Showing 6001 words to 9000 words out of 209297 words

Chapter 3 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

705

zata kalla ta dinga zagina? Tunda kana mata dariya dole ta Kalleni ta dinga cewa ban iya kula da miji ba se ita, ai seka Aure ta tazo ta kula da kai, wallahi ta kuma yimin abunda bemin ba, sena ɗau mataki mafi muni a kanta, zan nuna mata wacece Widad "

From no where Yusuf yaji wani farinciki yana ratsa shi, Widad ta fara kishinsa kenan? Murmushi yayi yace

" Ohh yasalam, shikenan tabbas nayi laifi, dukda badan ina mata murmushi ba, da tabbas ba zata rainamin 'ya ƙwalisar mata ta ba, amma ayi haƙuri zan kiyaye insha Allah, na dena mata dariya amma ayi min afuwa".

"Karma ka dena kai tayi mata, wallahi na dena ƙyaleta"

"Ayi haƙuri dai, kar ayi aika aika, ki dena kuka share hawayen ki maza, mijinki baze sake kallonta yayi mata dariya ba"

Shiru tayi masa ta cigaba da ajiyar zuciya. Yusuf a ransa yace  'insha Allah ko baki son meye so ba zaki sanshi a kaina, kuma ina fatan ki furta da bakinki kina son Yusuf, muje zuwa dai'

Shikam Saleh a tsakar gida ya cigaba da zazzaga musu masifa, akan abubuwan da Hanne ke yiwa Widad, sun sha mamaki jin yace ko za'a tattara kaf ƙauyen da kadarorin da mutanen ƙauyen suka mallaka ba zasu sai gidan mahaifin Widad ɗaya wanda take rayuwa a ciki ba.

Hari ta zaro ido tace  "Wudas ɗin?"

"ke dalla ware ai kece Wudas ɗin, meye wani Wudas"

Hindu ta yadda da maganar Saleh, saboda sam Widad ba tayi kalar wahala ba.

Ita kuwa Hanne jinsa kawai take badan ta yadda ba, shaƙar da Widad tayi mata tafi komai bata mamaki da ɗaga mata hankali.


Ramlah ce ta shiga falo, ta tarar da Amal a kwance tana kallo, amma hankalin ta sam baya kan tv tunani kawai takeyi, a ɗan gigice tace "Amal wai kinji Anwar kotu za'a kaisu next week"

Da sauri Amal ta tashi zaune tace  "kamar yaya kotu?"

"Yanzu Mummy ta dawo take gayamin"

"Dama ana kai mutum kotu, koda ba'a  tabattar da laifin da ake tuhumarsa ba?"

Ramah tace "ya za'ayi in sani? Nifa hankalina ya tashi, ashe abun nayi ne"

Amal tace  "mun shiga uku Ramla, da ƙyar in aka shiga kotu kiga ba'a kai shi prison ba, yanzu meye abunyi?"

"wallahi nima ban sani ba, gaba ɗaya kaina ya gama kullewa, Ga Mummy ta damu sosai, ko Abinci ma ba ta ci fa"

"Subhanallah, Allah sarki Yaya Anwar, yanzu fa da sunje koti se ace se prison"

Ramlah tace "wallahi nima abunda nake tunani kenan Amal, Allah sarki bawan Allah"

Nan suka yi ta jimantawa juna.

Har dare Widad taƙi walwala, ko kula Yusuf ta ƙiyi, yau ko harar da suke a tsakar gida dasu Hansai bata zauna ba, ta gyara shimfiɗar ta zata kwanta, Yusuf yaje kusa da ita yace

"My Queen dan Allah kidena fushi dani, nasan yau gaba ɗaya ranki a ɓace yake, na farko na sake gangancin sumbatarki, ga kuma wancan laifin shima da kika ce nayi, dan Allah kiyi haƙuri bazan iya jure ganinki cikin ɓacin rai ba"

Cunkusa baki tayi, ta cigaba da ƙoƙarin kwanciya.

"Amma inaga dole mu koma kan shawarata ta farko, na yakamata mu raba ɗaki, kinga ni ba waliyyi bane mutum ne kamar kowa, idan muna tare a guri ɗaya akwai matsala, ina gudun wani abu yazo ya faru, kinga na fara gazawa gurin riƙe Alƙawarin yarjejeniyar dake tsakaninmu"

"wallahi bazan kwana a ɗakin nan nikaɗai ba, duk inda zaka je sena bika"

"to idan na kuma kissing ɗinki kika haɗemin rai se nayi abunda yafi haka, kina bani ciwon kai Widad, komai nayi laifi ne a gurinki, ki dinga sassauta min mana, a dinga jin tausayina"

Kwanciya tayi ta juya masa baya, shima kuwa ya kwanta a bayanta, banza tayi masa taƙi magana, ta lumshe ido da nufin tayi bacci, a kunnenta ya dinga raɗa mata  

"I love you My Queen, ina sonki Widad, and I mean it from the bottom of my heart, i love you"

Cike da ƙosawa Widad tace "Naji amma dan Allah ka ƙyaleni inyi bacci"

"to ba kice komai ba, kin haƙura kin dena fushin?"

"eh na haƙura jeka"

"kora ta fa kike Queen"

"Niba korarka nayi ba, bacci nake ji"

Yusuf yace "shikenan, Asuba tagari masoyiyya"

"kaika santa"

Yai murmushi ya koma kan shimfiɗarsa.


Ana ta shirye shirye za'a kai su Anwar kotu domin fara sauraren ƙararsu, akan tuhumarsu da'ake da haɗa baki gurin sace Daula, Anwar ya duƙufa sosai da Addu'oi babu dare babu rana.

Yana zaune da safe wani ɗan sanda yazo ya buɗeshi, aka tasa ƙeyarsa zuwa wani guri, wannan mutumin dai daya zo ya kuma gani, aka bawa Anwar kayansa da aka karɓa.

Mutumin ya miƙawa Anwar hannu suka gaisa yace "masha Allah, you are free now malam Anwar, muje in ajiyeka a gida"

Cikin mamaki Anwar ya kalle shi yace "i am free as how? An game bani da laifi kenan?"

"eh baka da laifi, muje"

Kamar soko haka Anwar yabi mutumin, kuma ya kasa tambayar sa waye shi, ya kai shi restaurant yaci Abinci sannan ya wuce ya kai shi har ƙofar gida.

Mutumin ya kalli Anwar yace "Anwar ina maka fatan Alkhairi, ina maka murnar fitowa da kayi da kuma tsallake tarkon azzalumai, seka kula Allah ya kiyaye gaba"

Anwar yace "sedai ni tunda kake zuwa gurina ban gane ka ba"

Mutumin yace "nasan baka sanni ba, kuma bazaka ganeni ba, sedai nima aikoni akayi ba'a bani umarnin sanar da kai wayeni ba, babu buƙatar hakan Daula yana tare da ubangida na, shiyasa aka ɗauke shi a Asibiti, yana gurinsa dan haka ka kwantar da hankalinka"

A firgice Anwar yace "dan Allah waye uban gidan naka? Daula bashi da lafiya, yana buƙatar kulawar likita"

"ɗan samari kai dai ba Ruwanka, koma a wani hali yake ciki tunda dai kai ka fita, maza jeka zan tafi"

Jiki a sanyaye Anwar ya sauka, yana bin motar da kallo kamar wani soko, har motar ta bara layin.

Gate ɗin gjdansu ya nufa, ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin, Isa ne yazo ua buɗe ƙaramar ƙofar, yana ganin Anwar ya shiga mutstsuka ido ko gizo yake masa, Isa yace

"Kamar Yallaɓai Anwar nake gani"

Anwar yace  "eh nine Malam Isa"

Buɗe masa ƙofar yayi ya shigo, Isa yace "Yallaɓai an sakoka kenan?"

Anwar yace  "Alhamdilillah Isa an sakoni" nan ma'aikatan suka dinga murna suna taya shi farinciki.

Cikin gidan ya ƙarasa, yana shiga ya tarar babu kowa a falo, ɗakin mahaifiyarsa ya nufa, yasa hannu ya murɗa ƙofar ɗakin yayi Sallama, da sauri ta waigo dan mamar Muryar Anwar taji, aikuwa ba kama bane shi ɗinne, ai da hanzari ta miƙe, ta nufe shi da sauri 

"Anwar kaine? Garin yaya, ya akayi aka sake ka?"

Rungume ta yayi yace "Mummy ki bari in huta se in gaya miki, duk kin rame Mummy na"
Kuka ta saka tace "ba dole ba Anwar, baka nan na rasa me kemin daɗi, nasan zaman gurin nan sam ba daɗi yake maka ba, nayi zarya harna gaji anƙi a sakeka, ko Abinci bana iya ci, bana baccin kirki"

"shikenan, is over now, ai gani na dawo Alhamdilillah"

Suna nan zaune sega su Amal, dan ta manta ma bata sanar dasu dawowar Anwar ba, nan suka dinga murna suna farinciki da dawowar Anwar, aka shiga yi masa girki, yai wanka ya huta dan ko ina na jikinsa tsami yake masa saboda wahala.

Mummy tace "nikam ka gayamin, ya aka yi aka sako kame?"

Anwar yace  "wallahi Mummy ikon Allah kawai, ina zaune akace in fito, wani mutum ya ɗakkoni a motarsa yace bani da laifin komai, ya kawoni har gida ya tafi"

Ɗan yatsine fuska tayi tace "meye haka sekace wata almara?"

"Wallahi Mummy dagaske nake miki, kiyi waya ki tambaya kiji"

"ikon Allah ko wane mutumi ne wannan oho? Ta be gaya maka waye shi ba?"

"nayi nayi ya gayamin, amma yaƙi sam, be gayamin ko waye shi ba"

Amal tace "Mummy koma dai waye, tunda Allah yasa an sako mana shi ai shikenan, mu dama fatanmu ka dawo gida"

Mummy tace  "Amma da mamaki, ina mamakin waye haka? Dan na san ba'a cikin waɗan cam tsinannun bane marasa imani"

Anwar yace "Mummy suwaye kenan kkke zagi haka?"

Da sauri ta wayence tace  "A'a karka damu, 'yan sanda nake nufi, ba irin zaryar da banyi ba amma suka ƙi bani belinka"

"Allah sarki, ai Abincin su suke karewa suma Mummy, bekamata ki tsine musu ba"

Mummy tace "hakane kam, na dena tsinemusu tunda nidai ɗana ya fito"

Yau Widad har takwas na safe bata tashi ba, tunda tayi sallar Asuba, Yusuf yaje kan shimfiɗarta ya riƙe hannunta a nasa yana ɗan matsawa yace  "My heart, ki tashi baccin ya isa haka, ki tashi kici Abinci"

Motsawa tayi a hankali tayi juyi tace "kaci Abincinka, ni bacci nake ji"

"A'a ni gaskiya bazan iya cin Abincin babu ke ba, ki tashi please"

Shiru tayi ta sake lumshe ido, "zanyi miki abunda bakya so yanzun nan fa"

Murmushi tayi tace "banyi brush ba dai" ta ƙarasa tana dariya, Yusuf yace "aini bana ƙyamar ki, kece kike ƙyamata komai naki ni so nake"

Widad tace "naji, ɗakkomin brush ɗin inje in wanke baki"

Ya duba inda take ajiyewa, ya ɗakko ya bata, tana zaune akan katifar bata tashi ba, Yusuf yace "ya dai? Ko sena ɗauke kine?"

Jinjina masa kai tayi alamar eh, aikuwa ya ƙaraso ya ɗauketa cak, dariya take tace "ajiyeni tun kan Baba Hari tamin ba'a ko ace na aikata wani babbam zunubi a koreni daga garin nan"

A tare suka kwashe da dariya, Yusuf yana kallonta cike da farinciki.

Tayi waje, taje tai brush ta dawo suka fara cin ɗumamen tuwo.

Yusuf kallonta yake, da alama tana cikin nishaɗi, yanzu ne lokacin da ya dace ya gaya mata abunda yake son gaya mata, yai shiru yana saƙe saƙen yadda ze ɓullo da zancen yaji tace

"Me kake son gayamin ne da yake razanaka har yanzu ka kasa gayamin? Ka gayamin kawai ina saurarenka"




Littafin kuɗi, dan Allah a biya kafin a karanta badanniba dan girman Allah
A tuntuɓeni ta wannan lambar
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: 50_51

NA KUƊI NE, BOOK 1 NE FREE, DAN ALLAH A BIYA KAFIN A KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH 🙏🙏🙏









gaba ɗaya Yusuf ya ɗan ruɗe yace "ba wani abu da nake son gayamiki ba fa, kece kike ganin kamar ina son in faɗi wani abu ne"

Murmushi tayi tace "Hmm Yoseef kenan, a ɗan zaman da nayi da kai daga lokacin da ka fara min aiki, na fuskanci halayenka da yawa, koba haka ba ina iya karantar abunda ke ran mutum ta hanyar fuskarsa, bana son ƙarya, karka ji wani abu, babu abunda zan maka, se abunda Allah yayi nufin ya faru da kai"

Yusuf yace "dama ina son in gaya miki yau nake son na cigaba da fitane, ina son in sai mana wasu abubuwan na buƙatunmu, wasu abubuwan duk sun ƙare"

Widad tace "Yaushe ka warke da har zaka fara zancen fita? Se kaje ka kuma haɗuwa da wata rashin lafiyar ko? toni babu ruwana, tunda dai ban takura maka nace seka saimin abunda baka dashi ba, ka ƙyaleni komai aka bani zanci, in wanda zan iya cine se inci, in bazan iya ciba kuma se in haƙura kawai"

Sosai ta bawa Yusuf tausayi jin abunda ta faɗa, Yusuf yace " duk da haka Yakamata ace nima ina taɓuka wani abun da kaina, in sauke haƙƙinki da yake kaina, in sai miki abubuwan da kike buƙata koba duka ba"

"Shikenan, amma nidai bance kayi abunda zaka cutu ba koka wahala ba, ka kula da lafiyarka"

Yusuf ya gama shirinsa tsaf ze fita, Saleh ya shigo gidan ya kalli Yusuf yace "Ahh Yusuf ina zuwa haka? '

" zani cin kasuwane Saleh " Yusuf ya bashi amsa

Saleh yace " Haba Yusuf, kasan fa baka da lafiya sosai "

Yusuf yace " shima zaman guri ɗayan babu daɗi Saleh "

Harice take a tsugune tana ta tattara ƙwan da kazarta tayi zata bayar akai kasuwa, Yusuf yace " Baba Hari, wannan ƙwan na siyarwa ne?"

Hari tace " Eh za'a akaimin kasuwane"

Yusuf yace "Masha Allah, inba damuwa a zuba na kaji biyar na zabi biyar, a kaiwa Queen idan na dawo insha Allah zan bada kuɗin"


Hari tace "meye kuma Kun?"

Yusuf yayi murmushi yace "A kaiwa Widad nake nufi"

"Awo sekace min Wudas, amma kun ai bazan gane ba idan kace haka"

Saleh yace "Hari baki abun magana, Queen yace ba kun ba, yana nufin sarauniya"

Kwaɓe baki tayi tace "Wace sarauniyar? Sarauniyar fitsararru ba"

Yusuf yace "Ayi haƙuri"

Hari tace "dan dai kaine, kuma ina jin kunyar ka, amma da ita zata siya bazan sayar mata da ƙwan nan ba"

Yusuf yayi dariya yace "ayi haƙuri, A temaka mana"

Saleh yace  "kedai kinji kunya, ki rasa da wadda zaki dinga faɗa se wannan Yarinyar"

Widad ta ƙaraso inda suke da kwanukan wanke wankenta a hannu tace
"Idanma baki siyar dan Allah ba, zan buɗe gurin ƙwan ne in kwashi san raina, ko in kama kajin naki in yanka in soye muci nida Yusuf tunda bashi da lafiya dama"

Dariya suka yi, Saleh ya dinga mamaki, dama Widad ta iya magana haka hadda tsokana?

Hari tace tunda Yusuf ne ze sai ƙwan, ya biya kuɗin biyar, ta bashi biyar kyauta, amma bata yarda ya bawa Widad wanda ta bashi ba.

Widad tace "Hari dama kina ɗan dafa ƙwan nan kici, dase kinfi haka ƙiba da kyau, ke kullum cikin neman kuɗi kamar zakiyi ƙwace, kuma na rasa inda kike kai kuɗin"

Hararta Hari tayi taƙi ta kulata, aka ɗakko kwano za'a sakwa Widad ƙwai, Widad tace

"kuma idan kika samun ƙanana bana so, manya za'a bani dan nima ƙatuwa ce"

Haka Widad tasaka Hari a gaba, tana ta zolayarta ita kuwa Hari tunda Widad ta shaƙe Hanne take ɗan shakkarta.

Yusuf yace "Queen zan tafi"

Widad tace "ba zaka soyamin ƙwan ba zaka tafi?" tai maganar kamar wata ƙaramar yarinya tana sa hannu a gashin kanta.

Gwaggo ta sunkuyar da kai tana jin taɓara, Yusuf yace "ki bari in dawo"

Maimakon tayi magana se ta cuna baki tana kallonsa,

Yusuf yace "Shikenan Muje in soyamiki, amma nasan ba iya ci zaki yi yanzu ba, dan yanzu kika gama cin Abinci"

Gwaggo tace "Yusufa jeka abunka, za'a soya a bata kaji"

Widad ta cunkusa baki tace "Ni gaskiya Mama nasa nake so, naga kin fi son Yoseef dani, ni kowa baya sona"

Gwaggo tace "nina isa ince bana sonki, waceni niko nake sonkj, amma ina nema masa Alfarma, a ɗaga masa ƙafa tunda fita zeyi"

Widad tace "shikenan Allah ya temake ka, jeka seka dawo" tai maganar tare da kashe masa ido ɗaya.

Hari tace  "A'uzubullahi wannan Yarinyar idan ka zauna a inda take seta karya maka alwala"

Dariya Yusuf yayi sukayi waje shida Saleh, Saleh yace "Salute to you Yusuf, babu wanda ya isa ya biyaka namijin ƙoƙarin nan da kake, kalli yarinyar da take rayuwa kamar wata halitta daban, me gudun jama'a da son rayuwar kaɗaici, amma ita ta sake a ƙauye haka take rayuwarta, cikin farin ciki fjye da wanda take a gidansu da yake da tarin arziki "

" Saleh, ai dama kuɗi dukiya ba sune kwanciyar hankali ba, farinciki zama cikin wanda suka damu da kai shine farinciki, mutanen wannan zamanin muke ganin in kana da kuɗi kana da komai, ka wuce baƙin ciki "

Saleh yace" tabbas hakane maganarka Yusuf, da fa tsakaninta da mutane kallon banza da hantara, amma yanzu kalli yadda ta sake da Gwaggo ta maida ta kamar wata kakarta"

Yusuf yace "sosai makuwa, akwai shaƙuwa a tsakaninsu, Gwaggo nada sauƙin kai, kuma tana janta a jiki, bata hantararta idan tayi mata wauta ko wani abu, shiyasa itama take sonta"

Saleh yace  "hakane, amma ya batun ciwon ta kuwa? Na taɓin hankali?"

Yusuf yace "ina doubting akan wannan ciwon da take dashi, ina da question mark akai, amma lokaci nake jira"






"Alhaji Musa, kaji wata maganar banza wai an saki Yaron nan Anwar"?

Alhaji Musa yace "haka nima labari ya isheni, ni kaina abun ya ɗauremjn kai Munir, wane mara mutuncin ne haka, waye yayi wannan karambanin?"

Alhajj Munir yace "munyi waya da Bukar, yace ze bincika nima nasa a bincikamin amma har yanzu babu wani labari, an rasa waye yasa a sake shi, wai daga sama aka bada umarni"

Alhaji Musa yace "waye a saman ya bada umarni damu bamu sani ba? Ta yaya ana tuhumarsa da wannan babban laifin za'a sake shi, idan kuwa hakane to tabbas muna da abokan Adawa wanda suke mana zagon ƙasa akan lamarin nan"

Alhaji Haruna da tun ɗazu bece uffan ba ya nisa yace "ni kaina gaba ɗaya ya kulle, na rasa abunyi semun toshe nan se can ya buɗe, na rasa wane banzan ne yayi wannan aikin"

Alhaji Musa yace "tabbas akwai lauje cikin naɗi, yanzu abunda ze faru shine, zamu saurari Bukar muji me zece, lallai a binciki wanda yayi wannaan aika aikar, sannan a tabattar an kama yaron nan an maida shi"

"haka ma za'ayi, wannan shine abunda ya dace, akama shi harse an ga Daula"


Anwar yana zaune yana cin Abinci yace "Mumsy kin san wani abu kuwa?"

"A'a seka faɗa" ta bashi amsa

"wato bawa baya taɓa gane Allah subhanahu wata'ala yayi masa ni'ima, se yayinda wannan ni'imar ta gushe, kinga ko 'yancin kayi yawonka ɗin nan inda kaga dama, ba ƙaramar ni' ima bace, zama guri ɗaya bala'ine Mum, ga rashin gurin kwanciya me kyau, ba Abinci me kyau, wai danma nine fa wasu haka suke tagayyara a cikin gurin nan "

Hajiya Halima tace " Aini duk zance ya ƙare, tunda Allah ya fito min da kak, Se fatan Allah ya kiyaye gaba"

Anwar yace  "Ameen Mummy, ni yanzu fatana ubangiji Allah ya bayyana Daddy, yasa yana hannu nagari, dan na tsorata da abubuwan da suke faruwa"

Mummy tace "kai kam wannan dashi ya haife ka da an shiga uku, kai har yanzu baka shiga hankalinka ba, ba kaga masifar daka shiga saboda temako ba, still kai tunaninsa ka keyi"
. "Mummy ba zan taɓa iya dena tunaninsa ba, saboda gudunmuwarsa a rayuwar mu"

Wayar Anwar ce ta shiga ringing, ya ajiye spoon ɗin da yake cin Abincin ya ɗaga wayar yasa a kunnensa.

Lambar Bulama ce, bayan sun gaisa Bulama yace "Anwar ashe ka fito?"

Cike da ladabi Anwar yace "eh Daddy na fito"

"to Alhamdilillah, Allah ya kiyaye gaba inba damuwa ina son ganinka anan gida, zamuyi magana"

"to shikenan, Insha Allah idan nayi sallar la'asar zanzo"

Bulama yace "to babu laifi"

Anwar Ya ajiye wayar, Hajiya Halima tace "waye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login