Showing 171001 words to 174000 words out of 209297 words

Chapter 58 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

746

zata kwaɓawa aiki haka? Waini garin yaya abubuwa suke ta cakuɗewa ne babu mafita sam a cikin lamuran, daga wannan se wancan? Kai baze yuwu ba da sake gaskiya"

Mahaifiyar Nurat fa babu sauƙi a lamarin nata, dan a kwanaki ukun nan ko yatsan ƙafarta bata motsa ba, yadda take a kwance a haka take, sedai a juya ta nan a juyata can, babu wani cigaba kuma a wannan kwanaki ukun still, lokaci lokaci jini na fita ta hancinta da bakinta.
     Nurat ta ɗaga hankalinta akan san sanin Halinda mahaifiyarat ke ciki, amma se dai ace mata tana ƙarƙashin kulawa ta musamman ta likitoci, dan haka bazata ganta ba, Bata da aiki se kuka, danta fara zargin ko ta mutune ake ɓoye mata, Khalil neke aikin rarrashi kullum cikin rarrashinta yake akan ta kwantar da hankalinta, Mum ɗinta zata tashi zata warke da yardar Allah.
Sam bata son ganin mahaifinta yazo inda take, data ganshi se taji ranta babu daɗi, mussman idan ta tuna irin muguntarsa da zalumcinsa, da rashin afuwarsa.

Bulama mussman ya shirya ya tafi gidan Justice A dutse da yamma, lokacin yasan ya dawo daga gurin aiki.
Bulama yace "Nifa A dutse na kasa gane bayanin ka, ji naifa kace wai harda wannan barrister me shegen bakin tsiya za'ayi shari'ar nan, yanzu meye abunyi kenan?"

A dutse yace  "eh to, kaga dai ko ana hauka kasan A Adam baze karɓi bribe ba, ni dai shawarata da kai shine karka yi wani Yunƙuri da zesa a ganoka, dan ba kaiba harni zamu shiga cikin matsala, saboda irin shari'ar da nayi, musamman idan aka gano na karɓi cin hanci daga hannuka, abun baze mana kyau ba"

Bulama ya dafe kai yace "yanzu shikenan, babu wata mafita kenan?"

"Karfa ka damu, ka kwantar da hankalinka ai su Barrister Sadik suna nan, za suyi iya yinsu akan shari'ar, suma jajirtaccune karka damu koka ɗaga hankalinka, babu abunda ze faru fa"

Bulama yace "to shikenan, dan Allah idan da wani information ka dinga sanar dani"

A Dutse yace "Insha Allah, kar kaji komai, ba zasu yi Nasara ba"

Fahad kuwa yana zuwa gida, ya ɗau waya ya kira Ramlah, yana kira ta ɗaga.

Aikuwa tana ɗagawa yace  "munafukar banza da ta wofi, ashe ƙarya kikewa Mahaifina zaki haɗani faɗa da ubana, mara mutunci ƙaramar karuwa"

"Lallai Fahad, Bulama ya maida kai gaula, gashi ka ka raineni ka bani training a harkar karuwanci, amma kuma na shallake tunanink, dan na kai inda baka kaiba, to idan uban naka ya isa, ya kirani a waya a gabanka yace ƙaryane abunda na faɗa mana, ko kuma yaje a binciki lafiyarsa ko yazo har gida ya sameni yace ƙarya nayi mana, ai baka isa ka cuceni a banza ba, gidanku ma kun ƙara yawa masu ciwon, seku dage da shan magani tare "
Ta katse kiran wayar gaba ɗaya, Fahad ya jinjina kai tabbas tunda ta dage babu ko shakka mahaifinsa ya aikata abin da Ramlah ta faɗa, kuma da wuya idan ba'a sameshi da cita me karya garkuwar jiki ba, dan tunda ya iya neman Ramlah to yana biye biyen mata.
A hankali ya furta wayyo Allah Mummyna, ya nufi gida da sauri, yana zuwa ya tarar da mahaifiyarsu Hajiya Sarah ta shirya ta sha gayu zata fita, dama gata mace me iyayi da son kwalliya.

Ya ƙura mata ido, yana jin tausayinta a ransa,
"kai lafiya kuwa? Wannan kallon ƙurillar da kakemin fa? '

Fahad yai murmushin ƙarfin hali yace" kyau kikamin Mummy "

Tai murmushi tace "Allah ya shiryeka, sarkin zolaya"

Tai maganar tare da murmushi, ta shige motarta taja ta fita.

Jiki a sanyaye Fahad ya tafi part ɗinsa, yana zuwa ɗakinsa ya zube akan akan gadonsa yana rusa kuka kamar ransa ze fita  "wayyo Allah na, kaicona da irin wannan rayuwar da nayi, a sanadina rayuwar mahaifiyata zata shiga garari, Daddy bakamana Adalci ba, wayyo Allah kaicona"

Jin hargowar kukan Fahad ne yasa Ramadan farkawa daga bacccin da yake yi, ya fito daga ɗakinsa ya shiga ɗakin Fahad, ya tarar da shi a zaune zaman dirshen yana ta gursheƙen kuka.

Jiki a sanyaye Ramadan yace  "Fahad lafiya kuwa? Waye ya mutu?"

Fahad ya ɗago ya kalli Ramadan, ya goge hawayensa tare da daidaita nutsuwarsa yace  "ba kowa"

"Amma kake wannan kukan? Idan ba mutuwa akayi ba meyafaru? Kukan kane fa ya tasheni daga bacci"

Fahad ya share hawayensa yace  "Ramadan Daddy be mana adalci ba, wai ashe Daddy yana da mummunar alaƙa tsakaninsa da Ramlah"

Ramadan yace "wace Ramlan?"

"Ramlah dai, Ƙanwar Anwar"

Ramadan yace "subhanallah, wai kana nufin da Daddynmu take mummunar mu'amala"

Fahad yace "ba wai bane Ramadan, gaskiya ne ita ta gayamin da bakinta"

Ramadan yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, meyasa Daddy ze mana haka? Fahad abunda kake aikatawa ga 'ya' yan wasu ne muma yazo mana har cikin gida, kai kayi Daddy yayi alhalin muna da uwa muna da ƙanwa mace wannan abun dame yai kama?"

Fahad yace "wallahi Ramadan nayi nadama, nadamar da bata da amfani sam, a yanzu haka maganar da nake maka da ƙyar idan Daddy bashi da cuta me karya garkuwar jiki, saboda Ramlah ta tabattar min tana da ita"

A razane Ramadan ya kalli Fahad, "HiV kake nufi fa?"

Fahad ya jinina masa kai alamar eh.

"La'ilahaillalah Muhammadu rasulillah salallahu alaihi wassalam, Fahad HIV? Mummy kenan itama ta ɗauka a jikinsa? Subhanallah kun jawa wadda bata ji ba baya gani ba Fahad, ka ga illar zina da nake ta nuna maka ka kasa ganewa, Anwar ma ya nuna maka ka toshe kunnenka, gashi sanadin zina Daddy ya kwaso mana masifa, illar zina kenan idan kayi kai kaɗai illarta seta shafi al'umma da dama, Daddy be kyauta mana ba"

Fahad a ransa yace  "Ramadan idan na gaya maka ni na sakawa Ramlah ciwo ta sakawa mahaifina ban san wani kallo zakamin ba"

Ramadan ya zauna yana share hawaye, tare da baƙincikin abunda mahaifinsu ya aikata, tausayin mahaifiyarsu ya mamayeshi, ya kalli ɗan uwansa yace  "yanzu Fahad yaya zamuyi mu gayawa Mummy wannan maganar? Itama taje a binciki lafiyarta tunda wuri?"

Fahad yace "Ramadan abunda nake ta tunani kenan, na rasa abunyi gaba ɗaya, ban san ta inda zan ɓullowa wannan maganar ba, da ƙyar idan Mummy bata ɗauka ba, dan babu wanda yasan tun yaushe yake tare da ita, suke mu'amala"

Ramadan ya dafe kansa, ya dinga jujjuya kansa cike da ƙunar rai, ya fice jiki a sanyaye daga ɗakin Fahad, zuciyarsa na masa wani irin zugi da takaici, gami da tausayin mahaifiyarsu.

Shirye shirye sukayi nisa, akan ɗaukaka ƙarar Yusuf, manyan lawyoyi da masu kare haƙƙin ɗan Adam suka shiga lamarin, suna ta tattar hujjoji da shedu wanda suma zasu gabatar, a sake sharia'r Yusuf.
Yayinda Widad ke zaune a inda take ɓoye, inda Bulama yake ɓoye da ita, take communicating da mutane a waje, ta hanyar Sabuwa me aiki, taita aikenta da takadda ba tare da Sabuwa tasan ma'anar hakan ba, ga cikinta ya ɗan ɗaga sosai ya fito, dan sosai yake motsi yanzu, sedai duk lokacin da cikin ya shiga wani watan, se wata matsala ta taso, kodai yawan amai, ko ciwon kai, ko rashin son Abinci, haka Widad keta wahala tana ƙumbiya ƙumbiya da cikin a hijjabi kar wani ya gani, ga Bulama ya shafe kwanaki bezo ba, tunda yayi mata barazanar kama mahaifiyar Yusuf bata sake ganinsa ba.

Bulama kuma yaga canji a tattare da yaransa, abun da ya bashi mamaki be wuce yadda Ramadan ɗin dayake nutsatse yabi sahun Fahad ba, sam basa gaisheshi ko kallon inda yake basayi, balle ya saka ran wani abu na kirki ya shiga tsakaninsu dashi, suka dena shiga cikin gidan ma sam.

Bulama yace "Sarah, kin lura da yadda yaran nan suka canza gaba ɗaya a gidan nan? Na rasa me nayi musu, sam basa shiga harkata sun dena ko gaishesni, ko wani abun sukace nayi musune?"

Hajiya Sarah tace   "ni dai bani da masaniya akan komai, ni Ramadan yafi bani mamaki ma, nasan ba haka yake ba, amma ban san yadda akayi shima ya ɗauki wannan mummunan halin ba, amma dan Allah kayi haƙuri, zanyi magana dasu insha Allah"

Bulama yace "shikenan, yakamata kam"

Daga nan ya kintsa ya fita, bayan fitarsa Hajiya Sarah taje har BQ ta samesu,
'Fahad, wani abu nake gani wanda na kasa gane kansa, meye dalikinku na dena kula mahaifinku ne?'

Fahad yace "babu komai"

"ƙarya kuke yi, akwai dalili idan ba haka ba, meye na wannan shareshin da kuke yi?"

Ramadan zeyi magana, Fahad ya girgiza masa kai yace "Mummy, kin san daddy da yawan faɗa, komai ya gani se yayi magana, se yayi mita da faɗa, shiyasa muke ɗan janyewa kawai"

Tace "Ai ba yanayi ne dan ya takuda muku ba, dole idan kukayi ba daidai ba a tsawatar muku, dan haka bana son wannan abun da kuke, a gyara dan ya fara zargin koni nake saku kuke masa haka"

Fahad yace "to insha Allah, zamu gyara"

Bayan fitarata, Ramadan yace "Fahad meyasa ka hana a gayamata?"

Fahad yace  "Ramadan, ba'akowane irin yanayi ake gayawa mutum magana ba, ka bari zamu gayamata '

" Aikuwa bashi da amfani ko mun gaya mata, nasan aikin gama ya gama, ya riga ya cutar da ita "

Fahad yai shiru be kuma cewa komai ba.

Jini fa yaƙi tsayawa Amal, gaba ɗaya ta ɗashe tayi fari, ta kira doctor Hamisu a waya, ya rubuta mata magani, taje ta siya amma idan ta sha wuni take a kwance tana jiri, gaba ɗaya tayi wani iri, tambayar duniya taƙi gayawa Hajiya Halima abunda ke faruwa.
Tana kwance ta lallaɓa, zataje Asibitin da aka cire mata cikin ganin Likitan, se taga message nata shigowa wayarta, tana dubawa me zata gani? Kuɗinta na Account ake ta kwashewa, ta tashi a gigice sedai ba wani abu data iyayi an kwashe kuɗin nan tsaf, sakamakon wani website data shiga, akace ta saka BVN Number ɗinta, kuma ta saka akayi amfani da shi aka kwashe kuɗin nata.
Ta fito falo a gigice tana kuka, Hajiya Halima tace "ke lafiya kuwa?"

"Mummy kuɗina, an kwashemin kuɗina a Account"

Ramlah tace "ke kuwa kina me? Garin yaya?"

"Wani website ne, na shiga na saka BVN ina ga ta nan aka kwashemin kuiɗn, gashi nayi investing kusan million biyar a wani business shima an kwashe ma shiga uku"

Hajiya Halima tace "million goma kuma? A kna kika samu million goma?"

Sekuma ta dawo hayyacinta, ta shiag inda inda, cikin tsawa Hajiya Halima tace  "magana nake miki, a ina kika samu million goma?"
Tai shiru tana tura baki, "zakiyi magana ne? Ko kuma sena tashi na tattaka ki?"

"Alhaji Haruna me yamin fyaɗe, ni kuma na sace masa kuɗi a account"

Ramlah ta buɗe baki, Hajiya Halima ta miƙe tsaye  "ya miki fyaɗe kamar yaya?"

Nan Amal ya kwashe komai ta gayamata, har jinin da take ta zubarwa tunda aka cire cikin.

Nan da nan jikin Hajiya Halima ya ɗau rawa, ta kasa magana ma gaba ɗaya, ta dinga bin Amal da Ramlah da kallo.

Tunda mutane suka ji batun Yusuf zeyi appeal, suke ta ɗokin sake zaman ganin shari'ar nan, ranar da za'a fara sauraren ƙarar kotu ta cika maƙil, musamman jin labarin a ƙarƙashin jagorancin gogaggaun Matasan lawyoyi dodannin Azzalumai za'ayi shari'ar, kotu tayi maƙil assurance ɗin da Bulama ya samu a gurin Justice A dutse, da kuma su Barrister Sadik yasa ya je kotun da ƙwarin gwiwarsa, sedai duk da haka bashi da wani karsashi, saboda Alƙalin koyun bashi da wasa, balle ka tunkareshi da wata maganar cin hanci Justice Muhammad Mustapha.
Shikansa Yusuf yayi mamakin ganin, manyan lawyoyin da sukazo dan tsaya masa, da yawa a radio yake jin sunayen su, sekuma a dandalin sada zumunta, amma yau gashi gasu wai zasu tsaya masa, a iya saninsa ba kowa ke iya ɗaukarsu shari'a ba, saboda lawyoyine masu tsadar gasme, kuma basa tsayawa shari'ar Azzalumai, to ta yaya akai shi suke son tsaya masa? Bayan ta bayyana ƙarara shi me laifine?.

Barrister Adam A Adam ya fito gaban alƙali ya gabatar da kansa a gaban alƙali, sannan ya kalli kotu yace  "sunana Barrister Adam A Adam, ni lawyer ne me zaman kansa, ina daga cikin tawagar lawyoyin da zasu tsayawa wanda ake ƙara, don bashi kariya, a tare dani akwai hujjoji da shedu da zasu tabattarwa da alƙali cewar wanda ake tuhuma, be aijata ɗaya daga laifukan da ake zarginsa dasu ba, idan kotu ta bani dama ina buƙatar ganin Sada, wanda yace Yusuf ya kai masa mota ya siya "

Sada ya fito yana rarraba ido, dan kallo ɗaya zakayiwa Barrister Adam A Adam kasan babu wasa a tare da shi, sannan abune mawuyaci a kada shi a shari'a, saboda gogaggen lawyer ne, kuma ɗan gwagwarmaya.

Barrister ya kalli Sada yace " ko zaka iya gayawa kotu sunanka, da abunda ka sani akan wanda ake zargi?"

Sada ya maimaita abunda ya faɗa a kotun baya, Barrister Adam yace  "wow, ko zaka iya gayawa kotu wame irin motoci Yusuf ke kai maka gyara daga gidan Daula?"

Sada yace "motocine dai, kamar su jeep su Honda da sauransu"

Barrister yace "wace irin mota ce Yusuf ya kai maka ta gidan Daula ka siya?"

"Prado ce" ya bada amsa

"wow, kasan irin wannan motocin se gidan attajirai irinsu daula kam, amma ya akayi ka siyi motar da kuɗinta ya haura naira million talatin a matsayinka na bakanike?"

"Amm ai, ai, ai dama bani nake...

Objection ya me shari'a cewar Barrister Sadik, " Barrister Adam yana ƙoƙarin jefa tsoro da razani a zuciyar sheda, kuma ai shi arziki sirrine, dan mutum yana ƙaramar sana'a shikenan baze mallaki dukiya ba? "

Justice Mustapha yace  "tambayoyin da Barrister Adam yakewa Sheda, zam basu kauce ba dan haka wannan ƙorafin be karɓu ba, cigaba da aikinka"

"Nagode ya mai girma me shari'a" cewar Adam A Adam.

"Sada, waye megidanka da ya sai motar?"

"Amm, wa.. Wani oganane ubangidanane"

"Amma meyasa kuka sai motar, bayan kun san Yusuf bashi da arzikin daze mallaki wannan motar?"

"Amm, ai, ai dama bece min satota yayi ba, kawai yace in siya nace masa bana siyan mota, na haɗashi da me siya na zata ko bashi motar Alhaji Nasir yayi, kasamcewarsa mutum me kyauta"

Barrister Adam yace "hakane, ina neman alfarma da kotu ta bani dama dan gabatar da wata ƙwaƙwarar sheda da zata tabattar da abunda Sada ya faɗa ba gaskiya bane"

Aka bawa Adam dama, aka shigo da Nura, aka tsayar da Nura a gurin Tsayuwa, Barrister Adam yace  "ko zaka gayawa kotu sunanka"

"Sunana Nura Idris"

"Kasan wannan" aka nuna masa Yusuf, Nura ya jinjina kai alamar eh, "wannan fa?" aka nuna masa Sada, Nura yace "A'a"

"toko zaka iya shedawa Kotu, abun da ka sani game da abunda ake tuhumar Yusuf dashi?"

Nura yace "kamar yadda na faɗa sunana Nura, kuma nine direban Alhaji Nasir Daula, kafin zuwan Yusuf ya fifita Yusuf sama da kowane ma'aikaci a gidan, na shekara a ƙalla tara ina aiki a gidansa, a haƙiƙanin gaskiya idan mota ta lalace a gidan Alhaji Nasir, Har gida ake zuwa a gyara ta, kuma Yusuf baya kai gyaran mota iya abunda nasan yanayi, shine tuƙa 'yaf gidan Alhaji Nasir Daula, sekuma shikansa Alhaj Daulan wasu lokutan, kuma idan mota ta lalace ma ba' a fiye barinta a gidan ba, gyara ta ake a bayar da ita, dan haka gaskiya ni ban san wannan bawan Allah ba, kuma a gidan Alhaji Nasir Daula, babu irin motocin daya faɗa, manyan motoci na alfarma su ake hawa a gidan Alhaji Nasir"

Barrister Adam yace "Malam Nura muna godiya, ban sani ba ko Sada yana da abun faɗa?"

Sada ya soma inda inda, yana kallon inda Su Bulama suke, akace ko su Barrister Sadik suna da abun faɗa? Sukace babu.

Barrister Adam yace  "sheda ta gaba da zan gabatarwa da kotu itace, shedar da aka bawa Yusuf a hukumance, daga hukumar 'yan sanda, na cewar yaje gidan Alhaji Daula yai bincike sannan ya bawa' yarsa kariya a ɓoye, a matsayinsa na ɗan sandan farin kaya, wanda hukumar ta musanta hakan, Amma akwai takadda da aka samu, wadda da saka hannun hukumar da stamp ɗinta, wanda babu wanda ya isa ya samu wannan stamp ɗin, idan har ba daga ofishin manyan cikin jam'ian tsaron ba "  Barrister Adam ya fito da takadda aka karɓa ka miƙawa alƙali, shi dai Yusuf yana tsaye, yana tunanin waye ya masa wannan ƙoƙarin haka?"

"dan haka muna neman jin cikakken bayani daga bakin 'yan sanda, idan har bata hannunsu wannan takadda ta fito ba, ta yaya akayi stamp ɗinsu ya fito a takaddar, idan kuma da saninsu yaje yin aikin, meyasa suka musanta sune suka bashi aikin?"

Nan fa sa'insa ta kaure tsakanin lawyoyin, su Barrister Sadik suna da'awar ai ƙarewa Wadda abun ya faru akanta da kanta ta bada sheda, seda alƙali ya buga guduma, yace ya ɗage shari'ar zuwa sati biyu gaba.




AMANA! AMAA!! AMANACE!!!

AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"

_(INNALILLAHI WA INNA IALAIHI RAJI'UN  ina amfani da wannan damar gurin miƙa saƙon ta'aziyya ga Ɗaukacin zuriyar Hajiya Aisha Muhammad (Baba) bisa babban rashi da mukayi na rasuwar ta ina fatan ubangiji Allah ya jiƙan ta yai mata rahama, ya kai haske kabarainta, ubangiji Allah ya duba zuriyar da ta bari, ya bata ladan ɗawainiya da iyalI da tayi tsawon ranta, ubangiji Allah ya jiƙan kafatanin  wanda suka rigamu gidan gaskiya Musulmi, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani_)

IN THE MEMORY OF LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD, I DEDICATED THIS PAGE TO LATE HAJIYA AISHA MUHAMMAD (BABA) MAY ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, GRANT HER JANNATUL FIRDAUSI AMEEN _

150_151


Zare ido Bulama yayi jin an ambace shi haka, abun da be taɓa kawowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login