Showing 102001 words to 105000 words out of 209297 words
wani abu a hannun sa, da ire iren wannan ha' incin, A haka Yusuf yai tunanin yadda rasuwar mahaifinsa ta kasance, a nan ya gane tabbas set up ne mutuwar mahaifinsa da ubangidansa, sedai bashi da evidence dan in be manta ba, suna kan wani case ne, aka kira shi shida ubangidansa can Lagos, daga tafiyarsu se gawarsu, Yusuf baya son ɗagawa ummansa hankali dan haka be gayamata bata ba, ya bar zancen.
Yusuf ya dage da aikin ginin gidansu, dukda muguntar da'ake masa a gurin koyon aiki, a haka ya iya aikin kafinta, ya kama shago ya zuba yara suke masa aikin yana biyansu.
Duk yadda aka so asa Yusuf a harkar cin hanci amma yaƙi, aka dinga cewa shima tsinannen kafiya da taurin kaine dashi kamar ubansa marigayi, ko talauci ze kasheshi baya karɓar kuɗin rashawa.
Yusuf ya kammal ginin gidansu, da kansa yayi furnitures ya zuba a gidan, kamar gidan wata amarya, gidan yayi kyau hatta kayan sawa seda ya canzawa ummansa kafin su koma gida, ya zuba kayan Abinci rana ɗaya yaje ya ɗakkota ya kawo ta gidan nan, umma sarkin kuka seda tayi kukan nata data saba, yaita rarrashinta, suka kwaso sauran kayan buƙatunsu suka dawo sabon gida, Yusuf ya sai Babur lifan me kyau.
Alhamdilillah rayuwa ta fara yi musu sauƙi, Daidai gwargwado suna hutawa, ga salary ɗinsa ga gurin furnitures, ya hana Umma sana'ar komai, data motsa se yace "Umman Yusuf me kike so, Ummana me za'ayi miki?"
Sam bata da damuwar komai, dama gata ba wani girma tayi ba dan lokacin da Suka tsinci Yusuf ba tafi sha bakwai ba, dan da ƙuruciyarta sosai akayi mata Aure, bayan mutuwar Bashir wasu sun nuna suna sha'awar Auren ta, amma taƙi Aure saboda rayuwar Yusuf, tasan ba lallai a riƙe mata ba.
Babban abunda yake damun Umma da Yusuf shine ko abokan kirki bashi dasu, gashi kamar mace wani lokacin kullum yana naniƙe da ita, da girmansa da komai amma idan zata unguwa, seya bita, ya jirata a waje itakuma ta shiga, ko zata wuni yana gurin a zaune, idan kasuwa ce haka zasu tafi tare, haka idan Asibiti ne, idan ya dawo daga makaranta, idan ba masallaci ba baze je waje ya ɗanyi hira da abokai ba, tayi faɗan harta gaji amma yaƙi denawa, abun da Ummansa bata gane ba shine, shi hana gudun magana ne, ko ace anyi rigima yana gurin ko kuma wani abu ya haɗashi da wani ayi masa gori.
Yanzu gashi ya kammala karatu, ga aikin yi gashi ya zama cikakken namiji amma ko budurwa bata taɓa jin Yusuf yayi ba, to mutumin da bashi da abokai mazama balle wata budurwa, ko a gurin aiki abokinsa ɗaya da yake biyo shi gida shine Abbas, banda wannan Yusuf bashi da wasu Abokai.
Rannan yayi musu Abincin dare, ya zubi suna ci Umma tace "Wai nikam Yusuf, kai ko budurwa baka da ita ne, sa'aninka sun fara Aure, amma kai ko zancen budurwa baka yi, ko dai nice ake ɓoyewa"
Ya ɗan tura baki yace "Umma ni me zanyi da wata budurwa kuma, ni bani da wata budurwa"
"Saboda me baka da budurwa? Se kace ba namiji ba, haka zancigaba da zama da kai gunsumeme ba Aure, sedai duk inda zani kana biye dani? Ai lokaci yayi da zaka nemi iyali kaima"
"Nidai umma bana so, ki ƙyaleni a hakana kawai"
"Iyeee, kai kodai baka da lafiya ne? Idan bahaka ba, amma kace baka so in ƙyaleka, idan baka da lafiya ne ka gayamin in san abunyi, amma ta yaya za ka ce baka son Aure?"
Ya gane inda Umman ta dosa amma yace "Umma wane irin rashin lafiya, niba zazzaɓi ba ba wani ciwo ba, kina ganina rasam danu, kawai ni matan ne se a hankali, bana son wadda zata zo ta damemu"
"Ai ina maka addu'a, kuma nasan Allah ya amsa, Insha Allah mace tagari zaka samo mana, amma dai gaskiya anemomin sirika, ko kuma ni in nemo"
Yusuf ya miƙe tsam yace "Hajiya Umma kenan, me abun mamaki Allah ya ƙaro mana Arziki in biyamiki Makka, ni nayi nan seda safe"
"Au zancen ne baka so shine ka gudu ko? Zakazo ka sameni kuwa dan ƙaniyar ka, jikoki nake son gani, na ƙagu ka ƙara gaba yara nake son gani "
Yusuf yayi waje yana dariya yace "Hajiya Umma, tawa ta kaina.
Yusuf ya cigaba da aikin sa, da neman kuɗinsa.
Wataran ya dawo a babur ɗinsa, ze wuce gida yaji ance " Sannu da zuwa "
Ya waiga yaga wata matashiyar budurwa ce, shi dai yasan yana ganinta a nan unguwarsu, amma besan daga inda take ba, kuma ba abunda yake haɗashi da ita, dan haka be kawo dashi take ba yai gaba abunsa.
Aikuwa yaji haushin ƙin kulatan da yayi, haka ta wuce ta tafi nata Aiken.
Da safe ya fito ze sai bredi, suka kuma haɗuwa da ita, tace masa ina kwana, ya waiga ya kuma kallonta tace "nace ina kwana"
Yusuf yace "lafiya ƙalau" daga nan yai gaba.
Ya zamana kusan kullum in dai ze fita kokuma ya dawo seya ganta, kuma seta kula shi, shi harta fara bashi haushi ma.
Wataran Asmar Umma ta tashi ga zazzafan zazzabi, Yusuf ya kaita Asibiti aka rubuto mata ruwa da allurai, aka sama ta wasu a can ya taho da sauran gida.
Da daddare za'ayi mata allura, yaje chemist ɗin bakin titi, yaje ya gayawa me chemist ɗin ko zezo yayi mata allurar a gida seya biya shi
Me chemist yace "karka damu, kaje zan turo ƙanwata tayi mata"
Yusuf yace "tasan gidan ne?"
Yace "eh ta sani, zata zo insha Allah"
Yusuf ya koma gida yana jira, yai girki ya tattara kwanukan yana wankewa, tayi sallama, ya miƙe kalleta aikuwa ya haɗe rai yace "ke lafiya?"
Taya fari da ido tace "ba gurinka nazo ba kake wani haɗemin rai, ina mara lafiyar tamu?"
Yusuf ya harareta yace "wace mara lafiyar? Malama ƙara gaba ba nan bane"
"Kamar yaya, Yaya Sani ya cemin inzo zan mata allura fa"
"Wai dama kece?"
"Eh nice, ina Umman tawa take?"
Yusuf a ransa yace "ji wani iyayi, wai Ummanta ummana dai ni kaɗai"
Yai mata jagora gurin Ummansa, Yadda ta dinga lallaɓa Umman ne, yaji daɗi Sosai, bayan ta gama yace 'nawa ne? "
Ta Harare shi tace "in mutum yayiwa mamansa abu seya biya? Ummana Allah ya ƙara sauƙi"
Umma tayi murmushi tace "nagode sosai' yata, Allah yasaka da alkhairi"
Yusuf ya tsaya sororo yana kallonta tace "kaje ka cigaba da wanke wankenka mana, Umma seda Safe Allah ya ƙara sauƙi, likita ya rubuta a samiki ruwa, safe da yamma na kwana biyu, zanzo in samiki insha Allah"
Umma tace "to shikenan nagode Allah yayi albarka, amma baki gayamasa nawane kuɗin ba ya biya"
Yarinyar tace "Abunda ze biya shine, yaje ya ƙarasa wanke wankensa, yai miki shara ya siyo miki duk abunda kike so kici, kiji ƙwarin jikin ki"
Umma tace "to shikenan kana dai ji ko?"
Yusuf kawai ya sosa kai, Yarinyar tace "dan Allah ka fitar dani bakin hanyar nan taku, lungunku da duhu ina jin tsoro"
Umma tace "Yusuf raka ta mana"
Ya kalli Umma ya kalli yarinyar, ta kashe masa ido ɗaya tayi gaba.....
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/15/21, 4:53 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
104_105
Yusuf ya bita da kallo yana hararta, Umma tace "eh yakamata, Yusuf rakata hanya kaga dare ya fara yi, ni baki gayamin sunanki bama gashi zaki tafi"
Tai murmushi tace "Sunana Salma"
Umma tace "to Salma nagode, ki gaida mutan gidan"
Salma tace "zasuji insha Allah"
Badan Yusuf yaso ba ya biyota suka fito, Salma tace "wai kai baka amsa gaisuwa ne?"
"Eh bana amsawa"
Salma tace "A'a kace dai nice baka amsa gaisuwa ta, da safe idan na ganka koda yamma idan na gaisheka seka wani basar kamar baka ji ba, kuma fa kana jina"
Banza yai mata suka cigaba da tafiya, "au kana ji ina maka magana shine kamin shiru, ga mara hankali ko?"
Ko kallonta beba ya cigaba da takunsa majestically.
"Shikenan kar Allah yasa ka kulani ɗin, kuma ma bana son rakiyar"
Yusuf yace "to ki gaida gida"
Ya juya ya koma gidansu, Salma tace "lallai ka cika ɗan rainin hankali, dani kake zancen"
Washegari da Safe yakasance weekends ne ba aiki, dan haka bayan ya dawo daga salla, ya duba Umma yaga jikin nata da sauƙi, yakoma ɗaki ya baje ya dinga bacci, saboda baya samun hutu sosai, yana tara gajiya matuƙa.
Se kusan ƙarfe goma na safe ya tashi da sauri, dan ya manta shaf zeyi girki, ya tafi ɗakin Umma da sauri ya shiga da sallama ya tarar da Umma a zaune da ruwa a hannuta, Yusuf yace "Ummana dan Allah kiyi haƙuri, bacci ne ya ɗaukeni me nauyi, ashe har an samiki ruwan ban sani ba ne, bari inje in ɗora ko tea ne inje in siyo bredi"
Umma tace "A'a baseka ɗora ba, ni a ƙoshe nake"
"me kika ci haka, har kika ƙoshi?"
Salma ce tayi sallama ɗakin, hannunta ɗauke da plate da kofi, Yusuf yana zaune a falon Umma, daga shi se gajeren wando da vest, dan haka kyakkyawar surar jikinsa ta bayyana, namijin gaske me tsabar kwarjini da kamala.
Yana ganin Salama ya miƙe yace " ke meye haka zaki shigowa mutane babu sallama, baki tsaya an baki iziniba kika shigo?"
Umma tace "A'a ai tun ɗazu tana gidan nan, ita taimin shara da aikace aikace ma"
Ya kalli Salma da ta tsatstsareshi da ido yace "to waye ya sata, Da kin bari Umma idan na tashi ai zanyi, ke Malama ajiye kwanukan nan ki tafi angode, zan kaiwa yayanki kuɗinki ya ajiye miki"
Hararrasa Salma tayi harda murguɗa baki, Umma tace "jimin yaro da faɗan ba gaira ba dalili, daga taimako ita meta yi maka?"
"To Umma data gama aida seta tafi, amma kalli yadda ta ganni a haka ba kaya, kuma ta wani tsareni da ido"
Umma tace "to ubanwaye yace ka fito a hakan, ƙyaleshi kinji yau ban san dame ya tashi ba, naga yau rigima yake ji"
Yusuf ya fice daga ɗakin yana mita.
Haka aka ƙarashe kwanakin nan a haka, kullum tazo se sunyi faɗa da Yusuf, in dai tazo seta yiwa Umma 'yan aikace aikace kafin ta tafi, ko su zauna su sha hira ita da Umma, Salma tana da kyau dai dai gwargwado, gata' yar kwalliya da iya ƙwalisa, tana da hasken fata da matskaicin tsawo, sannan tana da ƙirar jiki me kyau, ta yadda ko tafiya take tana ɗaukar hankali.
Mazan unguwar nan dana wajen umguwar da yawa suna rushing a kanta, amma bata da lokacin su, ba matasan samari ba har manyan masu kuɗi suna nuna tayinsu amma basu isheta kallo ba, Saboda mace ce me class, a mazan ma ba kowa ke iya tunkarar ta ba, saboda duk girmanka idan kamata abunda beyi mata ba, zata keta kane yadda take so kuma ko a gaban waye, Tayi school of Nursing, tayi midwife tana ji da kanta sosai.
A bakin yayyyanta taji suna hirar Yusuf wataran da daddare, ɗayan yace "Habu gaskiya gayen nan da yaja salla da Asuba dama ya zasu bashi limanci, jar uba kaji ƙira'a kamar a Misra"
Habu yace "bari Usman, ni kaina da yaja sallar nan kamar kar ya dena karatun nan, ai rashin zuwan liman da wuri yau munga 'yan Islamiyya, anya wannan a ƙasar nan yai ilimin Addini?"
Usman yace "waya san masa, gaskiya ya iya karatu inaga zanje muyi bonding kona samu hasken makaranta"
"A gidan uwarwa zaka samu hasken makarantar? Bayan ko sauka Al'qur'ani ba muyi da kaiba ka fece neman kuɗi"
Habu yace "eh naji, aiba sharaɗine se mutum yayi sauka za'ayi abota dashi ba"
"To bari in gayamaka, kaga duk wannan ilimin nasa shegen girman kaine dashi, baha kula kowa, iyakaci in ze wuce yai muku sallama, ban da haka ko aboki bashi da shi a unguwar nan, inda gayen ya ban haushi kenan, dan kana da ilimi ubanwa zakayiwa girman kai, kai ba wani shahararraen attajiri ba, ba basarake ba amma kace bazaka kula mutane ba"
Habu yace "Aikuwa ilimin baze masa amfani ba, dan girman kai rawanin tsiyane, ni harnaji ya bani haushi wallahi '
Salma tace " Kukam Allah ya shirye ku, kawai kun zauna kuna tayi da bawan Allah kamar kun rasa abunyi "
Usman yace " ke abun da haushi fa, mutum be fika da uban komai ba amma ya dinga hura maka hanci, baze dingawa mutane magana ba, ai dole ayi dashi"
Salma tace "to ka sani ko haka nature ɗinsa take, maybe jan ajinsa yake yi".
Habu yace "Nature ɗin banza da wofi, kuma jan ajin me sekace mace, jan aji ai se mata, kana namiji ubanwa zaka jawa wani aji, yana gaddi ina gaddi za'a jamin aji, wallahi mutum be isa ba"
"Nikam nafison irin haka, inga mutum gentle, yafi ma wata macen jan aji amma ace duk inda mutum ya zauna dan yana namiji ya dinga sakin baki haba, ai abun ba tsari"
Habu yace "wannan yarinyar kinci kai tabbas baki da hankali, namiji in ba ɗan daudu ba meye na wani jan aji"
Haka suka cigaba da wannan jayayya a tsakaninsu, ya zamana kusan kullum se anyi zancen Yusuf, saboda ko minti biyar liman ya ƙara bezo ba, se kaji ana Malam Yusuf a jamu salla, saboda kawai suji ƙira'arsa me daɗin sauraro.
Zuciyar Salma ta kwaɗaitu da san ganin Yusuf, saboda yadda take jin ana maganar sa, wataran da yamma taje karɓar kuɗi a chemist ɗin Usman, Yusuf yaje siyawa Umma Inhaler, tunda ya shiga daga tafiyarsa ma taga yadda yake taku cikin nutsuwa, yayi sallama suka amsa sannan ya gaishesu, ƙamshin turarensa ya gauraye shagon, Salma ta shagala da kallonsa, wanda shi sam be san ta nayi ba, ya karɓi abunda ze siya yai waje.
Yana fita Salma tace "Masha Allah, Yaya wannan ma a unguwar nan yakene? Kaga mutum nutsatse, ga ƙamshin turare, wanda seka gifta maza goma ba kaji ba, se warin hamnata mussman irinsu Yaya Habu"
Usman yace "Allah yasa yaji abunda kikace ya casaki san ransa, shegiya uwar leƙe leƙe, duk tarin samarinki amma kuma kina yaba wani"
Tace "kai Yayana, wallahi ko kai da kake namiji kasan gayen nan ya haɗu, kaga da yai murmushi, wasu dimples suka lotsa wayyo Allah na, gaskiya me kyau ne, kuma me ajine"
Usman yace "dalla wuce can, haka zaki ƙare ƙarshe mummuna zaki aura"
Tace "Allah ya kiyaye, aini naga miji"
"A ina?"
"wannan wanda ya fita ɗin mana, in dai a unguwar nan yake, ina ciki"
. Usman yace "aikuwa zakiyo waje daga cikin da kika shiga, dan girman kaine dashi kamar ƙaruna"
Salma tace "kamar yaya kenan?"
"Shine fa Yusuf ɗin da muke magana, wanda Habu yake zagi"
Salma tace "haba dai? Wayyo Allah na gaskiya ya haɗu, bashi da makusa, ga kyau ga ilimi ga nutsuwa ga tsafta, gaskiya yamin"
"to 'yar wahala, wata wahalar ta ganki kenan, dan wannan banga ta inda ze kulaki ba, dukda wannan koɗaɗiyar fatar taki"
"to fatar tawa ma hassada ake mata, to Allah ya shiryeka, ni na tafi ka tayani addu'a kawai"
Ta juya ta fita da sauri, tun daga ranar ta gano gidansu Yusuf, take daidaitar lokacin fitarsa da dawowarsa, idan ta ganshi se tayi masa magana, farko da yake ƙin amsa gaisuwarta tayi zaton zancensu Habu haka yaje yana da girman kai, seda taje gidansu sawa Ummansa Ruwa taga yadda yake aikin gida, ga shagwaɓa kamar mace, ga tsananin biyayya ga mahaifiyarsa, anan ta gane mutane da yawa basu fahimce shi ba, bashi da son shiga mutane ne, amma mutum ne simple.
Tun daga nan Salma ta liƙe masa, idan ta ganshi seta masa magana kota tsikane shi, wataran sedai ya harareta yai tafiyarsa, ta maida gidansu Yusuf gidan zuwanta, ko tayo girki ta kawowa Umma, ko tazo nan gidan ta tayata aiki.
Sabo ne ƙarfi ya shiga tsakanin Umma da Salma, tana jin daɗin yadda take girmamata take tayata wasu ayyukan, dukda Yusuf haushin Salma yake ji amma a hankali, saboda soyayyar da take nunawa Ummansa da mutuntawa yasa, yake ɗan saurara mata kuma har cikin ransa yake jin daɗin kulawar da take nunawa mahaifiyarsa.
Wataran Salma taje gidansu Yusuf wajen ƙarfe sha ɗaya na Safe, ta tarar da babur ɗinsa be fita ba, ta shiga cikin gidan ta tarar da Umma a tsakar gida hannunta da mayafi, Salma tace "Umma ina zuwa haka? Kuma Yaya Yusuf be fita bane? naga babur ɗinsa"
Umma tace "dama chemist ɗin yayanki zanje, kwanan sa kusan biyar yana zazzaɓi sama sama, nayi nayi yaje Asibiti yaƙi yau jikin nasa rau da zazzaɓi ko gurin aiki ya kasa fita, shine nace bari in kira yayanki, ya duba shi idan akwai abunda ze iyayi masa to, in kuma babu mutafi Asibiti, yana jin jiki, kin san shi da dauriya da taurin kai, yauma dan yaji uwar barine ya kasa fita gurin aiki"
Salma tace "Ina Yaya Yusuf ɗin yake? Nima zan iya duba shi ai"
Umma tace "muje yana ɗakinsa"
Umma na maganar aka kirata a waya, ta tsaya ɗagawa Salma ta shiga ɗakin nasa da Sallama, ɗakin tas dashi kama r na mace, komai fes fes se ƙamshin turaren wuta da drumer ke tashi, gwanin ban sha'awa.
Ta hango Yusuf kwance akan gado, ya lulluɓa da bargo, a hankali ta ƙarasa gaban