Showing 165001 words to 168000 words out of 209297 words

Chapter 56 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

758

son inyi acire kafin ta gane"

"ba matsala, karki damu kinji yanzu za'a cireshi insha Allah, Nurse maza kaita ɗakin da ake aiki ta kwanta ta jirani".

Aka kai Amal ɗakin, ta kwanta tana jiransa, gabatan se faɗuwa yake, tana tunanin kar wani abu ya faru, bayan an cire cikin "

Tana nan kwance, yazo ya ɗaura mata ruwa, ya bata wani magani ta sha, ko mintuna goma ba'ayi ba da saka mata ruwan, da bata maganin ta fara wani irin ciwon mara kamar zata mutu, ta dinga murƙususu, kafin kace meye wannan tuni jini ya fara malala daga jikinta, bayanta kamar ze ɓalle da ƙugunta, ta dinga antayar da jini, Nurse ɗin nan ta dinga temaka mata, yazo ya sake mata wasu allauran, yace
"Sister, maza idan ta ɗan huta ki kaita gida ta samu rest, jinin ze tsaya insha Allah"

Haka kuwa akayi, Ta kai Amal har gida, Amal ta shiga da motar, a dudduƙe ta tafi ɗakinta ba tare da kowa ya ganta ba, taje ta baje akan gadonta, dan wani irin sanyi take ji da jiri a lokaci ɗaya.

Duk yadda Suleiman yaso ɓoyewa Umma yadda shari'ar Yusuf ta kaya seda taji a radio, kasancewarta mace ms son jin radio, da farko zamanta a gidan tare da Surayyah ta ɗanji daɗi, dan koba komai motsin mutum rahama ne, tana ɗebe mata kewa ita da yaran ta, kuma ta kan sakata a gaba lallai se taci Abinci, ta sha magani amma tunda taji hukuncin da akayiwa Yusuf ta kasa zaune ta kasa tsaye, se kuka nan da nan jikinta ya nemi ya rikice saboda tashin hankali da damuwa.

Suleiman yaje ya sameta a ɗakin da take, yace "Umma, babu yadda za'ayi Yusuf yayi wannan shekarun haka a gidan yari, ai kowa yaga irin shari'ar da akai, ana nan ana wani ƙoƙari, sedai cikin sirri ake komai, ki kwantar da hankalinki, nina gayamiki da yardar ubangiji se Yusuf ya kuɓuta, amma kidena wannan kukan haka da damuwa dan Allah "

Umma tace " Haba Suleiman, kaifa ka cemin duk wanda yai yunƙurin taimakonsa barazana ake masa, taya ya za'a samu wanda zasu taimaka masa alhalin kowa yana kallon yadda akai shari'ar, kuma babu wani taimako da aka masa? Ni na karaya kawai, haka Allah ya ƙaddara masa rayuwarsa, ƙaddara babi babi, daga wannan se waccan " tai maganar tana kuka me taɓa zuciya.

Sulaiman yace" Umma, kece fa kike bani misali da Annabawan Allah, da irin jarabtar da Allah yayi masa, dan haka mu ɗauka jarrabawar sa ce a haka, kuma Allah yasa sanadin ɗaukakarsa ne yazo a haka, duk yadda Allah ya kai ga jarabtar bawansa, se kinga ta wani ɓangaren Allah ya masa wata ni'ima wadda ba kowa yayi wa ba, ki kwantar da hankinki Umma, shirye shirye sunyi nisa ta ƙarƙashin ƙasa, kuma insha Allah zamu bawa maƙiya kunya "

Umma ta gyɗa kai tace " to Allah yasa"

"Ameen ya Allah, ki cigaba da Addu'a Umma, ubangiji Allah ya bamu nasara"

"Addu'a ina nan ina yi, Allah yayi maka albarka da kai da iyalanka, ubangiji Allah ya jiƙan magabatanka ya rahamshesu, ubangiji Allah ya raya maka zuriyar ka akan tafarki madaidaici, yasa su zamo masu jin ƙai kamar kai, Matarka Allah yayi mata albarka ya sake haɗa kanku, tunda abun nan ya samu ɗana kake tsaye a kaina, kana bani gudunmuwa iyayinka, kaine dana ganka nake jin daɗi, nake jin daɗin yadda kake tausata nagode nagode "

Suleiman yace " bakomai umman Yusuf, karki damu duk yiwa kaine, ni ban rayu da mahaiyata ba, marayane ni tun ina yaro ƙarami, ina jinjina soyayyar uwa ga ɗanta, shiyasa nasan kina cikin damuwa rashin Yusuf da dole kina buƙatar a tausasa miki, ga Ɗanki mutum ne nagari kamili, wani abu da Yusuf ya taɓa yimin da bazan manta ba, lokacin mahaifina yana ciwon ajali sunje duba shi, baya iya cin Abinci sam, Yusuf ya kai masa dafaffen ƙwai da kayan marmari, naje siyo masa magani Yusuf ya zauna yana bashi ƙwan nan a baki, bayan ya gama bashi Baba yayi amai, ya ɓatawa Yusuf jiki, kayansa masu kyau a jikinsa suka ɓaci, amma be nuna damuwarsa ba ya ɗaga shi ya gyara masa jiki, kullum aka tashi daga gurin aiki se yaje ya duba mahaifina, har suyi hira, alhalin ni a lokacin ko kulani bayayi sosai, dukda ina shugabansa a gurin aiki, duk ranar da beje ba Baba ya dinga tambayar ina yaron nan me fararen idanuwa kuwa? Ranar da Baba ze bar duniya seda yayi masa addu'a sosai, bazan manta ba, naji daɗin yadda ya nuna damuwa akan mahaifina fiye da tunani, dukda wannan abun alkhairi da yayi min ba fiye shiga sabgata ba sedai in sha'anin aiki ya haɗamu, hakan ya tabattar min halinsa ne a haka, halin taimako da tausayi ga mutane, shiyasa bazan taɓa bari inga wani mummunan abu ya samu iyayen Yusuf ba"

Umma tai ajiyar zuciya tace  "Kaga ni be taɓamin wannan hirar ba"

Suleiman yace   "Ai Umma wannan ɗan naki halinsa se shi, miskiline ajin farko sedai akwai tausayi da jin ƙai, ni dai fatana kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki"

(Wato shi alkhairi a rayuwa, idan har zaka aikata shi ko bayan ranka waninka ze mora, Kayi ƙoƙari kayi abunda mutane zasu dinga tunaka da alkhairin ka, ba da mugun aiki ba)

Nan Sulaiman yaita kwantarwa da Umman Yusuf hankali, shida matarsa.

Kamar yadda Bulama yai umarni, cikin dare su me Adda suka bazama gidansu Yusuf, inda suke kyautata zaton Umman Yusuf tana nan.

Amal har dare yayi tana fama da matsanancin ciwon mara kamar zata yi hauka, gashi ta kasa cin komai, se uban amai da take faman yi, ga jini se zuba yake yaƙi tsayawa ita kaɗai a ɗaki babu wanda yasan halin da take ciki sam.

Gaba ɗaya babu wanda hankalinsa ya kai kan cewar Nurat bata nan se bayan kwana ɗaya, tai ihun tayi bugun ƙofar babu wanda ya ji balle ya buɗe ta, gashi bata san halin da mahaifiyarta ke ciki ba, sakamakon taji ihutmnta amma bata da tabbas ɗin abunda ya faru da ita.

Khalil ne ya kalli Alhaji Musa yace  "wai ina Nurat ne? Tunda mu kazo Asibitin nan ban ganta ba fa"

Cikin inda inda Alhaji Musa yace "Amm da yake itama bata da lafiyar ne, ban san ya nata jikin ba, bana son hankalin ta ya tashi ne, bari inje gidan in taho da ita"

Khalil yace "kace duk gidan ma basu da lafiya?"

"wallahi kuwa, Nurat ɗince ma ta fara sannan uwar"

"Amma an kaita Asibiti kuwa? Meke damun Nurat ɗin"
. "A'a ba wani abu bane dama, dama nace zata koma karatu ne itakuma bata so, shiyasa take ta damun kanta dai, kusan damuwace ta saka take rashin lafiya"
   "Amma meyasa baka ƙyaleta ba, tunda bata so ba? Ka takura se taje kaga gashi ta shiga wani hali"

Maman Khalil tace "kai Khalil, wai nan a kotu muke ne? Jimin ja'irin yaro ka tasa mutum a gaba da tambayoyi".

Khalil yace "Allah ya bada haƙuri, muje semu taho nida Nurat ɗin kai seka huta kawai".

Alhaji Musa yace "No, bakomai ai ka bari zan kawota da kaina"

Maman Khalil tace "kuje tare mana, ai bakomai se su taho taho shida ita"

Khalil ya saka Alhaji Musa a gaba, da wani irin kallo wanda ya kasa tantance na menene.

Haka suka tafi kowa a motar Alhaji Musa, koda sukaje gidan Alhaji Musa yace "bari in kirata tana saman bene"

Khalil yace "shikenan babu laifi, bari in jira a nan" ya zauna a falo.

Alhaji Musa ya hau sama da sauri, danshi gaba ɗaya ya manta daya kulle Nurat a ɗaki, yana zuwa ya buɗe ya tarar da ita a baje a sume a ɗakin, a gigice ya ƙarasa yana kiran sunanta amma bata motsi, da sauri ya ɗakkota ya sakko daga benen, hannunsa riƙe da ita.

Khalil ya miƙe tsaye yace "lafiya kuwa?"

Alhaji Musa yace "a sume na tarar da ita"

Basu tsaya ba sukayi waje gurin mota, aka saka Nurat a ciki suka nufi Asibiti cikin gaggawa.

Itama a emergency ɗin aka karɓeta, aka rufu akanta don ceto rayuwarta itama, rufetan da yayi dama bata karya ba, ga kuka ga damuwa ga tashin hankalin da ta shiga jin ihun mahaifiyarta, hakan yasa ta shiga tashin hankali, garin kuka tai shaƙuwa numfashinta ya sarƙe ta faɗi, ga yunwa dan haka abun ya tarar mata, daya buɗe ɗakinma ya ɗakkota numfashinta iya ƙirjinta ne kawai, babu inda yake motsi a jikinta.

Alhaji Musa ya koma reception ya zauna ya dafe kai, yana tunanin wannan wace irin masifa ce haka kashi kashi? Ze kashe iyalansa ɗaya bayan ɗaya da kansa, da hannunsa duk a dalilin aikin banza, dalilin neman kare a Karofi, Bulama nata musu gafara sa amma babu ƙaho tsayin shekaru.

Bulama yana ta jiran yaji su me Adda sun bashi feedback akan aikin daya sa kasu, amma shiru ba suyi magana ba, ya kira layin me Adda babu adadi amma tun tana shiga ta dawo bata shiga, sema ace masa line busy, daga ƙarshema aka kashe wayar gaba ɗaya.

Alhaji Musa yana nan zaune, aka kira shi a waya aka sanar masa da an gano inda Anwar yake, yayiwa Bulama magana, akan me yakamata ayi? An kira wayarsa bata shiga se ace busy.

Kamar ya share ya basar, amma dai ya kira Bulama, Bulama ya ɗaga yace "ya naji muryarka a hakane? Baka da lafiya ne?"

"A'a lafiyata ƙalau, amma ina Asibiti"

"me kake a Asibiti kuma?"

"Wallahi abubuwa sun damalmalemin gaba ɗaya, bisa tsautsayi daga zan ture Maman Nurat daga bene in sakko, bisa tsautsayi ta faɗo kwananta biyu a Asibiti har yanzu bata hayyacinta, na rufe Nurat a ɗaki saboda ta gano halin da ake ciki, ta gano da saka hannuna a abunda ke faruwa a gidan Daula, itama gata can a emergency bata san wake kanta ba, gaba ɗaya na rasa abunyi ma"

Maimakon Bulama ya tausayawa Alhaji Musa halin da yake ciki, seya haushi da faɗa  "wai kai wand irin mutum ne haka Musa? Ya za'ayi kabari yarinyar ka ta gano? Gaskiya baze yuwu ba sam, wancan karon dana maka magana ashe baka ɗau mataki ba? To dole kasan yadda zakayi tun wuri dole a ɗau matakin daya dace akanta, bazs yuwu ta tona mana Asiri ba"

Ran Alhaji Musa yai matuƙar ɓaci da jin Kalaman Bulama, bs tausaya masa halin dayake ciki ba, amma ya haushi da faɗa, dan haka a hasale yace  "kaga ya isa  naji, ance in gaya maka an gano inda Anwar yake, ɗan gidan Hajiya Halima"

Bulama yace 'to me kace musu? "

" me kuwa zance musu? Umarninka suke jira"

"Aina riga na gama bada umarni, a kasheshi kawai dan baze yuwu a ƙyaleshi ba"

Alhaji Musa yace "seka kirasu ka gaya musu, ni yanzu ina cikin wata matsalar ne"

Yana gama faɗin hakan ya katse kiran, tunani ya fara yi, Hajiya Halima tana da Alaƙa da Bulama 'ya' yanta kamar nasane, amma yace a kashe ɗanta dan kar Asirinsa ya tonu, dan haka babu shakka idan ya gama da Anwar kan Nurat ze dawo.

Ai nan da nan ya ɗau wayarsa ya kira Hajiya Halima, ta ɗaga wayar da ƙyar alamar tana jin jiki, tai sallama a hankali

Alhaji Musa yace "malama idan zaki ware muryar ki ki ware, an gano inda ɗanki yake Anwar, amma Bulama yace A kasheshi dan karya tona masa Asiri....


AMANA! AMANA!! AMANACE!!!

AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN  ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin  wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_)

IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _

Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)

      Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji

  Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata

Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219
Chat 08063114606








144_145




Ai zumbur ta miƙe zaune tace "ban gane a kasheshi ba? Anwar ɗin nawa za'a kashe? Me yayi masa haka?"

Alhaji Musa yace "ke nifa tuni na dawo daga rakiyar mutumin nan, Azzalumi ne kawai, kansa ya sani bashi da imani sam, ni kaina yanzu haka muna Asibiti nida su Nurat, amma gaba ɗaya ko yamin jaje se masifa da tashin hankali da yake min, shiyasa na kwashi kuɗina na saka a siyasa, in samu su bani takara in huta da wannan mulkin mallakar da yake mana, ga uwar dukiyarmu da muke narkawa amma har ynzu babu wani bayani "

Hajiya Halima ta fashe da kuka tace " ni Bulama zeyi wa haka? Anwar kamar ɗa yake a gurinsa amma shine zece a kashemin shi? Baze yuwu ba kuwa "

Ta ajiye wayar, ta miƙe ta shiga ɗakinta ta zura doguwar riga, kusan ƙarfe goma saura na dare, amma tayi waje ta ɗau mota ta fita ta tafi gidan Bulama a daren.

Shikuma Bulama yana zaune yana ta nazari akan yadda ze ɓullowa al'amura da suke neman damalmale masa, ya dinga kiran layin su Me Adda amma shiru babu Labari, waya taƙi shiga sam.

Masu gadi kansu sunyi mamakin ganinta a wannan daren, kamar wata mahaukaciya ko gabanta bata gani sosai saboda tashin hankali, kai tsaye ya shiga falon dake ƙasa tana bala'i  "Ina Bulama yake? Ina Bulaman?"

Iman ce zaune a falon tana kallon zee world tace "Mummy lafiya kuwa?"

"ban sani ba, ina uban naku yake tsohon macuci azzalumi?"

Iman ta kalleta da mamaki jin irin furcin da take akan mahaifinsu wanda ya kasance ɗan uwa a gareta, Iman tace "Mummy ya riga ya hau sama, inaga ma ya kwanta fa"

Ai bata tsaya jiran me Imana zata kuma ce mata ba ta haura saman da kanta, ba zato ba tsammani ya ɗaga kai yaci karo da Hajiya Halima a tsaye a kansa.

Ya kalleta yace "Halima, lafiya kuwa zaki zo a daren nan? Bakya jira ayi miki iso kawai ki hauromin ɗaki haka?"

"Dalla rufemin baki, me zaka gayamin har wani iso zan jira ayimin, munafuki azzalumin banza dana wofi, tsawon shekaru ina maka aiki, kana sani duk abunda kaga dama ina maka, dan ka cinma burinka ba tare da na nuna gazawata ba, shine halin naka na baƙin kumurci zaka gwadamin, shine kayi umarni da idan anga Anwar a kasheshi, ɗan nawa za'a kashe? Wallahi baka da imani ba kada Alƙawari tun wuri ka dakatar da wannan maganar idan ba haka ba Wallahi ran ɗana baze tafi a banza ba"

Zazzaro ido Bulama yayi ya dinga ƙifta mata ido akan tayi shiru, amma tace "bazan shirun ba, wallahi babu inda zani se an dawo min da ɗana"

"Halima wai wace irin magana kike hakane? Kamar yaya nace idan anga Anwar a kasheshi? Me Anwar yayi min wanda zesa ince a kashe shi, ni da na kaiwa jam'ian tsaro maganar dan ayi bincike akansa a gano inda yake ya zakice nace a kasheshi? Wani munafukin ne ke neman haɗani da 'yar uwata?"

" Kaga bana son kame kame da ƙaryar banza, wanda ya gayamin baze maka ƙarya ba, macucin banza da na wofi kuma wallahi idan ɗana ya mutu you must pay for it, wallahi aka kashemin Anwar seka fanshi ransa, nima kasan halina ka san abunda zan iya aikatawa "

Gaba ɗaya Bulama ya dirirce ya rasa abunyi, ya shiga tsuma yana fatan Allah yasa wani beji abunda ta faɗa ba.

Ya biyo bayanta ya leƙa, yaga ba kowa a falon ƙasa dukda ɗakin a rufe yake babu wanda ze iya jiyo me sukayi, ya koma bedroom ɗinsa ya tarar da Hajiya Sarah tana ta baccinta hankali kwance, yai ajiyar zuciya tare da tunanin bata jiba, amma ya zauna yai shiru akan gadon yana tunani, tabbas babu wanda ze gayawa Halima wannan maganar idan ba Alhaji Musa ba, tabbas dole yayi maganin Alhaji Musa.

Cikinsa ne ya murɗa ya tashi ya tafi banɗaki, kusan kwana huɗu kenan yana fama da gudawa taƙi tsayawa, dan haka ya sa ransa idan ya gama da wannan matter ɗin zeja yaga likita.

Yusuf se sake juya takaddar nan yake, yana tunanin wani hali Widad ɗin ke ciki, tabbas yasan da  tana da dama bazata barshi a gurin nan ba, dole akwai wani abu da yake gudana a ɓoye, idan ya kalli sentence ɗinta na ƙarshe na ba lallai su sake haɗuwa ba se yaji gabansa ya faɗi, lallai ko a ina take tana cikin mawuyacin hali, "Allah ya ƙara haɗa fuskokinmu my wife, Allah yasa kina hannu na gari, i love you too" yai maganar a hankali tare da lumshe idonsa.
Rayuwar da suka yi tare a ƙauye ta dinga dawo masa, koba komai zamansa da ita ba ƙaramin farinciki ya samu ba, zamansu a ƙauye yasa Ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ta samu hutu na wani ɗan lokaci, ya daɗe beji cin zarafi da gorin rashin iyaye daga mutane ba, sedai matukar kewar Ummansa da yayi, be sake zaton ze samu wadda zata aureshi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login