Showing 180001 words to 183000 words out of 209297 words

Chapter 61 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

718

Yusuf ya kalleshi, dukda Yusuf a wahale yake amma hakan be hana Khalil ganin kyau da Yusuf yake dashi ba, yace  "Malam Yusuf, kamar yadda kayi iƙrarin bincike kaje yi gidan Alhaji Nasir Daula, kotu zata so ta san wane sakamako ka samu na binciken? Sannan ina kudin binciken da kayi?"

Yusuf ya ɗaga ido yai ido huɗu da Hajiya Halima, ya kalli inda Bulama ke zaune, ya ɗauke kai yace "An karɓi kundin binciken, lokacin da aka kamoni ina hannun 'yan sanda, sannan a bincikema na farko, akwai yunƙuri da akayi na sace' yar gidan Daula, a gidan wani tsohon ɗan majalisa da taje taya 'yarsa murnar zagayowar haihuwarta"

Khalil yace "ko kana da sheda?"

Yusuf ya girgiza kai, alamar a' a.

Khalil yace "cigaba ina jinka"

"Matar Alhaji Nasir, tana da wani ɓoyayyen nufi akan Widad, suna bata maganin gusar da hankali, sannan suna da wani nufi akan dukiyar Alhaji Nasir, dan akwai babbar 'yarta data taɓa cemin in bata password ɗin Banki na' yar Alhaji Nasir"

"ya akayi kasan password ɗin nata kai?"

"Saboda tana aikena, Na kanyi kwanaki da ATM ɗinta a hannuna"

Barrister Saminu ya mike yace "Objections sir, wannan tambayoyin da Barrister kewa wanda ake ƙara, basu da tushe balle makama kame kame ne kawai sukeyi, dan haka ina Roƙon wannan kotu me Alfarma, da tayi watsi da wannan magana da wanda ake ƙara yake faɗa"

Cikin zafi Khalil yace  "ina da tabacci da ƙwararan shedu akan abunda wanda ake ƙara gaskiya yake faɗa, idan kotu ta bani dama ina son ganin Hajiya Halima, matar Alhaji Nasir Daula, don gabatar mata da wasu tambayoyi"

Aka bashi dama, Hajiya Halima ta fito, gaba ɗaya ta tsoste tsufanta ya fito jikinta se rawa take yi, bayan ta tsaya Barrister Khalil ya nemi ta gabatar da kanta, ta gabatar da kanta a gaban kotu, Khalil yaje gabanta ya ɗakko wata takadda a aljihunsa, ya ajiye a gabanta yace "kin san rubutun waye wannan?"

Jikinta ne ya hau rawa, wasiƙar da Anwar ya bari ce, ta kalli Khalil a razane ta girgiza kai tace  "A'a ban sani ba"

Yace  "waye Anwar a gurinki? '

Tace " ɗana ne"

"kina nufin bashi ya rubuta wannan takaddar ba?"

Ta jinjina kai alamar eh, Khalil ya juya ya kira Murtalah, Murtalah ya fito ya tsaya, Khalil yace   "kotu na buƙatar ka gabatar da kanka, sannan ka faɗi abunda ka sani"

Murtalah yace  "Sunana Murtalah, kuma ɗaya daga masu aiki a gidan Alhaji Nasir Daula, wata ɗaya zuwa biyu baya, naje ɗakin Anwar zan gyara masa, na ga ya bar wannan takaddar, na ɗauka na karanta na kaiwa mahaifiyarsa ba tare da na nuna mata na karanta ba, bayan na kai mata da yamma 'yarta Amal tazo zata fita tana ga sauri, bata sani ba seta yarda takaddar, nikuma na tsinta, kamar yadda ya rubuta a takaddar, tun daga wannan lokacin ba' a ƙara ganin inda yake ba ya bar gidan gaba ɗaya "

Barrister Khalil yace "zaka iya komawa ka zauna"

Yaje ya dudduba cikin takaddunsa ya ɗakko wani littafi, ya dawo gaban Hajiya Halima ya miƙa mata littafin yace  "wannan kamar littafin ɗanki me Anwar, na Jami'a ko?"

Ta karɓa ta duba, ta jinjina kai, Khalil yace  "ki dubamin ko akwai bambanci tsakanin rubutun cikin wannan littafin dana takaddar gabanki?"

Take ƙafafunta suka hau rawa, taji tana numfashi sama sama, ta tsaya tana rarraba ido.

Khalil ya ɗau takaddar da littafin da takaddar, ya miƙawa Alƙali.

Alƙali ya karɓi takadda da littafi, Khalil ya kalli Hajiya Halima yace " wane irin rashin gaskiya ne haka ɗanki yake tuhumarki dashi? Wanda yasa har ya bar gida?"

Hajiya Halima tace
"Ni babu wani rashin gaskiya da nake aikatawa fa, kawai maganace tsakaninsa da 'yar uwarsa akan abunda take aikatawa, da kuma zargin nafi fifita' yan uwansa akansa"

Barrister Khalil ya jinjina kai yace  "shikenan zamu gani"

Akace taje ta zauna, ta koma inda ta taso tana godewa Allah.

Barrister Khalil yace  "ina neman wannan kotu ta bani dama, domin yiwa Babban Amini ga Alhaji Nasir wasu tambayoyi wato Alhaji Bukar Bulama!!!"





Ayshercool
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

152_153

Suleiman yace "Yusuf ka kwantar da hankalinka, dama Allah ya ƙaddara hakan seta faru, ta wannan dalili naka, mudai fatanmu Allah ya baka lafiya ka warware"

Yusuf yace "Ameen, nagode sosai Yallaɓai"

Suleiman yace "bakomai Yusuf, Allah dai ya baka lafiya ya ƙara wanke mana kai daga sharrin maƙiya"

Yusuf yace "Ameen ya Allah, to su lawyoyin da suka tsayamin sun sanni ne? Meyasa suka tsaya min, kuma meyasa basu taimakeni da farko ba?"

"Yusuf, lokacin da ake maka shari'a ta farko, su Bulama sunyi mamaya ga wannan shari'a fiye da tunaninka, ta ƙarƙashin ƙasa aka bi aka dinga samo shedun nan fa, a yadda Khalil yake gayamin, Nurat ce ta takurashi akan lallai ya tsaya a fitar da kai, saboda tasan wasu daga abubuwan da mahaifinta ke aikatawa, to yazo dai ya kawomin ziyara, muka tattauna na gaya masa abunda nasani daga abunda Saleh yake zuwa yana gayamin, yayi duk binciken su daya dace na tallafa masa da abunda nasani, to su dai sauran lawyoyin bansan yadda akai ya samosu ba, nidai ya sanarmin zasu ɗaukaka ƙara, shikenan se ranar shari'a nima na gansu "

Yusuf ya jinjina kai  yace " Alhamdilillah, Allah nagode maka "

Suleiman yace" An gode Allah kam, ka kwantar da hankalinka, komai ze wuce insha Allah "

Umma tace " dan Allah ka kwantar da hankalinka, sannan kai shiru da wannan surutun ka samu isashen bacci "

Yusuf yace " to Umma "

Har Yusuf yayi shiru, ya kuma cewa " Yallaɓai ya Widad fa? A wani hali take ciki? "

Umma tace " Meka ce? "

Yusuf yace   " cewa nayi a wani hali Widad take ciki? "

A fusace Umma tace " waya san mata, baka da zuciya Yusuf, yarinyar tazo ta bada sheda akanka, bayan a dalilinta ka shiga halin da kake ciki, amma kana wani maganar tana ina, in sake jin kayi maganarta sena saɓa maka"

Yusuf yai shiru, Amma yana tunanin shiya kuɓuta, to matarsa fa?.

Widad kuwa tuni 'yan sanda sukaje suka ɗakko ta a gidan nan bayan an kama Bulama yaji matsa ya faɗi inda take, tana zaune a ɗakin da take, taji ana guje guje, ba inda ta iya motsawa daga inda take zaune, Sega' yan sanda sun shigo, suka ɗakko ta suka tafi da ita Asibiti, tayi baƙi duk ta kukkumbura, haka suka ɗakkota a gakabaice ga babu isashen Abinci da kulawa.
'yan sanda suka kama har wannan Sabuwar, wadda take kuka da Widad a gidan.

Da aka kaita Asibiti ma, a emergency aka ajiye ta, saboda ciwon zuciya da jininta daya hau fiye da kima, ga dislocation data samu a hannunta saboda ball da Bulama yake da ita.

Likitoci sun fara tunanin ko a cire mata cikin, saboda kar yai sanadiyyar rasa ranta, Amma Widad a wahal ce tace  "likita, dan Allah ka barmin cikina, gara in mutu dashi a jikina, dan Allah a bawa Yoseef haƙuri, na bada sheda ne dan in ceci rayuwarsa, amma nasan ya bani gudunmuwa, dan Allah ya yafemin, nagode Allah tunda ya kuɓuta"

Haka taita surutai, seda aka mata Allura sannan bacci ya ɗauketa, ta ɗau tsawon lokaci tana wannan baccin, kafin ta farka sedai ga mamakin su, bayan ta farko jininta ya sauka ba kamar da ba, suna yi suna monitoring ɗin yanayin jikinta, da kuma probability na surviving ɗinta da wannan cikin.
   Sedai babu kowa a gurin Widad, musamman mace wadda zata dinga kula da ita, Nurses ne suke mata komai, nan ta sake kukan rashin dangi, da tana da dangi da an samu me kula da ita.
    Ramlah gaba ɗaya itama a zabure take, mutuwar Anwar ta da keta, bata taɓa zaton dagaske Bulama yasaka a kashe Anwar ba, gashi 'yan sanda suna kama mahaifiyarsu, ga Amal ita bame hankali ba ita ba mara hankali ba, haka suke zaune gaba ɗaya rayuwa ta juya musu baya.

Seda Yusuf ya kwan tara a Asibiti, ana masa screening daban daban dan tabattar da ingancin lafiyarsa, Yusuf ya ɗan murmure sakamakon Abinci da kulawa da yake samu, kullum se an dafo Abinci daga gidan Suleiman an kawowa Yusuf, ya ɗan farfaɗo sedai uwar rama da yayi.
Aka sallameshi daga Asibiti, tare da magunguna zuwa gida, tunda suka koma gida 'yan jaje ke sintirin zuwa gidan nan, wasu dan suyi jaje wasu dan suyi kallo, sedai Yusuf ko tsakar gida baya fitowa saboda baya san Hayaniya.
Abokan Aikinsa suka yi tawaga guda sukazo duba Yusuf, seda wasu suka yi kukan farinciki, dukda miskilancin Yusuf, amma akwai kirki da girmama mutane, duk wanda ya ganshi se yayi mamakin ramar da yayi.

Ɓangare guda kuma, hankalin Yusuf yana kan ta ina zega Widad, a wani hali take ciki?

Seda Widad tai sati biyu a Asibiti, cikin ikon Allah ta murmure, jininta ya sauka amma an kafa mata sharaɗin idan ta tashi haihuwa ta taho Asibiti, saboda tana cikin hatsari karta ce zata haihu a gida, dama tunda aka kai Widad Asibitin kullum 'yan sanda cikin patrol suke a Asibitin, har zuwa sallamarta da akayi.

Da aka sallameta ma headquarter na' yan sanda aka tafi da ita, domin amsa wasu tambayoyi da za'a mata, gaba ɗaya saboda yadda akayi shari'ar Yusuf da yadda abubuwa suka wakana, an sauya manyan shugabbani dake riƙe da manyan muƙamai a hukumar, duk an canza wanda Bulama ya siye da wasu.

Widad ta faɗi yadda komai ya faru, tun daga kan kisan mahaifiyarta, da irin Abubuwan da Bulama ya dingayi, ba tare da yasan tasan shine Bukar ba, har sace ta da akayi tare da Yusuf, ta nuna musu inda aka harbeta a hannu, da yadda Yusuf ya dinga wahala da ita, ƙarshe seda aka kamo doctor Hamisu wanda yake mata allurar hauka, da sauran wanda suke da hannu a miyagun laifukan ta'addanci da aka dinga aikatawa Daula da iyslinsa, Shima Saleh can aka samoshi a wani Asibitin gwamnati babu kulawa, saboda garin dukan daya dinga sha ya samu rauni a hantarsa.

Widad bata da gurin wanda zata ta zauna, Akace a kaita gidan gwamnati fa zauna, kafin Allah ya bayyana mahaifinta, tace ita gidan gonar nan zata je ta zauna, akace baze yuwu ta zauna ita kaɗai ba, Amma Widad ta dage ita babu gidan wanda zata ta zauna, aka ajiye jami'an tsaro a layi da kuma cikin gidan dan tsaron lafiyarta aka barta ta zauna ɗi .
Widad Ta dinga tunanin ya akayi Yusuf be nemeta ba, dukda yayi free yanzu, sedai tayi tunani babu lallai Yusuf ya sake karɓarta, bayan ta gaza taimakonsa a lokacin da yake buƙatar hakan.
Gaba ɗaya gidan ya canza, babu manyan dawakan nan nata, da wasu daga dabbobinta duk babu su, haka manyan motocin dake gidan duk babu, an kwakwance wasu abubuwan masu mahimmanci daga gidan, taga gidan ya mata faɗi, babu Daddy babu kowa a tare da ita yanzu.
Ta zauna tai shiru tana tunani, ta fito harabar gidan tana zagaye, ma'aikatan se zuwa suke suna mata fadanci, suna mata jaje tare da barka da Arziki, ta kira wani daga cikin ma'aikatan gidan Imrana, yazo gabanta ya durƙusa tace  "naga gaba ɗaya gidan nan ya canza, ina wasu daga cikin dabbobina da motocin duk da suke cikin gidan nan?"

Imrana yace  "ranki ya daɗe, Hajiya ce take turowa a ɗiba a fita dasu, kuma bamu da ta cewa"

Widad ta jinjina kai tace  "shikenan jeka"

Haka ta dinga zaga gidan, tana tuna abubuwa da suke shuɗe, da abubuwan da suka faru daren da akayi garkuwa dasu, ta shiga ɗakin data kwanta a ranar, tana dube dube, can ta hango wayarta guda ɗaya a ƙasan gado, Da daddy yazo ya azalzaleta ta tashi ta fito wayar ta faɗa ƙasan gado, ta ɗau waya ɗaya ta fita, waya ɗayan da yanzu bata san a inda take ba, ta ɗakko wayar ta ganta a kashe, ta jona a jikin caji aikuwa ta kama.
Ta jona wayar ta koma ta zauna, a hankali tace  "Yoseef am missing you, i have no one, help me to relay on you, ka yafeni ka dawo gare ni mana"

Ta yanke shawarar komawa tayi zamanta ita kaɗai, ta cigaba da Addu'a Allah ya bayyana mata mahaifinta, kota rage wata damuwar, amma da kunya a gareta ta tinkari Yusuf a yanzu.

Gaba ɗaya damuwa da kaɗaici suka baibayeta, ta fito ta ɗau mota zata fita ɗaya daga cikin 'yan sandan dame gadinta yazo yace  "ranki ya daɗe, ina zakije ne haka?"

"Fita zanyi" ta bashi amsa

Yace "ranki ya daɗe har yanzu kina ƙarƙashin kulawar' yan sanda ne, idan kika fita ke kaɗai hakan ze iya zame mana laifi a sama"

Widad tace "shikenan, dan kuna gadina bazan fita ba? Da can wake kula dani idan ba Allah ba? Ina kuna garin nan da saninku aka siye wasu daga cikinku akaci zarafin mijina, aka sacemu babu wanda yai yunƙurin kawo mana ɗauki, se yanzu zaka zo kana gayamin zancen banza? Ban fidda ran a sake dawowa a haɗa baki daku a cuceni ba"

Ɗan sandan yace " Allah ya temakeki, kiyi haƙuri kin san duk yadda kaso ga kamanta gaskiya, se an baka umarnin aimata wani abun daga sama kafin kayi, amma dan Allah kiyi haƙuri karki fita ke kaɗai, dan Allah ki rufamana Asiri, za'a iya ladabatar damu idan mukayi sakaci wani abun ya same ki, har yanzu kina ƙarƙashin kulawar jami'an tsaro ne"

Ta jefa masa key ɗin mota tace  "kaini gidanmu, inda muke zaune"

Ɗan sandan ya ɗauki key ɗin, yana mamakin wannan izza ta Widad, ta shiga bayan mota ta zauna, ta tuna idan Yusuf ze fita da ita, a gaban mota take zama, suna tafe wataran tana zazzaga masa masifa, ko kuma yana wani abun da ze bata haushi suyita faɗa.
Ta lumshe idonta tana jin yadda sonsa ke ƙara ratsa ilahirin gaɓoɓin jikinta, se yanzu ta yadda so babbar cutane, bata taɓa tunanin haka yake ba, bata zaci tayi sabo da Yusuf haka ba, tana jin ya zama wani ɓangare na rayuwarta gaba ɗaya, kobe nemeta ba doke ita ta nemeshi.

Suna zuwa ƙofar gidan, tace ya tsaya yayi horn, yai horn aikuwa Isa yaeƙo yaga waye, kawai ya hangi Widad a bayan motar, aikuwa ya gigice ya tafi da gudu ze buɗe Gate, ya dawo ya kuma komawa ya rasa mema zeyi.
Widad ta sauke gkass ɗin motarta tai masa nuni da yazo, ya taho da sauri jiki na ɓari yazo ya durƙusa yana faɗin  "Allah ya temakeki, Allah ya tsare ki sharrin maƙiya" kawai ya fashe da kuka ya kasa cigaba da maganar.

Widad tace  "Lafiya kuwa? Me yasaka kuka kuma?"

"ranki ya daɗe dole inyi kuka, tunda kika tafi babu ke babu Yallaɓai, gaba ɗaya gidan annurinsa ya ɗauke, muka shiga mummunan yanayi, katsam kuma se gashi kun dawo amma ba'a yadda akeso ba, a wani yanayi na daban abubuwa sun faru marasa daɗi ranki ya daɗe Alhamdilillah tunda dai kin dawo kuma kin kuɓuta "

Widad tace " Isa dukda mugayen halayena da kuke faɗa, dama zaku iya shiga damuwa dan na bar gida? "

Isa yace " A'a a'aha, ai ranki ya daɗe Hausawa sukace kada Allah ya kawo ranar yabo, amma wallahi zamanki a gidan nan ba ƙaramin haske bane, mungode Allah"

Widad tace "shikenan, kiramin su Nura da Murtalah"

Yace "ranki ya daɗe, bazaki shiga gidan bane?"

Tace "Eh, kiramin su"

Isa ya zabura da sauri hadda gudu, ya shiga gidan yana ƙwalawa Su Nura kira.

Aikuwa gaba ɗaya suka rankayo suka biyo shi, suna zuwa suka ga Widad bakinsu yaƙi rufuwa, suka zube a gabanta suna surutai kowa da abunda yake faɗa.

Haka nan Widad taji ƙwalla ta rasa ta mecece? Tai murmushi tace  "Nagode Allah, tunda duk kun tsallake tarko da sharri na Bulama, naji daɗi Sosai da gudunmuwar da kuka bayar a kotu, gurin kuɓutar da mijina, nagode muku sosai Allah yasaka da alkhairi"

Murtalah yace  "wai dagaske ranki ya daɗe Yusuf mijinki ne?"

Abun mamaki wai yau Widad na hira da maa'ikatan gidansu, matar da ko murmushinta ba'a gani idan ba na mugunta ba, ko tana gaban mahaifinta ba.

Widad tace  "Eh mijina ne, ko akwai magana ne?"

Murtalah yace  "A'a, abunne da mamaki sosai ranki ya daɗe"

Widad tace  "IKone na Allah kawai, naji daɗi Sosai da kuka temaka da sheda a kotu"

Murtalah yace  "Ai bakomai ranki ya daɗe, Yusuf mutum ne ya cancanci a temaka masa, tunda na tsinci takaddar nan na rasa ina zan kaita, saboda barazana da akewa duk wanda yai yunƙurin temakawa Yusuf, katsam sega lawyern Yallaɓai, ya gayyacemu gidansa a ɓoye yai tattaunawar sirri damu, a nan na bada wannan takaddar "

Widad ta jinjina kai tace " Masha Allah, ina godiya sosai da gudunmuwar ka, kuma insha Allah kuna da tukuici akan wannan gudunmuwar da kuka bamu "

Nura yace " Allah ya temakeki, wai yanzu dama duk abubuwan nan Alhaji Bulama ke shirya su, tabbas banga laifinki ba na ƙin mutane da kike, amma abun ya bamu mamaki sosai "

Widad tai murmushin takaici, har bata son yuna irin azabar da suka sha, tace " ya ake cikine? Me gidan namu yake ciki dan bazan shiga ba"

Nura yace  "ranki ya daɗe, gida babu daɗi dan ya watse gaba ɗaya, bayan ɓatanku, Yallaɓai ya faɗi yai wata rashin lafiya, babu me zuwa gurinsa ko kula dashi se Anwar, shine yake masa komai yake jinyarsa, da aka sace Yallaɓai a gadon Asibiti ma aka kama shi, akace  da saka hannunsa ya sha wahala sosai, Amma ya kula da Yallaɓai "

Jiki a sanyaye Widad tace " Allah sarki Anwar, yana gidan ne yanzu haka? "

Su Isa suka kalli Juna, jin bata san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login