Showing 75001 words to 78000 words out of 209297 words

Chapter 26 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

731

dinga jin ina ma tatace, ace wannan 'yarta ce, a ranta tace "da ina zan sa kaina dan daɗi'

" Yoseef so nake in ɗaga ta "

" ki ɗaga ta ki kaita ina? "

" Sonake ta buɗe ido in ganta, se kuma in mata wasa"

Yusuf yace "ikon Allah, ina wannan yarinyar tasan wani wasa? Jaririya cefa dan Allah ki ƙyaleta tayi baccinta, idan kika tasheta kuma kuka za taitayi, mamanta ta karɓeta daga hannunki"

Widad tace "to bazan tashe ta ba, amma sonake ta buɗe idonta"

"zata buɗe ne, amma ki ƙyaleta mana tayi baccinta"

"to na ƙyaleta"

Widad ta cigaba da kallonta, tana ta sake ayyana ina ma ace wannan 'yarta ce.

Yusuf yana canza kaya, yana yi yana kallon Widad, dan karya ɗauke ido Widad tayi wani abu daze cutar da jaririyar, Widad ta nutsu sosai danko ƙwaƙwƙwaran motsin kirki ba tayi, ta riƙe jaririyar sosai.

Widad tace ' Yoseef ka samin ita a bayana, irin yadda akeyi ɗin nan"

Yusuf yace "yau naga ta kaina ni Yusuf, Allah ya haɗani da rigimammiyar mace, keda kike koyon ɗaukar jaririyar ma yanzu, shine zaki wani ce a goya miki ita? Zan ƙwaceta in kaiwa mamanta, ki cigaba damin rikici"

Zumɓura masa baki tayi, tana sake gyara zamanta, ya ɗakko Abincinsa ya zauna ya fara ci, Amma Widad ta hau kici kicin ɗaga jaririyar nan wai zata saka a kafaɗarta, Yusuf ya miƙe da sauri yaje ya karɓe yarinyar nan, danma jaririyar me haƙuri ce, ba tayi kuka ba se buɗe ido da tayi tana miƙa.

Yusuf ya fito tsakar gida yace  "Mama ungo Jaririyar nan, bawa mamanta ita  tun kan Widad tayi aika aika"

Widad kamar zata yi kuka ta biyoshi da sauri tace "Mama dan Allah ki bani, kawaifa dan nace ina son inga ta buɗe ido, shine se cewa yake ban iya ɗauka ba"

Yusuf yace "karki bata, wai sena goya mata ita, ko ɗaukar jaririyar bata iya ba ta ina za'ayi goyo?"

Jamila dai banda dariya ba abunda take yi, Widad tayi kicin kicin ita a dole anyi mata laifi.

Megari dake ɗakin Hansai yana jinsu ya fito yana cewa "haba Malam Yusufa, yama za'ayi kace bata iya ɗaukar jariri ba, Rabu dashi yarinyar kirki Allah ya baki naki kema"

Widad tace  "Ameen"

Hari tace "jimin mara kunya, kikace Ameen a gaban mutane, kai Wudas baki da kunya Al'qur'an"

"baza'aji kunyar ba ɗin, meye abun kunya kuma dan nace Ameen"

Jamila taji daɗin yadda dukda Widad bata kula ta amma ta nuna tana son 'yarta.

Bayan sun koma ɗaki Yusuf ya kalleta yace "Sannu uwar rikici"

Murguɗa masa baki tayi, ta tafi kan katifarta tai zamanta.

Yusuf kamar yayi dariya, haka ya dinga dariyarsa ƙasa ƙasa yana cin Abincinsa, har akayi sallar magariba bata kula Yusuf.

Ta fito tsakar gida zata yi alwala, taga Gwaggo tana aikinta  a tsakar gida, Widad tace  "Mama wai nan garin ba'a samun Irish potato ne?"

Gwaggo tace "meke nan?"

Tace  "dankali"

Gwaggo tace  "Auho, ai da kiyiwa Yusuf magana, ko kuma Ila idan sunje kasuwa su samo miki"

Widad tace "bafa wannan ba Mama, dankalin nan 'yan ƙanana, ba masu zaƙin ba su nake sha' awa fa"

Gwaggo tace "au dankalin turawa zakice min"

Widad tace "eh shi nake nufi"

Gwaggo tace  "taɓ aikuwa yana ɗan wahala, dan se anje can birni ake samu"

Widad tace  "shi nake sonci fa"

Gwaggo tace  "Amarya ko an gamu ne?"

Widad tace "aka gamu dame?"

"Ahh nasani ko addu'ar Baffa ta karɓu an samu rabo"

Widad tace "wai kina nufin ina da ciki?"

Gwaggo kawai tayi murmushi, ana ɗan sayewa kar a faɗa kai tsaye amma ita ta faɗa, Gwaggo ta ƙyaleta ta cigaba da aikinta, Widad taje tayi sallarta, ta zauna akan dadduma tayi shiru, kawai taji har cikin ranta tana son ta samu ciki, ace yau gata ɗauke da ɗanta na kanta a jikin ta, idan ta haihu ta samu ɗa da zata dinga gani tana jin daɗi.

Tana zaune tana ta karanta wasiƙar jaki, Yusuf yayi sallama tana jinsa tai masa banza, ta miƙe ta fara shirin kwanciya.

Seda ya bari ta kwanta sannan ya tafi rarrashi, tana jinsa ya hawo katifar yana lalubenta amma ta shareshi.

"Kina jina amma kika shareni ko Queen, laifin me nayi miki ne?"

"ni ƙyaleni bacci zanyi"

"Naƙi in ƙyalekin, ni kike sharewa ko?bafa na son haka"

Cikin Shagwaɓa tace "to ba kaine komai nayi kake cewa ban iya ba"

"To kin iya ɗinne? Matar ƙauye kawai sarkin rigima"

"Kai kuma mijin ƙauye ba"

"Eh naji na yadda, ni mijin ƙauyene kuma mijin matar ƙauye, karki damu zan siyo miki teddy ki dinga wasa dashi, shima kamar baby ne seki koyi goyon a jiki"

"bawani nan teddy daban, teddy mutum ne? Toni mutum nake so"

Yusuf yace "Eh tunda baki da mutum, seki rainon teddy da haka zaki koyi rainon jaririn gaske"

"Bana son teddyn, ni mutum nake so"

Sosai Widad ke bawa Yusuf dariya wasu lokutan, Yace  "idan mutum yana yaro idan yayi wasa da dolls 'yar tsana, yana iya raino koba jariri a gidansu, amma ke baki iya ba '

Widad tace" waye ya gaya maka da ina yarinya ina wani wasa ni? Nifa kamar boss nake da ina yarinya, ba ruwana da wani wasa irin na yara"

Yusuf yayi murmushi yace " Yanzun ma ai boss ɗince"

Kawai tayi murmushi tace "nice boss ko, zan ramane"

A haka suna taɓa hirarsu har bacci yayi awon gaba dasu gaba ɗaya.


Da gari ya waye, Widad tana fitowa taga Hindu na tattare tsakar gida tana shara, Widad tace "Hindu kin warke ne kike aiki?"

Hindu tace "jikina da sauƙi Amarya, gani nayi tsakar gidan yayi wani iri, duk ganyen bishiya ya faɗo, shiyasa nace bari in gyara kafin a firfito"

"Kai Hindu, kina fama da kanki ki bari a share mana gaskiya bari"

Widad ta ƙwace tsintsiyar ta hana Hindu sharar, ta gama abunda zata yi ita ta share, sannan ɗakinta koma ɗakinta tayi kwanciyarta.

Wajejen takwas da rabi Widad ta farka, ta hangi Yusuf a zaune da gashi se gajeren wando yana buɗe kwanon Abinci, da alama har yayi wanka ma, dan jikinsa se ƙyallin mai yake.

Ƙura masa ido tayi tana kallonsa, sam Yusuf bashi da makusa gashi da ƙira me kyau, gashi shikansa me kyau ne, ga kuma uwa uba zuciya me kyau.

Tasowa tayi tazo inda yake ta zauna, ta kwanta a jikinsa hannunta kuma tana shafa gadon bayansa.

Yace "Kin tashi kenan? Fatan kin tashi lafiya?"

Maimakon tayi magana sema wani sake lafewa da tayi a jikinsa, tana sake shafa bayansa.

Yusuf yayi murmushi ya cigaba da abunda yake, can yace "in kin gama shafanin seki ɗagani zanci Abinci, tunda naga kamar ke bakya jin yunwa"

Yanzunma shirun ta kuma yi, ta cigaba da abunda take, janyota yayi gaba ɗaya ya ɗorata akan cinyarsa, yana ƙaremata kallo yace "ƙalau kuwa? Ko yau da son jiki kika farkane?"

Murmushi tayi masa, ta kwanta sosai a jikin nasa, tana ƙare masa kallo tun daga fuskarsa har ƙirjinsa, ta kai hannu tana wasa da gashin nasa.

Buge hannunta yayi yace   "mara kunya nan kika gama cewa abun ƙyamane, amma indai kika gani sekin taɓa"

Murguɗa baki tayi tace "ai idan baka yi wasa ba, da fork zan maka shaving, duk in cire shi"

Yai dariya yace "Kin fasa tsigeshi ɗaya bayan ɗayan?"

"Duk wanda ya samu zanyi ai"

Yai murmushi yana cigaba da cin Abincin sa, still kallon Yusuf take yadda yake komai a nutse, Yusuf yace "Malama karfa ki cijeni"

Bata san lokacin da dariya ta ƙwace mata ba, tace "aikuwa dan kasan na saba ba, da an takurani idan naga bani da mafita, se cizo kuma haƙorana dafi garesu, duk abunda na kama sena fasa shi, shiyasa Fahad ɗin Bulama yake cemin Mayya, tunda na huda shi da haƙorana"

Jiki a sanyaye Yusuf yace "yanzu idan muka rabu, muka koma gida Fahad zaki aura ko?"

Da sauri tace "Allah ya kiyaye, wallahi ko maza sun ƙare bazan auri wannan ba, mashayin giyane fa, ga neman mata kai zaka so in Auri wannan?"

Yusuf ya girgiza mata kai, ya ɗan tsura mata ido yace   "I can't imagine my life without you Widad, ko mu koma idan zaki Auri wani bazan iya jurewa ba, ban san ya zanyi ba"

"waye yace maka zanyi Aureni? Ni ba zanyi Aure ba, bani Abincin nima inci, amma a baki zaka bani yau" tai maganar cike da son da basar da wancan zancen da suke yi.

Haka ya dinga bata Abincin tana karɓa, kamar 'yar yaye suka gama sannan yayi shirin fita, yau da kanta har soro ta raka shi, ta tsaya ta kalle shi tace "bana son ka fita Yoseef, kamar kazo mu koma ɗaki"

"Yau kuma? To idan ma dawo me zaki ban?"

"Kawai inta kallonka, kana bani nishaɗi, da jokes ɗinka da halayenka masu kyau"

Yai murmushi yace "nima idan na fita, duk damuwa nake in dawo, saboda inzo inga abar sona, am missing you fa idan na fita".

Tace "nima haka, keep missing me harkaje ka dawo kaji"

Yusuf yace "yanzu abunda za'ayi shine, Yimin wani abu da in na fita har in dawo bazan manta ba"

Tace "kamar me kenan?"

Yusuf yace "just kiss me here 'yai maganar yana nuna mata kumatunsa na dama.

Ganin tsakar gidan ba kowa yasa Widad, ta rungume Yusuf ta fara kissing ɗinsa a baki, he was so much surprise da abunda Widad ɗin tayi, dan haka yasa hannu biyu ya rungumeta yana murmushi.

Hari ta bankaɗo labule zata fito daga ɗaki, hannunta da kofin da' aka karya, kawai tai gamo da Yusuf da Widad a bakin zaure, Yusuf ya bawa Hari baya dan haka be ganta ba sam, Widad kuwa ta ganta, amma tana sane ta basar ta ƙara maƙalƙale Yusuf ta cigaba da abunda take.

Da gudu Hari ta koma ɗaki, ta bankaɗo labule ta rufo ƙofa, Widad ta zame bakinta ta hau dariya, Yusuf yace "ya dai?"

Tace "bakomai, muje hanyar waje in raka ka"

Yusuf yace "rana me matuƙar tarihi a gurina, ba iya yau zan cigaba da tunanin ki ba har abada zanyi tunanin ki My Queen"

Murmushinta me ƙayatarwa ta cigaba dayi masa, da sukaje soronma soyayyarsu suka cigaba dayi, dukda Yusuf ne kawai ke furta mata yadda yake sonta, Widad kam ta kasa ce masa uffan.

Ya riƙo ƙugunta yana kallon ƙwayar idonta, Widad tace "Idan ma makara baka fita da wuri baf ba ruwana"

"Aiko ke kike da ruwa, dan ke kika hanani fita, ɗan ƙara min kiss ɗin mana kona 10 seconda ne"

Tureshi ta shiga yi tana dariya, tim suka ji an saki kwano, Hanne ta taho da fantekarta cike da Albasa, tayi karo dasu Yusuf, take taji ganinta ya ɗauke ta saki fantekar albasar, Yusuf yace "Subhanallah garin yaya kika zubar? '

Yai maganar yana sakin Widad, ya yunƙura da nufin ya durƙusa ya tayata tsince albasar, amma Widad ta riƙe shi ta tsatstsare shi da ido tace " meye naka a ciki? Ko kai ka zubar mata? "

Yusuf yace  "A' a amma kinga mu muka tsoratata ta zubar da albasar, yakamata a tayata kwashewa"

Wani mugun kallo tayi wa Yusuf, taja tsaki ta koma cikin gida, Yusuf ya durƙusa ya taya Hanne suka tsince Albasar, yace  "ki dinga kula sosai, ki dena yawan tsorata kinji?"

Hanne ta jinjina kai tace "to nagode"

Ta ɗau fantekarta tai waje, tana kuka tana tunanin me zata yiwa Widad yadda zata ɗan ɗana mata taji abunda take ji.





Alhaji Musane yace  "Nifa gaba ɗaya na fara gajiya da wannan wahalar, daga wannan se wannan abu sekace jaraba? Abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, shi ya ɓace ɓat kamar kuɗi an neme shi an rasa, shima wannan ɓangaren yarinyar har yanzu babu wanda ya ganosu, suma lawyoyin nasa sun kawowa mutane wasu surutansu na banza "

Alhaji Haruna yace "haba Alhaji Musa, ni ban taɓa ganin ka karaya ba akan abu se yau, duk abunda aka fiye shan wuya akansa za'a samu ne, yanzu mafita yakamata mu nema amma dole mu kassara Daula, mu kassara wannan dukiyar dayake taƙama da ita"

Alhaji Musa yace  "to meye mafitar, nagaji wallahi haba, ni zuwa zanyi in maida hankali akan harkar takarata kawai"

Alhaji Munir yace "kaga dan Allah Kadena mana zancen wata takara please, zancen takararka kai kaɗai ta shafa, mu muyi abunda ya dame mu kawai, Alhaji Haruna meye mafita"

"na saka a duba mana, wanda ze iya kwafar mana saka hannun Daula, sannan kafin a samu me saka hannun ayi fafutuka a bincika mana bankin nan, shima mu gwada muji ta ina zamu dace"

Alhaji Musa yace "to ai shikenan, Allah yasa mu dace, amma ni na fara gajiya wallahi, gashi shima wancan banzan yaron har yanzu ba'a gano shi ba, nifa sonake a kamashi kafin su shigo garin nan"

Haruna yace "karka damu, ai matakan da muka saka baze tsallake tarkonmu ba, ka kwantar da hankalinka komai ze tafi dai dai"

Alhaji Musa yace "shikenan Allah yasa hakan, ynzu a duba mana me iya kwafar signing ɗin nan"





Gidan Alhaji Daula kuwa, Hajiya Halima se shagalinsu suke da dukiya suna facaka, A ɓoye Ramlah take satar wasu abubuwan ba tare da mahaifiyarta ta sani ba ta kaiwa Fahad ya sayar ya kawo mata abunda yaga dama, sannan kuma su raba abunda ya kawo mata ɗin, Amal kam gaba ɗaya a cikin damuwa taje, dukda irin romon bakan da Mahaifiyar su take mata, akan cewar ai bakomai dan an kama Yusuf, amma hankalinta yaƙi kwanciya, sam bata da nutsuwa sosai take jin Yusuf a ranta, take tausayin halin da ze shiga idan aka kamashi da laifin ya sace Widad.

Anwar kam kasuwarsa ya koma zuwa, sam baya zaman gidan nan saboda irin takaicin da yake ƙunsa a cikin gidan, a kan idonsa yana ji yana gani haka Fahad yake zuwa ya ɗauki Ramlah a mota su fita, kuma mahaifiyarsu na gani bazata ce komai ba, shikansa ya fara lura da sauyin ɗabi'a na Ramlah, ya fara zargin ko ta fara shaye shayey, amma yasan da yayi magana mahaifiyarsu zata ƙarhata shi ƙarshe ma su ƙareta babu daɗi dan haka ya zuba musu ido.

Ma'aikatan gidan kuwa, su Isa se yanzu suka gane zaman Widad a gidan nan Rahama ne a garesu, saboda tsagwaron wulaƙanci da cin mutunci da suke fuskanta daga gurin Hajiya Halima da 'ya' yanta, zagi da cin zarafi gami da wulaƙanci ba irin wanda ba'a musu, Albashinsu kuma duk Hajiya Halima tabi zaftare musu, shima se sufi wata ba'a basu ba, zaman haƙuri kawai sukeyi a gidan nan, duk inda suka zauna banda tsinewa Hajiya Halima da 'ya' yanta babu abunda sukeyi, suna shiwa Widad da Alhaji Nasir Albarka, saboda kaɓakin arzikin da suke basu shida 'yarsa se yanzu suke ganin duk izzar Widad a cikin gata suke, dan gashi a yanzu an maidasu kamar bayi a gidan haka suke zaune.


Saleh ma yana ji yana gani, a gidan gonar nan haka Hajiya Halima ke zuwa ta ɗau abunda takeso ta fito dashi daga gidan ta siyar, ba yadda ya iya dan idan ya zaƙe su Alhaji Musa zasu iya gano shi, balli ya tashi dan haka se dai ya zura ido.



Hanne bayan ta dawo daga kai albasarta kuwa, ɓangaren Jamila ta wuce taje tayi jifa da fantekar albasar, Jamila tace "ke lafiya kuwa, ke da yayanki yana nan kikazo kika mana jifa da kwanon nan da yaci ƙaniyarki ai"

Hanne tayi tsaki tace "wallahi Jamila na tsani wannan koɗaɗiyyar bayahudiyar, na rasa me zan mata in huce"

Jamila tace "wace bayahudiyar?"

"wannan farar banzar ta gidanmu mana"

Jamila tace "dama ba musulma bace?"

"Musulma ce mana, sedai shegiya ce, bata da mutunci"

Jamila tace "wai meye tsakanin kune? Me tayi miki haka kuke takun saƙa"

"Wai ba damar magana ta haɗani da mijin ta, seta hau gayan magana, kokuma seta ganni se ta hau wani rungumeshi"

Jamila tace  "ikon Allah, toke meye naki a ciki, ba mijin ta bane ba?"

"to dan mijin ta ne seta dinga min haka? Naga dai namiji na maya huɗune, shikenan kuma baza'a kula shi ba?"

Jamila tace "Auho, yanzu na gane inda kika dosa, to tun wuri ki kiyayi kanki, ina ruwanki da mijin ta? Ke ke inake ina wannan bawan Allah, yana da wannan mace kamar ita tayi kanta, ki taba kanki da wahala ki lallaɓa da wanda aka sa miki rana"

Ji tayi wani mugun haushi ya kuma kamata, ta ja tsaki ta ɗau fantekarta tayi waje.

Saboda tsabar takaici Widad kam a ɗaki ta wuni, tunda ta fito ta gaida Gwaggo ta koma ɗakinsu, dan ta riga ta gama kawowa iya wuya akan abunda yake faruwa, so take tayiwa Hannne abunda idan ta taho suka haɗu seta canza hanya, ace yarinya 'yar ƙauye kamar wannan ta dinga shigar mata hanci, wata zuciyar tace ' me zakiytsaya tankawa waccan kucakar, shi Yusuf ɗin zaki yiwa'  haka ta wuni tana ƙunci da ɓacin rai, Abincin rana ma ta fara ci ta kasa ta ajiye, ta nemi guri ta kwanta.

Koda Yusuf ya dawo gida da yamma, yama manta da abunda ya faru da Safe, ya dawo ya tarar se cika take tana bastewa, Yusuf yace "Babyna wai meya farune kike wani haɗemin rai?"

Shiru tayi masa ko inda yake taƙi kallo, ƙarshema ta miƙe zata fice, Yusuf yay Wuf ya riƙota yace "haba gimbiyata, me nayi miki ne, bana jin daɗin irin wannan hukuncin da kikemin, ki hukunta ni ban san laifina ba"

Ƙwacewa tayi tace "ka ƙyaleni, ka koma gurin waccan 'yar ƙauyen daƙiƙiya ka Aureta, kuma kazo ka sakeni na gaya maka, nika ƙyaleni ita kaje ka aureta ka rabu dani, tunda itace mace"

Wai yau yake ganin kishi gangariyarsa, dan shaf ya manta da wani abu ya faru yau da safe, ashe abun yana ranta tun safen nan.

"Widad meye ya kawo wannan maganar kuma, ni nace miki ina son watane, ni ban gayamiki haka ba, meyasa kikemin hakane,? Haba Widad ki dinga jin tausayina inje in dawo a wahale, kekuma ki ƙaramin pressure"

Tsaki tayi, tai waje zata bar ɗakin, ya biyota yana cewa "naji na karɓi laifina, kiyi haƙuri dan Allah '

Amma Widad tayi fafur, fuuu tayo waje abunta.

Gwaggo ta kawo kai zata fito daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login