Showing 189001 words to 192000 words out of 209297 words
kwanta tunda na ganka"
Haka ya saka mata rigar, ta ɗau hijjabin zata saka, ya dakatar da ita ya ɗaga rigar jikinta, ya sake kallon cikim nata, ya sumbaci cikin ta yace "I love you my unborn, karka waharmin da Mum ɗinka kaji Babyna, i love both of you"
Widad ta dinga masa dariya, wai yana surutu shi kaɗai, kamar zasu cinye juna, ko sababbin masoya.
Nurat kam tana fita daga ɗakin, waje tayi amma bata ga Khalila ba, se motocin 'yan sanda dake gurin, dan haka ta koma tsakar gidan, can nesa da ɗakin da su Yusuf suke, ta zauna akan kujerar tsakar gida.
Sedai tana jiyo dariyar su, ta sunkuyar da kanta a tsakanin cinyoyinta, tai shiru tana tunani, tana son Yusuf so na haƙiƙa, tana sonshi saboda Allah, amma tasan tunda ya auri Widad abune me wahala ya saurareta, kuma ga dukkan Alamu Widad ma tana matuƙar sonshi itama, dan haka Yusuf babu lallai ya saurare ta.
A hankali ta fara hawaye, tana gogewa a hankali, tana addu'a a zuciyarta "Allah ka yaye min son Yusuf, Allah ka zaɓamin abunda yafi Alkhairi a rayuwa ta"
Jin abun nasu bana ƙare bane, yasa ta sake miƙewa ta fita waje, tana fitavtarar da Khalil ya dawo, ya kalleta yace "Ta Yusuf harkin fito ne? Ai bamu gaisa da Umman ba"
Nurat tace "Brother mutafi gida"
Yace "meyasa? Kefa kika damu in kawoki"
Nurat tace "ni dai mutafi gida kawai"
Tai maganar hawaye na ƙoƙarin tona asirin dake zuciyarta, a ɗan dirirce yace "ko wani abun Yusuf ɗin yayi mkki?"
Ta girgiza masa kai ta buɗe mota ta shige, cike da mamaki Khalil ya bita da kallo.
Umma ceta shigo layin hannunta ɗauke da ledoji, sedai ganin motar 'yan sanda a ƙofar gidan yasa gabanta ya faɗi, ta dinga nanata innalillahi wa inna ialaihi raji'un, hankalinta ya ɗan kwanta data hangi Khalil.
Ta ƙaraso inda Khalil ke tsaye, tace "Khalil lafiya kuwa? Naga motar' yan Sanda?"
Khalil yace "lafiya ƙalau Umma, sunce min wani aiki sukeyi, Nurat na kawo ku gaisa kuma bakya nanma ashe"
Umma tace "Ai da kun shiga Yusuf yana nan ai"
Yace "Ai ita ta shiga ɗinma, amma ta fito"
Umma tace "A'a ban yadda ba, Nuratu fitowa zaki mu shiga mu gaisa"
Nurat tace "Umma yamma tayi ai"
Umma tace "a'a, ai ga Khalil nan Tare kuke kuma ga mota fito maza"
Nurat bata son tayi sanadin da zata gusar da farincikin dake zuciyar masoyinta, amma babu yadda ta iya, Umma ta haifeta bekamata ta bijirewa umarninta ba.
Nurat ta fito daga motar, tabi bayan Umma suka shiga gidan, sedai suna shiga suka tarar Yusuf da Widad sun fito, yana riƙe da ƙugun Widad suna murmushi cike da kulawa da juna.
Suna yin tozali da Umma, Yusuf ya saki Widad da sauri, ita kanta seda Widad ta tsorata ganin kallon da Umman take musu.
Umma ta kalli Widad tace "kinzo ki sake kulle shin ne kokuwa? Ko prison ɗin kike son ya koma?"
Widad ta kalli Yusuf, ta sunkuyar da kai.
Umma tace "ya kikayi shiru baki bani amsa ba? Kinzo ki sake maida shi prison ne, bayan duk wahalar da ya sha saboda ke, ki kaje kotu kika bada sheda akansa, banda Allah yasa wannan yarinyar Nurat da ɗan uwanta sunyi masa ƙoƙari suma da yanzu shekaru talatin zeyi a kurkuku "
Widad ta ɗaga ido ta jefi Nurat dake bayan Umma da wani matsiyacin kallo, wanda yasa Nurat jin kayan cikinta kamar sun koma bayan ta, a hankali ta silale ta fice ba tare da Umma ta lura ba.
Umma ta kalli Yusuf tace " kai kuma na dawo kanka, mara zuciya kai har abunda yai saura tsakaninka da wannan yarinyar, saboda rashin zuciya tana mace amma ta biyoka har gida? Idan na ƙara ganinta a gidan nan duk abunda nayi mata ita siya, yakamata ma hukuma tai mana tsakani da ita, tunda Allah yasa dai an gane baka da laifi meye kuma na cigaba da bibiyarka, kowa se yayi hanyarsa Allah ya bada lada "
Yusuf yace 'Umma dan Allah kiyi haƙuri, Widad aurenta nayi mata tace, amma..
Umma ta katse shi tace " kai kasan wannan, ni ban san da haka ba, iya sanin da nayi baka da wata mata, Ni Nuratu nake fatan ka Aura, dan se tafi wannan yarinyar sauƙin kai "
Widad ji tayi zuciyarta ta buga da ƙargi, tankar Umma ta soka mata mashi, take taji ta tsani Nurat, dama ga abunda mahaifinta yai mata, gashi kuma yanzu tana bibiyar mijinta, hawaye ya fara zarya a fuskar Widad, a hankali ta sanya takalmanta tai waje.
Yusuf kamar ya ɗora hannu a ka ya kurma ihu haka yake ji, baya son kukan Widad yana matuƙar ƙaunarta, amma Umma na son datse igiyar farincikin dake tsakanin su.
Umma ta kalle shi tace "wato da Nuratun tazo gidan nan wulaƙanci kai mata saboda wannan yarinyar ko? Farar fatarta na ɗaukar maka ido kana nema ka gayamin magana saboda ita ko Yusuf?"
Yusuf ya girgiza kai, Umma tace "duk abun kaga nayi bazanyi dan in citar da kai ba, wannan yarinyar idan ta ƙara raɓarka za'a iya samun matsala, ka manta da ita kawai ka nemi wannan yarinyar Nurat, dan se tafi waccan tausayi, kuma dama kaga Auren naku mutane na shakku a kai, tunda ba kowane yasan da wani kunyi Aure ba, kayi haƙuri ka rabu da yarinyar nan, Allah ya zaɓa maka mafi Alkhairi kaji yaron kirki, bana son abunda ze sake ɗaga mana hankali tashin hankalin da muka shiga ma ubangiji Allah ya yaye mana ya kiyaye gaba, Allah yabaka mace tagari mafi Alkhairi a rayuwar ka "
Ta miƙa masa wata ƙatuwar leda tace " yawwa ga wannan, yadine guda uku masu kyau da shadda biyu, idan anyi sallar magariba dare yayi ka kaiwa magaji ya ɗinka maka, ga takalma nan ma, hadda sabon agogo na siyo maka, ka ƙara akan kayanka, sonake nan kusa ka koma gurin aikinka"
Jiki a sanyaye yasa hannu ya karɓa yace "Nagode Umma"
Ya juya ya shiga ɗakinsa, yana zuwa ya ajiye kayan ya zauna ya dafe kansa yace "ua zanyi da umarnin Ummana, matar da ta dimga ɗawainiya dani tun a zanin goyo harna zama mutum, bani da uwar data fita, sannan ya zanyi da matatat wadda a yanzu haka nauyin kula da ita a kaina yake, haba Umma ki fuskanceni mana"
Yai maganar yana sake dafe kansa dake sara masa.
Nurat kuwa har sukaje gida, bata ce komai ba, juyin duniya Khalil yai yai ta gaya masa abunda ke faruwa amma fafur taƙi, suna zuwa gida ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa ta shiga aikin kuka, tana jin yadda soyayyar Yusuf ke ƙafa tsuma mata zuciya, tana shiga dukkan wani sashe na jikinta, amma tasan ssamun Yusuf idan ba wani iko na Allah ba, abune da baze taɓa yuwuwa ba, ya riga ya mata nisa tunda ya zama miji ga Widad, ko ba'a gayamata ba Tasan Widad bazata zauna da kishiya ba, kishiyarma ita wadda mahaifinta ke da Mummunan tabo a gurin Widad ɗin.
Khalil duk ya shiga damuwa ganin Halin da Nurat ke ciki, a nan falo mahaifiyarsa ta fito ta sameshi tace "Khalil har kun dawo ne? Ina Autar tawa take ne?"
Khalil yace "Ta shiga ɗakinta"
Tace "yaya, da kuka fitan ta ɗam saki jikinta kuwa? Na fuskanci har yanzu Nurat tana cikin damuwa da alhini, bana son rashin walwalrata, gashi ni bani da 'ya mace balle ta samu' yar uwa, ni kuma ba son yawan hira take dani ba, na rasa ya zanyi, Abbanku ma ya faramin magana akan rashin walwalarta wai kowani abu nake mata? Nace masa ya za'ayi in takuramata tana 'yar ƙanwata? "
Khalil yai ajiyar zuciya yace " Mama akwai abunda yake damunta, kuma baze rasa nasaba da halin data tsinci kanta a ciki ba, dole se an bita a hankali "
Mama tace " to shikenan, naga kai taku tazo ɗaya sosai, dan Allah ka dinga kwantar mata da hankali, kana rarrashinta"
"to Mama Insha Allah, bari in shiga inyi alwala magariba tayi '
Ya tashi ya baf falon, uana jin inama ze iya ɗaukewa Nurat damuwar da take ciki.
Widad kam tasha kuka data koma gida, taji ta tsani Nurat bata ƙaunarta sam, ta barwa ranta sedai ayi duk wadda za' ayi, amma bazata bari Yusuf ya auri Nurat ba.
Yusuf ya fita yai sallar magariba ya kai ɗinkin kayansa, ya dawo yana daf da shiga gida wani yai masa sallama, ya tsaya ya amsa suka gaisa.
Mutumin yace "matarka ce ta aikoni, tace ga wannan in baka"
Yusuf ya karɓi ledar daya bashi, mutumin ya tafi, Yusuf ya shiga gida ya wuce ɗakinsa, yana zuwa ya buɗe ledar, sabuwar wayace kar a ciki da layi, tai rubutu a jikin kwalin wayar"
"switch on the phone, and call me Baby, Your wife"
Murmushi yayi cikin rawar jiki ya kunna wayar, ya duba yaga lamba ɗayace a ciki, maimakon ya kirata da wayar, seya kwafa a ƙaramar wayar dake hannunsa ya kirata.
Tana kwance akan gado, tayi rigingine wayar ta fara ringing, ai da sauri ta ɗakko wayar ta ɗaga.
"Hello My Queen"
"meyasa baka kirani da layin dana baka ba?"
"so kike Umma ta tambayeni ina na samo waya?"
"Shikenan, ya kake?"
Yace "lafiya ƙalau, ya ki kaje gida?"
Tai ajiyar zuciya sannan tace "Alhamdilillah"
Yace "Widad dan Allah kiyi haƙuri da abunda ya faru yau kin san"
"I understand, just forget sonake kawai muyi hira da kai, inji daɗi a raina, kaɗaici ya dameni ko Abinci bana iyaci Yoseef, ga bani da lafiya I need you Yoseef, i need your help"
Jiki a sanyaye Yusuf yace 'ki kwantar da hankalinki my wife, Insha Allah inaji a jikina komai ya kusa zuwa ƙarshe insha Allah, kiyi haƙuri karki cutarmin da kanki da Babyna, ki dinga cin Abinci please, karki mana illa "
" toni ya zanyi inci, babu me rarrashina ya bani a baki? Gashi bana samin irin Abincin da nake so, Yoseef dan Allah ka bawa Umma haƙuri ka dawo gare ni please "
" karki damu, Umma zata soki tana da sauƙin kai sosai, Insha Allah zam sam abunyi, amma dan Allah kici Abinci kinji Wudas ɗina "
" Wudas ko? " tai maganar a Shagwaɓe.
Yusuf yai dariya yace " ba haka Hari take ce miki ba? "
" to kai ita ne? Kasan meze faru kashe wayar, zanje inyi wanka video call nake son muyi in ganka "
Yace" shikenan, as you wish Babyna"
Yusuf ya rungume wayar nan.
Ko takan Abincin dare Yusuf bebi ba, Widad ta sake kiransa video call, ta saki dogon gashin nan nata, tana shafa mai.
Yusuf yace "Cikin nan ba ƙaramin kyau ya miki ba fa"
"Allah ne yayi cikin nan baze fita ba, amma allurar zubar da ciki Bulama yasa ayimin"
"cikin nawa aka so zubarwa?"
"Eh mana, sun kusa kasheni fa, akwai labari idan mun haɗu fa"
Yusuf yace "Allah sarki babyna, mun sha wuya sosai, ko da kikazo kotu kallo ɗaya nai miki na gane ba'a kwanciyar hankali kike ba"
Widad tace "bar wannan zancen kawai, kar ka ɓatamin rai ka rusa mana farinciki"
Yai murmushi yace "to shikenan, kina min ƙwalele da gashin nan fa"
Tai murmushi tana masa gwalo ta waya, tace "ziro hannu ka taɓa mana"
"Inama in rufe idona in buɗe in ganni a kusa dake, in tayaki shafa man nan"
"Harka tunamin lokacin da muna ƙauye, gaskiya Yoseef kana da haƙuri kayi haƙuri dani sosai, shiyasa ka taka wani gagarumin matsayi a zuciyata my love"
Har tagama shirin kwanciya, ta kwanga video call suke, ba tare da sun sam dare yayi ba.
Ƙarfe biyu da rabi lokacin ne Umma take sallar dare, ta fita alwala ta dinga jin maganar Yusuf ƙasa ƙasa, ta leƙa tagarsa ta hangoshi akan gadonsa ya tasa screen ɗin waya a gaba yana murmushi.
"Ki kwantar da hankalinki, Insha Allah zuwa jibi zanzo in ganki masoyiyata"
"Allah ya kawo ka lafiya, zaman kaɗaici ya isheni Yoseef, babu kowa a kusa dani fa"
"Ai mace miki zanzo insha Allah, inzo in ganki inji labarin da kike son gayamin, inji yadda akayi kika samu wannan tabon haka a jikin ki, ki kwanta kiyi bacci dare yayi fa"
Tace "ok come closer, hug me and kiss me, then we sleep together"
Yusuf yai murmushi yace "nayi missing ɗinki Widad, yai kissing ɗin screen ɗin wayar yana lumshe ido, ƙarshe ya kashe wayar ya ajiye, ya rungume pillow sosai a jikinsa yana lumshe ido.
Umma ta jinjina kai ga wuce banɗaki domin yin alwala.
Da safe Yusuf ya tashi yana ta nishaɗi kamar bashi ba, Umma tana kallonsa amma ba tace masa komai ba.
Ranar da yayiwa Widad alƙawarin ze je yana ta kallon agogo, yana zaune Umma ta sashi a gaba yaci Abinci, ya gama ci wayarsa ta fara ringing, sedai ba suna amma yaƙi ɗagawa, Umma tana kallonsa.
Can yace "Umma bari inje ɗaki zan kwanta bacci"
Umma tace "ɗakko pillow ka kwanta a nan"
Ba haka yaso ba, amma haka nan ya haƙura, ya ɗakko pillow ya kwanta a ɗakin Umman.
Aikuwa babu daɗewa bacci ya ɗaukeshi, saboda dama dare yake rabawa yana soyayya.
Umma ta ɗakko mafici tana masa fifita, Kasancewar an ɗauke wuta gashi ya fara gumi.
Sedai tun ba'aje ko'ina ba Yusuf ya fara surutan bacci.
"My Wife, kiyi murmushi mana yarinya fushi baya miki kyau fa"
Umma ta juya tana kallonsa, iya saninta dashi tun yana yaro ƙarami, baya surutan bacci, amma yau da ranar Allah yana bacci yana surutu akan wata.
Bata gama mamakin ba ya cigaba
"Baby ki dena kuka, bana so fa, kinga baki da lafiya, kuma Gwaggo yau zata kawo mana kunun tsamiya, ai zaki sha ko?"
Suleiman ne yai sallama a gidan, Umma ta amsa masa, ya shigo ya zauna yana faɗin "Lallai ɗan gata, yana bacci Umma na masa fifita, tashi c
Yai maganar yana taɓa Yusuf, Umma tace " ze tashi kuwa, yana mafarkin soyayya "
Suleiman yace " Soyayya kuma? "
" Eh mana, se surutai yake shikaɗai"
Suleiman ya daddaki Yusuf, Yusuf ya buɗe ido a hankali, ya tashi zaune yace "Yallaɓai dama kaine?"
"Eh nine, ka tashi ka shirya mutafi"
Yusuf yace "mutafi ina?"
Umma tace "gidansu Nurat zaka je, Munyi waya da Khalil bata da lafiya!!!"
Wayat Yusuf ta shiga ringing, ya kalli wayar lambar Widad ce, tana can tana jiransa
AMANA! AMANA! AMANACE!!!
DUK WANDA YACI AMANA, AMANA ZATA CISHI
AYSHERCOOL
07063065680
12/7/21, 11:04 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
158_159
Yusuf yace "Amma Umma, da wani guri nake son zuwa"
"zaka bijirewa umarnina ne?"
Yusuf ya girgiza kai, Umma tace "to tashi maza, jeka kintsa kazo ku tafi"
Jikin Yusuf babu daɗi, ransa sam ba daɗi yaje yai wanka ya shirya ya fito.
Umma tace "Suleiman, dan Allah ga Shi nan, ka tabattar yaje dan Allah ga kuɗi ku sai mata ko kayan marmari ne, aje a duba ta, gaida mai gaisheka ko baze amsa ba"
Yusuf dai bece komai ba yai waje, wayarsa na cigaba da ringing.
Suleiman ya fito ya shiga motar suka tafi, Umma ta maida Suleiman kamar ɗanta Yaya a gurin Yusuf, dan shima tana masa hidima shida iyalinsa, tunda yaita faɗi tashi akan case ɗin Yusuf.
Yusuf be kula Suleiman ba, gaba ɗaya ransa a ɓace yake, ya ɗakko wayarsa ya kira Widad, tana ɗagwa ta fara mita "Haba Yoseef, inata kiran wayarka kaƙi ɗagawa, na shirya ina ta jiranka fa"
Tai maganar cikin Shagwaɓa.
Yusuf yace "Am sorry, wata fitace ta gaggawa ta kama ni, amma idan na kammala zanzo insha Allah, ki kwantar da hankalin ki kinji my Wife"
Tace "to naji, ka siyomin abu me daɗi, ina jin kwaɗayi"
"To shikenan, zanje ƙauye in Hari tayi girki ta zubo in kawo miki"
A tare sukayi dariya, yace "shikenan sena zo"
Ya maida wayarsa ya ajiye, Suleiman yace "Yusuf zaka karya maganar Ummanka kaje inda Widad take kenan?"
Yusuf yace "yallaɓi, yakamata ka fahimceni Widad fa ita kaɗai take zaune a gidan nan, babu kowa kuma ina tare da Aurenta, duk haƙƙoƙinta suna kaina, Umma taƙi bani dama in mata bayani, bayan haka Widad tana buƙatar kulawa, duk ta kumbura saboda ciwon zuciya da hawan jini, kuma.. Kuma tana ɗauke da tsohon ciki fa" Yusuf ya ƙarasa magaanar cike da jin kunya da kuma damuwa.
Suleiman yace "hakane, yakamata ace Umma ta fuskance ka, amma tanaa gudun abunda ze sake kawo barazana ga rayuwarka ne, amma kabi a hankali, zata fahimta Insha Allah"
Yusuf yace "Allah yasa, amma ni batun Auren nam da Umma ta bijiro dashi, dan Allah Yallaɓi kasa baki, idan har nace zan Auri Nurat Widad zata rabu dani, kuma ina matuƙar son mata ta"
"Shikenan nagane halinda kake ciki, amma Nurat ma abun tausayi ce"
Yusuf yace "Nasani, badan kishi irin na Widad ba da zan iya auren Nurat, saboda tana sona sannan bata da wani aibu, sema nine nake da aibun da za'a gujeni saboda shi"
Suleiman yace " aibun me kenan?"
Yusuf yace "bakomai, manta kawai"
Suka cigaba da hirarsu, har zuwa gidan su Nurat.
Koda dukaje Khalil baya gida, megadi yaje ya sanar da zuwansu, aka musu iso.
Sedai Suleiman yace baze shiga ba sedai Yusuf yaje, haka kuwa akayi aka masa jagora har falon da aka saukesu wancan zuwa.
Yayar maman Nurat ce ta fara zuwa, Yusuf ya gaisheta cikin girmamawa, sannan ta koma ta turo masa Nurat.
Yusuf yana nan zaune yana sake kallon wayarsa, yana addu'a Allah yasa kar Widad tayi fushi, yaji ƙamshin turaren Nurat, ya ɗaga kai ya kalli Nurat, duk ta rame kallo ɗaya zaka mata kasan bata da lafiya, a hankali take tafiya tana ɗan lumshe ido irin na marasa lafiya, ta ƙaraso ta zauna a kan carfet.
Yusuf ya dawo kujerar da Nurat ke zaune a ƙasa, ya kalleta