Showing 21001 words to 24000 words out of 209297 words

Chapter 8 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

709

ɗinmu ya kusa ƙarewa na ɗanyi mana siyayya"

Tasa hannu ta karɓa tace  "Nagode sosai Allah yasaka da alkhairi" yaji daɗin godiyar da tayi masa tace  "amma zan bawa Hindu, itama ta dinga amfani da pad instead of cloth"

Yusuf yace "duk yadda kika yi"

Ta tashi tayo alwala, ta dawo ɗaki Yusuf ya zauna ya tsince shinkafar hausa tsaf, ya fita yana wankewa, Hanne ma ganinsa tace  "Laa dama ka iya aikin mata haka?"

Yusuf yai murmushi yace  "eh na iya mana, gashi inayi"

"Kawo in wanke maka, kar ayi sallama a ga kana wanke shinkafa da kanka, bayan kana da Aure kuma akwai mata a gidan"

Yusuf yace  "karki damu Hannatu, ai shinkafar kaɗance zan iya wankewa"

Hanne ta ƙaraso tana faɗin gaskiya a'a, nidai bani nan in wanke maka.

Widad ta gani tsaya a bakin ƙofar ɗakinta, tana watso mata wani mugun kallo, take Hanne ta tuno da shaƙar data sha, nan da nan cikinta ya kaɗa ta tsaya tayi sororo, Yusuf ya ɗaga kai ya waiga, yaga ashe Widad ta gani, bata ce musu komai ba ta shige ɗakin, tana jiran Yusuf ya shigo ta zazzage masa.
  Ita mamaki ma take yi, yadda ta kasa zagewa ta ƙare masa saboda abunda ya shiga tsakaninsu, tunda ya shiga ɗakin take binsa da kallo.

Be ce mata uffan ba, ya zuba shinkafar

"Malam daga yanzu idan zakayi kule kulenka ka bari seka sakeni tukuna na gaya maka"

Kallonta Yusuf yayi yace "Dagaske har ranki so kike ki rabu dani?"

Kallonsa tayi tace "to da tare aka halicce mu? Ko kuma ka manta bisa yarjejeniya mukayi Aure ne haba? Nifa bani nace ka fara sona ba, dan baka gara tun wuri kasan abunyi"

Shiru yayi ya cigaba da tunani, har ya kammala girkin ya sauke, ya ɗora mai akan wuta ya soya, sedai bisa tsautsayi saboda tunani mai ya zubar masa a hannu.

Firgigit ya dawo hayyacinsa yace  "Subhanallah"

Da sauri ta juyo taga abunda yake faruwa, ai nan da nan ta ƙarasa gabansa tana faɗin "Subhanallah, yoseef garin Yaya? Me kake tunani haka? Kalli yadda ka ƙone hannu, innalillahi"

Ta riƙe hannun nasa, ta sa rigarta tan goge masa inda man ya zuba a hannun sa, karaf idonta ya sauka akan ƙafar wandonsa, kamar jinine a jiki, ta kai hannu ta janye wandkn, rauni me yaji a gurin, kamar an saka ƙarfe anja gurin.

Ɗaga ido tayi ta kalle shi tace  "Yoseef, meye wannan?"

"wannan karki damu, dama zanje cikin garine in siya miki pad ɗin nan, to kin san hanya bata da kyau, shine muka faɗi a babur, amma karki damu zan warke Insha Allah"

Kallonsa tayi, wani irin tausayins ya game zuciyar ta, hawaye sharkaf a fuskar ta tace

"This is serious, ya isa haka, yakamata mu koma gida kome ze faru ya gara faru, ba zamu cigaba da zama a nan lafiyarka na taɓuwa saboda ni ba"

Yusuf yayi murmushi cikin jarumta yace  "wannan ai ba ciwo bane me girma, zan warke very soon insha Allah, ki kwantar da hankalinki"

Cikin kuka ta shiga girgiza kai tace 'No, Yoseef se mun bar garin nan haka, wahalar da kake sha saboda ni ta isa haka, is enough ba dangin iya ba na baba se wahala kake saboda ni? Idan har lafiyarka ta cigaba da taɓuwa bazan yafewa kaina ba, gida zamu koma ba zamu ci gaba da zama anan ba kome ze faru ya faru"

Tai maganar tana riƙe da ƙafar Yusuf tana kuka

LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

58 _59

Ɗan ƙura mata ido Yusuf yayi yace  "haba Widad, ya zaki ce mu koma gida a wannan yanayin? Komai ze iya faruwa fa"

"Koma meye yafarun, amma be kamata ratuwarka ta cigaba da cutuwa saboda ni  ba, kalli ƙaddara daga wannan se wannan yakamata inyi maka adalci bekamata in nuna son kaina da yawa ba"

Yusuf ya shiga share mata hawaye yace "Karki sake  cewa ba dangin iya babu na baba tsakanina dake, koba komai koda mun rabu kin taɓa zama wani ɓangare na tarihin rayuwata wanda baze taɓa gogewa ba, dan haka kome nayi a yanzu domin farincikin ki bakomai domin kuwa haƙƙina ne inyi miki, a gurin Allah babu wani abu like arranged marriage, duk abunda abunda ze sameni saboda kare rayuwarki baze dameni ba, saboda mahimmancin da kike dashi a gurina, kidena kuka zan warke insha Allah "

Girgiza kai ta shigayi, tana son yin magana amma ta kasa dan haka kawai ta faɗa jikinsa ta cigaba da kuka.

Yusuf a ransa yace 'alamu sun bayyana ƙarara Widad tana sona, sedai ita bata san hakan ba'

'Amma idan harka bari Widad ta fara sonka kayi mata adalci kuwa? Kayi mata ƙarya a karo na biyu, anya ƙaddarorin rayuwarku zasu haɗu a guri guda?' wata zuciyar ta shiga gargaɗinsa.

Jiki a sanyaye yake dukan bayanta cikin sigar rarrashi yace  "ni ban gaji dake ba, kuma duk abunda yake faruwa dani baze taɓa sawa in juya miki baya ba, saboda Amana ce na karɓa a gurin mahaifinki, kuma Allah ya jarabci zuciyata da sonki, babu yadda zanyi ƙaddrata kenan"
A hankali ta tashi daga jikinsa, ta ɗan zuba masa ido, shi kuwa Yusuf me yake ji haka game da ita da baya iya ganin laifinta, kuma yake tarar dukkan ƙalubalen daze taso?.

A hankali tace  "Muci Abinci, ina jim Yunwa"

Yusuf ya haɗa musu shinkafa da mai da gishiri, suka fara ci sedai Widad da ƙyar take cakalar Abincin, ƙarshe Yusuf ne ya bata Abincin.

"Kaje Asibiti kuwa da kaji ciwon?"

"Naje chemist, na sai magani ciwon bayamin zafi ai, bari nayi alwala inje waje inja salla"

"ba in da zaka, ka zauna ka huta"

Yusuf yace "Amma..

" ba wani amma, kawai kayi salla a gida, kar kaje ka fama raunin nan"

Da ƙyar ta yadda yaje yayi salla ya dawo, tazo ta zauna ta saka masa man zaitun a gurin, ta nayi tana jera masa sannu.

Da kanta ta gyara masa shimfiɗarsa, ya kwanta, tana sake kallon yadda ciwon ya ɗanyi zurfi.

"Allah ya baka lafiya kaji"

Tai maganar tana shafa sumar kansa, yai murmushi yace  "Ameen ya Allah nagode sosai"

"meye wani ka gode?" kawai se ya shagala da kallonta, ta kalle shi tace  "naga kana kallona, idan ka sake kayi abunda bana so koka tsokaneni ko, zaka ga yadda zanyi da kai"

"ya akayi kika san abin da zan miki?"

"Fuskarka kawai na kalla na gane hakan ' ta bashi amsa

Ya shammaceta ha janyota kan shimfiɗarsa, ya mirginata aikuwa ta ware baki zata kurma ihu, cikin hanzari ya toshe mata baki yace  "sekin tara mana jama'a tukuna?"

"Ka cikani ko inyi ihu Allah"

"to me nayi miki da zakiyi ihu?"

"Ai dole ka tambayeni me kaimin, tunda jiya...
Sekuma tayi shiru," Mhmm ƙarasa mana"

"dan Allah ni ka ƙyaleni bacci fa nake ji"

Shiru yayi bece komai ba, ya cigaba da kwanciya a jikinta.

"Masoyiyya, meyasa da muna gida kika cemin ke Karuwa ce? Alhalin ba haka bane?"

Widad tace "eh ai ba ƙarya nayi ba"

"Meyasa kikeyin abunda bakya so ai miki ne?"

"meye maraba ta da karuwa a wannan lokacin? A shigar da nayi, da kuma inda naje harka ɓatami rai ranar, Daka san me najeyi da bakamin haka a wannan ranar ba"

"Nifa tun a wannan lokacin ina matuƙar kishinki ne, tun a lokacin nake sonki shiyasa nake nuna kishina a fili, Abubuwa da yawa suna ɗauremin kai a wancan lokacin ina buƙatar warawara daga gareki"

"Yoseef kenan, kaine mutum na farko da ya shigo rayuwata a hagunce kuma ya zama garkuwa a gareni, ya samu damar da da ɗunbin mutane basu samu ba, kayi nasarar canza wasu daga cikin tunanina, sedai har yanzu baka bani labarin sakamakon bincikenka da kayi ba akan maƙiyana"

Yusuf yai murmushi yace "Naƙi na gaya mikin, nima ban yadda dake ba"

Dariya Widad tayi, harda kai masa dukan wasa a ƙirjinsa tace  "nice baka yadda dani ba? Ai nima daliline yasa hakan, koka manta niɗin mahaukaciya ce? Haukana ne yasa bana yadda da mutane, kai kuma kaga kana da hankali"

Yusuf yace "Nifa gaskiya inada question mark akan wannan ciwon naki, meya hana ciwon tashi anan?"

Kasancewar a duhu suke, yasa se shseshsheƙar kukan Widad yaji, cikin sauri yace  "Am sorry, i don't mean to hurt you, ban san ze ɓata miki rai ba tambayar yi haƙuri" yai maganar da sigar rarrashi, yana shafa bayanta.

Yauma Allah ne ya kiyaye, dan tana jin Yusuf ya fara zarce ƙa'ida ta narka masa cizo, ba shiri ya cikata ta miƙe ta koma kan shimfiɗar ta, tayi shiruu kamar ruwa ya cinye ta.

Kwanan Nurat uku a Asibiti, anata zuwa duba ta, Allah ya temake ta da akayi hoton ƙwaƙwalwar, babu wata matsala a cikin kanta dan haka aka sallameta daga Asibitin.

Suleiman ne zaune a gaban wani mutum a office, da gani mutumin babbansa ne a gurin aiki, mutumin ya kalli suleiman yace  "Nagaji da gafara sk ko ƙaho ban gani ba, har yanzu babu wani bayani akan Assignment ɗin nan da muka bayar"

Suleiman ya gyara zama yace  "Yallaɓai ai akwai matsala ne"

"Matsala wace iri?"

"yallaɓai wanda muka bawa aikin, shine direban 'yar gidan Alhaji Nasir kuma tare aka sace su"

Ɗan waro ido mutumin yayi yace  "ban fahimceka ba"

Suleiman ya gyara zama yace  "ƙwarai yallaɓai, Yusuf jam'in mune, yaje da saunan aikin direba amma shine wanda muka tura muka saka aiki, kuma yanzu haka tare aka sace su ita dashi"

Jinjina kai mutumin yayi yace  "Amma babu wani abu daya fara gabatarwa na sakamakon binciken da yayi?"

"gaskiya Yallaɓai babu, dan a satin da nayi masa magana ya cemin zezo office yayi bayani, a satin aka sace su"

Mutjmin yayi ajiyar zuciya yace  "shikenan you can leave"

Suleiman ya tashi yayi saluting mutumin sannan ya fita.

Susu huɗune zaune a wani matsakaicin falon Hotel, Alhaji Bukar yace "wata maganar banza da naji, wai yaron nan da'aka sacesu tare shine jami'in tsaron da aka tura yayi wannan binciken"

Alhaji Musa yace  "wane yaron?"

Bukar yace  "direbanta mana"

Alhaji Musa yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, shikenan na kaɗe har ganyena inda wannan yaron da suke yawo tare ne"

Alhaji Haruna yace "kamar yaya ka kaɗe?"

"Ranar da Nurat take birthday sukazo, lokacin da nayi attempting a sacemin ita, shiya ritsa Nurat da bindiga ta gaya masa inda Yar Daula take"

Alhaji Munir yace "ji wata maganar banza, to me yasa tun a lokacin baka faɗa ba se yanzu"

"to ta yaya zan in sani, na tambayi Nurat tacemin itama bata san waye ba, se yanzu da akayi zancen nan sannan na gane"

Alhaji Haruna yace  "gaskiya malam ka kwafsa mana, kayi mana gyɗa a gurin nan, maimakon tun a lokacin kasa ayi bincike a gano maka shi, aji dalilin da yasa ya hana a sace yarinyar, wataƙila ma da tun a lokacin munsan waye shi"

Alhaji Bukar yace  "ku dakata, kuskure ne dai an riga anyi shi, sedai a kiyaye gaba kuma a sake shiri, babban abunda ya ɗagamin hankali shine, bai bada komai na shedar binciken da yake yi ba, babu wanda yasan meye sakamakon binciken nasa, amma tabbas tunda ya gano kayi yunƙurin saceta, nasan ze maida hankali da yin bincike akanka"

Zufa Alhaji Musa ya shiga sharewa yace "yanzu meye abunyi? Hankalina fa ya fara tashi, gashi babu wanda yasan inda suke"

Alhaji Munir yace  "kaine a ruwa ai, tunda kikayi shirme da sakaci"

"Mune a ruwa dai, idan Asirina ya tonu ai naku ma gaba ɗaya ya tonu"

Alhaji Haruna yace "dan Allah kuyi shiru mu nemo mafita, aikin gama ya gama ba yanzu ya kamata a nemi mafita ba, abun da ya kamata mu yi yanzu shine neman mafita"

Alhaji Bukar yace  "yanzu magana ta farko dai shine, mu matsa lamba musan inda Daula yake, ɓatan Daula ma fa wani babban giɓine kuma hatsari a garemu, ga 'yarsa itama bamu san a inda take ba yanzu, ga wannan yaron da wannan maganar ta taso yanzu"

Alhaji Munir yace  "Sannan wanda ya sa aka saki Yaron gurin Halima shima ba ƙaramar barazana bane a gare mu, dan bamu san waye ba, kuma banu san manufarsa ba"

Alhaji Musa yace  "Aini nafi kowa shiga matsala, a hanzarta a nemo mafita gaskiya"

Alhaji Bukar yace "ku kwantar da hankinku, zan san abunyi insha Allah, nasan yadda zanyi da al'amarin"

Alhaji Munir yace  "Yallaɓai meye mafitar to?"

Bukar yace  "when I come out with the final decision I will let you know, Musa ka kwanta da hankalinka, ba abunda ze faru zanwa tufkar hanci"

Alhaji Musa yace  "to shikenan tunda kace haka yallaɓai"


"Mummy karɓi wayarki, tana ta ringing kin barta a falo"

Hajiya Halima tasa hannu ta karɓi wayar tace  "Salamu Alaikum"

"Wa'alaikum Salam, Halima yakike ya yara?"

Haɗe rai tayi tace  "Kai harkuna da bakin da zaka wani kirani kana ya Yara? Bayan rashin mutuncin da kukayi min akan belin Anwar?"

Alhaji Haruna yace  "ke, ki bar wannan maganar akwai matsala ne fa"

"Matsala ta ƙaremu ku acan tsakaninku banda ni, karka sake sani a cikin matsalarku tunda kowa kansa ya sani"

"Aikuwa kece a wannan matsalar, dan wallahi kina ruwa"

"Kamar yaya?" tai maganar cike da mamaki.

"Yaron nan Yusuf yake ko Yunusa, ashe jam'in sirrine, shine wanda yake binciken"

Mummy tace  "kai ɗan tsaya mana, Wai Yusuf direban Widad?"

"Oho nima ban sani ba, wanda dai aka sacesu tare, ashe shine yaron da yake binciken nan, muna ganin munyi dabara ashe da kanmu muka burmawa kanmu wuƙa, yaron nan shine yake gudanar da binciken"

"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, na shiga uku Haruna dan Allah yaron nan dagaske ɗan sanda ne?"

"ƙwarai kuwa, ɗan sanda ne ma farin kaya, kuma shike gudanar da binciken nan"

"Shikenan, wallahi idan ya dawo garin nan tabbas na kaɗe, an karɓi bayanin binciken kuwa?"

"ba'a karɓa ba dan ba'a samu ba, amma Alhaji Bukar yace mu saurare shi, ze faɗa mana abunda za'ayi"

Hajiya Halima tace  "ni dai dan girman Allah ku gaggauta samo mafita, wallahi akwai matsala"  tai maganar tare da ajiye wayar tana faɗin na shiga uku.

Amal tace  "Mummy meyafaru ne?"

Ramlah ma shigowa tayi tana faɗin "Mummy lafiya kuwa?"

"Yara akwai damuwa fa, wai ashe munafukin yaron nan ɗan sanda ne?"

Amal tace "wane yaron wai?"

"wannan shegen direban me siffar munafukai mana"

"Wai Yusuf?"

"Shi, wai ashe ɗan sanda ne"

Ramlah tace  "ta yaya ya zama ɗan sanda? Mummy ke waye ya gaya miki?"

"Yanzu mukayi waya da Haruna yake gayamin"

Ramlah tace "No wonder, sam wannan beyi kalar wanda za'ace yana cikin wahala ba, ko kuma rashin ilimi, ashe munafukine shiyasa na tsane shi, shege Azzalumi"

Amal tace "shiyasa wani lokacin nake hanaki yi masa wasu abubuwan Mummy, ki saki baki kiyi ta sakin maganganu anyhow, gashi abunda ya faru ai"

Ramlah tace   "dan Allah kiyiwa mutane shiru, yanzu mafita za'a nema ko surutan zaki cigaba dayi?"

Amal tace "ko anemi mafita ko kar anemi mafita aikin gama ai ya gama, sedai a kiyayi gaba"

Hajiya Halima tana jinsu tayi shiru, gaba ɗaya ta shiga tunani yadda take sakin magana yadda taga dama, ashe kallonsu kawai yake"

Ramlah tace  "Yanzu Mummy meye abunyi ne?"

Mummy tace "Nima ban sani ba, amma Bukar yace mu saurare shi, ze samo mafita"

"to Ubangiji Allah yasa mafitar me ɓullewa ce, amma nikaina abun ya tsoratani"

Ramlah tace  "ki kwantar da hankalinki Mummy, Insha Allah bakomai, dan ni kaina a tsure nake, kin san na taɓa zuwa nace ya samomin Password ɗin Widad, Amma tunda Alhaji Bukar yace akwai mafita, to tabbas akwaita, ki kwantar da hankalinki"

Mummy ta jinjina kai, Anwar ne yai sallama a ɗakin, ya kalli fuskokinsu yace  "Ya dai na ganku kunyi jugum jugum, akwai matsala ne?"

Ramlah tace  "babu wata matsala"

"Ya zakice babu matsala bayan fuskokinku sun nuna hakan?"

A fusace Mummy tace  'Kai fita ka barmin ɗaki, uban bin ƙwaƙwƙwafi, ance maka bakomai amma ka dage "

" Allah ya baki haƙuri "  daga nan yai waje abunsa.

Da Asuba tayi Yusuf ya dawo daga gurin karatu, lokacin gari yayi haske ya ɗumama musu shinkafa sukaci da safe.
Ya miƙe ze fara shirin fita, ta kalle shi tace " naga kana shiri, ina zakane? "

" Yau ranar kasuwa fa, zanje nema"

Widad tace  "ba inda zaka se ciwon nan ya warke"

"Meyasa?"

"Se kaje wani abun ya kuma faruwa? Ka bari ƙafar ta warke kana ɗingisawa da ƙyar kana maganar zaka fita"

Yusuf yace "Nifa lafiyata ƙalau, kawai dai..

" ba wani kawai, idan kace seka fita kana tafiya, nima zan ɗauki hijjabina in tafi "

" ki tafi kije ina? "

" duk inda Allah yayi "

Yusuf yace " to shikenan, naji na fasa fita"

Widad tace  "karma ka fasa ɗin"

Ta ɗau bokiti tayi waje, suka gaisa da Gwaggo, Gwaggo tace  "Amarya ɗan miƙomin robar can me ruwan ɗorawa"

Widad ta tsaya tana waige waige, tace "tana ina robar take?"

Gwaggo tace  "gata can a bayanki"

Widad tace  "to ai ban san meye ɗuruwar ba"

Gwaggo tayi murmushi tace  "ruwan ɗorawa nace, gata can a gefen randa"

Widad ta ɗakko robar, tace  "Gwaggo meye ruwan ɗaurawa"?

"Kalar robar ce ruwan ɗorawa"

Widad tace  "Ok Yellow kenan zaki ce Gwaggo"

Gwaggo tace  "Ahh mu nan haka muke cewa"

"Gwaggo dan Allah meye faskare?"

Hari tace  "na shiga uku da wannan lamari, waike komai baki sani ba? Kwarankwatsa ko a birni an san waɗan nan abubuwan, amma kiyi ta rainawa mutane hankali"

Kamar basuji me tace ba, Gwaggo tace  "Saran itace shine Faskare"

Widad tace  "a dinga saran bishiya?"

"Eh a sassara bishiya, a farfasa yadda aza'a iyayin girki dashi"

Widad ta ɗanyi shiru, sannan ta jinjina kai, ta kuma cewa  "Gwaggo wai meyasa naga ruwanku seya dinga yin kala,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login