Showing 108001 words to 111000 words out of 209297 words
son zuciya irin naki haka kika mayar min da 'ya' ya, yarinyata ta kalleni tana gayamin wannan maganganun, dama haka mukayi dake?"
Hajiya Halima tace "kaga, dan Allah karka ɗagamin murya a gaban ma'aikatana, kazo mu shiga daga ciki ayi duk wacce za'ayi mana"
Ya bita suka shiga cikin falo, Amal ta tafi gurin Ramlah ta buɗe ƙofar ɗakin nata ta shiga, ta sameta tana zaune tana danna waya, Amal tace
"Ramlah bekamata kiyiwa mahaifinmu haka ba, ai duk lalacewarsa shine ya haifemu"
Ramlah tace "wait, wai dan Allah dagaske wannan bagidajen shine mahaifinmu?"
"Ramlah ki gyara maganarki fa, wallahi babanmu ne ya zaki manta fuskarsa, wallahi babanmu ne"
"gaskiya sedai Babanku, kalli mutum a koɗe kamar baya cin Abinci, kalli suturar jikinsa yazo yace shi babanmu ne, gaskiya niba ubana bane, ai abun kunyane mu nuna wannan muce ubanmu ne, bayan duniya tasan da sunan Daula muke amfani, ai kawai babanmu ya mutu, amma wannan ai be kai mutum ba balle ace masa uba"
Amal tace "ikon Allah, wallahi Ramlah kina sane, babu yadda za'ayi kice kin manta kamanin mahaifinmu, dukda tunda muka bar gurinsa bamu kuma zuwa ba"
Ramlah tace "ke ina sane wallahi, na gane shi sarai, amma ni karan kaina kunya nakeji in kalle shi ince mahaifina ne, haba mutum a tsiyace kamar matafiyin da guzuri ya ƙare masa, kuma ya tsaya ze fara kora bayani a gaban wannan gidadawan, salon su raina mutane"
Amal tace "lallai Ramlah, ke abun naki babbane ma"
"Haba shu'aibu, ya zakazo a wannan lokacin da ake tsakiyar tarzoma da tashin hankali? Kazo babu aike bau Sanarwa haka akeyi, kuma ka tsaya kana neman ka tona min Asiri a gaban mutane, kai har yanzu bazaka waye ba?"
Shu'aibu ya kalleta yace "dama ina zan waye, mara mutunci dama haka mukayi dake? Nace haka mukayi dake? Akan yarjejeniya mukayi komai, amma da yake ke butulu ce, kinzo kin samu jin daɗi kin watsar dani, kinyi watsi da Yarjejeniyar da mukayi, shine nazo in miki tuni, ki cika Alƙawari sannan ki bani 'ya' yana"
"wane 'ya' yan naka, malam karma ka ɗakko wannan maganar, dan ba zata yuwu ba, me ka sani na 'ya' yan naka, seda na gama wahalar? Lokacin mora yayi sannan kace in baka no, baze yuwu ba"
Shu'aibu yace "kin san Allah Halima, sekin bani 'ya' yana gaba ɗayansu bazan bar ko guda ba, kuma sekin cika Alƙawarin da mukayi daku"
Tsaki tayi tace "bani account number ɗinka, zan baka dubu ɗari biyar, ka tafi ka bani guri dan Allah"
"Ni zaki kalla ki bawa dubu ɗari biyar, ki riƙe kayarki amma ki saurari abunda ze biyo baya"
"Kaga dan Allah karmuje ga haka, ka zauna muyi magana, Alƙawari da mukayi fa har yanzu wannan kuɗi basu samu ba, ya kake so inyi ne"
Shu'aibu yace "ƙarya kike, shakrar ki nawa a gidan nan, kima nufin duk zamanki a gidan nan baki samu komai ba, aiko duk jikina kunne ne bazan yadda ba Wallahi"
"Wai kai baka san 'yarsa itace ta hana ruwa gudu ba,? dan Allah karka ɗagamin hankali ka bani account number, zan samaka million ɗaya"
Shu' aibu yace "ashema bani da hankali, kusan shekara goma sha, ko ficika bata shiga hannuna ba kice zaki ban million ɗaya, baki nemi sulhu ba tabbas, kuma abunda ze biyo baya baze miki daɗi ba na gaya miki"
Hajiya Halima tace "kaga shua'aibu bazaka zo ka ɗagamin hankali ba Wallahi, yanzu ma daka zo a wani zullumin bala'in nake, ko dai ka haƙura da abunda zan baka kokuma ka haƙura, dan ban san ya kake so inyi ba, yarinyar daza'a karɓi dukiyar a hannuta ba'a san inda take ba, shi kansa me gidan ba'asan a inda yake ba, komai yana nema ya jagwalgwale min, kuma kazo kana gayamin maganar banza, dan Allah ka sauraramin"
"Naji zan saurara miki, amma nima ki saurari abunda ze biyo baya, kin sanni kin sam abunda zan iya aikatawa, wallahi nima zan baki mamaki, zan ƙara miki matsala akan wadda kike ciki, sannan ki gayawa 'ya' yana ina nan zuwa in ɗauke abuna"
"ka ɗauki wa? Can kaje ka nemi 'ya' yanka, karka ƙara ce mana 'ya' yanka, can ka nemi 'ya' yanka malam" Ramlah da ta fito daga part ɗinta take faɗa.
Shu'aibu yai murmushi yace "Allah sarki yaro yarone, Halima na fuskanci wannan yarinyar halina ta ɗakko, Rawar kanta da zafin kanta kamarni, amma ki gargaɗeta in ba haka ba, abunda ze biyo baya ke dasu baze muku daɗi ba Wallahi"
Mummy tace "ke Ramalh, wannan fa mahaifinku ne, kidena gayamasa maganar da kika ga dama kinji ko?"
"wallahi karki ƙara haɗani dashi, can ya nemi yaransa ba dai niba, uwar meya maganta mana a rayuwar daze zo yana wani mu 'ya' yansa ne, dan Allah mu yayi ya wuce ya bamu guri, kidena ssaurarensa ki fita a samo mafita akan ɓatan Anwar, idan ba hakaba kika biyewa wannan koɗaɗɗen mutumin, komai ze iya faruwa, Anwar ze iya tona miki asiri idan wannan be tona miki ba"
Zaro ido shu'aibu yayi yace "Anwar ɗin ne ya ɓata? Halima dagaske ne abunda nakeji?"
A fhaace tace "Eh gaske ne shu'aibu, duk akan a samu kuɗin nan, Anwar ya gudu ya bar gidan nan, se me ina nikaɗai naita ɗawainiya dasu ina ruwanka dasu, dan Allah ka barni inji da kaina"
"zan barki kiji da kanki, zan tafi a yanzu bazan kuma dawowa ba se a lokacin daya dace, ko kuma in cigaba dayi miki aike, zan baki account number na, ina buƙata kuɗi naira million hamsin, nan da kwana bakwai idan baki turamin wallahi, wallahi abunda ze biyo baya baze miki daɗi ba"
Ramlah tace "ai se kazo ka ƙwata ai, tunda kai ka tara mata"
Aikuwa ya shammaci Ramlah ya wanketa da mari, jikinsa na rawa kamar wanda aka kaɗawa gangi yace "da uwarki nake magana, ba dake ba ko ita lokacin da tana hannuna idan ina magana tana magana, tasan me yake biyo baya, idan kin manta dan lokacin kina ƙarama gara in tuna miki, Halima ki gargaɗeta ki gaya mata abunda zan iya, idan na kuma zuwa gidan nan, taimin tsinin baki sena yagalgalata a gurin nan, kuma nan ba gidana bane, zanzo in ɗauke ku, lokaci yayi da zan mori abunda na haifa nima"
Ramlah ta zabura zata yi magana, amma Hajiya Halima ta dakatar da ita, ta hanata, shi kuma ya juya ya fice yana huci yana sauke numfashi.
Tunda garin Allah ya waye, Widad take nan nan da Yusuf, se wani lallaɓashi take tana tarairayarsa, daya tashi da safe, idanunsa sunyi ja sosai sun ɗan kumbura, saboda kukan da yayi jiya, da ta kalli Yusuf se taji kamar ta fashe da kuka, idan ta tuna labarin daya bata, da irin wahalar da ya sha shida mariƙiyarsa, sun sha wahalar rayuwa sosai.
Ta ɗakko kunu, ta dinga ɗebowa tana bashi a baki, Yusuf yace "yau kuma nina koma jaririn? Se wani lallaɓani kike?"
"ba dole in lallaɓaka ba, nima kana lallaɓani ai, ko baka sone?"
Yace "ina so mana, ai gara kiyita lallaɓanin"
Ta dinga bashi Abinci a baki, yana ci yana lumshe ido, dan dauriya kawai yake, har yanzu zuciyarsa babu daɗi, gaba ɗaya a cunkushe ransa yake, amma ya daure yana murmushi dan kar ya ɗaga mata hankali.
Ta ɗago ido taga ya ƙura mata ido yana kallonta, ta miƙa masa kofin kunun bakinsa, kawai taga idonsa ya cika da ƙwalla, tasan dauriya yake kawai, amma ransa babu daɗi.
Ta ajiye kofin tace "Yoseef menene kuma?"
Girgiza mata kai yayi, alamar bakomai, "da komai Yusuf menene ke kuma?"
Kawai ya lumshe idonsa ya bawa hawayen daya taru a idonsa damar gangarowa, ɗaya bayan ɗaya suna zarya a fuskarsa, yasa hannayensa biyu ya tallefe fuskarsa, hawaye na cigaba da bin fuskartasa.
Itama hawayen ne ya shiga zubo mata, tasa hannu ta janye masa hannayen daya rufe fuskarsa, ta janyo kansa jikinta, tana son rarrashinsa amma tama rasa me zata ce masa, aikuwa ya kwanta sosai a jikinsa, yana kuka hadda sheshsheƙa, kai kace wani ɗan yaye ne.
"Haba Yoseef, habe Yoseef is ok please, kana son wani ciwon ya kama min kaine? Idan ciwo ya shige ka ya zanyi, baka son kaga Lokacin da zamuyi building namu family ɗin, Allah yayi maka gata daya baka rai da lafiya Yusuf, Insha Allah zan share maka hawayen ka a rayuwa, bazan ƙara bari a maka gori ba, komai ya wuce ai, ya zama tarihi tunda ba shiri duk da kowanne mu ya fidda ran samun abokin rayuwa amma Allah ya haɗamu ya ƙaddara aurenmu, ba tare da mun shirya ba, tabbas ƙaddararmu tana kamanceceniya da juna, ni wallahi jinake dama ni na samu uwar riƙo kamar ummanka, Yoseef kana kallo ni ga gatan ga komai, amma inaji ina gani aka maidani mahaukaciyar ƙarfi da yaji, aka haɗani da larurar Ƙwaƙwalwa da zuciya, ga rashin kwanciyar hankali, ina so kamanta da wannan abun kamar be faru ba, kodai tunanin Salman kake ne? "
Duk da kuka yake, seda ya ɗan murmusa sannan ya girgiza kai yace " inda ke babu macen da Yusuf ze tuna"
"to ina son ya zamana in dani, babu damuwar da yuzaraef ze tuna"
Yace "to Allah yasa hakan"
"Ameen ya Allah, Amma ai yanzu zaka yadda mu koma gidanmu ko?"
Yusuf ya girgiza kai, alamar a'a, Widad tace "saboda me?"
"Saboda ke nake so ba dukiyarki ba, ko abunda kika mallaka, dukiyarki ta kice mallakinki ce, dan haka zan sai mana gida daidai ƙarfina, in cigaba da aikina da sana'ata in riƙemu, ai zaki zauna dani da talaucina ko, duk abunda zan baki zaki karɓa ki zauna dani? "
Yai maganar yana kallonta, tai murmushi tace " na zauna da kai a ɗakin ƙasa, duk abunda ka banj na karɓa naci, kuma muke rayuwar mu a haka, ina ne zaka kaini bazan bika ba, amma gaskiya ni bana son aikin nan naka"
"Saboda me?" ya tambaye ta
Ta ɗanyi shiru sannan tace "Yoseef, DSP Bashir shine Abbanka da aka kashe saboda case ɗin Ammina fa"
Yusuf yace "na sani"
Kallonsa tayi tace "ya akayi ka sani"?
Yusuf yace "tun lokacin ina miki aiki, na nake bincike akan statement ɗin kashe mahaifina da akace 'yan fashi sunyi, inata tunanin abun, kina bani labarin ki Nagano musababbin kisan Abba, kuma na gane dalilin da yasa da najewa Umma da batun aiki a gidanku, take cemin bata so, dukda bamu taɓa hirar da ita ba"
Widad tace "Amma ya akayi baka gayamin ba?"
Yai murmushi yace "a gurinki na koya ai"
"Yoseef Kayi haƙuri kaji, ka dena koke koken nan hak, kana karyamin zuciyata sosai, ka dena kuka kaji ɗan gidan Umma"
Ya ɗan ja kumatunta yace "tom insha Allah zan dena"
"ka dena ko zaka dena"?
"Nima ban sani ba, amma ina fatan Allah ha haɗani da wani, wanda yake yana da alaƙa da iyayena, ko 'yan uwana komai talaucinsa ina son in samu in ga wani daga dangina, koa yake is not possible, tunda babu wanda ya sanni a dangin nawa, kuma nima ba wanda na sani "
Widad tace " bazaka dena kukan ba kenan? Ba gani ba, ba nace maka zamu haɗa namu family ɗin ba, mu haifi yara ga Daddy, ga Umma gamu da 'ya' yan da zamu haifa, ba Family ya haɗu ba kenan?"
Yusuf yace " bazaki gane ba Baby, anyway nagode sosai da kulawarki, banjin wani bayan Ummana ya taɓa min rarrashin daya shigeni kamar wanda kikamin, ban taɓa zama nayi makamancin hirar nan da wani ba, duk alaƙata dashi kuwa, ko Umma bama wannan hirara da ita, balle wani saboda kar in ɗaga mata hankali, taga hawayena dan kar taga kamar ta gaza da kula dani ne, dan nasan tabbas idan na saɓamata Allah baze barni ba, ta shayar dani ta bani duk wata kulawa ta uwa da ɗa, kece kawai nayi wannan hirar dake, shiyasa I express all how I feel in my heart, kuma naji daɗin gayamikin da nayi, naji na rage kaso mafi yawa na damuwata thank you sweet heart"
"Allah sarki mijina, kayi haƙuri kaji, tamu jarabatar kenan, amma ko abokinka Abbas baka taɓa yiwa zancen ba?"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a ban taɓa yi masa ba, amma me yasa kika tambaya?"
Widad tace "saboda na tsane shi, gaba ɗaya siffar munafukai ce dashi haushi yake bani, shiyasa nasa aka rabaka dashi, aka maida shi nesa da gurin aikinka"
"Amma Widad meyasa? Abokinane fa ya bani gudunmuwa sosai fa a harkar aiki da sauran mu'amalar rayuwa"
Widad tace "Oho nidai na tsane shi, kuma wallahi idan ya kuma raɓarka sena ɗaureshi"
Cikin mamaki ya kalleta yace "but Baby why"
"Z" ta bashi amsa tare da ƙura masa ido, alamar bata son zancen.
"Yanzu za kamin Addu'ar in samu Babyn, kokuwa har yanzu baka son in haihu da kai"
Ya girgiza kai yace "Ai magana ta ƙare, tunda har kika amince dani dukda kinji labarina, Allah yabamu masu albarka Babyn Yoseef"
Washe baki tayi tana murmushi, ta rasa mema zata yi dan murna, kawai ta rungume Yusuf ta haɗe bakinsa da nata tana kissing ɗinsa, Yusuf ya rungumeta shima yana kissing ɗinta suna murmushi, daga nan kuma aka shiga wani bigire daban ..... (Nikuma na fece 🚶 🚶 🚶)
Bayan fitar shu'aibu Halima a fusace ta hau Ramlah da faɗa
"Ramlah kinyi haukane? Koba komai mutumin nan mahaifin kune? Kin san hatsarin dayake dashi kuwa? Ko dan kuna ƙanana na bar gidansa baku san irin halayensa ba, shu'aibu da kike ganinsa bashi da imani, bashi da tausayi tsohon ɗan dabane gawurtacce makuwa kuma matsafi, idan kika zaƙe wallahi ze iya kauda ke, dan akan rigimar gonar gado har ɗanuwansa uwa ɗaya uba ɗaya ya kashe, dan haka ki kiyayi wannan tsinannen bakin naki, wanda besan yakamata ba kina zaƙewa dayawa, tynda kika ga ina binsa sannu sannu, nasan hatsarin dayake da shine, idan kinƙi ji bakyaƙi gani ba, idan kin gadama ki gyara idan bahaka ba, matakin daze ɗauka baze mana daɗi ba dagani harku"
Ramlah tace "wallahi, wallahi ba ruwana da hatsabibincinsa, tunda ya haifeni ze gane ya haifi uwarsa a hatsabibanci, harni ze ɗaga ƙazamin hannunsa duk faso ya mara? Zan nuna masa ya haifi 'yar da zata kawo ƙarshen hatsabibancin da yayi a rayuwarsa, besan wacece niba ze gani"
"Ke rufemin baki, bana son cika baki kin san shi rashin jin da yayi"
Ramlah tace "shi ta shafa bani ba, but he must pay for what he did"
Tai gaba fuuu tana ci gaba da masifa.
Hajiya Halima ta girgiza kai tace "Amal ɗakko mayafinki, kizo ki rakani gurin Alhaji Haruna, zan kira shi a waya yanzu, idan yana nan muje mu sameshi ayi maganin wannan matsalolin"
Amal tace to, ta tafi ɗakko mayafi a ɗakin ta.
Gidan Alhaji Haruna sukaje, aka musu iso part ɗinsa, yana zaune yana kallon labarai a tashar Al Jazeera.
Suka samu guri suka zauna, tunda suka shigo yake bin Amal da kallo, kamar tsohon maye.
Hajiya Halima tace "gurinka nazo"
Yace "yaukuma da wacce kikazo? Danke kullum cikin rigima kike"
Hajiya Halima tace "nikam duk a bar wannan maganar, yaron wajena daya ɓata ba sace shi akayi ba, guduwa yayi daga gida, kuma baun takaicin shine, ya gano abubuwan da nake aikatawa, dan hara takadda ya bari"
Alhaji Haruna yace "Halima kina me haka ta faru? Garin yaya yasani, wannan yaron naki me kama da ustazai kin san ze iya tona mana asiri fa"
Halima tace "hmm wallahi ban san yadda akayi ya sani ba, shekara Goma ina ƙumbiya ƙumbiya muna wannan harƙallar tare, amma be sani ba, ban san wane munafikin ne ya gaya masa ba, kuma ma ba wannan ba ɗazu fa uban 'ya' yana yazo"
Yace "Wake nan?"
"Shu'aibu mana, koka manta bisa yarjejeniya da aka yi dashi ya sakeni, kuma tunda muka rabu, ba'a cika masa Alƙawarin ba, dan haka yazo yana barazanar karɓe yaransa, kuma wai sena tura masa wasu maƙudan kuɗaɗe koya tona mana Asiri"
Alhaji Haruna yace "toki tura masa kuɗin mana, ko kin fi son asirin naki ya tonu?"
Hajiya Halima tace "wace irin maganace wannan, kafa san hatsarin da mutumin nan yake dashi fa"
Alhaji Haruna yace "lallai akwai matsala gagaruma makuwa, amma yanzu abunda za'ayi ki saurareni, zamuyi magana dasu, yadda aka yanke zan miki magana"
Hajiya Halima tace "to shikenan, amma dan Allah kuyi maganar da wuri"
Yace "shikenan, karki damu wannan ma yarinyar kice ne? Naga harta fi yayarta kyau"
Hajiya Halima tace "eh itace 'yar auta ta ai, daga Ramlah se ita"
"Masha Allah, yaran naki masu kyau, sunfi kama da yayarta, Anwar ne ban san kamannin wa yayi ba"
Hajiya Halima tace "kamanin Ubansa yayi, wasu lokutan kuma dani yake kama"
Alhaji Haruna yace "A' a baya kama da shu'aibu sam, kamarsa daban shima"
Hajiya Halima tace "Amal jeki falo ki jirani kinji"
Amal ta miƙe tana haɗe rai, saboda kallon da Alhaji Haruna yake mata.
Tana fita Hajiya Halima tace "Anwar fa ubansa daban shima, dana rabu da mijina na fari akwai cikinsa ko wata ɗaya beba na auri shu'aibu, na haifeshi a gidansa amma ba shine ubansa ba"
Alhaji Haruna yace "ikon Allah, to waye nasa uban?"
"kaga a bar maganar nan kawai, ba wanda na taɓa gayawa se kai duk yadda kukayi se muyi waya"
Ta miƙe ta fito, ya biyo bayanta yana sake bin Amal da kallo, kamar wani maye.
Saleh yayi 'yar siyayyar daya saba yi, ya shirya domin kaiwa su Widad ziyara, ya tafi tasha da nufin ya hau mota, da yake tafiyar dare yake yi in dai zeje garin dasu Widad suke, ya zuba kayansa a motar haya, ya zaga banɗakin tasha domin ya kama ruwa, yana fitowa yaji an shaƙa masa wani abu anyi sama dashi, daga nan be sake sanin inda kansa yake ba se......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya,