Showing 207001 words to 209297 words out of 209297 words

Chapter 70 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

763

bargon, cikin dare ta tashi a firgice saboda tsoro, Daula yace "lafiya kuwa?"

"tsoro nakeji"

Yai murmushi yace "aiba abunda ze sameki, ki rage yawan tsoro dan wataran ke kaɗai zaki kwana a gidan nan, ki kwanta kiyi addu'a, ba abin da ze sameki"

Haka ta kwanta tana cigaba da rarraba ido.

Sedai a yau ɗinne dai Hindu ta zama cikakkiyar matar aure, dukda tsoro da razanin data tsinci kanta a ciki.

Su Hari kuwa haka suka koma ƙauye, suna zuzuta haɗuwar gidajen da suka je, Abinci kam wannan duk azabar cin mugunta da suka yi seda suka barshi, akayi musu rakiya da sha tara ta arziki, yayin da ayyukan da ake musu sunyi nisa sosai, dan har an kai musu wutar lantarki ma.

Washegari Widad ta aika direba da Abinci ya kai gidansu, sedai ita amaryar ce taƙi sakin jiki sam, lokaci lokaci se Daula ya kalleta yayi murmushi, yarinya ce sosai sedai akwai kunya sosai.

Yace "ga Abinci Widad ta aiko, kizo kici ko in kirata in gayamata kinƙi cin komai"

"Aa' dan Allah karka gayamata"

"to zokici Abincin nan"

Ta sakko ta zauna, ya zuba abincin a plate, ya haɗa mata da tea ya bata, sedai kunyar ci take a gabansa, ta ɗan dinga cakala, ya karɓi plate ɗin, ya ɗebo a spoon ya kai bakin ta, kunya takeji sosai, ta sunkuyar da kai yace  "haka zamuyi dake? In gayamata kina gaddama ko?"

Ta girgiza kai, yace "in bakya so in gayamata, maza karɓi kici"

Abun har mamaki yake bata, babban mutum haka amma ya zauna yana lallaɓata, seda taci ta ƙoshi ya jata zuwa wani ɗaki ya nuna mata kayan lefenta.

Banda wanda aka shirya mata a drower.

Umman Yusuf, kwana uku da ɗaurin Aure ta tare a babban birnin tarayya, Widad taso zuwa sedai tana daf da shiga watan haihuwarta, dan haka akace ta haƙura.

Bulama kuma tuni aka shiga zaman kotu, aka dinga shari'a ana warware duk wata ƙulalliya da makirci daya aikata, laifukan nasa da yawa danshi ƙarshe se hukuncin rai da rai aka masa, sauran kuma daga me shekaru Ashirin da wani abu seme talatin, Hajiya Halima kuma shekaru Ashirin da takwas itama, Ramlah kuwa hauka ta dingayi tuburan saboda azabar shaye2, ƙarshe se gidan mahaukata aka maida ita.

Bulama kuma ya dinga larura, ciwo bayan na ƙanjamau ya din rashin lafiya, aka kai shi Asibitin gidan yari ashe cancer ce ta kama masa hanji zuwa duburarsa, ga kotu dukata ƙwace kadsrorinsa ta mayarwa da Daula, bashi da komai ba shi da kuɗin daza'a masa aiki, ƙarshe haka gurin bayan gidansa ya dinga tsutsa, ga wani irin wari yanayi, shima Fahad ya samu shekaru sha biyu a gidan yari, gashi ga ubansa Alhaji Musa kuwa shima rai da rai ne hukuncinsa, saboda hadda laifin kashe matarsa, ga sugar ya fito masa a ƙafa, shima ƙafa ta dinga ruɓewa kamar bata ɗan Adam ba.

A hankali Hindu take ɗan sakin jiki da Daula, babban abunda yake burgeshi da ita shine, tsananin biyayya kamar zata shige cikinsa, ko magana yake mata kanta a ƙasa, wanda rabonsa da samun farinciki tunda Huda ta rasu.

Satinta biyu yasa ta a makaranta, ya ɗaukar mata me zuwa gida yai mata lesson, na ilimin addini dana zamani, kuma gata da saurin ganewa.

Yanzuma yana zaune ta ɗora kanta akan cinyar sa, yana nuna mata hotunan maman Widad daya ɗauka a wayarsa, Hindu ta zuba musu ido tace  "masha Allah, tana da kyau sosai gata kamarta ɗaya da Widad"

Sam bata nuna masa kishi ba, sema addu'a data dinga yi mata.

Daula ya bata wani littafin turanci, yace ta karanta yaji, aikuwa ta dinga karanta masa, gashi makarantar da yasa ta, malaman su turawa ne, tana yi yana tafa mata yana murmushi.

Jin sallamar su Widad a falon, yasa cikin hanzari ta tashi daga kan cinyar Daula, tana neman ɗankwali, wai kar Widad taga kamar ta raina shi.

Widad tai murmushi tace  "kekam Allah ya shiryeki, ni idan nice ba kunyarki zanji ba, mijin nakima da yake tsoho"
Hindu ta duƙunƙune fuska tana jin kunya.

Yusuf dai sedai ya kallesu yayi murmushi, sun daɗe a gidan se bayan goma sannan suka tafi gida.

A satin Saleh ya dawo, an masa aiki ya warke tsaf dashi, yayi murna da jin Daula ya Auri Hindu, shima an masa halacci sosai, sannan Daula ya canza masa aiki, aka maida shi Lagos.

Amal ma a nan Nigeria aka mata aiki, sedai taji sauƙi sosai anata ƙoƙari karta rasa hankalinta, likitan da yayi mata aiki ya nuna yana sonta ze Aure ta, Daula be ɓoye masa ba ya gaya masa komai game da Amal yace "Amma itama 'ya tace, idan kasan zaka aure ta ka wulaƙantata ka ƙyalemin' yata"

Yace "shi tsakani da Allah yake sonta"

Daula ya shige gaba ya karɓi kuɗin Aurenta, sedai ita tana Asibiti har yanzu.

Wataran da Safe, Hindu ta tashi daga bacci, sega kiran Widad, ta ɗaga wayar tana cewa "Maman biyu kin haihune?"

Widad tace "kedai bari, ina nan ina ja, ima wannan dattijon yake? Zanyi magana da shi"

"Hindu tace " waye kuma dattijon? "

" Mijinki mana "

" gaskiya kidena ce masa dattijo "

Widad ta dinga dariya tace" lallai Hindu, Allah ya baki haƙuri yana ina? "

Hindu tace "bacci yake yi"

"idan ya tashi kice masa, zan tafi Asibiti na fara jin ciwo, yayi min addu'a zanje inji abunda zasu ce, zan iya haihuwa ko kuma aikin za'ayi"

Jikiua sanyaye Hindu tace "insha Allah zaki haihu lafiya, ki kwantar da hankalinki"

Widad tace 'to Allah yasa"

Hindu ta ajiye wayar tai shiru, Daula ya tashi zaune yana cewa matar dattijo ha dai.?

Kallonsa tai tayi murmushi tace "lafiya, Widad ce tace zata Asibiti a duba, idan zata iya haihuwa ko kuma aiki za' a mata"

Da sauri ya karɓi wayar, ya sake kira Yusuf ya ɗaga yace "Daddy mina Asibiti, daga zuwanmu suka riƙe ta sukace haihuwa zata yi"

Daddy yace 'wani Asibitin ne? Gani nan zuwa "

Ya gayamasa, aikuwa anan da nan suka shirya shida Hindu suka tafi Asibitin.

Ansha daru da Widad kafin ta haihu, Allah ya temake ta ta haihu da kanta, sedai Yusuf ya sha kira sosai da Daddy.

Aka fito aka miƙo musu, santalelen jariri me kama da Yusuf sak, Daula ya karɓi Jaririn yana faɗin masha Allah, Alhamdilillah.

Nan ya shiga bige bigen waya, yana sanar da haihuwar ta Widad, nan da nan aka cika Asibitin 'yan barka, se bayan awanni huɗu sannan aka sallameta, suka tafi gida.

Daddy ya rasa inda ze saka ransa da murna, a ranar Umma ta dawo kano, Umma kamar ita akayiwa haihuwar, ta dinga murna tana farinciki ta ɗau jika.

Saura kwana biyu Suna su Hari suka zo daga ƙauye, da abun arzikinsu, megari yabada raguna biyu manya yace a yankawa jaririn nan, Yusuf yai masa huɗuba da Muhammad Bashir sunan mariƙinsa, anyi shagali sosai a sunan nan, jariri ya samu kyaututtuka daban daban daga gurin mutane.

Ana zaune a falon Widad, bayan an dawo daga event ɗin da akayi sunan, ba zato ba tsammani Widad tace "wai yaushe ne bikin Hanne"

Hari tace "to ai mijin natane har ynzu be shirya ba, lega yake tafiya neman kuɗi, amma dai abun dai duk se a hankali ba wata Ƙwaƙwaƙwarar sana'a da yake yi"

Widad tace "aiga 'yar uwatta nan Hindu, ta tambayar mata mijinta a sama masa abunyi shima"

Hindu ta kalli Widad, dan ita harga Allah bata iya tambayar Daula komai, to mema zata tambayeshi bayan komai ya ajiye mata.

Hindu tayi fuska ba tace komai ba, da daddare Daddy da kansa yaje ya ɗakko Hindu, bayan sunje gida har sun kwanta yace "Hindatu Widad tacemin zakiyi magana dani ko?"

Hindu ta girgiza kai tace "A'a"

"gayamin, nasan bazata miki ƙarya ba"

"Bafa nice ba, cewa tai wai ince maka a samawa wanda ze auri Hanne aiki"

Yai murmushi yace 'ta gayamin, ina son ji daga bakinki ne, daga yau kome kike buƙata kowa kike so ayiwa alfarma ki faɗa kanki tsaye zan masa, ance ya iya tuƙin mota, zamu bashi jan manyan motocinmu, sannan zan basu gida a nan garin, itama ta dawo ta zauna a nan ta shiga makaranta "

Hindu harda kukan murna, ta durƙusa har ƙasa tana masa godiya, ya girgiza kai yace" meye abun damuwa haka kuma? Karki damu kinji"

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, lokaci ɗaya akayi bikin Nurat da kuma Amal, kuma duk Daulane yayi musu walicci, da kayan ɗaki da manyan kyautuka ga kowaccensu.

Muhammad Bashir wanda suke cewa Aryan yayi wayo, kusan koda yaushe Daula ya kan je gidan Widad saboda Aryan, yana matuƙar ƙaunar Yaron.

Wataran da daddare Daula ya shigo yace "Hindatu, kisa hijjabinki zamuje muyiwa su Widad sallama, gobe in Allah ya kaimu zamuje Abuja, daga nan zamuje Dubai ki rakani taron kasuwanci"

Hindu tace "sekaje dani taron kasuwanci har wata ƙasar, abokanka za suyi maka dariya ka auri 'yar ƙauye"

"Ni matata ba' yar ƙauye bace, kuma ba inda zanji shakkar shiga da ita, in nunata ince wannan matata ce, saboda ina sonta a haka"

Hindu ta rufe fuska tana murmushi.

A daren suka tafi gidansu Widad, Hindu ta kama Aryan ta rungume tana ta masa wasa, Widad ta karɓi Aryan ta bawa Daddy, taja Hindu ɗakinta, ta bata wata riga tace ta gwada, Hindu ta cire hijjabinta ta gwada rigar, abun da Widad ke son gani, kuma ta gani ciki ne a jikin Hindu.

Widad tai kamar bata gani ba, ta bata kyautar riga, a ranta tace "shine Daddy bemin Albishir ba.

Widad tana jin daɗin yadda mahaifinta ya samu nutsuwa, Dan ita kanta ta lura da yadda Daddy ya samu nutsuwa, da biyayya da take masa, daga ita har Daddy sunyi tsaf dasu sunyi ƙiba, watan Aryan biyar Widad tabi Yusuf Lagos, ya kama harkar kasuwancinsa sosai.

Watannin cikin Hindu tara ta haihu, amma seda aka mata CS aka cire yaron daga cikinta, saboda yai girma da yawa, kwana biyu tana labor, sannan aka mata cs ɗin aka cire yaron.

Widad kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan murna, an yi mata ƙani, yaron kamarsa ɗaya da Yusuf sak, kamar shiya haife shi, kuma kusan duk kamaninsu ɗayane dai da Daula.

Daula be taɓa saka ran ze sake haihuwa ba, lokacin da aka gayamasa Hindu na da ciki ma, shiru yayi da bakinsa yaita Addu'a, da cikin ya fara girma kuma ya dena zuwa ko ina da ita, saboda kar itama ayi mata yadda akayiwa Huda, se yanzu data haihu sannan kowa yaji, an taya Daula murna sosai, da kyautar da Allah ya bashi na ɗa namiji.

Widad anyi ƙani, ga kuma ɗa da miji, murna ba kama hannun yaro, se bayan sati biyu akayi gagarumin shagalin suna, a garin kano, har Nurat da 'yan gidsnsu sunje barka, sedai Widad sam bata shiga sabgar Nurat sosai, seda Daddy ya zauna ya sata a gaba, yaita mata faɗa da Nasiha, sannan take ɗan sakin jiki da ita kaɗan.

Duniya ta dawo sabuwa ga wannan ahali, suka dinga tara zuriya, dukda Daddy ya manyanta amma seda Hindu ta haifi yara huɗu dashi, Widad ma ya haifawa Yusuf yara uku.

Bulama kuwa bayan shekara shida a haka ya mutu a gidan yari, yana wannan tsutsar da zubar da ruwan, babu wanda yake iya zuwa inda yake saboda wari da ɗoyi, haka aka yasar dashi a gadon Asibiti, harya mutu babu wata cikakkiyar kulawa haka ya mutu a wulaƙance.

Lokaci lokaci Amal ta kanje ta kaiwa mahaifiyarta ziyara a gidan yari, sannan tana zuwa gidan masu rangwamen hankali, Ramlah ta zama mahaukaciya tuburan, se an ɗaɗɗaureta haka zatai ta ihu tana fizgar gashin kanta, idan bayan gidane a nan za tayi, komai a gurin take yi, ta zama mahaukaciya tuburan, abun da Hajiya Halima taso Widad tayi, shine ya faru a kanta.

Duk wanda ya zamana da sa hannunsa a badaƙalar da Bulama yayi, seda aka masa hukunci daidai da shi, daya mutu ma ds ƙyar aka samu masu masa jana'iza, sedai kowa yana toshe hanci saboda yadda jikinsa ya dinga ruɓewa tun yana raye, ga kowa baya faɗan alkhairi akansa, sedai sharrinsa da Allah wadaran.

Daula baya ƙasar lokacin daya samu labarin rasuwar Bulama, amma seda ya zubda hawaye jin irin mutuwar da Abokin nasa yayi, tabbas da yana Nigeria dashi za'a sallaci Bulama, ya dinga kuka yana "Allah ya jiƙanka Abubakar, Allah ya maka rahama ya yafe maka, yasa jinyar da kayi kaffara ce, ni dai na yafe maka abubuwan da kamin, Allah ya yafe maka"

Seda Widad taji haushin yadda Daddy ya damu saboda mutuwar Bulama.

Daula a haka ya  dinga sawa ana kai kayan Abinci gidan yari, da gidan mahaukata, Arziki ya cigaba da bunƙasa, Hindu ta zama hamshaƙiyar mace itama, Daula ya ɗau nauyinta taita karatu na addini dana zamani.

Umma dai Allah be bata haihuwa ba, amma bata sa hakan a ranta, saboda tana da Yusuf ga sirikata ta ɗaiketa uwa, ga yara sun haifa suna da jikoki, gashi tana zaune da mijinta da matarsa lafiya, yaransa suna matuƙar girmama ta.

Yusuf ma suka samu kyakkyawar rayuwa, suna zaune abunsu a garin Lagos da yaransu, ƙauyen su Hindu kuwa, banda wanda yasan ƙauyen ƙayaune a baya ba zakace shine a yanzu ba, saboda cigaban da suka samu ta kowane fanni, bazasu taɓa mantawa dasu Widad ba, saboda a sanadinsu ne Allah yasa suka samu wannan cigaban wanda basu samu ba a baya.




TAMMAT BI HAMDILLAH

9/12/2021

ALHAMDILILLAH ALA KULLI HALIN, ALLAH YA NUFA NA KAMMALA WANNAN LITTAFIN NA AƘIDATA, INA FATAN DARUSSAN DAKE CIKI ALLAH YA BAMU LADA, AKASIN HAKA UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI ƊAYA.

A TARA NAN GABA KAƊAN DOMIN JIM LITTAFIN DA ZANZO MUKU DASHI, AKWAI LITATTAAFAI JINGIM A TASKAR COOL, WASU NA KUƊI WASU NA KYAUTA, INA FATAN DUK WANDA NAZO MUKU DASHI, ZAKU KARƁA HANNU BIYU, NAGODE SOSAI DA KULAWARKU DA KUMA ƘAUNARKU A GARENI

SANNAN INA SON JIN RA'AYOYINKU AKAN WANNAN LABARIN DA KUKA KARANTA

NAGODE SOSAI, A KODA YAUSHE INA MATUKAR ALFAHARI DAKU MASOYA.

ƘOFATA A BUƊE TAKE, DAN GYARA, SHARHI KOKUMA SHAWARA

AYSHERCOOL
07063065680

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login