Showing 174001 words to 177000 words out of 209297 words
ba, yaga dai duk shedun da aka gabatar babu wanda yai wata magana da ta shafe shi, amma yaji an ambaci sunansa.
Ya tsaya yana zazzare ido, ya miƙe cikin fargaba ya fito ya tsaya a inda ake tsayawa, Barrister Khalil yace
"Alhaji Bukar Bulama, duniya tasan kaine babban abokin mahaifin Widad, wato Alhaji Nasir Daula, ko zaka iya gayamana abunda kasani game da ɓatanta?"
Bulama yace "Eh to, kafin ɓatan nata dai, kamar yadda ka faɗa ni ubane a gurinta, dukda rashin yaddarta ga mutane akwai kyakkyawar alaƙa tsakani na da ita, Daula da 'yarsa sun bada amanna sosai ga wannan bawan Allah, sun yadda dashi sosai.
Har nake ja masa kunne akan yayi taka tsan tsan, da wannan yaron saboda be kamata ace yana shishigemasa haka ba, saboda duniya babu gaskiya, wata rana ina bacci cikin dare, sega wayar Daula ina ɗagawa a gigice yake gayamin ai Widad direbanta ya gudu da ita, a daren na tafi gidan gonarsa, yake gayamin ya kira Yusuf akan ze kai Widad Abuja, yana son ya kwana a nan gidan gonar dan suyi tafiyar Asuba suje da wuri, amma cikin dare Yusuf ya sace ta ya gudu da ita"
Barrister Khalil yace "duk ina ma'aikatan gidan, da har ya gudu da ita a mota babu wanda ya sani?"
"Nima ban saniba, tunda seda abun ya faru sannan ya kirani"
Khalil yace "Kasancewar ka Uba ga wannan yarinya, bayan an gano inda take, an karɓota daga hannun masu garkuwa, an kaita Asibiti an gama mata dukkanin wasu gwaje gwaje da yakamata, tana hannunka a zaune kenan?"
"Eh tana gurina"
Bulama ya bada amsa, Khalil yace "tana gurinka, amma ba'a gidanka da kake zaune da iyalinka ba?"
Bulama yace "Eh, tana wani gidan daban sakamakon rashin jituwa dake tsakaninta da ɗana Fahad, da kuma ta samu hutu"
"Amma me yakawo rashin jituwa tsakaninsu, dukda cewar kusan uba kake a gurinsu duka"?
Bulama ya rasa yadda zeyi da tambayoyin Khalil, yace "Eh, nima ban san dalili ba, amma basa jituwa '
Khalil yace "bekamata ace baka sani ba kuwa, sannan duk wanda yasan Alhaji Bukar Bulama a baya bashi da wannan tabon ɗinki a fuskarsa haka? Ko ya akayi ya samu wannan tabon? "
Barrister Saminu yai suka akan abunda Khalil yake yi, amma Justice Mustapha yaƙi saurarrasa, yace Khalil ya cigaba.
Bulama yace "'yan dabane suka yankeni a fuskar"
"meya haɗaka da' yan daba kana babban mutum har suka maka wannan yankan a fuska haka?"
Bulama yace 'kuɗi suka nemi in basu ban bayar ba, shine suka yankeni a fuska da cinya ta "
" ka kai rahoton faruwar hakan ga hukuma? "
' A'a"
Khalil yace "saboda me?"
Bulama kawai yai shiru, yama rasa meze cewa Khalil, saboda yadda ya titsiyeshi da tambayoyi, tabbas da tun a shari'ar farko irin wannan shari' ar akayiwa Yusuf, da baze je prison ba, Umma dake zaune na kallon shari'ar banda tasbihi da hamdala ba abunda take yi a ranta.
Barrister Khalil yace "bayan kai akwai wanda Yasan inda gidan daka ajiye Widad Nasir Daula yake?"
Yace "Eh"
Khalil yace "wakenan?"
"'ya' yana duk sun sani"
'ka bawa' yan jarida damar ganawa da ita? Ko kuma jam'ian tsaro sun san inda take? , ko kuma meyasa iya kaida 'ya' yanka ne suka san inda take, alhalin ana kan shari'a, dole za'a so bincike se anji wani abun ta bakin ta, ka kaita ka ɓoye ta, ka tirsasata ta bada shedar ƙarya a kotu, kai yunƙurin cutar da ita, tai maka rauni da wuƙa, Bulama kaike da alhakin daukkanin abunda ke faruwa a gidan Alhaji Nasir daula, saboda babu wanda yasan sirrinsa sama da kai"
"Objection yame shari'a, wani irin abu Barrister Khalil yakeyi haka? Yana ƙoƙarin liƙa laifi ga wanda be jiba be gani ba, ba tare da wata hujja ko sheda ba, yana ta ƙoƙarin ƙirƙirar labari da hanyar da ze jingina laifi akan wanda bashi da laifi" cewar barrister Sadik.
Alƙaki yace "Barrister Khalil, ko kana da shedar abunda kake faɗa?"
"Ina da ita yame girma me shari'a"
Khalil ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko wata waya, yazo gaban Yusuf ya nuna masa wayar yace "ko za ka iya tuna wannan wayar?".
Yusuf ya karɓa ya jujjuya wayar yace "eh na gane wayar"
"wayar waye?"
Yusuf yace "Wayar Nurat ce, 'yar gidan Alhaji Musa"
Khalil yace "meyasa baka gabatar da wannan wayar a matsayin shedarka ba lokacin da ake maka sharia' ar farko?"
Yusuf yace "saboda an hanani duk wata dama da zan kare kaina"
Khalil yace "ina son ka karɓi wannan wayar, kayiwa kotu bayanin abunda ke ciki"
Yusuf shi gaba ɗaya ya manta ma da batun wayar Nurat, ko ya akayi Khalil ya gano da wani abu a wayar harya ksrɓota oho, saboda Yusuf besan akwai alaƙa a tsakanin Nurat da Khalil ba.
Yusuf ya riƙe wayar yace
"Kamar yadda nake gudanar da bincike na a ɓoye, a gidan Alhaji Nasir Daula, katsam watarana nayi dare a gidan na fito zan tafi gida wasu mutane suka tareni, sunamin kashedi akan lallai suna daga cikin masu bibiyar Alhaji Nasir da 'yarsa, kuma nima zasu dinga bibiyata akan lallai sena samo musu wani abu a hannun Widad, har mukayi sa' insa dasu suka dakeni, still bayan wani lokaci suka sake biyoni, nan ma suka dakeni sedai na ɗau lambar motar tasu, naje na kai Office muka bibiyi lambar, a nan na gano lambar motar gidan Alhaji Musa ce, wato mahaifin Nurat.
sannan na taɓa kai Widad wani hotel, na jirata a waje, ta shiga ta fito tana kuka, bayan mun koma gida, na maida ita naji lallai ina son sanin me taje yi a Hotel ɗin nan, bayan na koma na kasa gane komai, sena nemi manager nace ina buƙatar ya bani record na wanda suka kama ɗaki a hotel ɗinsu, mun kai ruwa rana kafin ya bani, dan seda na biya shi, aka bani Jerin record na wanda suka kama ɗaki na kusan watanni huɗu, a nan naga Alhaji Bulama yafi kowa kama ɗaki, dan yakan kama na wata guda, kuma da na ƙara bincike sena gano suna yawan zama dashi Alhaji Bulama, da Alhaji Musa, da Alhaji Munir da kuma matar Alhaji Nasir Daula, yanayin yadda Widad ke matuƙar tsoron mutane da kuma nima yadda akace za'a dinga bibiyata, yasa naji cewar lallai ya kamata inyiwa binciken da nake kyakkyawan ɓoyo, bayan na system ɗina na wayata, da wanda nake haɗa report a takadda, dan haka na yanke shawarar zuwa gidan Alhaji Musa, Na samu Nurat, na samu bayanai daga bakinta na yadda rashin jituwar mahaifinta da Alhaji Nasir ya samo Asali.
nai amfani da wannan damar, na karɓi wayarta na buɗe wani website nai hiding ɗinsa, na tura mata duk wani sakamakon binciken da nayi, sannan nai linking ɗinsa da wayata duka lokacin dana tura wani abu website ɗin ze shiga wayarta, kuma ze zauna akan wayata, nasan babu wanda zeyi tunanin da wani abu a wayarta, ko da na rasa na gurina"
Aiba Khalil ba hatta jama'ar kotun, sun jinjinawa Yusuf wannan basira tasa, Khalil yace "Amma ya akayi kai garkuwa da 'yar Alhaji Nasir Daula?"
Yusuf yace "banyi garkuwa da itaba, Alhaji Nasir ya nemi da inje gidan gonarsa in kwana, zan kai Widad Abuja dan ganin wani likitan Ƙwaƙwalwa, cikin dare aka turo masa saƙo a wayarsa, ina kwance ina bacci yazo tasoni nida Widad, ya nunamin saƙon yace maza maza in ɗau Widad mu bar gidan, na tsaya ina tambayarsa ina zamuje, yace maza maza in bar gidan da Widad, saboda saƙon da aka tura masa ana barazana ne ga kodai ya bada abunda akeso, ko kuma a hallaka 'yarsa, nace masa mu kira' yan sanda amma yace aa', in kula da Widad, na ɗauketa muka fita ba tare da nasan inda zamuba, munyi tafiya me nisa ga dare, kawai aka zagaye motarmu, da Widad kawai suka so su ɗauka, ta riƙeni tana kuka na hana su tafi da ita, shune suka haɗa dani, kwananmu biyar a hannunsu, Saleh ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan gonar Alhaji Nasir, yaje ya kuɓutar damu, an harbi Widad a hannu ya kaimu Asibiti, aka cire mata bullet, sannan ya bamu mafaka a wannan ƙauyen, ya cemin idan har muka dawo za'a hallaka Widad dani kaina, dan haka mu zauna zuwa lokacin da komai ze lafa, amma bani na sace ta ba"
Barrister Saminu ya mike yace "meyasa baku shigar da ƙara ga hukumar 'yan sanda ba? Ka cigaba da zama da ita a inda babu wanda yasani tsawon lokaci?"
Yusuf zeyi magana Barrister Khalil yace "zan gabatarwa da kotu, wata shedar wadda take nuna wanda ake zargi bashi da laifi a zaman kotu na gaba"
Nan kotu ta hargitse da Hayaniya, kowa yana tofa albarkacin bakinsa, Alƙali ya buga gudumarsa, akayi shiru, yai rubuce rubuce sannan yace
Duba da yadda lawyoyi suka gabatar da shedu da hujjoji, wannan kotu me albarka zata ɗage cigaban wannan sharia'r zuwa nan da sati biyu masu zuwa, dan yin zama na ƙarshe da yanke hukuncin daya dace akan wannan shari'a, sannan kotu tana umarni da hukumar 'yan sanda su binciki Alhaji Bulama da tawagarsa"
Kotu ta ɗau hargowa da sowa, 'yan sanda suka tafi da Yusuf gidan yari, Umma ta kalli Suleiman tace " Suleiman ya haka? Naga za' a maida shi"
Suleiman yace "ki kwantar da hankalinki, kin san shari'a komai a hankali a binsa ki kwantar da hankalinki"
Suleiman yaita kwantar mata da hankali, yana bata baki.
Hajiya Halima ganin ba'a kama da ita ba, yasa ta silale tai gida, zuciyarta cike da fargaba da kuma tsoro, tana tunanin meye mafitarta ta ƙarshe? Tasan tunda Bulama yaje hannu itama tata ta ƙare, sedai tana zuwa gidan ta tarar da gate ɗin gidan hanhai a buɗe, ga motar 'yansanda, ga mutane sun cika gidan, kamar ta juya ta gudu, amma ta fasa ta ƙarasa, tana zuwa me zata gani, an rufe mutum da zani alamar ya mutu, Ramlah se uban kuka take, ga Amal a sume a gefe ana ta mata fifita, jiki na rawa ta ƙarasa gaban gawar, tasa hannu ta yaye zanin, Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!!!
Gawar Anwar ce ɗanta, gawar se zubar da jini take, idonsa a rufe kamar me bacci, kamar kace tashi ya tashi a nutsensa yake, amma ya mutu.
Ta ɗora hannu a ka tana kurma ihu "Wayyo Allah na shiga uku ni Halima, Bulama ka cuceni ka tarwatsa rayuwata, Allah ya isa tsakanina da kai Bulama, Bulama seda kasa aka kashemin Anwar? Nayi dana sanin saninka, da farko ka rabani da gidan uban Anwar, na Auri Shu'aibu shima ka kashemin Auren, ka haɗa kai da Shu'aibu kuka kashe matarsa ya sakeni dan Daula ya aureni, duk biyayyar da na maka, amma ka kashemin ɗana Me ƙaunata da gayamin gaskiya, wayyo Allah Anwar ɗina, wayyo Anwar ka tashi dan Allah, na shiga uku "
Tana wannan ihun, tana maganganun nan ana mata video, ita dai Ramlah kasa cewa komai tayi, se bin mahaifiyarsu da ido, ga Amal wadda babu tabaccin tana da rai itama, dan abun yazo mata akan gaɓa, dama ta gama galabaita babu jini a jikinta, kuma ga wannan mutuwar ta Anwar, ƙarseh wannan kururwar da Hajiya Halima keyi, se rufeta akayi a ɗaki akayiwa Anwar sutura.
Khalil kuwa yana ta rawar jiki yaje ya bawa Nurat labarin yadda shari'a ta kaya, akwai alamun nasara akan shari'ar Yusuf sedai yana zuwa gida ya tarar da fuskaokinsu wani iri, Nurat a zube a ƙasa ana ta fama numfashinta ya tsaya.
Khalil yace "lafiya kuwa?"
"Allah yayiwa mahaifiyar Nurat rasuwa, yanzun nan an tafi ɗakko gawarta daga Asibiti" Anty Saddiƙa tai maganar tana kuka.
Khalil yace "la'ilahaillalah Muhammadu rasulillah salallahu alaihi wassalam, Antyna ta rasu kenan?wallahi Musane ya kasheta, shine ya kasheta"
Yai maganar yana zubar da hawaye.
Haka itama akayi mata sutura aka sallaceta, aka kaita makwancinta na gaskiya, Nurat kam tasha kuka kamar ranta ze fita, gaba ɗaya ta birkice an kasa gane kanta ma gaba ɗaya, se da aka samo likita yai mata alluarar bacci dan ta samu relief.
Amal kuwa har aka kai Anwar bata dawo hayyacinta ba, gawar Anwar ya tara mutane sosai kasancewarsa mutum ne na mutane, ga sauƙin kai da girmama jama'a.
Fahad ya kaɗu da jin labarin an kama mahaifinsa, da kuma harƙallar da suka ƙulla da shi da Hajiya Halima, suka dinga siyar da dukiyarsa ba bisa ƙa'ida ba, ga mutuwar Anwar data dake shi, ya kaɗu matuƙa da jin Anwar ya mutu, ya lallaɓa komtsan sa ya ɗau mota ya gudu.
Haka Bulama ya kasance a hannun 'yan sanda shima, Aka kama Alhaji Musa, shi laifuka biyuma aka kama shi dasu, ga laifin hankaɗo matarsa daga bene, gana wanda suka aikata da Bulama.
Tunda Amal ta farka ta farka ba a daidai ba, tunda ta buɗe idonta bata magana kwata kwata, sedai taita bin mutane da kallo, kamar bata sansu ba, Hajiya Halima kuwa kamar wadda ta shekara a daji, tai wujiga wujiga ko tayi shiru idan aka jima se surutai, taita tonawa kansu Asiri ita da su Bulama, itama ƙarshe ana cikin makoki 'yan sanda suka zo suka yi gaba da ita.
Nurat tana cikin tashin hankali, na rashin mahaifiyarta, ga kama mahaifinta anyi da wannan manya manyan laifuka haka, dukda tarin abunda yai mata na laifuka, amma ya haifeta, gaba ɗaya ta rame tai wani iri, ga labarin mutuwar Anwar ya risketa, mutuwar ta girgiza ta ƙwarai, ba zata manta halacci da kara irin na Anwar ba, Anwar mutum ne nagari me haƙuri da nagarta gaske.
Bulama a hannun Hukumar 'yasanda ɓangaren SWAT aka danƙasu, domin tuhumarsu, dama kuwa masu fushi da fushin wani, dan haka ba'a ragawa su Bulama ba sam, kamar yadda suke sawa a azabtar da wasu, haka suma suka shiga hannu aka dinga azabtar dasu.
Ana wannan halin, a haka sati biyu ta cika, aka koma kotu ranar da aka koma kotu kallo ɗaya zakayiwa Khalil kasan yana cikin alhini sosai.
Kamar kullum an cika kotun nan maƙil, haka aka shigo dasu Bulama, wujiga wujiga.
Khalil ya fito gaban kotu, ya gabatar da shedarsa da suke dashi akan Bulama.
Babban abunda ya bawa Yusuf mamaki, be wuce yadda yaga Sunusi ya shigo ba, ya buɗe baki yana kallon Sunusi.
Sunusi yazo ya tsaya, Khalil ya masa umarni ya gabatar da kansa, Sunusi ya gabatar da kansa sannan yace "tabbas wanda ake zargi bashi da laifi, Saleh ɗan uwanane, kuma akwai Bala Yayansa, Saleh ya haɗa kai da Alhaji Bulama da niyyar ya ɗau fansa akan Alhaji Daula na sakawa da 'yarsa tayi aka tsare ɗanuwansa, dan tana zargin da hannunsa a kashe mahaifinta, sedai Bulama ya gaza cika Alƙawarin da yaiwa Saleh ma ze saka a saki ɗan uwansa, su ɗau fansa akan Daula, ganin haka yasa ya koma taimakon' yar gidan Daula, ya kuɓitar dasu daga hannun masu garkuwar, sannan ya kaisu ƙauyenmu gurin mahaaifina, saboda muddin suka dawo za'a kashe yarinyar, kuma shima Saleh ze shiga matsala, lokacin da sukaje ƙauyen bata yadda da kowa se Yusuf, ga jikinta duk rauni se anyi jinyarta, shi kuma yace ita ba muharramarsa bace, babu yadda zeyi jinyarta wannan dalilin ne yasa Saleh ya shige gaba aka ɗaura musu Aure bisa amincewarta, shedar da aka saka ya bayar a kotu shedar ƙarya ce, tursasashi akayi kuma aka masa rauni a cikinsa saboda duka, akace za'a kasheshi in be bada shedar ba, shine aka kawo shi kotu ya faɗi wannan shedar, sannan lokacin da suke ƙauye ya gayamin idan har aka kama Yusuf za'a kasheshi dashi da Widad baki ɗaya, tunda Daula ma ba'asan inda yake ba, nace masa ya gayawa 'yan sanda, amma yace a"a akwai haɗaka me ƙarfin gaske tsakanin Alhaji Bulama da Hukumomin tsaro, dan haka yana da ɗaurin gindi, idan ya faɗa tamkar ya sake jefasu a garari ne"
Nan kotu ta ɗau salallami, Barrister Khalil yace " Alhaji Bukar Bulama, kaine mutum na farko da Alhaji Nasir ya kira bayan an sace 'yarsa, ya akayi wanda suke turo masa saƙo suka san inda suka tafi idan ba kai ka gaya musu ba? "
Bulama yace " ni.. Ni bani bane ba, ya za' ayi in saka a sace yarinyar da takemin kallon uba? "
Khalil yace " Akwai sheda, ina son kotu ta bani dama, in gabatar da sheda ta ta ƙarshe wanda zata tabattar da Alhaji Bulama shike da alhakin dukkan wannan abubuwan da suke faruwa, yasa akayi garkuwa da 'yar Amininsa, kuma yake bibiyar yadda ze mallake dukiyar Aminin nasa"
Aka bashi dama, wa Bulama ze gani? Su me Adda aka jero a layi, akaje aka tsaidasu, nan da nan Bulama ya sadaƙar yasan ƙarshensa yazo.
Aka tsaida me Adda, Khalil yace "gayawa kotu sunanka"
"Sunana Hashimu, amma ana cemin me Adda"
"meka sani game da garkuwar da akayi da 'yar Nasir Daula?"
Me Adda ya kalli Bulama yace "eh, Alhaji Musane da farko ubangidana, dashi da Alhaji Musa da Haruna da Munir suke sa kamu aiki, nine na dinga bibiyar Yusuf nida yarana, Bulama ne ya kiramu a waya, yace mana ga inda zamuje, motar gidan Daula zata zo da Widad a ciki da direbanta, mu kama Widad, muka je kamata amma shi Yusuf yai ƙoƙarin hanamu, yace mu haɗa dashi, kwananmu biyar muna basu wahala, akan ta faɗi inda dukiyar nan take, amma taƙi, shine yace mu kasheta, dan har mun harbeta ma a hannu, kuma mun musu horon Yunwa da duka, bayan yace a kashesu muna zuwa muka tarar sun gudu, tsawon watanni ba'a gansu ba, seya gano Saleh yana mufuntarsa, shine yace mu kamo Saleh, bayan mun kamk Saleh ne shima muka dinga dukansa muna bashi wahala, daga baya ya bawa 'yansanda shi yace a tuhumeshi ya faɗi inda ya ɓoyesu, bayan wannan kuma yace muje gidansu Yusuf da daddre mu ɗakko masa babarsa, ashe akwai' yan sanda a kewaye da gidan bamu sani ba, muna zuwa suka kama mu "
Khalil yace " tsawon wane lokaci ka ɗauka kana masa aiki? "
Me Adda yace " gaskiya an daɗe, muna masa aiki yana biyan mu, yana bamu kuɗi sosai, a haƙiƙanin gaskiya mune mukayi garkuwa dasu, 'yan sanda sun tambayemu kuma mun faɗa musu gaskiya"
Barrister Khalil yace "Ya me girma