Showing 30001 words to 33000 words out of 209297 words

Chapter 11 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

712



"If you ask me to be your king, i will turn around and said, you mean to tell me that I can have you when ever I want, i can tell you that I love you when you love me too, no more waiting for ever our love...

Kwashewa da dariya Widad tayi tace " Ai ba haka ake waƙar ba, kuma flower ake bayarwa, amma ni ka bani ciyawa sekace wata Akuya"

Yusuf yayi murmushi yace  "A yanzu bani da wani abu da zan baki ai, shiyasa na baki wannan instead of flower"

Hannu tasa ta karɓa, ta kalli Yusuf tana murmushi.

Saleh ne a gigice ya shiga babban Ofishin dake cikin harabar gurin, Suleiman ne zaune yana danna system ɗinsa, Saleh ya shigo da sallama.

Suleiman ya ɗago tare da yin murmushi yace  "Masha Allah, yau kaine a ofishin nawa? Kwana biyu"

Saleh ya miƙa masa hannu suka gaisa, yace  "Suleiman ya aikin naku?"

"Alhamdilillah, ya Yusuf fatan yana lafiya?"

Saleh yace  "lafiya ƙalau, yana gaisheku ina sa ran zuwa gurin mahaifiyarsa, im sake kwantar mata da hankali tare da tabattar mata yana cikin ƙoshin lafiya"

Suleiman ya gyara zama yace  "hakane, hakam abune me kyau nima da week ends ɗin nan, naje gidan sedai har yanzu ta kasa kwantar da hankali ta, akwai buƙatar ka ɗakko mata muryarsa, kokuma ka haɗasu a waya su gaisa"

Saleh yace  "No baze yuwu ba, ai bama zuwa garin nan da waya, kai mutanen nan fa sun shallake tunanin ka, nima ina lura da duka abunda nake yi, bana shiga da waya, haka nake zuwa in fito"

"to ubangiji Allah ya kuɓutar dasu, ina mamakin yadda abubuwan suke tafiya, kullum sake taɓarɓarewa sukeyi"

Saleh yayi ajiyar zuciya yace  "yanzun ma matsala ce gagaruma ta taso"

Suleiman ya tattara hankalinsa yace 
"wace irin matsala kuma?"

"mutanen nan sun gano waye Yusuf, kuma suna shirin ɗaukar mataki akan hakan?"

Suleiman yace "ya akayi suka sani?"

Saleh yace "niba wannan ba, babban abunda ya dameni shine, rashin sanin wani irin mataki zasu ɗauka akansa, gashi kuma yana can yana cikin zulumi akan ta yaya ze sanar da Widad gaskiyar waye shi, kasanta bata afuwa bata yafiya ga duka wanda yayi mata ƙarya, muddin suka dawo garin nan sannan ta gane waye shi akwai matsala "

Suleiman yace " ai tasan waye shi? "

" kamar yaya? Sannan ta yaya?"

Suleiman yace '" dukda gargaɗina da tayimin, amma bari in gaya maka yadda akayi tasan waye shi, wataran da yamma na kammala abunda nake zan bar office ɗin nan, kawai sega wata mota ta shigo gurin nan a guje, kamar zata tashi sama,
ma' aikatanmu sukayi kanta don son ganin wane mara ɗa'ar ne haka? Ko a jikin me tuƙin, Ta buɗe motar ta fito, wata matashiyar budurwa ce jikinta sanye da abaya, ta saka face mask, sannan ta rufe fuskarta da glass.

Kai tsaye inda nake ta shiga tunkarowa, da ma'aikatanmu sunyi kanta zasu hanata ƙarasowa, nace su barta ta ƙaraso.

Ko kallonsu batayi ba tazo inda nake ta tsaya ta kalleni tace "kaine Suleiman?"

Nace mata "Eh nine"

Tace   "ina son muyi maganane"
Nace mata shikenan, nai mata jagora har office ɗina, muka shiga muka zauna, ta kalleni ta cire glashin fuskarta da face mask tace  "kasanni?"

"Nace mata a'a"

Tace "Amma kasan Nasir Daula?"

Nace "ai duk Nigeria babu wanda be sanshi ba"

tace "sunana Widad Nasir Daula, nazo me zan maka wasu tambayoyi, kuma idan ka amsamin ba dai dai ba, ka shirya karɓar abunda ze biyo baya, bana sassauci ga mutane maƙaryata, waye Yusuf?"

Suleiman yayi ajiyar zuciya yace "wane Yusuf ɗin?"

"Direbana" ta bashi amsa

Suleiman yace "Yusuf jami'inmun ne, ɗan sanda ne na farin kaya" Suleiman ya bata amsa

"danme zaku turoshi? Me yasa kuka turoshi,? wato an haɗa kai daku a cuceni"

Suleiman yace  "Yusuf bashi da laifi, jajirtaccen ma'aikacine me kishin ƙasa, umarni aka bamu daga sama akan cewar, a baki kariya sannan kuma ayi bincike akan wanda suke bibiyar rayuwar ki, amma bayan haka Yusuf be san komai ba"

Cikin isa da izza tace  "akan me? Sannan kuma waye ya bada umarnin hakan? Ko kuma ni nace ina buƙatar hakanne? An haɗa kai daku za'a cutar dani, in ba hakaba meyasa Yusuf yasa hannu akan takardar zeyi aiki dani, dukda na gaya masa hakan tamkar saka hannu akan kwangilar mutuwarsane? Na kama Yusuf da bindiga"

Tun anan Suleiman ya jinjinawa Yusuf, ya yabawa ƙoƙarin sa na jure zama tare da yin aiki da Widad, saboda yadda take magana cike da izza da isa.

Suleiman yace " kamar yadda na gaya miki, Yusuf jajirtaccen ɗan sandane, kuma ba abun mamaki bane samun ɗan sanda da bindiga, sannan Yusuf baza'a taɓa bashi aiki ya dawo dashi yace ya karaya ko baze iyaba, amma sam bashi da laifi, kuma da farko bashi mukayi niyyar bawa aikinba, abokin aikinsane yace a bashi saboda jajircewarsa da haƙurinsa"

Ajiyar zuciya Widad tayi tana huci, inda Allah ya temaki Sulaiman gaskiyar data buƙata ita yake gaya mata, ta kalle shi tace  "Ina buƙatar sanin waye yasa a dinga bin diddigi na?"

Suleiman yace  "kamar yadda na gaya miki ne, ban saniba nima umarni aka bani daga sama, ban san komai akai ba"

Widad tace "shikenan, ni zanje in bincika da kaina, amma zan maka gargaɗi da jan kunne, Yusuf be san na ganshi da bindiga ba, kada ka kuskura Yusuf yasan nasan waye shi, idan har ka gaya masa nasan waye shi zan gane, and you know what am capable of doing"

Suleiman yace "karki damu, Insha Allah baze sani ba, bazan gaya masa ba"

Tace "and Mark you, bana son kowa yasan da nice nazo gurin nan, and zan cigaba da bibiyarka, duk lokacin da Yusuf yayi misbehaving ko wani abu na yunƙurin cin amana ta, to dasa hannunka a ciki"

Suleiman yace "ina me tabattar miki da babu abunda zeyi na cin amanarki"

Ta miƙe a gadarance, ta maida face mask ɗinta, ta saka glass ɗinta ta fito, sedai tana fitowa Abbas ya kawo kai yana shigowa, ta tsaya ta ƙura masa ido, harya shige wani office, sam Abbas be lura da kallon da take masa ba, ba tace komai ba tayi gaba da sauri ta hau motarta ta bar gurin.

Bayan wasu 'yan kwanaki da yin hakan, Widad ta kira Suleiman tace tana son ya gayamata full name na Abbas da rank ɗinsa, amma Suleiman yace  hakan ya saɓa da ƙa' idar aikinsu, sedai ta gaya masa meyasa take neman hakan, bata kuma bi takansa ba bayan kwana uku, aka kawo transfer later na Abbas aka maye gurbinsa da Yusuf.

Saleh ya jinjina kai yace "wato duk inda mutum yake tunanin hatsabibancin yarinyar nan ta wuce haka, yana cam yana ta zullumi akan yadda ze gayamata, ashe tuni ta sani"

Sulaiman yace "tabbas tasan waye Yusuf, kallonsa kawai take sannan kamar yadda naimata Alƙawari ban gaya masa ba"

Saleh yace "Allah sarki, ni gaba ɗaya tausayi yake bani wallahi, bejiba be gani ba yana ta ɗawainiya da yarinyar ta bata san kimar mutane ba, duk naga ta rage wannan zafin kan nata, ta kwantar da mai tana rayuwa a ƙauyen da babu wuta, babu ruwa babu abubuwan more rayuwa, abun gaanin ban tausayi"

Suleiman yace  "Allah sarki Yusuf, samun mutum me irin zuciyarsa se an tona, ina masa fatan ubangiji Allah ya kuɓutaf dashi, daga sharrin Azzaluman nan"

Saleh yace "Ameen ya Allah, amma tabbas Yusuf yana cikin jarrabawa, dan ina tunanin matakin da zasu ɗauka akansa, basu da imani sam"

Suleiman yace "Allah ya fisu kam, amma indai batun sadaukarwa ne, to tabbas Yusuf yayita"

Haka suka cigaba da tattaunawa a tsakanin su.




Se bayan la'asar, lokacin kayansu sun bushe sannan Yusuf ya tattaresu ya ninke, suka kamo hanyar gida, suna tafe suna hira gwanin ban sha'awa, Widad nata takura masa da tambayoyi dan duk abunda ta gani bata sani ba seta tambaya.

Suna zuwa gida Gwaggo tai murmushi tace "Amarya yau gidan nan ba daɗi ba kya nan, duk naji ba daɗi"

Widad tai murmushi tace "nima haka naji ba daɗi yau Mama"

Hindu tace  "wallahi kuwa Gwaggo, gaba ɗaya yau gidan se a hankali ba daɗi da bakya nan"

Hari tace "Nikam naji daɗi, bakin mutane shiru yau ba neman magana"

'
Widad tace  "in mutane na magana ki dena saka baki, danke ba mutum bace"

Gwaggo tace  "Amarya yau wake muka dafa, ban sani ba ko zaki iyaci, dan haka na dama miki kunu gashi can da zafinsa"

Widad tace "wayyo Allah Mamana ta kaina, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, wakenma duk zan iyaci nagode sosai Mama"

Gwaggo tace  "Babu godiya a tsakaninmu ai"
Yusuf kam bayan sun gama gaisawa, ɗakinsu ya wuce, ya bar Widad tana cigaba da neman maganarta.

Hari tana ta ƙulla gyaɗarta ta siyarwa, Widad tazo ta cika hannu ta zuba a hijjabi tayi ɗaki, Hari ta buɗe baki tace  "Wudas yaseen sekin biyani kuɗin gyaɗar nan"

Gwaggo tace  "yi haƙuri, zan baki kuɗin"

Seda tayi me isarta sannan ta koma ɗakin, Yusuf tun yana mamakin halin Widad har ya dena, ta kwaso kwanukan wanke wanke tayi, gaba ɗaya yau wani irin nishaɗi take ji, taji daɗin fitar da suka yi sosai, wani irin farinciki ya dinga ratsata.

Ta karɓo musu Abincin gurin Gwaggo, suka zauna suka ci, bayan sun gama ne ta ɗanyi shiru sannan tace  "Naji daɗin fitar nan sosai Yoseef, ban taɓa tunanin ana samun farinciki haka ba koda babu dukiya"

Yusuf yace "aishi farinciki da jin daɗi base ka tara dukiya ba, indai zakayi tawakkali da yadda Allah ya ajiyeka, zakayi rayuwarka cikin farin ciki da jin daɗi, kuma har kafi me Dukiya walwala ma".

Widad tace  "ƙwarai kuwa yau na gani, rabon da inyi farinciki haka tun Ammi na nada rai, shekara goma baya kenan"

Yusuf yace "kina nufin duk tsawon wannan shekarun, bakya farinciki?"

"tun bayan rasuwar Ammi, ban kuma samun farinciki haka ba, babu club ɗin da bana zuwa a waje, dan inyi nishaɗi, nice club ɗim wrestling stadiums na ball da sauran wasanni, amma babu sauyi, na kanji nishaɗi ne kawai idan nai wasan doki, kona kasance da dabbobi kuma idan ina Tare da Alhaji Nasir Daula "

'yar Wulaƙanci yau kuma saunan baban nata take faɗa gatsal"

Ta cigaba da cewa "nasan Daddy zeyi murna sosai, idan ya ganni cikin walwala haka, danya fidda ran faruwar hakan a rayuwata" ta ƙarasa maganar muryarta na rawa alamun zata yi kuka.

Rungumota Yusuf yayi yace  "haba Jarumata, kuma Gimbiya ta, karkiyi kuka please kiyi haƙuri kinji babyna, nifa jarumtar nan taki burgeni take yi, dan haka idan muka koma gida, zan saki a aikin ɗan sanda kema"

Kwashewa tayi da dariya, tace 'kai dai kaje kaita aikin ɗan sandan, nikam a kai kasuwa "

" Zaki iya kama' yan fashi fa da ɓarayi da wannan dakakkiyar zuciyar taki Baby"

Shiru ta ɗanyi tace  "da wanda suka kashemin Ammi ma ko?"

Yusuf yace "am just kidding, idan wanda suka kashe mahaifiyarki ne, Insha Allah ni zan ɗau nauyin yin wannan binciken"

Girgiza masa kai tayi tace  "this the most dangerous case, don't take the risk of it, ni suke bibiya suke son ganin bayana, dan haka koni ko su, karka sa kanka  a ciki, a yanzu ma kalli yadda kake wahala"

Yusuf yace "Amma suwaye suka kashe ta, kuma meyasa? '

Widad tace " nima ban sani ba"

Yusuf yace "i have to know even a little bit of your life"

"bazan faɗa ba, ban yadda da kai ba" tai maganar tana dariya.

Yusuf yace "ai yadda ta ƙare, tunda muka zama abu ɗaya, har muka kasance a inuwa ɗaya"

Hararsa tayi tace "wace irin inuwa ɗaya"

"Inuwar Aure mana Baby na, kuma gashi.... Sekuma yayi shiru

Widad tace " Kuma gashi me? Ƙarasa mana, kai ko kunyata na baka ji ko? Allah ya shiryeka, ni cikani"

Ƙara rungumeta yayi yana murmushi yace "Kunyarwa zanji? Mutum da matarsa"

"Matar ƙauye ba, dan iya nan ne, kafin mu koma gida zamu rabu'

Murmushi kawai Yusuf yayi bece mata komai ba, a hankali yace " ki gayamin mana "

" wai mai meyasa ka damu se kaji tarihin rayuwata? Ko nima binciken ake a kaina? "

Yusuf yayi dariya yace " wane ni?"

"idan kana son in baka labarin, kwanta in kwanta akan ƙirjinka"

Yusuf yace "dan dai wannan, ai shi yafi komai sauƙi"

Yusuf ya kwanta, ta kalle shi tace "kuma wallahi idan kamin wani abu, se munyi faɗa na gaya maka"

Yusuf yace "idan nai miki me?"

"Bansani ba"

"Allah ya baki haƙuri, niba abunda zanyi miki"

A hankali ta kwanta akan ƙirjinsa, tayi shiru na wani ɗan lokaci



WACECE WIDAD NASIR DAULA.....






LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

60_61


Mahaifin Widad Alhaji Nasir haifaffen garin Kano ne, su biyu Allah ya bawa iyayensu, Shida Yayansa me suna Yusuf.
Yusuf shine babba sannan Nasir, kusan shekaru takwas Yusuf ya bawa Nasir, Nasir da Yusuf suna da matukar haƙuri da biyayya, dan har Yusuf yafi Nasir haƙuri, Yusuf yana matuƙar ƙaunar ƙaninsa, tun suna yara duk wata hidimar Nasir Yusuf ne yake yinta.
Mahaifiyar su Marainiya ce, bata da wani cikakken gata, mahaifinsu Nasir kuma, shikaɗai mahaifiyarsa ta haifa, sauran duk uba ɗaya suke, hakan yasa take fuskantar ƙalubale daga ɓangaren dangin miji, tsangwamar da suke masa ta shafeta.
   Ko a unguwa ana jinjina tarbiyyar Su Nasir, saboda suna da matuƙar nutsuwa, ko tarin abokan nam basu dasu, tare suke komai nasu, kansu a matuƙar haɗe yake, Nasir yana girmama Yusuf a matsayinsa na wansa, shi kuma Yusuf yana matuƙar ƙaunar Nasir da tausayinsa a matsayinsa na ƙaninsa, hakan ne yasa duk inda me sunan Yusuf yake Alhaji Nasir Daula yake girmama shi sosai.

    Lokacin da suka fara tasowa, Nasir ya fara yin abokai, saboda yafi yayansa baki da son mutane, mahaifinsu yana da rufin Asiri daidai gwargwado basu nemi komai sun rasa ba.
Sun fara kawo ƙarfi Allah ya karɓi rayuwar mahaifinsu, sunji mutuwar nan sosai, sun daɗe suma alhinin mutuwar nan, da ran mahaifinnasu dama dangimsa ba damuwa sukayi da su ba, balle yanzu ya bar duniya, dan haka suka sake yin watsi dasu, suka ci gaba da faɗi tashi suda mahaifiyarsu.

A wannan ƙadamin wasu mutane suka tare a kusa da gidansu Nasir, sedai mutanen ba masu ƙarfi bane ba, Nasir yana matuƙar tausayin Yaran gidan, saboda rashin gata, a haka ya janyo ɗaya daga cikin 'yan gidan ya zama abokinsa, Yaron sunan kakanshi ne dashi, shine ake masa inkiya da irin inkiyar kakan nasa wato Bulama, kullum tare suke cin Abinci da Bulama, suje yawon balla tare da sauransu.

Sedai halayar Bulama da Nasir tasha bamban, Bulama baya shakkar iyayensa, ga mugun rashin ji da yake fama, dan haka Yusuf ya tsani Bulama, yayi yayi ya raba Nasir da Bulama abu ya gagara.

Yusuf yana jami'a, Nasir yana babbar sakandire Allah ya karɓi rayuwar mahaifiyarsu, Sunyi kuka sosai, saboda ita kaɗai ta rage musu, wadda suke kalla suji daɗi, saboda dangin mahaifinsu dasu da babu duk ɗaya, ga mahaifiyarsu itama ba wani gata ne da ita ba, dan haka koda aka share makoki babu wanda yabi ta kansu, cewar dangin mahaifinsu ai su ɗin mazane zasu iya kula da kansu, base am ɗau ɗawainiyar su ba.

Nan Nasir ya ƙullaci dangin mahaifinsu, dama harda sakacinsu yayi sanadiyyar rasuwar mahaifiyarsu, tana rashin lafiya sun yi sintiri gidan ƙanin mahaifinsu ya basu kuɗi su kaita Asibiti amma ya hana, suka dinga 'yan uwan uban akan su temaka musu amma suka ƙi.

Haka suka tattara ɗan abun hannunsu, suka kaita Asibiti aka rubuta musu Allurara dubu saba' in, suna cikin taradaddim yadda zasu samu kuɗin rai yayi halimsa.

Tunda Allah yayi mata rasuwa, Nasir be ƙara takawa inda dangin mahaifinsu suke ba, haka Yusuf ya cigaba da buga buga da faɗi tashi, ya sai musu Abinci ya biya musu kuɗin makaranta, amma duk da haka Nasir be rabu da Bulama ba kuma be dena tamaka masa ba.

A haka da ƙyar Yusuf ya kammala karatunsa, ya dinga faɗi tashi neman sana'a, ya samu aikin banki da ƙyar ta hannun wani ɗan siyasa.

Cikin ikon Allah, Allah ya rufa masa Asiri har yayi Aure, dukda Nasir ya kawo ƙarfin daze fita ya nema, amma Yusuf be fasa ɗawainiya dashi ba, hatta sabulun daze wanka Yusuf seya siya ya bashi, akayi sa'a Nasir yana ɗasawa da matar Yayansa sosai, saboda bashi da ƙyuya, duk aikin data sashi yi mata yake, dukda kasancewarsa ya zama saurayi, wasu lokutan har zama suke suyi hira tare, ko suyi shawara.

Ɗan zuwan da suke gidan, haka Bulama yake mata 'yan sace sace, haka take shiru saboda Nasir, Yayan Nasir ya sha dunƙule kuɗi masu kauri ya bawa Nasir da nufin yayi sana' a, amma se Bualama ya ziga shi, su kewaye kuɗin suyi bushasha, aita kashewa 'yan matan Bulama, su sai kaya su sai kayan Ball ayi shagali kuɗi su ƙare, da Yusuf yaga abunda yake faruwa seya koma yake kafawa Nasir sana' a, nan ma Bulama ya bishi su ragargaje komai.

A hankali Nasir ya fara yiwa kansa faɗa, yaga asarar da yakewa Yayansa tayi yawa, gashi be taɓa nuna masa ya gaji ba, sedai yayi fushi yace baze sake bashi jari ba se yayi hankali.

Ya koma ya sameshi yace ya bashi jari, in Allah ya yarda ze alkinta, Amma Yusuf yace baze bashi suje su haɗu da sakarkarun abokansa su cinye ba se yayi hankali, haka yaita sintiri amma ya hana shi.

Da yaga hakan yaƙi seya koma ta gurin matar Yusuf wato Nadiya, watarana yaje ya sameta a falo, bayan sun gaisa yace  "Anty taimako nake nema fa"

Tace "temakon mefa?"

"Anty Yaya ya hanani Jari, nayi nayi amma yace se nayi hankali, dan Allah kisa baki, nasam yadda yake sonki da kince a bani ta zauna"

Nadiya tayi murmushi tace "ai kai lamarin naka ne se a hankali, se an baka kaje ku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login