Showing 54001 words to 57000 words out of 209297 words

Chapter 19 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

724

muka yi magana, Barrister Hafiz, har yanzu bece mana komai game da abunda suka yanke ba"

Alhaji Munir yace  "Aishine, yau kusan sati biyu amma babu wani feedback, idan ba zasuyi ba kawai muje mu haɗo kai da banki, mu kunno wata wutar"

Alhaji Haruna yace "kamar yaya kenan?"

"Ahh ayi takkaddun boge mana, ace ana bin kasuwancinsa wasu mahaukatan kuɗi mana, idan yaso se muyi agreement da bankin, mu basu wani percentage"

Alhaji Musa yace  "amma fa kasan Daula baya cin bashin banki?"

Munir yace "Nida kai muka san wannan, sauran mutane basu sani ba, dan haka muyi tunani akai, idan can baze samu ba se mubi nan, kasan na san Ambassador Auwal Inuwa, kuma kunsan suna da banki, komai zezo da sauƙi"

Haka suka cigaba da ƙulla tsiyatakunsu, kala kala babu ko tsoron Allah a ransu.

Nurat a wuni ɗaya amma gaba ɗaya ta zube ta rame saboda zunzurutun damuwa da tunani, tana tunanin irin hukuncin da za'ayiwa Yusuf idan har aka gabatar da shi a gaban kotu, tana tunanin wannan zalunci ace an sace mutum, kuma a koma da baya a ɗora masa laifin da hukuncunsa daze iya sanadiyyar ɓata feature ɗinsa, tunani ta shiga yi, me za tayi wanda zesa ta samu abunda zata taimaki Yusuf dashi idan buƙatar hakan ta taso?

Ta ɗakko wayarta ta kira Anwar, sedai wayarsa bata shiga sam, ta kuma jarraba layin Khalil amma shima se ace mata busy, ƙarshe dai se haƙura tayi ta ajiye wayar ta maida kai ta kwanta.

Yanzu ɗaliban Widad in sunzo, suke mata wanke wanke da shara, dukda ta nuna bata so amma sesu dage se sunyi, suna matuƙar sonta, dukda bata da fuska amma tana jansu a jiki tana koya musu abubuwa da dama.

Yau Habi ce ta taho mata da soyayyiyar gyɗa me ɓawo, kusan kwano guda tace babarta ce ta kawo mata, Widad tace  "Aini dan Allah nake koyar daku, ba dan ku bani wani abuba, ina dai roƙonku ku dingamin addu'a, amma ni base kun biyani ba, kuma duk wanda yake sha'awar koyar wani abu, ko abunda nake koya muku ƙofata a buɗe yake yazo ya koya"

Gwaggo tace  "Amarya ba kyau maida hannun kyauta, ai basu isa sun biyaki abunda kike koyar dasu ba, jin daɗin abunda kike musu ne yasa suka baki, ki karɓa kawai"

Habi tace  "yawwa Gwaggo, wallahi ba zamu biyata ba kam, amma dan Allah malama ki karɓa"

Da ƙyar dan Gwaggo tasa baki sannan ta karɓa, bayan tafiyar su Gwaggo ta cigaba dayi mata nasiha, na cewar zasu ga kamar wulaƙanci ne yasa bata karɓar abu idan sun bata.

Tafiyarsu keda Wuya kuma, megari ya shigo, yanzu Widad tana sakin jiki ta gaisheshi, harma wasu lokutan ya dinga tsokanar ta, ya shigo yara suka biyoshi da manyan ƙwarya, ɗaya an shaƙeta da ƙwan zabo, ɗaya kuma Nono ne a ciki, megari yasa Hindu ta kira Widad, ta fito suka gaisa yace  "Nasan Malam Yusuf be dawo ba, ga wannan inji ɗalibansa suka ce a bashi"

Abun ya bawa Widad mamaki, mutanen ƙauyen nan sudai suna girmama malamai, kuma suna da rige rigen son suga sun kyautatawa mutane, saɓanin irin rayuwar da ake a birni, mutum yana ganin ɗanuwansa a matsala amma ya share, koma a haɗa kai dashi a cutar da mutum.

Widad ta karɓi kayan tace  "to Baba, Yoseef ya gode sosai zan gaya masa idan ya dawo"

Megari yayi murmushi yace  "bagwariyar 'yata, Yusuf ake cewa ba Yoseefa ba"

Widad tayi murmushi tace  "na kasa gyarawa, kuma shima ai yafison in ce masa Yoseef ɗin, kona fara cewa Yusuf se in manta"

Megari yace  "Ahh masha Allah, tunda me gidan da kansa haka yakeso gara a kira shi da hakan"

Widad ta ɗau kayan zuwa ɗakinsu, Hari tace  "wai me gida duk kayan nasu ne gaba ɗaya mu kuma fa?"

Yace "ke dai Allah ya shiryeki, nan har siyar da ƙwan zabo kike a gidan nan dana kaji, baki taɓa dafawa kin bawa kowa ɗaya a gidan nan ba, a gabanki dai na faɗa nace ɗalibai da yake koyar damu a masallaci sune sukace a bashi, zalamammiya kawai"

Ya wuce ɗakinsa yana cigaba da mita, Widad taje ta samu guri a ɗakinta ta ɗauki gyaɗar da aka bata tana ci, Yusuf ya dawo ya tarar da ita.

"Gimbiya yau kuma me aka samu haka?"

"Gyaɗa aka bani"

"kuma haka ake cin gyaɗar?"

Raba gyaɗar take biyu da bakinta, idan ta fito shikenan, idan bata fito ba ta haɗa da ɓawaonta ta cinye kayarta.

Seda Yusuf yaci dariya sannan ya nuna mata yadda ake ci, tace  "ga wannan kayan, Megari ya bani yace a baka inji ɗaliban ka"

Yusuf ya kalli yawan Nonon nan da ƙwan zabi aƙall zeyi guda hamsin, yanzu ma a hanya wani ya tareshi ya bashi Albasa.

Yusuf ya jinjina kai yace  "Ni wallahi kunyar karɓar kayan nan nakeji Widad, nifa saboda Allah nake koyar dasu"

Widad tace "nima kaga duk yawan gyaɗar nan haka suka bani, nace bazan karɓa ba Mama taitamin faɗa"

Yusuf yace "gaskiya zan mayar, abun yayi yawa ai"

Widad ta Harare shi tace  "ai sedai ka maida wannan albasar, amma baza'a maida wannan ƙwan da madarar nan ba"

Yusuf yace "kaga kwaɗayayyiya"

"Eh naji, kawai kaje kace mungode"

Yusuf yayi murmushi yace "wai yau uwa ɗakina aka bawa kyauta ta karɓa, har take baza'a mayar ba, saɓanin da kana bata abu zata ce ka rainata, ko zaka cutar da ita"

Widad ta ɗan ja ajiyar zuciya tace "baka manta faɗanmu akan kayan daka bani ba ko?"

Yusuf yace "ya za'ayi in manta? Sedai ya wuce a ai"

"daka san faɗan da Daddy yayi min akan abun da nayi seka yi mamaki, kamar ze dakeni, shi dai Daddy a rayuwar sa kar a wulaƙanta Yusuf, kar a ɓatawa me suna Yusuf rai, ya ƙwace kayan yace shi yana so, bayan ya fita naje na ɗauke abuna, na saka rigar saboda hankalinsa ya kwanta ya dena fushi dani, sedai daya ganni a cikin kayan seda yayi kuka, kasancewar Ammi na matuƙar son irin wannan shigar tasu ta dogayen riguna"

Yusuf yace "Allah sarki, ubangiji Allah yayi mata rahama"

Widad tace "Ameen"

"Amma yaushe zaki ƙarasamin labarin ne?"

"ba rana ba wata" tai maganar tana miƙewa.

Yusuf yaje yayi musu godiya da karamcin nan da suka yi masa, suka ce yafi ƙarfin haka a gurinsu, tunda yake koya musu karatu ai ya gama musu komai.

Yusuf haka ya karkasa kayan nan, yayi rabonsu a cikin gidan nan, Widad kam taji daɗin ƙwan nan da Nono, dan Abinci ma seta ga dama take ci.

A hankali ɗaliban Widad suka ƙara yawa, harda ƙana nan yara, ta koya musu na boko ta koya musu na Addini.

Yauma wajen ƙarfe biyar na Yamma, tana ƙoƙarin sallamar ɗalibanta ƙananan yara, sega Saleh yazo, Kallo ɗaya Widad tayi masa ta ɗauke kanta, jin Sallamar wasu ne yasa ta sake ɗaga kai ta kalle su, Saleh ne shida wani mutum, da wata mace da manyan Akwatunan su.

Mutan gidan ne suka ruɗe da shewa ganin mutanen da suka shigo tare da Saleh, da alama dai sun san mutanen, Maida kai Widad tayi ta cigaba da abunda take.

Matar ba zata wuce shekaru Ashirin ba, ta kalli Widad tace  "Gwaggo ina muka samu balarabiya ne?"

Gwaggo tace  "'yata ce itama, Allah ya bani"

Wadda suka kira da Jamila tun shigowarta, yara suka karɓi jaririyar bayan ta, ta kalli Widad tace  "Sannunki"  kallonta kawai Widad tayi tai shiru.

Jamila tace  "ko bata jin Hausa ne?"

Hari tace  "iya shege ne, tana ji sarai kulaki ne da ba zata yi ba, haka take wannan wulaƙancin"

Saleh ya kalli Widad yace  "Barka da yammaci ranki ya daɗe"

Yanzu ma kallon Saleh tayi ta ɗauke kai, yai murmushi yace  "Ina Yusuf ɗin yake ne?"

Ai kamar da yana magana da dutse, wanda suka shigo tare da Saleh yace  "to wannan da alama 'yar Mulki ce dai"

Ƙarshe da Widad taga zasu takura mata gaba ɗaya seta bar musu tsakargidan ma, ta koma ɗaki.

Baƙin nan suka shiga ɗakin Gwaggo, suka ajijiye kayansu, mutan gidan sunata farincikin ganin Jamila, da mijinta da kuma jaririyarsu.

Saleh da mijin Jamila wato Sunusi, suka shiga turakar megari, bayan ya sallami baƙinsa ya shigo ya tarar dasu, megari yayi murmushi yace  "Soja marmari daga nesa, ya akayi kuka haɗu?"

Saleh yace  "A tasha na gano su sunzo hutu, muka hawo akorikurar shu'aibu tare ya kawomu gida"

Megari yace "Madalla, ya Jamilar ya meɗakin nawa?"

Sunusi yace "duk muna lafiya, gamu munzo muyi muku hutu"

"eh babu laifi, amma Nasan kun kwasarwa yarinyar nan iskar hanya, dan ko Arba'in basu rufa ba"

Sunusi yace "Baffa ya za'ayi, ta matsa ita dai tazo gida, kasan can inda muke babu hausawa sosai, zaman se a hankali gaba ɗaya"

Megari yace "hakane, Allah yayi mana jagora gaba ɗaya, Saleh ya ka baro binni, da mutan kanon Dabo?"

"kowa lafiya ƙalau, na shigo ma ban tarar da Yusuf ba, se ita matar tasa, nayi magana kuma ta shareni"

Megari yace "Malam Yusufa be dawo ba ai, aini tunda nake ban taɓa ganin Yarinya meji da isa kamarta ba, akwai mulki kam, ni kaina na daɗe bata saba dani ba, ko gaisheni ba tayi, ba ruwanta da kowa daga mijinta se Hassana (Gwaggo), se a hankali kuma ta fara sabawa dasu Hindu, se daga baya kuma na gane ɗabi'arta ce rashin yadda da saurin sabo, amma tana da kirki sosai "

Saleh yace " Ai Baffa baka ga komai ba, in dai mulki da ji da kaine, ba abunda ka gani, yanzu ai ta sakko ta saki jiki daku sosai, Amma ai bata da yadda sam"

Sunusi yace "to meyasa, nima daga zuwana na gani, Jamila na mata magana tayi banza da ita, kaima kayi mata ta share"

Saleh yace "idan na gaya maka wacece ita, seka riƙe baki abar maganar kawai"

Megari yace "waini yaushe zasu tafi ne?"

"Ka gaji da zama da sune?"

"Haba wane mutum, aini zuwansu garina Alkhairi ne wallahi, basu takurani ba sam, sedai ina tunanin kana ganin babu wata matsala zamansu anan ɗin, nifa matsala ce bana so"

Saleh ya nisa yace  "babu wata matsala Insha Allah Baffa, amma zamansu anan shine tsira da rayuwarsu, zuwa wani ɗan lokaci insha Allah zasu bar nan, ni dai fatana a cigaba da haƙuri dasu"

"Saleh aini zuwansu nan alkhairi ne, baka tarar da yara gidan nan ba? Da Asuba ko magariba shi Yusuf ya koyar da karatun Addini, gashi da ladabi, ba hantara ba cin mutunci yake gyaramana kwaɓar da mukeyi, da Yamma kuma ita ke koyar da yaranmu darussan boko, da Addini, kasan mu babu makarantu haka na muke zaune da jahilci se ɗan abunda ba'a rasa ba"

Saleh ya jinjina kai yace "Yanzu, ita ke koyar da yara karatun?"

"daka shigo ba kaga yara da 'yan mata a gidan nan ba, dukda gidan nan na mutane ne amma karatu take koya musu"


Saleh yace "Allah sarki rayuwa"





Se daf da magariba sannan Yusuf ya dawo, Yusuf be tarar da Saleh ba dan haka ya gaisa da su Hari ya wuce ɗaki, yana zuwa ya tarar da gimbiyar ta cika tayi fam, kallo ɗaya yayi mata yace  "Subhanallah, me kuma ya faru? Ko nine na miki wani abu?"

Girgiza masa kai tayi tace  "A'a, Saleh ne yazo na ganshi shi da wasu, na kasa yadda hankalina yaƙi kwanciya, ban san suwaye ba"

"To shine zaki ɗaga hankalin ki haka? Ki bari muji ta bakinsa mana"

"A'a, nifa bana son irin wannan abun, ko dai musan suwaye, ko kuma wallahi bazan kuma kwana a garin nan ba, komai dare sena bar garin nan"

Yusuf yace "yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, zan masa magana idan mun haɗu a gurin salla"

Bata son tayarwa da Yusuf hankali, shiyasa ta ƙyaleshi, kamar yadda ya zata sun haɗu da Saleh a masallaci, bayan sun idar da salla, suka gaisa Yusuf yace  "kwana biyu, yau kusan watanka guda rabonka damu"

Saleh yace "wallahi kuwa, abubuwa ne sun ɗanmin yawa, ai ɗazu naga gimbiyar taka, na mata magana juyin duniya taƙi kulani, a gaban mutane"

Yusuf ya ɗanyi murmushi yace  "kasan dama kuna takun saƙa da ita, kuma ta ganka da baƙi bata san kosu waye ba, dole ba zata kulaka ba"

Yace "hakane, amma duk da haka yakamata ko gaisawa muyi, ina gaisheta amma ko kallo ban isheta ba"

Yusuf yace "Allah ya baka haƙuri, zata gyara insha Allah"

'hmmm Yusuf kenan, in dai wannan ce babu ranar gyarawa, baƙin da take magana kuma ba wasu bane, mata da miji ne, namijin shima ɗan megarine, matar ma kusan haka, ya tashi da' yan fitintunu ne baya ji, ga yawon tsiya se a shafe watanni uku huɗu, ba a ganshi ba, shine na ɗauke shi na kai shi makarantar horar da sojoji, to beyi karatun boko ba, dan haka kurtu ne yana barrack suna gadin gidan wani babban hafsin soja, shine yayi Aure ya tafi da matar, yanzuma ya samu hutun ƙarshen shekara ne, ga matar ta haihu shine muka haɗu a tasha sunzo gida, suyi hutunsu a nan amma banda haka babu wani abu, amma kai ɗan sanda ne ai, zaka iya bincikawa"

Yusuf yace "A'a babu buƙatar hakan, gara ta sanine ai, kasan bata da yadda"

"hakane amma ita nata yayi yawa ne"

"Hakane, amma ayi haƙuri dai, yanzu meye labari? Ya ake ciki a gida?"


Saleh ya ɗanyi shiru sannan yace  "Yusuf labari ba daɗi kama, sedai fatan ubangiji Allah ya shiga lamarin"

"Saleh, dan Allah kamin bayani gwari gwari mana, ban gane labari babu daɗi ba, aani abune ya samu Ummana? Ko mahaifin Widad? Ko kuma wata matsalarce ka gayamin mana"

Saleh yace "kwantar da hankalinka babu ɗaya, mahaifin Widad dai kamar yadda ka sani, har yanzun babu wanda yasan inda yake se Allah, ana ta bincike amma shiru, ko yana hannunsu, ko yana wani gurin Allah ne mafi sanin wannan, sannan mahaifiyarka tana lafiya, mun rabu da Suleiman akan zeje ya gaishe ta ma, sedai....... "  Se kuma yayi shiru.

" Se kuma me? Dan Allah ka gayamin kana ɗagamin hankali fa"

"Yusuf jin meke faruwa bashi da wani amfani a gareka, abun da nake so da kai shine, kayi taka tsantsan gurin zuwa cin kasuwar nan da kake yi, sannan ka ƙara tsananta Addu'a, kuyi haƙuri kunci gaba da zama anan, dan sun saka a nemoku duk inda kuke"

Yusuf ya dafe kai yace  "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, yanzu meye abunyi? Zuwa yaushe ne zamanmu ze ƙare anan, kar mu takurawa mutan gidan, sannan kuma cigaban zamana da Widad a inuwar Aure shima matsala ne babba, babu wanda yasan batun Aure mukayi se kai"

Saleh yace  "batun takura, baku takura musu ba, dan munyi magana da megari, sannan Aurenku aini na san anyi, ina da sheda, kawai Allah yasa ku kawai Daula jika"

"Saleh, why are you not serious about this issue? Bafa abun wasa bane, wani irin kallo mahaifinta zemin, wani suna ze kirani dashi idan har muka koma gida da ɗa?"

"Ahh kallon siriki ze maka mana, karka damu Daula ba baƙon zafi bane, idan har 'yarsa tana ƙaunarka, kaje ka tabattar da irin son da take maka tukuna, nidai fatana iya wuya, idan bani nazo nace kubar gurin nan ba, kuyi zamanku anan, ka koma maza karta fara zargin wani abu "


Har Yusuf ya shiga cikin gidan jikinsa a mace yake, gaba ɗaya ya easa meye yake masa daɗi, Saleh ya sake dagula masa lissafi, yanzu idan aka gano inda suke shida Widad meye sunansa? Idan ya kasance Widad ta samu juna biyu meye makomar yaron, sannan yayi mata adalci makuwa, idan har ya bari suka haɗa zuriya da ita, bayan bata san shi waye ba, ba tasan mecece tasa ƙaddarar ba balle yaji hukuncin da zata ɗauka akansa? Baya tunanin ɗorewar Alaƙa a tsakaninsu muddin taji waye shi, ba ita ba hatta mahaifinta baze farinciki ya zamo siriki a gareshi ba.



LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏



76_77

A haka Yusuf ya ƙarasa ɗakinsu, yana zuwa ya zauna yayi shiru ya zurafafa a cikin tunani.

"Meya gaya maka haka, wanda ya jefa ka cikin wannan dogon tunanin?" yaji muryar Widad.

"Bakomai" ya bata amsa

"Har yanzu fa ban canza daga Widad ɗin daka sani ba, bana son ƙarya bana son ɓoye ɓoye, ka gayamin tun kafin kaima in saka a Jerin wanda nake zargi"

Ya kalle ta yace  "zargin me kenan?"

"zargin zaku haɗa kai ku cutar dani, in ba haka ba, meye na ɓoyemin wasu abubuwan da dole nasan sun shafi rayuwata?"

Yusuf ya kalle ta yace  "har yanzu kina tunanin zan iya kasancewa cikin masu cutar dake?"

"Yoseef, zuciya bata da ƙashi ya kamata kamin uzuri, musamman a irin rayuwar da na tsinci kaina, amma ya kamata in dinga sanin al'amuran da suka shafeni"

"Ba wani abu bane, dama ya gayamin muƙara haƙuri da zama anan ne, saboda ana can ana nemanmu, maƙiyanki sun baza komar anemomu, tunda tuni labarin guduwarmu ya iskesu, sannan baƙon da suka zo tare, shima ɗan uwansane, soja ne sunzo hutune shida matarsa, shikenan "

Ba tayi magana ba, se riƙe gashin kanta da tayi, sekuma ta shiga jan numfashi tana zazzare ido, ta dunƙule hannunta, tana girgiza kai.

A Rikice Yusuf yace " Subhanallah, lafiyar ki kuwa Widad? Meyafaru? "

Girgiza kai take hawaye na zuba daga idonta tace " almost ten years, good ten years ana cutar dani, bani kaɗaiba har wanda ya raɓeni, yana ɗaya daga abunda ya nesanta ni daga mutane, bana son rayuwar wani ta shiga matsala saboda ni, amma ƙaddara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login