Showing 24001 words to 27000 words out of 209297 words
ni wanda Yoseef yake ɗebo mana yafi wannan kyau sosai"
Gwaggo tace "ban hana kiran sunansa kai tsaye ba"
Widad ta toshe baki tana dariya, tace "yi haƙuri na manta ne, wanda mijina yake ɗebowa"
Hari tace "hmmhmm wa yaga kwaɗo, ba kunya wai mijinta"
Widad tace "to da mijinmu ne nida ke?"
Hari tace "A'a ni Allah ya tsareni, mijinki ne ke kaɗai"
Gwaggo ta girgiza kai tace "Inda Yusufa yake ɗebo muku ruwane, ba giri ɗaya da namu ba, shi birtsatse yake zuwa ya ɗebo muku, kuma tafiyar da yake a ƙasa kafin yaje gurin ta ɓaci, da nisa sosai ita kaɗai ce burtsatse a garin nan"
"Gwaggo dan Allah meye burtsatsi?".
"Ruwan famfo, amma na tuƙa tuƙa"
"Nasan dai famfo, amma ban san meye tuƙa tuƙa ba"
Shikan sa Yusuf da yake ɗaki yana jiyosu, seda yace "Allah yasa kar Gwaggo ta gaji da wannan tambayoyin na Widad.
Allah yasa aka zuba mata ruwan ɗumi ta tafi wankanta.
Bayan ta fito daga wankanne tana shiga ɗaki, ta tarar Yusuf ya tattara kayansu na wanki ya ɗaure a guri ɗaya.
Ta kalle shi tace " wannan fa?"
"wanki zanje inyi mana"
"A ina?" ta tambayeshi
"Can wani gurine bakin ruwa, nake wankin, jira nake in ƙarasa yi miki girkin rana in tafi in wanko kayan"
Widad ta ajiye bokitin, ta ƙarasa tace "gaskiya zan bika"
"Ki bini ina?"
"Gurin wankin mana"
"No kiyi zamanki a gida inje in dawo, gurin ba kowa kuma bakin ruwane"
"gaskiya ban yadda ba, tunda muka zo garin nam ban taɓa fita ba, gaskiya ka tafi dani, nima base in koyi yadda akeyi ba im dinga yi mana"
"bana so Kisha wahala ne, ki bari inje inyi indai fitane, zam fita dake mu zaga gari"
A hasale tace "bana so tunda ba zaka dani ba shikenan"
Ya fuskanci haushi taji, dan haka ya ƙarasa inda take yace "Meyasa kike da saurin Fushi ne Masoyiyya, shikenan zamuje tare, kinsan bana son ɓacin ranki"
Tura baki tayi taƙi magana, ya juyota ta fuskance shi yace "smile mana habibty"
Tura baki ta sake yi tace "baza ai smiling ɗinba"
"In kina tura bakin nan i just feel like to kiss you"
Ɗago ido tayi da sauri cikin Shagwaɓa tace "kaga ka bari bana so"
"to yi min murmushi in ƙyaleki"
"to ai murmushin ne be zoba"
Yadda tayi maganar ne ta bashi dariya, yace "shikenan, ina bim bashi se anmin murmushin nan. To ko in ta yaki sa kayan?"
Da sauri tace "A'a bana so wallahi" tai maganar tsoro ƙarara a idonta.
Murmushi yayi, ya juya ya cigaba da haɗa kayan, seda ya kammala yayi musu girki, sannan yai waje.
Ta tsaya ta saka hijjabinta, da silifas ɗinta ɗan madina ta fito, Hindu taga Widad ta sha hijjabi, dan bata saba gani ba idan ba salla Widad zata yi ba sunyi hannun riga da hijnabi, Hindu tace "Amarya ina zuwa haka?"
"Fita zamuyi nida Yoseef, naga kamar Gwaggo wanka take inta fito ki gayamata"
Hindu tace "shikenan zan gaya mata insha Allah, sekun dawo yau zanyi wunin kaɗaici"
Widad tace "Allah sarki Hindu, nima zanyi kewarki, semun dawo"
"Shikenan Allah yasa karku daɗe"
Widad tayi hanyar fita, sedai tana zuwa ta tarar an zubawa Manyan ragunan megari harawa a hanyar fita wajen, gasu da manya manyan ƙaho a murɗe, sun kai su goma sha, suna ture ture suna cin Abinci.
Ƙura musu Ido Widad tayi, tana tunanin ta ina zata wuce.
Jin shiru Widad bata fito ba yasa Yusuf dawowa yaga ko lafiya.
Ya tarar da ita a tsaye tana kallon raguna, Yusuf yace "Madam ke nake jira fa, kim tsaya kallon raguna"
"Nifa tsoro nakeji"
"Tsoron mekuma?"
"kar inzo zan wuce su dakeni da wannan ƙahon nasu"
Yusuf ya girgiza kai yace "yanzu ragunan ne yasa kika tsaya kika kasa fitowa? Duk soyayyarki da dabbobin kuma yanzu tsoronsu kike ji?"
"To wai so kake, su dakeni da wannan ƙahon suji min ciwo, ko ance maka ni 'yar sanda ce?"
Yusuf yace "iyee au abun hadda baƙar magana, ai shikenan"
Ya ratso cikin ragunan ze kama hannunta su wuce, amma taƙi wai sedai ya koresu ta wuce, amma bazata shiga ta tsakaninsu ba.
Cak ya ɗagata ya ratsa ya wuce, sannan ya ajiyeta, hakan yayi dai dai da fitowar Hari taga abunda ya faru, ai take ta fara salati
"la'ilahaillalahu, yau nake ganin gardiyar lukutar baɗala a tsakar rana, wane irin abune haka goɗoɗo ba fasali bakomai?"
Seda Yusuf ya ƙunshe baki yana dariya, Widad har tayi shirin ramawa, ya janyo hannunta sukayi waje.
"Alhaji Haruna, nayi muku duk iya ƙoƙarin da zanyi muku, duk ayyukam da kuka sani nayi muku, yakamata ku zama masu cika Alƙawari fa"
"Kai Saleh wai baka san a halinda muke ciki bane? Wai ashe yaron da aka sace 'yar gidan Daula dashi, wai ashe ɗan sanda ne"
Hantar cikin Saleh ta kaɗa amma ya basar yace "kamar ya ɗan sanda, direba dai"
"to ɗan sanda ne, anyi bincike an tabattar mana da jami'in tsarone ma farin kaya"
Saleh yace "lallai biri yayi kama da mutum, amma yaya aka yi haka ta kasance?"
"Kai zamu tambaya, tunda kai muka wakilta a wannan ɓangaren"
Saleh yace "to ai nima ban san komai ba, ban san shi aka saka ba sam, amma gaskiya ya iya yaudara, shine yazo a matsayin direba"
Alhaji Haruna yace "to gashi nan dai, kuma bincike ya tabattar kamar maye yake akan aikin sa, idan ya saka case a gaba se yaga bayansa, kuma bimcike ya nuna ya fara gano Alhaji Musa, sannan Hajiya Halima tayi ɓarin zance a gabansa"
Saleh ya dafe kai yace "to yanzu meye abunyi?"
Alhaji Haruna yace "abunyi kam a yanzu babu, Alhaji Bukar yace mu saurare shi, ze nemo mana mafita"
Saleh yace "lallai abubuwa sun fara lalacewa, ya zama dole a hanzarta samo mafita, tun kafin su dawo garin nan in bahaka labari fa ze canza"
Haruna yace "gaskiya ne maganar ka, muna nan dai muna sauraren Bukar"
Saleh yace "Amma ya maganar ɗan uwana kuwa? Naga bakwa wani abu akan Alƙawarinmu fa"
"kai dalla ana ta kai wake ta kaya? Muna ruwa tsundum muna tsakiyar masifa kana maganar wani mutum da a yanzu bashi da wani amfani"
"Alhaji Haruna, ɗan uwan nawane bashi da Amfani, dama haka mukayi daku?"
"to ba dole ince bashi da amfani ba, tunda a yanzu ba ta tashi muke ba, muna tsakiyar masifa kana wani zance daban, ni kaga tafiyata, ina da appointment ƙarfe biyu da rabi"
Ya tashi ya bar masa falon, Saleh ya jinjina kai yace "lallai ashe kuwa an yanka, kuma zata tashi"
Suna tafe suna hira, tana yaba kyan garin dukda rashin ababan more rayuwar dake ƙauyen.
Widad ta kalli Yusuf tace "ya naga kana ɗingisawa ne, ko in goyaka ne?"
Yusuf yay murmushi yace "wai zaki goyani, kamar ba kece kika kasa wuce raguna ba ɗazu"
"to ba tsoro nakeji ba, so kake sumin illa?"
"wane ni ince wani abu ya samu Gimbiyata, ai bam san idan zan sa raina ba"
"Eh ai ka iya saurin kare kanka"
Suka cigaba da tafiya, Widad tana ta tambaye tambaye, wata tambayar idan tayi sekace wannan tsabar rainin hankali ne, nan ko harga Allah abubuwa da yawa bata sani ba, can tace "Allah sarki, wai se gani a ruɓabiyar motar ice aka kawoni garin nan, Allah sarki rayuwa"
Yusuf yace "hakane, Allah yasa hakan ya zama silar alkhairi"
"Mhmm Ameen, amma naji jiki ranar, ji nayi kamar zan bar duniya ba dan da kai ba da ban san meze faru dani ba, Nasan idan muka koma gida kana da tukuici a gurin Daddy, ka kula da amanarsa"
Yusuf yayi murmushi yace "ni bana buƙatar komai a gurin Daddy a matsayin tukuici se abu ɗaya"
"Meye abu ɗayan?"
"Ya barmin Widad in cigaba da rayuwa da ita, har ƙarshen rayuwata
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
60_61
Kallonsa ta ɗanyi tace "ina fatan Allah ya rabaka da son abunda ba zaka samu ba, na gaya maka babu Aure a tsarin rayuwata, bazan ji daɗi ba ace wani abu ya sameka saboda ni ba, amma ina fatan zumuncinmu ya ɗore nida kai"
Yusuf yayi Ajiyar zuciya yace "naga jarrabawa daban daban a rayuwata, ciki harda Jarrabawa a kan Soyayya, sam bani da sa'a a wannan ɓangaren, dukda tarin gargaɗi da kashedin da kikemin akan Sonki da nake, nakasa jin zan iya dena sonki, a kowane lokaci ina sake jin sonki a raina"
Shiru tayi suka cigaba da tafiya, ba tare da sun sake cewa komai ba.
Ta kalli Yusuf tace "ko mu tsaya ka huta ne? Saboda ƙafarka"
Yusuf yayi murmushin yaƙe yace "waye yace miki nagaji ne? Ko ance miki nima ragone irinki?"
"Nice ma raguwar?"
"Eh kece, me tsoron rago da spider ba"
Dariya tayi tace "kaikam baka mantuwa ko? Saura mu koma gida kace ga abunda nayi ka jamin raini"
"Ni na isa in faɗi abunda Gimbiya tayi, ai wannan sirrine kuma tarihi ne me matuƙar girman gaske daze zauna a zukatanmu nida ke"
Widad tai murmushi tace "gaskiya ne, wannan rayuwar ba zata taɓa gogewa a zuciyata ba"
Yusuf yace "dukda ragoncin nan naki, akwai inda na jinjina miki Gimbiya, ban taɓa tunanin samun jarumar mace kamarki ba, yadda kika sa hannu kika rama dukan da kidnappers ɗin nan sukayi miki, na jinjina miki ta wannan fannin"
Murmushi tayi tace "hakan ya samo asaline tun daga ƙuruciya ta, Allah Sarki, Allah ya jiƙan Ammi na da Baban Yoseef"
Da sauri ya kalle ta yace "Kaman Babana kikayi wa Addu'a"
Tace "Eh iyayenmu da muka rasa nayiwa Addu'a, ko baka so"
"Ni na isa imce bana so, Ameen ya Allah, ubangiji Allah yayi musu Rahama"
"Ameen"
Sunyi tafiya me nisa sannan suka iso rafin, ba kowa a gurin, gurin shiru se kukan tsintsaye, da kaɗawar bishiyu.
Widad tace "Wow masha Allah, ɗan uwa gurin nan yayi kyau sosai"
"enjoy yourself"
Yusuf ya shiga aikin yi musu wanki, yayin da Widad keta kalle Kallen tsuntsaye.
"Ɗan uwa da ruwan nan yana da kyau sosai, da swimming zanyi"
"kin iya ruwane?"
"Taɓ sosai ma, na iya ruwa sosai fa, ina shiga"
"Ai da alama kina da rashin ji, ba wanda ze gane hakan se wanda yake zaune dake"
"Wanda yake zaune da ni ɗin ma ba kowa ne ze gane hakan ba, kaima ban san yadda akayi na sake da kai haka ba, haka kurum naji kamar in yadda da kai"
"Aikin gama ya gama ai, kinma yarda dani ni ɗin"
Cigaba tayi da wasanninta a gurin, tayi nan tayi can ta Leƙa nan ta leƙa can, Yusuf yana ta wanki har ya kammala, yai shanya ya zura ƙafafinsa a cikin ruwan, kusa da Yusuf tazo zauna itama ta zura ƙafafunta a ruwan tana kallonsa.
"Meye kuma kike kallona?"
"Me zan kalla?"
"Muni mana" ya bata amsa
Murmushi tayi tace "kaine mummunan? Ai baka da muni sam"
Murmushi kawai yayi, yana jefa dutse a cikin ruwan.
Widad tace "kasan wani abu?"
"A'a sekin faɗa"
"Ban taɓa sanin a duniya akwai mutane nagari kamarka ba, da ina yiwa talakawa kallon mayun kuɗi, maciya amana, amma gaba ɗaya you proves me wrong"
Yusuf yace "dama bekamata ka yankewa mutane hukunci da laifin tsirari daga cikinsu ba, duk lalacewar zamani akwai na kirki"
Widad tace "Aikama nagani, dan yadda nake treating ɗinka a gida ban taɓa zaton zaka iya taimakona ba, nayi mamakin ganin hawaye a idonka lokacin da ni kaina na yanke tsammani da cigaba da rayuwa"
Ta ƙarasa maganar tana kwanciya a jikin Yusuf.
"Habibty, a wannan lokacin da kin mutu ban san ya zanyi ba, Nagode Allah da ya nunamin na Aure ki, dukda ba kya sona"
Shiru tayi ba tace komai ba, can Yusuf yace "Widad, yanzu idan na mutu zaki damu?"
Tsaki tayi tace "wace irin tambaya ce wannan?"
"Tambayarki kawai nayi"
"To wannan wace irin tambaya ce mara amfani, kawai muna hira ka kama wannan zancen ni bana so"
Ɗagota Yusuf yayi ya kalli idonta, ƙwallace kwance a idonta, se wani tura baki take, murmushi yayi ya maida ita jikinsa ya kwantar da ita, ya shiga shafa bayanta.
Ɗagowa tayi ta kalle shi tace "Ɗan uwa"
Yusuf yace "Yaushe na zama ɗan uwane, naji kin canza min suna'
" Gwaggo ta hanani faɗar sunan ka, kuma kaga ni bani da ɗan uwa, se gaka ka bani jini, kaga mun zama 'yan uwa tunda an samun jininka, mun zama' yan uwa kenan"
Dariya Yusuf yayi yace "wannan philosophy ɗinfa,? Lallai kam shikenan nima nayi ƙanwa tunda bani da ƙanwa mace"
Ta gyara kwanciyarta a jikinsa tace "Yoseef, idan muka koma gida zaka dawo gidanmu ka zauna kaida ummanka?"
"Ai muma muna gida" ya bata amsa
"Dan Allah ka dawo gidanmu, nasan bazaka cigaba da tuƙani a mota ba, nasan maybe ma in koma ƙasar waje, amma dan Allah ka dawo gidanmu kaji"
Girgiza mata kai yayi yace "so kike Mamansu Amal ta dinga wulaƙanta Ummana? Kuma zaman me zanzo inyi a gidanku, bayan bamu da wata alaƙa, kafin nan fa mun rabu"
"Dan mun rabu shine zaka ce bazaka dawo gidanmu ba, sannan idan na koma gida dole ta bar mana gida"
Yusuf yace "meyasa?"
"Saboda wani dalili me girman gaske, amma yanzu ba wannan maganar muke ba, dan Allah idan mun koma gida ka dawo gidanmu da zama,"
"Nida bakya sona, me zan zo gidanku inyi? Idan dai har ina ganinki zan cigaba da sonki ne, kuma ni bakya sona"
"Nifa ba tsanarka nayi ba, kawai ni bana son soyayya ne, ban santa ba kuma ban iya ba, dan bata birgeni, ƙarya ce da tarin damuwa a cikinta, amma ni bana son ko mun koma gida kayi nesa dani, na saba da kai sosai, kana iya haƙuri da dukkanin halayena, kuma kai garkuwa ne a gareni, dan Allah Yoseef ka yadda kaji ɗan uwa"
Yusuf kam murmushi yayi, a ransa yace 'sarkin taurin kai, kina sona amma kina garani'
A fili ya maze yace "Idan muka koma gidanku ace munje kwaɗayi, ni nafison in zauna a gidanmu nida Ummana"
"dan Allah, ba wanda zece muku haka, Dan Allah Yoseef kaji"
Juyowa yayi yana kallonta, har cikin ranta take maganar.
Wani abune ya dinga fizgar Yusuf game da Widad, yana jin wani irin farinciki a tare da shi, abunda bata son dai yayi mata, sedai wannan karon bata hana shi ba, sema biye masa da tayi.
A hankali ya cire bakinsa daga nata ya riƙe hannunta yace "ina sonki Habibty"
Ajiyar zuciya tayi ba tace masa komai ba.
Kawai ya tsaya ya zuba mata ido, a hankali tace "yakamata muje muci Abinci"
Yusuf ya cikata, suka miƙe ya shimfiɗa musu abu suka zauna, ya buɗe shinkafa da wake, da manja ya ɗakko tumatir da gurji ya yayyanka, ya juya suka fara ci.
Suna ci yana kallon Widad, ta kwantar da hankalinta, ta rugumi ƙaddarar rayuwarta, da farkom zuwansu ne se yayi fama kafin taci Abincin, amma yanzu hankali kwance ta dinga cin Abincinta.
"Wai meye kake kallona haka?"
"Gani nayi kina loma fiye da tawa, zaki cinye Abincin ki barni"
"Cigaba da kallona, cinyewa zan in barka"
Ya dinga jin farinciki, ganin yadda Widad ɗinsa ke nishaɗi tana fara'a, saɓanin Widad ɗin daya sani a baya, me shegen haɗe ran tsiya da koke koke, mara afuwa da tausayi.
Juyawa yayi gefensa ya tsinko wata 'yar ciwa, ya miƙo mata yana cewa
"If you ask me to be your king, i will turn around and said, you mean to tell me that I can have you when ever I want, i can tell you that I love you when you love me too, no more waiting for ever our love...
Kwashewa da dariya Widad tayi tace " Ai ba haka ake waƙar ba, kuma flower ake bayarwa, amma ni ka bani ciyawa sekace wata Akuya"
Yusuf yayi murmushi yace "A yanzu bani da wani abu da zan baki ai, shiyasa na baki wannan instead of flower"
Hannu tasa ta karɓa, ta kalli Yusuf tana murmushi.
Saleh ne a gigice ya shiga babban Ofishin dake cikin harabar gurin, Suleiman ne zaune yana danna system ɗinsa, Saleh ya shigo da sallama.
Suleiman ya ɗago tare da yin murmushi yace "Masha Allah, yau kaine a ofishin nawa? Kwana biyu"
Saleh ya miƙa masa hannu suka gaisa, yace "Suleiman ya aikin naku?"
"Alhamdilillah, ya Yusuf fatan yana lafiya?"
Saleh yace "lafiya ƙalau, yana gaisheku ina sa ran zuwa gurin mahaifiyarsa, im sake kwantar mata da hankali tare da tabattar mata yana cikin ƙoshin lafiya"
Suleiman ya gyara zama yace "hakane, hakam abune me kyau nima da week ends ɗin nan, naje gidan sedai har yanzu ta kasa kwantar da hankali ta, akwai buƙatar ka ɗakko mata muryarsa, kokuma ka haɗasu a waya su gaisa"
Saleh yace "No baze yuwu ba, ai bama zuwa garin nan da waya, kai mutanen nan fa sun shallake tunanin ka, nima ina lura da duka abunda nake yi, bana shiga da waya, haka nake zuwa in fito"
"to ubangiji Allah ya kuɓutar dasu, ina mamakin yadda abubuwan suke tafiya, kullum sake taɓarɓarewa sukeyi"
Saleh yayi ajiyar zuciya yace "yanzun ma matsala ce gagaruma ta taso"
Suleiman ya tattara hankalinsa yace
"wace irin matsala kuma?"
"mutanen nan sun gano waye Yusuf, kuma suna shirin ɗaukar mataki akan hakan?"
Suleiman yace "ya akayi suka sani?"
Saleh yace "niba wannan ba, babban abunda ya dameni shine, rashin sanin wani irin mataki zasu ɗauka akansa, gashi kuma yana can yana cikin zulumi akan ta yaya ze sanar da Widad gaskiyar waye shi, kasanta bata afuwa bata yafiya ga duka wanda yayi mata ƙarya, muddin suka dawo garin nan sannan ta gane waye shi akwai matsala "
Suleiman yace " ai tasan waye shi? "
" kamar yaya? Sannan ta yaya?"
Suleiman yace '" dukda gargaɗina