Showing 63001 words to 66000 words out of 209297 words

Chapter 22 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

728

gurin Widad, akayi masa kiran gaggawa Lagos, akan hanyarsa sukayi artabu da' yan fashi aka kashe shi.

Daula ya kaɗu matuƙar gaske da jin wannan labarin, ya shiga damuwa haka kurum zuciyarsa ke raya masa, ba haka abun ya faru ba, yanzu kenan duk me niyyar taumakonsu se anga bayansa?

Wannan karonma farkawar Widad yazo da sabon salo, bayan rashin magana ma, sam bata son haske sedai a rurrufe ko ina, ko yaya haske yake bata sonsa komai sedai tayi a ɗaki.

Ta ƙara shiga damuwa da taji labarin mutuwar DSP, dukda ba magana take son yi ba amma tayi kuka sosai.

Tace  "Daddy"

Daula yace "Na'am lovely na"

"Daddy dan Allah, ko duk kuɗinmu zasu ƙare, karka bari a saki Bala megadi"

"Insha Allah Baby, bazan bari ba amma na fara damuwa, gashi baki da lafiya, gashi an fara kashs duk masu niyyar temakonmu"

Ta kalli Daula tace "idan an kashe masu taimakon mu, Allah ze temake mu, idan kaje gaisuwa kayiwa iyalinsa alheri, ka basu haƙuri"

Daga nam ta kwanta bata sake magana ba.

Gaba ɗaya Daula ya ajiye batun harkar kasuwanci a gefe, ya tattara hankalinsa akan lafiyar 'yarsa.

Suna zaune da Bulama a falon gidansa, Bulama yace "Daula, zamanka fa da Widad a gidan nan baze yuwu ba, zuwa yanzu ya kamata kayi Aure kodan ka samu me ta yaka kula da ita, ga harkokinka suna nema su tsaya, ni da zaka yadda dana ɗauketa, saboda ina son Yarinyar nan"

Daula yace "nasan kana son 'yata Bulama, sedai koms za' ace sedai ace, zan cigaba da kula da ita, ina nema mata lafiya, yanzu abunda ya dameni ina son in samo malamai suzo su raba gadon Huda"

Bulama yace "wane irin gado kuma? Naga dama idan wani abu take dashi kaika bata, tunda ta mutu ai ya zama naka"

Daula ya girgiza kai yace "A'a, akwai kuɗaɗenta masu yawa da bani lokacin da mukayi Aure, ina son a ware natane a cikin dukiyata, idan aka ware zan mallakwa Widad su"

"Kamar yaya? Da can ka ware kashi bakwai, yanzu kuma Allah kaɗai yasan kashi nawa zaka kuma warewa, Widad ɗin da take yarinya me zata yi da dukiya? Kuma yanzu idan duk ka kwashe kuɗaɗen nan, kasan adadin mutanen da zasu durƙushe kuwa? Mutane dayawa da Allah suka dogara, amma suna daga kwamce suke Arziki saboda kasiwancinka"

"Nasani Bulama, amma hakan baya nufin zan janye kuɗaɗen ne, zan cigaba da juyasu, amma zan canza suna na dana 'yata akan abunda yake mallakinta, kuma insha Allah idan naga maganin da ake mata anan beyi ba, zamu dan gana da ƙasashen waje ne kawai"

Widad fa ba zuwa makaranta, kullum se a gida banda zabure zabure da ihun da take yi cikin dare, ga ƙin mutane dan a tsorace take da mutanen nan kar su sake dawowa su cutar da su.

Sedai a hakan an cigaba da yiwa Daula barazana iri iri ta waya, ace za'a kasheshi ko za'a sace Widad idan be faɗi inda takaddun nan suke ba, tun yana zarya hukumar 'yan sanda harya haƙura gaba ɗaya.

Bulama ya saka Daula a gaba da yayi Aure, dan ba mutuncinsa bane babban mutum kamarshk ace bashi da Aure kuma yana zaune da gashi se ƙaramar yarinya a gida ba.

Daula yace "sam baze Aure ba, yazan babu me maye gurbin Huda"

Bulama yace  "idan balarabiya kake so, kana da kuɗin da zaka je kowani ƙasa ka auro mace, wadda kake so"

Daula ya kan ce masa "ba balarabiya nake so ba, nagarta nake nema irin ta Huda"

Bulama ya matsa, ya dage ya takurawa Daula, Daula yace "nifa ka ƙyaleni, lafiyar 'yata ta fiyemin wani Aure"

Amma Bulama ya cigaba da matsawa, gefe guda kuma anata bankawa Widad allurai da ƙwayoyi da suke birkita mata lissafi, ƙiri ƙiri ta dena zancen zata faɗi wanda ya kashe Amminta, gaba ɗaya aka tsaya da zancen ma, a haka aka daddafa aka fara shari'a da Bala, anan Daula yayi amfani da tasirin dukiya, shari'a taƙi gaba taƙi baya aka tsare Bala, da rundunar sojoji sunso kawowa Bala ɗauki, Kasancewar nasu ne, sedai Daula yai amfani da kuɗinsa, hakan yaƙi tasiri.



Ganin Daula bashi da niyyar yin Auren nan, gaba ɗaya ya tattara hankakinsa akan 'yarsa yasa Bulama da kansa nemawa Daula matar daze Aura, sedai me.......






LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

80_81












Daula yace "se Widad ta amince tukuna"
abun ya bawa Bulama Haushi sosai yace "haba Nasir, kaima ka zama ƙaramin yaron kenan? Ya za'ayi kace se Widad ta amince? ita meta sani game da wannan maganar?"

Daula yace "Yarinyar nan itace uwata, itace Ubana itace komaina a yanzu, dan haka duk hukuncin data yanke shikenan"

Bulama yaji kamar yayiwa Daula dukan tsiya ya huce, haka ya ci gaba da cusa masa matar nan, 'yar uwace a gurin Bulama matar, sun rabu da mijinta tana da yara Uku, mijin idan ya shura takalmansa se yayi wattanni ba'asan inda yake ba, ga ba Abinci ya barta da yar taita wahala shine aka raba auren.

Daula fafur yaƙi maganar sam, Ita kam Gimbiyar wato Widad ana cigaba da sake birkita mata tunani, ta hanyar ƙwayoyi da kuma allurai, gaba ɗaya ta koma wata iriya abun tausayi, wani lokacin idan ta rasa me yake damunta sedai tayi ta kuka, takasa banbance a aace duniyar take.

Wani lokacin haka kurum tana zaune, sedai taji ana mata ihu ko ana kuruwa a cikin kunnuwanta, ko taga duniya tana juyawa, ko kuma taji kamar ana buɗe ƙofa za'a shigo kawai se zuciyarta ta bata mutanen nan ne zasu shigo.

Abun duniya ya ishi Daula, ga surutun mutane ya fara masa yawa akan yakamata yayi Aure, bekamata ya cigaba da zama haka ba.

Bulama yace  "kaga Daula, tun wuri ya kamata ka nemawa kanka mafita, kai ba dan Allah yasa kana da nasibi akan harkar kasuwanci ba, da tuni kasuwancinka yazo ƙarshe gaba ɗaya, kuma kaɗaici ze iya sawa Widad ta ƙara shiga wani hali, babu yadda za'ayi rayuwar yarinya ƙarama ta yuwu ba tare da mace me kulawa da ita ba, kai a yanzu taurin kai ba naka bane, kaje ka samu kayi Auren nan ko hankalinka yafi kwanciya "

Daula yace " Bulama ba naƙi inyi Auren nan neba, bana son in Auri wadda zata zo takasa jure zama dani, wadda zata ƙarasa kassarani, yanzu duk macen da zan aura, zata aureni ne dan dukiyata, matata ta fari kuwa ta Aureni tun banda komai, shiyasa nake jin tsoron hakan, ko in Auri mace ta haihu dani in kasa daidaita adalci a tsakanin 'ya' yan, dan bazan taɓa kamanta ƙaunar abunda Huda ta bari da wani ba, Allah sarki Huda ba ita ba abunda yake cikinta, Allah ya jiƙanki Huda ya saka miki kissan gillar da akayi miki"

Bulama ya dafa kafaɗarsa yace "Nasir, Kayi haƙuri, zan samo maka mace me hankali, kaga Haliman nan muyuniyar kirkice 'yar uwatace, mijin tane ta Aura Azzalumi, ƙarshe aka raba Auren, nayi imani da Allah zata zauna da kai lafiya, harta kula da Yarinyar nan tunda kaƙi bani ita, da naso ka bani ita kafin kayi Auren se in dawo maka da ita, amma kace kafi son ka kula da ita, tunda hakane gara ka lallaɓa kayi Aure, amma zaman da kake haka be dace sam, kuma kaima ka sani"

Haka Bulama yaita lallaɓa Daula, harya yadda zeje su gaisa da ita matar.

Duk da rashin lafiya na Widad, haka ya shiryata suka tafi tare, gidan da Halima take duk a kwararraɓe ba gyara, aka masa iso sitting room ɗin gidan, tunda sukaje Widad take kallon gidan, ita bata taɓa ganin gida a haka ba, gashi ɗan ƙarami gashi wani irin.

Halima taitawa Widad magana amma taƙi kulata, Alhaji Nasir yace  "Halima kinga 'yata Widad, kuma bata da cikakkiyar lafiya tun rasuwar mahaifiyarta ta samu matsalar Ƙwaƙwalwa, bata yadda da kowa ban saniba ko zaki iya zama da ita, danni da banyi niyyar yin Aure ba, amma saboda Bulama ya matsa, kuma ke' yar uwarsa ce yasa nace to shikenan na amince, amma ya kikace? "

Halima tace " insha Allah zan iya zama da ita in kula da ita, tunda kaga nima ina da yara, in Allah ya yarda baze gagara ba"

Daula yace "Masha Allah, idan ba zaki damu ba, mahaifin yaran baze ce komai ba, zaki iya tarewa tare dasu, mu zauna gaba ɗaya"

Nan ta rusuna tace "Masha Allah, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi Alhaji"

Yarane sukayi sallama, suka amsa musu gaba ɗaya, su ukune bini in bika, sanye da uniform ɗin makarantar gwamnati, kowannensu hannusa ɗauke da jakar nan ta da wadda ake cewa Baba nagode, takalmansu Sandal wanda ake cewa ganda, duk sun tsufa sun cinye, sun tsitsinke.

Yaran Biyu mata ne ɗaya namiji, suka gaida Daula, ya amsa musu cikin fara'a, Widad ta dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya, tana kallon suturar jikinsu, duk wani iri haka take ganinsu.

Namijin ne wanda aƙalla ze kai shekaru goma sha huɗu yace  "Mama, wannan wacece?"

Yai maganar yana nuna Widad, Halima tace "to sarkin surutu, aje a cire Uniform".

Daula yace "A'a ba'a gwale yaro ai, Ya sunanka ne?"

Yaron yace  "Anwar"

Daula yace  "Masha Allah, itakuma sunanta Widad ƙanwarka ce"

Anwar yai murmushi yace  "Mekyau da ita, Baby zomu gaisa"

Haɗe rai Widad ta ƙarayi ta kwanta a jikin Daula, Daula yace  "ai bata da lafiya ne Yaya Anwar"

Anwar yace "Allah ya bata lafiya, ina da sweet bari in baki kina so?"

Yai maganar yana zura hannu a jakar makarantar sa, ya miƙo mata alewa 'yar uku biyar guda biyu, ga mamakin Daula yaga tasa hannu ta karɓa tace  "thank you"

Nan Daula ya shiga murmushi, abunka dame ɗa, nan ya fara jin insha Allah a hankali Widad zata ware, ta saki jiki dasu idan ya Auri Halima, Sukam yaran matan kallon Widad kawai sukeyi, kyakkyawa da ita, ga gashi dan kanta ko ɗankwali babu, tana sanye da riga da skirt kamar 'yar turawa, tana kwance a jikin Babanta ta buɗe alawar nan tasa a bakinta, ta buɗe ɗaya tasawa Daula a baki gwanin ban sha' awa.

Suka tashi tafiya Daula ya babbasu kuɗi, babu ko kara suka karɓe, sedai fafur Anwar yaƙi karɓa yace tunda an bawa Su Amal da mamansu baze karɓa ba, juyin duniya yace a'a, Widad ta zura hannu a aljihun mahaifinta ta ɗakko kuɗi taje ta miƙawa Anwar kuma ta tsatstsareshi da ido.

Daula yace "Good, kuma ba'a maida kyautar Gimbiya, ni idan na baka kaƙi karɓa, ita ba'a maida mata da abu idan ta bayar"

Haka Anwar yasa hannu ya karɓa ya dinga godiya.

Nan Daula yaji daɗin ƙauna da karamcin da sukayi musu, dan haka ya amince da Auren Halima, amma yace baze zauna a wannan gidan ba canza gida zeyi.

Ya sanar da Bulama sun amince, haka Bulama ya wuce gaba Daula ya auri Halima, sannan yace ta taho da 'ya' yanta ze riƙe mata.

Suka tare a sabon gidan Daula, sedai fa wannan rashin yaddar na Widad yana nan, sam basa gabanta bata damu dasu ba, har gara Anwar shima wani lokacin take ɗan yadda dashi, amma Ramlah da Amal kam bata ɗaukesu wasu mutane bama.

Part ɗinta daban a cikin gidan, dan karma wani ya takura mata.

Halima kam tana Auren Daula nan da nan 'ya' yanta suka koma ce mata Mummy daga Mama, nan da nan sukayi shar, Daula ya sauya musu makaranta zuwa ta 'ya' yan masu kuɗi, ha ajiye musu direba da yake kaisu yana dawo dasu, komai shar dasu nan da nan suka fara canzawa, sedai babban abunda yake tsayewa Halima shine, Daula ya fifita 'yarsa akanta, ko magana tayi idan Widad ta rusheta ta zauna a gurin Daula, idan wani abu kake so a hannun Daula muddin Widad ta amince ka samu, wani lokacin ma itace zata baka, dan haka ta ɗorawa Widad karan tsana.


Ƙwayoyi da Alluran da akewa Widad sunyi tasiri a jikinta, ya zamana ko ba abata ba, haka kurum zata fara wannan fizge fizgen da iface ifacen, idan har Daula baya nan haka zata yi ta faman wannan kuruwar, suna jinta babu me kawo mata agaji, haka wasu lokutan zata jiyawa kanta rauni, ta gama ihun harta gaji ta faɗi, Anwar ne kawai idan yana nan yake iya taimakonta, Abinci idan anyi se anga dama za'a bata, ita kuma baza tace a bata ba, amma a gaban Daula Suyita nan nan da ita suna bata kulawa da nuna mata soyayya, baya kaso komai a ransa saboda halin ko in kular da take wa su Halima, saboda yana tunanin yanayin ciwon nata ne.

Tun daga nan Widad ta ƙara tsinkewa da lamarin mutanen nan, suyita nuna mata kulawa a gaban mahaifinta, amma  daga ita sesu suyi ta zaginta, suna ce mata mahaukaciya.

Hakan yasa ta ƙara zame jikinta daga garesu, sam bata iya fitowa tayi karo dasu, babban abunda ya ɗaure mata kai, be wuce yadda taga mutumin da taji an ambaci sunansa ranar da aka kashe Amminta, yazo gidanba a lokacin Daddynta baya gari, abun ya ɗaure mata kai sosai, ya daɗe a gidan sannan ya tafi, kafin ya tafi zuciya ta dinga azalzalar Widad taje tai masa wani abu daze illatashi, amma ta gagara aikata komai.

Jikintane ya fara tsuma, ta dinga tuna abunda ya faru, nan ta faɗi tana wannan ihun da take yi idan abun ya motsa, suna jiyo kururuwar Widad amma kota kanta basu biba, haka ta dinga gurnani ita kaɗai.

Anwar ne ya shigo, yace "Mummy ina Widad ne?"

"Kaje ka duba mana"

Anwar  ya tafi ɓangarenta, yaje ya tarar da ita a zube a ƙasa a falonta, gaba ɗaya bata hayyacinta, a gigice Anwar ya fito falo yace  "Mummy, Widad fa ba lafiya, tana sume a ɗakinta"

Halima ta lura da yadda Anwar yake nan nan da Widad, taga alamun bazata samu goyon bayansa ba, dan haka ta maze sukaje kan Widad, ya kwantar da ita akan kujera, aka kira likita, yace akaita can Asibitinsa, nan fa ya kuma ɗura mata wannan allura me kama da ta doki, wadda ke gigita Widad.

Cikin tangaɗin wahalarwa da allurar ke mata, bata gane komai ga idonta a buɗe amma sam bata cikin hankalinta, Wannan mutumin da aka ambaci sunansa ne yazo kanta, ya ƙura mata ido sannan yace 

"Ke ki gayamin inda kayan nan suke, takaddun nan da ubanki ya baki ayce akwai mesu, suna ina?"

Kallonsa Widad take, bata gane gaskene abun yake faruwa ko kuma mafarkin ne, ta kai idonta gefe taga Halima a zaune a gurin, lumshe idonta tayi taƙi magana.

Cikin tsawa yace " zakiyi magana ko sena miki azaba, irin wadda ba'a taɓa miki makamanciyarta ba"?

Ko gezau ba tayi ba daga inda take, ta lumshe idonta tamkar bacci ya ɗauketa
Halima tace  "bafa a hayyacinta take ba"

Mutumin yace  "Aikuwa zata dawwama a haka muddin ba zata faɗa ba, semun kashe Uban nata, an dinga ɗirka mata allurar nan kenan, da ƙwayoyi seta zama mahaukaciya tuburan ta girma tana yawo tsirara tana bin bola saboda rashin gata"

Widad najinsa, wani irin ƙuna ranta ya shiga yi, yasa an kashe mata mahaifiya, kuma yazo kanta yana gayamata maganar banza, sam takasa gane ko mafarki take ko a zahiri abun ya faru, ganin haka yasa hawaye ya fara bin gefen idonta, ta tabattar da ta haukace.

Can bayan wasu awanni, taji an taɓata ai wani kukan kura tayi dan a zatonta wannan mutumin ne, ta kai masa wata irin mahaukaciyar shaƙa tana zazzare ido, sedai kuma se taga ashe mahaifinta ne, da farko fuskar wancan ta gani, daga baya kuma taga ashe Daddynta ne, ba ƙaramin tsorata Daula yayi ba, tunda har Widad ta fara ƙoƙarin shaƙeshi to tabbas hauka ya tabatta, a hankali ta ajiye hannunta ta kwanta a jikin Daddynta.

Ko mintuna biyu ba'ayi ba kuma se bacci, amma cikin baccin banda mafarke mafarke ba abunda take yi, seta dinga ganin mafarkan kamar gaske, dan haka seta ƙwala ihu.

Sosai fa Daula ya shiga damuwa, Doctor Hamisu yace  "Ranka ya daɗe, kaga ana treatment ɗin nan but her body is not responding to the treatment, dan haka she needs to be admitted to psychiatric Hospital, yadda za'afi kula da ita"

Hawaye ne ya ƙwacewa Daula yace "Over my death body, in ɗau 'yata da hannuna in kai psychiatric, bazan iya ba, zan cigaba da kula da ita, idan yaso a cigaba da mata treatment"

Bayan ta ɗan farfaɗo, ya ɗau' yarsa yayi gida, kwana biyu ta ɗanji sauƙi amma lokaci lokaci takan yi ihun nan na dare.

Daula yana zaune da Halima da yaranta a falo suna hira, harda yaranta da jansu yake kamar 'ya' yansa, Widad ta fito tana taku ɗai ɗai tana kallonsu, Babban abunda ya ƙular da Halima be wuce yadda Daula ya miƙe tsaye ba domin tarar Widad, sekace yaga wa shugabarsa, gata gwansamemiya da ita, kusan shekara tara amma haka yake ɗorata a cinya kokuma ya goya ta a bayansa, ta zauna a cinyar Daula tace

"Daddy, tunda babu me dubamin wanda ya kashe Ammina, ina son gidan nan da Ammi ta rasu ka siyomin su zomo, su mage da duk domestic Animals, ka haɗa dana Ammi in dinga ganinsu"

Daula yace  "considered it done your majesty, yadda kike so haka za'ayi, kwanan nan ina son in buɗe miki Account mu dinga tara ribarmu ta kasuwanci nida ke"

Murmushi kawai Widad tayi ba tace komai ba, se can tace   "Daddy wai na dena zuwa makaranta ne?"

Daula yace "ina so ki warke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login