Showing 147001 words to 150000 words out of 209297 words
hadimi a katafaren gidan Daula"
"Waye wannan?" ya nuna masa Yusuf.
"Shine direban 'yar gidan Daula, shi yake kaita duk inda zata je"
Barrister Sadik yace "ya akayi kuka haɗa baki kuka sace ta, harka basu mafaka?"
Saleh ya kalli Yusuf, ya sunkuyar da kai yace "Bayan Yusuf yayi duk shirin daze, ya nemi da ina nema masa inda ze zauna ya ɓuya, ba tare da an gano inda suke ba, yayi Alƙawarin ze bani kuɗi, ni kuma na yadda na amince, daya sato ta na gaya masa inda zamu haɗu, shine na kaisu wannan ƙauyen daga baya ya je ya saida motar, muka raba kuɗin "
Yusuf ya ƙurawa Saleh ido, amma Saleh ya kasa ɗaga kai ya kalli Yusuf, ya sunkuyar da kai yai shiru, yakasa kallon Yusuf, shima Yusuf bashi da zaɓin daya wuce ya sunkuyar da nasa kan, Umma se kuka take tana mamakin, ya za'ayi ace ɗantane yai wannan abubuwan haka? "
Barrister Khalil yace 'idan kotu ta bani dama, zan gayyato Malam Audi, wanda shine Saleh ya nemo ya ɗauki Yusuf da' yar gidan Daula, a ƙurƙurarsa zuwa cikin ƙauyen da akayi garkuwa da ita"
Malam Audi ya fito shima, Barrister Khalil yai masa tambayoyin duk daya dace yai masa, shima ya bada amsa, kamar yadda aka buƙata.
Barrister Khalil, ya kira doctor Mustapha wanda shine Likitan daya duba Widad lokacin da aka harbeta, shima ya fito ya tsaya ya bayyana sunansa a gaban kotu.
Barrister Sadik yace "Doctor Almustapha, kaine Likitan daya karɓi 'yar gidan Daula, lokacin da Wannan bayin Allah suka kaita Asibitinka ha akayi?"
Doctor Mustapha yace "eh hakane, Wataran da safs ina aiki, suka shigo cikin Asibiti na, ɗauke da wata matashiyar budurwa wadda take a galabaice, jini nata zuba daga jikinta, suka shiga da ita Office ɗina, sukace patient suka kawo in duba musu, nace musu bazan karɓi case ɗinba, saboda harbine a hannunta, amma Saleh ya ciro bindiga yace idan banba ze kasheni, haka na cire mata bullet daga jikinta, ko gama watstsakewa ba tayi ba suka ɗauketa suka gudu"
Justice Abdullah A dutse yace "wanda ake ƙara ko kana da abunda zaka ce?"
Yusuf ya girgiza kansa alamar A'a, ya juya ga Barrister Sadik yace "muna saurarenka Barrister"
Barrister Sadik yace "ya me girma me shari'a, wannan sune ƙwararan shedunmu da zamu gabatarwa wannan kotu, sannan in Allah ya yarda a zaman kotu na gaba zamu ƙarasa kawo shedunmu da tarin hujjojunmu, wanda zasu tabattar da wanda ake zargi shine ya sace 'yar gidan Alhaji Daula"
A dutse yace "duba da yadda barrister ya gabatarwa da kotu shedunsa, kuma aka tambayi wanda ake ƙara be musa ba, da kuma yadda Barrister ya nema, wannan kotu tayi umarni da' a maida wanda ake zargi gidan gyaran hali, zuwa sha biyar ga wata me kamawa"
Daga nan ya buga gavel, wato gudumar kotu.
Yusuf ko ɗaga kai baya yi, saboda bashi da idon daze kalli al'umma dashi mussman masoyansa, wani abun idan ba'ayi ba anyi wank, ga tarin hujjoji da shedu da aka gabatar, shi kuma gashi ba masanin fannin shari'a ba, to idan ya musa ma yace me? Bashi da zaɓin daya wuce ya amsa, haka aka kuma zura shi a motar gidan yari, ba'a bari 'yan jarida sunyi magana da shi ba, kowa wani yayi magana da shi ba aka tafi da shi.
Koda Nurat taga yadda kanun shari'ar ya gudana yau gaba ɗaya ta ɗimauce, ta rasa inda zata saka ranta yanzu shikenan babu wanda ze tsayawa Yusuf kenan? Dukda wannan shedun da aka gabatar har yanzu zuciyarta bata saduda ba, tana jin sharri ne kawai akewa Yusuf ɗin.
Ta fita taje ɗakin Mummynta, ta tarar tana salla, ta ɗauki wayarta akan gado tai waje, bata tsaya ko ina ba se ɗakinta, ta shiga ga kulle ƙofa ta ciki ta kira Khalil.
Yana ɗagawa ta fashe masa da kuka, yace "subhanallah, Nurat ya haka?"
"Khalil kana gani an gabatar da shedun ƙarya akan Yusuf, shikenan haka za'a bari a kulle shi, ba zaka iya komai ba?"
Khalil yace "Nurat, abun ya wuce tunanin ki, ke yarinya ce kuma kina gida a zaune baki san meke wakana ba, wallahi ana nan ana barazana ga duk wanda yai yunƙurin shiga shari'ar nan da nufin kare Yusuf, kedai ki cigaba da Addu'a, Allah zeyi ikonsa, kuma..
Ai bata jira meze ƙarasa faɗa ba, ta ajiye wayar tai shiru ta dafe kai, ta rasa abunyi dan yanzu kukanma bata iyawa, gaba ɗaya taji kamar jiri na kamata, ta buɗe ƙofa ta fito tana dafa bango, sedai tama zuwa falo kawai ta faɗi a gurin, hakan yai dai dai da shigowar Alhaji Musa, ya ƙaraso kanta da sauri yana kiran sunanta, sedai bata san meke cewa ba.
Ya ɗakko ruwa me sanyi yana shafa mata, a hankali ta dinga sauke numfashi, Mummynta ta fito falo kawai ta tarar da Alhaji Musa rungumen da Nurat yana shafa mata ruwa.
Tace "subhanallah, Daddy meye ya sameta?"
Alhaji Musa yace "nima ina shigowa na tarar ta faɗi ƙasa"
Tace "subhanallah, ko Asibiti zamu tafi?"
Yace "A'a, ɗan tsaya muga naga kamar ta farfaɗo"
Yace "Nurat"
Ta buɗe idonta ta kalle shi tace "Na'am Daddy"
Yace "meke damun ki ne haka? Ina shigowa naga kin faɗi, meke damun ki?"
Ta girgiza masa kai alamar bakomai.
"Kyace fa bakomai? Gata nan ko Abincin kirki bataci, na rasa meke damunta, bayan tea ko biscuit, bayan nan bata cin komai, haka yake wuni duk tabi ta ƙare ta bushe"
Ya kalleta cikin kulawa yace "meke damunki ne Nurat, meyasa bakya cin Abinci? Duk kin rame"
"Daddy ni bana son tafiya karatun nan dan Allah ka ƙyaleni"
Yace "shiyasa bakya cin Abincin?"
Ta jinjina masa kai, yace "zanyi shawara, fitinarki da rawar kanki ce tai yawa, shiyasa nake son turaki can, zanyi shawara amma kidena ƙin cin Abinci"
Ya ƙura masa ido, yana sonta dukda halinsa dayake ita 'yarsa ce yana sonta, amma meyasa ze jefa rayuwar' ya'yan wasu cikin damuwa? Adalci kenan hakan? "
Hawaye ya shiga gangarowa gefen idonta, ya dinga share mata yana ya isa haka, tashi muje ki kwanta ki huta anjima zan kira likita yazo ya dubamin ke.
Ya kama hannunta, ya kaita ɗakin ta ta kwanta, sannan ya fito ya rufe mata ɗakin.
Yauma Widad na zaune, ta ari wayar sabuwa ta duba yadda shari'ar ta kasance, sedai babu wata hanyar mafita ko nasara akan lamarin, babu wata hanya da zata bi ta temaki Yusuf, gashi bata da tabbacin da wace manufar wannan matar ke nuna mata kulawa da tausayi, saboda Bulama makirine, babu abunda baze iya ba, haka ta bata wayarta ta, ta koma ta kwanta, tare da lumshe idonta.
Har yanzu tana jin alamun cikin ta na nan, dan babu abunda ya sauya na daga abunda takeji, na laulayi shikuma Doctor Hamisu ya tabattarwa da Bulama cikin Widad ya fita, gaba ɗaya ta koɗe kamar ba Widad 'yar ƙwalisan mam ba, matashiyar' yar hamshaƙin attajiri, 'yar gayu me cin zamaninta ba, duk tayi wani iri, ga tashin hankali da tunani ha pressure ciki, abunda bata saba ba bata san yadda yake ba, ga kuma sauran ciwukan da suke damunta, banda uban duka da take sha a hannun Bulama, da sauran mugunta da yake mata.
Yusuf yana zaune a gidan yari, akace yazo yayi baƙi, shi dai yasan an dena barin kowa yazo inda yake, Umma ma sau ɗaya aka bari ta ganshi, ko saƙo aka kawo masa ba bashi ake ba, haka yake zamansa a wahale, Yusuf ɗan gayu daya saba da tsafta, rayuwar gidan nan ba ƙaramin wahala take masa ba.
Aka fito da shi zuwa ofishin gandirobobi, yaga wannan ɗan sandan me kula da sashin manyan laifuka, daya zauna a sashensa lokacin da yana hannun 'yan sanda, wanda ya dinga azabtar dashi, Yusuf na ganinsa ya sake haɗe rai ya ƙaraso ya zauna.
Ya kalli Yusuf yai murmushi yace "haba Yusuf, ba faɗa meya kawo gaba kuma? Meye na haɗe rai dan ka ganni, ashe an fara shari'arka?"
Yusuf yai masa banza yaƙi magana, yace "shikenan, tunda bazakamin magana ba, na fuskanci kai dai halinka ne a haka, miskilanci da taurin kai, zamanka a hannunmu be sa ka canza ba, kai dai haka Allah yayi ka kenan?"
"mekazo yi gurina? Bayan an hana kowa yazo gurina kai meyasa aka barka kazo gurina, me zan maka?"
"kwantar da hankalinka, ai dole zan gaya maka ms zakamin".
Yasa hannu a aljihunsa, ya ɗakko biro da farar takadda a cikin wani file, ya miƙawa Yusuf yace "ɗan Yimin signing ɗinka a nan in gani"
Yusuf ya kalli takaddar ya kalli ɗan sandan yace "na menene wannan?"
"kai meye naka na tambaya? Ka saka hannu nace"
"bazan saka ba" ya bada amsa kai tsaye.
"Ni kake cewa bazaka saka ba, kai idanma tinƙahonka kaima ɗan sandane, aiko a aiki na girmeka, haka a shekaru ni zaka gwadawa taurin Kai?"
Yusuf yace "eh bazan saka hannunbau, bazan saka hannu akan abunda ban san meye ba"
Aikuwa ɗan sandan ya kashe Yusuf da mari, Yusuf kuma ya rama, kafin kace kwabo gandirobobin nan sunyo kan Yusuf da duka, kota ina suka haɗu suka masa lilis, ko motsi baya iyayi, sannan aka sureshi aka maida shi, a galabice.
Ɗaurarrun gidan dayawa sun sanshi, baya magana ba ruwansa da kowa, kamun kansa yasa suke girmama shi, musamman da suka jiya ana masa laƙabi da maitama, akace musu ɗan gidan marigayi Bashir maitama ne, su suka karɓeshi, suna mamakin wane laifin yayi aka kama shi aka dake shi haka? Suka samo ruwan zafi a kitchen aka dinga gasa masa inda ha farfashe a jikinsa.
Duk takurar da akayiwa Yusuf akan ya gwada yin signing ɗinsa, su sake gwadawa dana Bulama su gani ƙi yayi, aka ƙara tsananta masa a gidan kurkun nan, hantara cin mutunci zagi, ayyuka ma wahala amma Yusuf yaƙi sakawa fafur, danma wani abun fursunoni sukan shigar masa saboda suna ganin salihancinsa da haƙurinsa be kamata a dinga cuzguna masa ba. Ranaku gudu suke, lokaci na ƙara sauri, kamar ƙyaftawar ido, lokacin komawar Yusuf kotu yayi, suka sake shiga kotu domin cigaban shari'arsa.
A wannan karon kuma Barrister Saminune ya fito dan gabatar da shedu da hujjoji akan Yusuf.
Barrister Saminu ya gabatar da kansa, sannan yace "kamar yadda wanda aka yi ƙara yayi da'awa a hannun 'yan sanda cewar a hukumance aka bashi umarnin yayi aiki a gidan Daula, domin bawa' yarsa kariya, sedai a iya binciken 'yan sanda babu wanda ya sashi wannan aikin, sannan hukumar' yan sanda tayi Allah wadai da abunda yayi sun sallameshi daga aikinsa gaba ɗaya, kuma abokin aikinsa me suna Abbas Habib, wanda wanda ake ƙara yace shine shedarsa akan an sashi aiki a gidan Daula, ya tabattarwa da kotu cewa, Babu wanda yasaka Yusuf wannan aiki, Yusuf ƙarya yake masa dan haka Yusuf yayi basaja ne a gidan Daula, yaje da suffar mutanen kirki danya sace 'yarsa "
Babu abunda ya bawa Yusuf mamaki se jin sunan Abbas, da kuma abunda akace yace a game dashi, ya jinjina kai ya tuna yadda Widad take nuna tsanarta ga Abbas, ashe Abbas ze iya yi masa haka? Sekuma yai tunanin Amma Suleiman yana kotun nan, kenan shima baze iya taimakonsa ba? Yusuf yai shiru kawai yana sauraren ikon Allah.
Babban Abun mamaki, harda su Ramlah aka kira a matsayin wanda zasu bada sheda akan Yusuf ne ya sace Widad.
Barrister Saminu ya kalli Ramlah yace "ko zaki iya shedawa kotu wacece ke?"
Ramlah tace "Sunana Ramlah, kuma Widad 'yar uwatace"
"ko zaki shedawa kotu abunda kika sani game da Yusuf, alaƙar dake tsakaninsa da Widad yarinyar daya sace?"
Ramlah tace "eh to, lokacin da aka kawo shi zeyi aikin direba, da bata aminta dadhi ba ita Widad, saboda halinta na rashin yadda, ganin mahaifinta ya yadda dashi, shiyasa itama ta haƙura da hakan ta yadda dashi a matsayin direban nata, Daya ke mukan ɗan gaisa da shi, wataran yake tambayata wai dan Allah nasan Password ɗin Widad na banki, dayake daga baya ta ɗan yadda dashi har ɗakinta yana shiga, nace masa me zeyi da password ɗinta na banki, se yace min bakomai tambayata kawai yayi, se nace masa nima ban sani ba, to haka dai Widad ta kan yi complaining akan ana mata sace sace bayan babu wanda yake shiga ɗakinta seshi, har wataran sukayi sa'insa ta kusa korarsa, mahaifinta ya hanata, sedai ba daɗewa wannan lamarin ya faru aka neme ta aka rasa "
Barrister yace " Shikenan, mungode Malama Ramlah zaki iya komawa kije ki zauna "
Yusuf yabi Ramlah da ido, har taje ta zauna, me shari'a yace " ko wanda ake ƙara, yana da abun cewa? "
Yusuf ya girgiza kai, ya maida kai ya sunkuya, Umma ta tashi da sauri ta fice daga kotun, tana kuka.
Barrister Saminu yace "idan wannan kotu ta bani dama, zan sake gabatar da sheda akan wanda ake zargi"
Wani ma'aikacine daga gidan gonar Daula ya fito, aka gabatar da shi a matsayin Iliya.
Barrister Saminu yace "ranar da abun ya faru, ance kana nan da daddare kana aiki a gidan meyafaru?"
Iliya yace "eh to, a ranar sunzo gidan dashi da Ita, da Alhaji Nasir Daula, cikin dare suka fito shida ita kamar ze nuna mata wani abu a wajen mota, kawai ya buɗe motar ya dannata ta ƙarfi, lokacin ina saman benen dake kusa da inda suke, kafin in sakko wasu mutane sun ɓullo daga gurin fulawoyi a laɓe, da alama dama suna laɓe ne gidan a ɓoye suka buɗe masa gate, Jin motsi yasa Daula ya fito a guje, yace lafiya? Se Saleh yace ai wasu mutane ne suka shigo suka fita da Widad, shine Daula ya faɗi a gurin "
Suleiman ya sunkuyar da kai kawai, dan kowa yaji yadda ake gudanar da wannan shari'a, tsantsar son zuciya ne kawai da rashin imani, wata irin bahaguwar shari'a ake ba fasali babu komai, kuma duk wanda ya bada sheda babu wani bin diddigi a masa tambayoyi dan tabattar da abunda yake faɗa, kawai se a karɓi wannan shedar.
Barrister Saminu yace "idan kotu ta bani dama, zan gabatar da sheda ta ƙarshe wadda itace me ɗungurungum, wadda zata tabattar da Wanda ake zargi shine yai garkuwa da 'yar gidan Alhaji Nasir Daula.
Yusuf ya ƙura ido yaga waye ze shigo, me ze gani Widad ce aka shigo da ita, tayi haske amma da gani kasan hasken cutane, ta rame tayi wani iri, duk wanda yasan ta a baya, idan ya ganta baze ganeta ba se mutum yayi dagaske, saboda tsabar rama da fita hayyacinta da tayi.
Yusuf yabi Widad da ido, yadda ta koma yana tunani daban daban a ranta.
Akaje aka tsaida Widad, amma ta gaza kallon Yusuf, yayin da Yusuf ya kafe ta da idanuwa, Barrister Khalil yace "ko zaki iya bayyanawa kotu wacece ke?"
"Widad Nasir Daula" ta bashi amsa, ba tare da ta kalle shi ba, ya nuna mata Yusuf yace "kin san wannan?"
Ya nuna mata Yusuf, ta jinjina masa kai, waye shi? Meye alaƙarki dashi? "
Bata kalli inda Yusuf yake ba tace "da farko direbana ne, yayi aiki tare dani a gidanmu"
"Lokacin da yayi aiki dake, kin san cewar ɗan sanda ne?"
Ta girgiza kai, "Ana zargin shine ya sace ki, yai garkuwa dake, me zakice akan haka?"
"Eh Yusuf yayi garkuwa dani, na zauna a hannunsa tsawon watanni biyar, sedai babu wani abu na cutawarwa ko tsoratarwa da yayimin"
"Ya isa haka Malama Widad, zaki iya tafiya"
Barrister Khalil ya katseta, ganin hawaye ya cika idonta tana neman ta saki layi, aka fito da ita zasu tafi, se a lokacin ta ɗaga kai ta kalli Yusuf, taga yadda yake binta da kallon da bata gane na menene ba? Hawayene ke shirin gangarowa a idonta, ta girgiza masa kai, ta fita daga cikin kotun.
Tana fitowa tai karo da Umman Yusuf, cikin kuka Umma tace "Wallahi keda Allah, Allah ya sakawa ɗana, wallahi Allah ze bi mana haƙƙinmu, saboda rayuwarki ta ɗana ta kassara, a sanadiyarki aka kashemin miji, yanzu gashi sanadinki za'a kullemin ɗa, bayan danke duk ya shiga wannan halin, Allah yana kallonki fa, kiji tsoron Allah "
Umma na zubda hawaye, Widad na zubda hawaye, tana son tayi magana amma ta gimtse maganarta saboda abunda hakan ka iya haifarwa, ta shige mota ba tare da ta cewa da Umma Uffan ba.
Alƙali ya sanya sati biyu, domin yanke hukunci na ƙarshe akan Yusuf, kotu ta watse ana Yusuf bashi da sauran mafita, tunda ita da bakinta ta tabattar da ya sace ta.
Gaba ɗaya hope ɗin Yusuf ya ƙare, tunda Widad ta tabattar da hakan ba shakka bashi da mafita sam.
Abun duniya ya ishi Widad, aka maida ita inda ake tsareta a gidan Bulama, ta ɗora hannu a kanta tana wani irin kuka, jikinta har rawa yake, zuwa yanzu tana jin yadda abunda ke cikinta yake ɗan motsawa kaɗan kaɗan.
Bulama ya shigo ɗakin da Widad take, yana kallonta ya kwashe da dariya yace "ban taɓa tunanin zaki so wani abu a rayuwarki bayan mahaifinki, kamar wannan shashashan Yaron ba, kamar ma kinfi sonshi akan Daula, sedai na ƙarar da soyayyar a nan, na saka mata aya, tunda gidan yari za'a kaishi"
Widad ta kalli Bukar tace "Kayi kuskure, kai Yusuf gidan yari baze taɓa kawo ƙarshen soyayyar da nake masa ba, dukda kai ba mutum ne me cika Alƙawari ba, nasan ba lallai ka cika Alƙawarin da kamin akan Yusuf ba, ni dai fatana kamar yadda mukayi da kai kar kuyi sanadiyyar rayuwarsa dan Allah "
Tai maganar tana kuka a gaban Bulama, yai dariya yace " wannan kaɗai be isa in bar yaron nam a raye ba, harse kin gayamin inda kayan nan suke "
Widad ta kalle shi tace " A zatonka kafini wayo da dabara ne, to bari in gaya maka abunda baka sani ba tsayin shekaru, Daula ba dukiyar ya ɗauka ya danƙamin ba, ya naɗi video akan yadda takaddun suke, da yadda dukiyar take da kuma a inda take, ni kuma dana tashi na bawa Amintacce na ya ajiyemin, nasan ko