin?"

"ɗan gidan Hajiya Halima mana, yazo wucewa ne yace bari ya tsaya a gaisa ai an sako shi shekaranjiya"

Mummy tace "Allah sarki, yaron kirki ashe an sake shi, bari gani nan bari inzo mugaisa"

Ta sako mayafi ta fito, Anwar ya risina ya gaishe ta tace  "Anwar ashe an sako ka? To Ubangiji Allah ya tsare gaba"

"Ameen ya Allah Mummy nagode sosai"

"bakomai Anwar, dan Allah ka gaisarmin da maman naka idan ka koma"

"zataji insha Allah Mummy, nagode sosai"

"Yawwa Allah ya tsare"

Suka amsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login