Showing 204001 words to 207000 words out of 209297 words

Chapter 69 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

759

mutane, ba manyan motocim dake harabar gidan, abun duk se  a hankali.

Nan su Murtalah, Nura da sauran ma'aikatan gidan suka dinga tururuwar zuwa gaban Daula, masu kuka nayi masu murna nayi, ai nan da nan labarin bayyanar Daula ya karaɗa gari, da jaridu Widad kam cikin gidan ta wuce, tana ganin gidan ya koma kamar wani kango.

Alhaji Daula yace "ina sauran mutanen gidan?"

Nura yace "ai ranka ya daɗe ai an kama Hajiyar"

Daula yace "nasani"

Nura yace "to yanzu dai, 'yan sanda sunzo sun kama Ramlah jiya, se Amal ce kawai a cikin gidan"

Daddy ya jinjina kai, ya shiga cikin gidan, yana shiga ya tarar Widad ta wuce ɗakinta, Amal tana zaune a falon tana ta kuka kamar an mata mutuwa, ta rame sosai kamar wadda aka zuƙewa jini, tayi baƙi sosai duk ta canza kamanni gwanin ban tausayi.

Maimakon Daddy yaji haushinta sema wani tausayinta daya kama shi, kafin yai magana Widad ta fito, Umma tace "Yusuf wannan kuma wacece?"

Yusuf yace "Umma wannan itace Amal, 'yar matar gidan nan ce"

"Amma ya naganta kamar mara lafiya?"

Yusuf yace "nima ban san abunda ya sameta ba"

Widad ta kalli Amal tace  "Malama You have to leave this house, within some minutes, azzalumai kawai marasa tsoron Allah, masu butulci"

Amal ta shiga girgiza kai tana cigaba da kuka, dan idan ta fita bata san ina zata ba, dan bayan mamansu ta auri Daula, a dangima ba kowa take gani da gashi ba, yanzu idan ta fita ina zata?

Cikin tsawa Widad tace "Am talking to you"

Daddy yace "No Widad, ɗan dakata tukuna"

Ya ƙarasa gaban Amal ya durƙusa, yace  "Amal ɗin Daddy, baki da lafiya ne? Kikayi wannan ramar haka?"

Amal cikin kuka tace  "Dan Allah kuyi haƙuri, kuyafemin, dan Allah, dan Allah kuyi haƙuri"
Tai maganar tana haɗa hannayenta alamar neman afuwa  🙏

"Daddy, waiya kake wani lallaɓatane? Do you want give them another chance to finish us?"

Daddy ya girgiza mata kai, ya sake kallon Amal yace  "yanzu meke damunki kika rame haka?"

Nan ta gaya musu yadda akayi mata fyaɗe, Alhaji Haruna ya keta mata mutunci da abunda likita yace, a maganartata zaka fuskanci ta samu taɓin hankali.

Yusuf kansa seda tausayinta ya kama shi, duk rashin mutuncinsu, Amal ta ɗanfi sauƙin kai, dama Ramlah tafi zaƙewa da wulaƙanci.

Daddy yace "ki kwantar da hankalinki, nasan yanzu dole zaki shiga damuwa sosai, saboda gaba ɗaya 'yan uwanki da iyayenki suna hannu, ina fatan ze zame miki izina akan abunda ya faru, ban miki Alƙawarin saka baki akan taimakon mahaifiyarki da yayarki ba, saboda sun cutar dani a rayuwa, amma daga nan ko zuwa wace ƙasane, daga naira ɗaya zuwa miliyoyi, zan kashe a nema miki lafiya, kidena kuka kiyi musu fatan Allah ya shiryesu, sannan ki dimga musu Addu'a "

Aikuwa a hasale Widad tace " Daddy, why? Me yasa zakayi wannan hukuncin, dukda tarin laifukan da suka aikata mana? "

Yusuf ma cikin tsawa yace " Widad, Daddy kikewa magana fa, talk to him with respect "

" Haba Yoseef, a gabanka akace Mahaifimsu aka saka ya kashe min Ammina, yanzu meze sa Daddy ya temake ta? Bayan yadda suka so ganin bayana, da ganin ma zama mahaukaciya tuburan?"

Daula yace  "Widad, ɗan halak baya manta alkhairi, ko bakomai ɗan uwanta yamin wahala, yayi ɗawainiya dani a Asibiti, yamin biyayya, kuma itama ba laifi tana girmamani, albarkacin Anwar nakeso Amal taci, ba ita tayi miki laifin ba, dan haka kiyi haƙuri, kiyi haƙuri ba danni ba dan Allah "

Daddy ya riga ya ɗaureta da jijiyoyinta, dan haka dole tayi shiru.

Daga gidan suka wuce inda nan ne gidan da Daddy yace nasu Yusuf ne, a unguwar lamiɗo crescent, gida ne hargida ya haɗu ya tsaru iya tsaruwa, kamar ba'a Nigeria ba, Widad nata murna yayinda Yusuf ke jinjina abun, waishine da wannan gidan haka?

Amma Babban abunda Widad bata ji daɗinsa ba, be wuce yadda Daddy yace " wai anyi bookin ɗin jirgi shida Yusuf a ranar zasu tafi lagos da yamma, dan canne inda kamfanin Yusuf yake, zeje a nuna masa abubuwa tun yanzu, Widad taji haushi sosai, dan harga Allah tana kewar mijinta sosai, kusan watanni shida ana neman na bakwai basa tare, amma haryanzu sun kasa samun dama su kasance tare, shikansa Yusuf mazewa yake dan yana da kunya sosai amma yana kewar matarsa sosai, Widad ce dai wani lokacin se a hankali bata fiye jin kunya sosai ba, duna da yanayin rayuwarta.

Amal kuwa a ranar Daula yasa aka ɗauketa aka kaita Asibiti, dan a dubata a ga idan aikin ze yuwu a nan Nigeria.

Haka Widad tana ji tana gani, da yamma su Yusuf suka tafi Lagos, ta koma gidan Umma tai zamanta, kwana ɗaya da tafiyarsu Lagos, Daula yai hira a kafafen watsa labarai a can Lagos, ya sake bayyana kansa, ya bayyana dukiya ta Yusuf ce, da irin wahala da azabtarwar da Bulama yayi masa, ƙarshe yai jan hankali da nasiha me ratsa jiki, akan mutane su lura da suwaye masoyansu na gaskiya.

Umma da Widad basu san anyi hirar ba, se gani sukai mutane na zuwa gidan, wai sunzo yiwa Umma murna,ashe Yusuf ɗan Daula ne, babu kunya ciki hardasu Yaya ɗanllami masu yi masa gori, Sunga Arziki ya sameshi, Widad ta dinga mamaki wato a rayuwa idan kaga ana nan nan da kai, wata damace Allah ya baka, ko kuma kuɗine da kai.

Garin su Hindu kuwa, tuni aka kai kayan aiki dan cika alƙawarin da Daddy ya ɗauka, da yake akwai kuɗi, nan da nan aka fara aiki, kuma yace a ɗau leburori a garin dan su samu wani abu suma, gefe guda sunata shiri suma murna akan Hindu zata Auri Daula, yayin da ita Hindu gaba ɗaya yake mata kwarjini, take tunanin taya zatai zaman aure dashi, mutumin daya girmeta nesa ba kusa ba, yama haifeta? "

Nurat kam ta riga ta haƙura da batun Yusuf, tayi murna sosai jin labarin ashe yana da alƙa da Widad, itama in akabi nasaba ɗan uwantane.

Ta samu Khalil a falo tace masa" brother, kaga wani iko na Allah ko? Duk wannan wahalar ashe dai ɗan uwan Widad ne Yusuf, kuma akan dukiyarsa aketa wannan abun "

Khalil yace " hakane kam, Allah babu yadda be iya ba, Sakamakon haƙuri da juriya ga abunda Allah yayi masa, haƙuri me tadda rabo, kema Allah ya baki miji nagari wanda yake sonki"

Nurat tace  "Aima ya bani"

"A ina yake? Baki gayamin ba"

"Sunanshi Barrister Ibrahim Khalil gora"

Da sauri ya kalleta yace  "Are you serious?"

Ta jinjina masa kai tana murmushi, "yanzu kin yarda kima sona zaki aureni Nur?"

Ta jinjina masa kai alamar eh, murmushi ya shiga yi yana faɗin Alhamdilillah, Alhaji na dawowa zan sanar masa "

" Haba brother, meye na gaggawa kuma? "

" kar inje wani yayi min ba daidai ba, gara in hanzarta inyi wuf dake"

Nurat ta rufe fuskarta tana murmushi.

Wasa wasa, seda Yusuf sukayi Sati biyu sannan suka dawo Kano, kuma da suka dawo ɗinma seda Daula yaje har gidansu Nurat domin yi mata ta'aziyyar mahaifiyarta, abunda bata taɓa zaton Daula zeyi ba, tana ganinsa ta tsaya tana mamaki.

Daula yace  "Nurat, ƙaraso mana"

Ta ƙarasa ta zibe ƙasa tana gaishe shi"

Ua amsa tare da faɗin "ya ƙarin haƙuri kuma?"

"Alhamdilillah Daddy"

"ubangiji Allah ya jiƙan ummanki, yai mata rahama"

Nurat tace "Ameen"

Nanma Yusuf ya sake yi mata gaisuwa, Daula yace  "Nurat, idan akabi nasaba ina da alaƙa ta jini da mahaifinki, dan haka ki ɗaukeni Uba, duk abunda ya taso miki kike buƙatarsa, ki nemeni ko menene insha Allah, zanyi iya ƙoƙarina imga na miki, am your father now, kinji Nurat"

Nurat tace "to Daddy nagode sosai"

Seda Daula ya tsaya suka gaisa da mariƙin nata, sannan suka tafi.

Yallaɓai Suleiman kansa, seda ya samu tagomashin katafaren gida, da kuma kuɗi masu yawa a gurin Yusuf, saboda irin jajircewa da taimakon da yayi masa.

Kwanansu Uku da dawowa suka tare shida Widad a sabon gidansu, ya samu rakiyar abokan aikinsa gidan, Kasancewar bashi da wasu abokan kirki, Widad kamar tayi tsalle dan murna da farinciki.

Bayan kowa ya watse, gajiya duk ta damu Yusuf, saboda hada hada da mutane, dan har walima akayi na tariyar a event center, Daddy ya gayyato manyan abokansa, Yusuf duk ya gaji dan be saba da hada hadar mutane haka ba, ya shiga yai wanka, lokacin tuni Widad ta shiga ɗaya ɗakim tayi nata wankan, dan itama a gajiue take sosai, ta fito cikin riga da wando na bacci masu jikin bargo pink, ta kashe fitilar ɗakin ta bar dump side lamp, ta ƙaraso inda Yusuf ke zaune yana taje sumar kansa, Yusuf yace  "malama ce miki akayi na gama kika kashemin fitila?"

Tace "kai ba mace na amma se ƙaƙale, da mace ne Allah kaɗai yasan me zakayi"

"Shi namiji baze gyara ba kenan, se kincemin ƙazami?"

Widad tace "kuma mayukana zaka dimga shafawa, na bleaching ne dai ba ruwana in ka zama fari"

Yusuf yai dariya yace  "dan dai bleaching ai ba damuwa ranki ya daɗe, ince mata tace takemin"

Sukayi dariya tare, ta ƙaraso ta rumgumeshi ta bayansa, tana numfashi a hankali, kwararar hawayenta yaji a Ƙirjinsa da sauri yace  "lafiya kuwa Widad?"

Kasa magana tayi, ta cigaba da kukan, ya janyota gabansa yana sake tambayarta, amma sema ƙara saugin kukan da tayi, yace  "haba Babyna, mena yi miki kuma? Kodai shagwaɓarce?"

Still bata amsa masa ba, dan haka ya jata zuwa kan katafaren gadon su, ƙato ya zaunar da ita sannan ya zauna yace "gayamin, menene? Ko laifi nayi miki"

Rumgumeshi tayi tana kuka take faɗin "thank you very much Yoseef, thank you very much for your love, caring the sacrifice and all you have done for me, you change my life Yoseef, i love you"

"I love you too my wife, you also done a lot of things for me, bani da bakin godiya se dai zuciyata taki ce mata ta"

Haka suka cigaba da gayawa jinansu kalamai masu daɗi, masu cike da nuna kewar juna, daga nan kuma suka wula wani gurin.
🚶 🚶 🚶 🚶
Ji suke tankar lokacin suka yi aure, dan a wannan lokacin suke cin nasu amarcin a nutse, ba inda Yusuf yake fita, kullum yana gida tare da Widad, yana bata kulawa ta musamman.

Alhaji Ahmad ma ya nemi Auren Umman Yusuf, akasaka lokacin daidai lokacin bikin Daula, ayi biki gaba ɗaya

Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, tun saura sati biyu biki, Widad taje ƙauye ta ɗakko Hindu daga ƙauye zuwa kano domin shirin biki sosai, motar da aka kawo Hindu Tint glass ne da ita, dan haka bata samu damar ƙarewa garin kallo ba, seda suka shiga gidan Widad, data fito daga motar cak ta tsaya tana ƙarewa harabar gidan kawai kallo.

Widad ce ta fito tana murmushi ta ƙaraso tana faɗin "oyoyo amaryar mu, sannu da zuwa Anty Hindu"

Hindu ta sunkuyar da kai cikin jin kunya.

Widad taja Hindu zuwa cikin gidan, yayin da Hindu ta kasa magana saboda tsantsar mamaki, ace a duniya akwai irin wannan gidan lallai jin daɗi yana birni, suna shiga falon Widad taji wani irin sanyi ya ratsata wanda babu shi a waje, tun Hindu na mamaki harta zubawa sarautar Allah ido, dan abun ya shallake hankalinta.

Widad ta dinga koyamata yadda ake amfani da wasu abubuwan, ta dinga kaita gurin gyaran jiki kafin lokacin biki.

Hindu tayi shar da ita, tayi kyau sosai sedai tana jin kunyar Widad sosai, saura kwana huɗu biki sannan Widad ta kira Daddynta a waya tace masa yazo ga amaryarsa a gidan ta.

Ba musu kuwa sega Daddyn a gidan, Hindu na jinjina rashin girman kai na mutumin nan, yana da matukar sauƙin kai da sanyin hali, dukda kuɗin da yake dashi, da kuma shekarunsa.

Yana zaune a falo, Hindu suka fito ita da Widad tayi kyau sosai, Widad tana ja da kyar saboda nauyin cikinta, Widad tace "Daddy ga amaryarka nan, bari in kawo muku abin sha" ta juya ta koma ciki.

Ƙafar Hindu na rawa ta ƙarasa gaban Dula, ta tsuguna tace "ina wuni"

Daddy yace "lafiya ƙalau Hindatu, ya baƙunta? Ina fatan dai Widad bata takuramiki?"

Hindu ta girgiza kai alamar a'a, yace "to in dai tana matsa miki, ki gayamin nida ita ne" yai maganar yana murmushi ƙarshe shikaɗai yai taɗin ya gama bata iya cewa komai, saboda kunya da kwarjinin sa.



Lokacin biki Aka aika da motoci ƙauyen su Hindu, aka kwaso su zuwa birni dan bikin 'yarsu, a tsohon gidansu Widad aka sauke su, sedai Hari tafi kowa rikicewa da ganin gidan nan, tun daga gate motocin dake harabar gidan suka rikita ta, suka shiga katafaren falon gidan, Hari ta rasa a ina zata zauna, tace "ohh ni Hari, yanzu wannan ko' a aljanna ka samu wannan ai ka more"

Hansai tace "ke Hari, ance talaka a gidan aljanna shine gidansa kamar girman duniya, kike cewa ki samu kamar wannan"

"Ke bari Hansai, ke kina tunanin kin aikata abin da da zaki samu wannan ne? Ai ni indai irin wannan ne yaseen ya isheni, kai jama'a kun lura da wani abun mamaki kuwa? Waje lafiya ƙalau amma ɗakin nan hunturu Aradu, sanyi ake sosai a cikin ɗaki ikon Allah"

Widad tasa aka dinga sauke musu Abinci, Abinci kala kala Gwaggo tace "Amarya wai ina 'yar tawa ne?"

Widad tace "wace' yar bayan nikuma?"

Gwaggo tai murmushi, Widad tace "zasu taho tare da Daddy, da kuma Umma"

Gida ya ɗau harama, aka kawo Hindu, suka dinga zuba guɗa, gaba ɗaya Hindu ta canza a sati biyun nan, tayi kyau sosai kamar ba ita ba.

Aka dinga ɗorawa ana sauke musu Abinci, aka ɗakko masu aiki da an ɓata guri su gyara, Da Yamma aka ɗauki Hindu aka tafi reception, na Daddy da abokansa da kuma Ahmad, dama umma cewa tayi ba zata ba.

Hanne kam ji take kamar tayi kuka, tafi Hindu kyau da haske amma zata auri wannan haɗaɗɗen mutum a birni, amma ita zata auri ɗan ƙauye, tunda suka zo Widad ko kallon inda Hanne take ba tayi balle tayi mata magana.

Washegari juma'a, aka ɗaura Auren Umma, da kuma na Hindu da Daula, anyi shagali sosai a gidan nan, dukda ba wani gagarumin taro suka yi ba, amma anci an sha sosai kowa yasan anyi biki, akaita yiwa Hindu Nasiha, akam haƙuri da tsoron Allah, Widad tace Gwaggo, da Hari suzo a raka Hindu gidan ta "

Hari tace" au wai dama nan ba'a gidanta muke ba? "

" Gidan Amaryar za'a sauke ku? Sannu Hajiya Hari me taɓargaza"

Haka suka cigaba da faɗansu da suka saba ita da Hari, Farm House aka sake gyarawa, aka canza furnitures wanda ya tattaka gidan da aka sauki su Hari, Hari se salati take da salallami  wai "Nidai Hindu, idan ana neman 'yar wanke wanke dan Allah zanyi"

Widad tace "Kina uwatta zaki zo wanke2"?

"eh wallahi zanyi"

Tun Widad na biyewa ƙauyancin Hari harta ƙyaleta, saboda abun nata bana ƙare bane.

Bayan sun rakata, sun mata addu'a Gwaggo tace "to Hindu, mu daga nan gobe in Allah ya kaimu zamu wuce gida, ki zauna lafiya da mijinki da kowa ma, nasan dai baki da matsala amma dai ayi haƙuri"

Hindu ta rirriƙe Gwaggo tana kuka, da ƙyar ta cikata suka tafi, suna tafiya tsoro ya cika Hindu, saboda ita girman gidan ma abun tsorone, gashi tana jiyo kukan dabbobi kaɗan kaɗan  a falon, tana cikin zare idone sega Daula ya shigo da abokansa.

Ta cukuikuye a cikin lifaya taƙi ɗago kanta balle ta kalli wanima, nan suka musu fatan Alkhairi sannan suka tafi.





Ayshercool
07063065680
12/22/21, 11:07 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

170

Bayan fitarsu Daula ya kalleta yace "taso mu tafi"

Ta ɗago a hankali ta kalleshi, sannan ta miƙe tana waige waige, ya miƙe yai gaba tana binsa a baya, wani gurin seta tsaya kallo, seta ɗago taga ya tsaya jiranta setai maza ta taho, ya dinga ratsawa da ita faluka, wai nan duk dan zaman mutum ɗaya akayi shi, suka zo ƙafar bene ya fara hawa tana binsa, sedai ta zame ta faɗi, saboda matattakalr benen kanta wata iri take ganinta, ga ƙananan fitilu a jiki, gata kamar ta glass ta tsaya kallo shine ta faɗi, a ɗan gigice ya waigo yna faɗin "subhanallah, garin yaya? Kodai ɗaukarki zanyi ne?"

Da sauri ta girgiza kai yace "sannu, miƙomin hannunki in riƙeki"

Ta miƙa masa hannu, ya riƙe hannunsa kamar bana namiji ba saboda laushi.

Haka suka ƙarasa saman bene, cikin katafaren falonsa, ji tayi sanyin data keji ya ƙaru, hartana nema ta fara rawar sanyi, yaje ya rage AC suka shiga bedroom, ai a jikin ƙofa ta tsaya tana kallon ikon Allah, lallai gaskiyar Saleh, da yace ko za'a saida duk kadarar da 'yan ƙauyensu suka mallaka baza su siyi ko da motar hawan Widad ba, balle wannan uban gidaje haka.

Ya bata gurin zama, ta zauna already kaji da kayan shaye2 suna ɗakin da plate da komai, amma juyin duniya Hindu taƙi ci, ba yadda beyi da ita ba, amma taƙi ci, se ƙyaleta yayi, sukayi alwala sukayi salla, bisa ga koyi ga sunnar ma'aiki salallahu alaihi wassalam, tare da yin addu'oi, ya miƙe yace mata ga gado cam taje ta kwanta, shi kansa gadon abun kallo ne, lallai Su Widad sun tara abun duniya.

Shima da ƙyar ta hau ta kwanta, ta dunƙule a guri ɗaya, ya ɗakko ƙaton bargo ya lulluɓa mata, ya cire babbar rigarsa taga ya sake tada salla, sannan hankalinta ya kwanta ta shiga baccin ta.

Wani irin laushine da katifar, ga bargon ma laushi se ƙamshine ke tashi a jikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login