Showing 84001 words to 87000 words out of 209297 words
da zarar ya fara rarrashinta ta kan manta ɗinbin damuwarta, tayi wani irin sabo na bazata da Yusuf, wanda har take jin ya zata kasance idan ta koma gida, Yusuf ya nesanta ida?.
"Yayana, zaka dawo gidanmu da zama dan Allah"
"meyasa kika dage sena koma gidanku da zama?"
"Saboda Halima zata bar mana gida, da kaina zan samowa Daddy mata ya aura, zaka dawo gidanmu ko?"
"Meyasa kika damu sena dawo gidanku bayan bakya sona?"
"Nima ban san dalili ba, sedai ina jin a jikina, rasa ka a rayuwata babban giɓine, kuma tamkar rasa garkuwa ne a gareni"
"Nima rashinki a gareni babban giɓine, saboda na kamu da makauniyar soyayya cikin bazata, amma ban saniba ko zaki iya cigaba da zama dani idan kika san wani abu game da rayuwata"
"Ni dai koma meye, dan Allah ka zauna a gidanmu idan mun koma kaji"
Ta maganar cikin Shagwaɓa tana kallonsa, "Babyna wannan wane irin kallone haka kikemin? You look so cute da kika juya idonki"
Kamar ƙaramar yarinya ta kuma cewa "dan Allah kec zaka dawo mana"
Yace "sedai in dawo im cigaba da kaiki unguwa, ni nafi son aikina"
"Aikuwa demotion zan maka, ka koma gadin ɗakina"
"Bakomai in dai hakan zesa in dinga ganinki"
Yai maganar yana saka hancinsa a wuyanta.
Ji suke tamkar suka ɗaine a duniyar, Kasancewar gidan ba kowa dan haka hankali kwance suke soyayyarsu a tsakar gida, basu san Hanne tana ɗaki tana jiyo dariyarsu ba, dan har leƙsensu take ta taga tana share hawaye.
Anwar yayi tunanin bari ya tsaya a gidansu Nurat su gaisa, kwana biyu kota waya basa haɗuwa dan bama hawa yake social media ba sosai balle su gaisa, sannan su jajantawa juna abubuwan da suke wakana, sedai a bakin gate megadi ya tareshi yace "wa kake nema ne?"
Anwar yace "gurin Nurat nazo"
Megadin yace "baka da labarin abunda ya sameta wancan zuwan naka ne? Mahaifinta seda ya kusa halakata, ni ban san hali irin na mutumin nan ba, dan haka yun wuri kabar gurin nan tun kafin kaja mata wata wahalar"
Mamakine ya cika Anwar sosai da jin abunda megadin yace, amma yace "Shikenan, nagode sosai, dan Allah ka gayamata nazo mu gaisa ne kawai, kace ina gaishe ta sosai, sannan idan ta samu lokaci ta taɓani a waya se in kirata"
Megadin yace "Shikenan, zan gayamata wannan karka damu kanka dan dai saƙo"
Anwar ya cika da mamakin me zesa a hukunta Nurat dan yaje gurinta, alhalin mahaifinta be nuna masa komai ba har gaisawa sukayi dashi, amma ace an hukunta ta kuma bata gaya masa ga abunda ya faru ba.
Haka yakama hanyar gida, yanata zancen zuci, yana danja a tsaye yana ta tunani a ransa kamar ance ya ɗaga kansa, ya hango Ramlah a farajiyar wata plaza, da Fahad da wasu maza suna ta shan shisha, kayan jikinta sun Matseta sosai kamar ba 'yar musulmi ba, abun ya ɗaure masa kai ya sake mustsustuke idonsa ya kalli gurin, babu ko tantama itace, ya dafe kai yace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Mummy kina me Ramlah ta lalace haka? Kalli yadda ta koma"
Motarsa ya fizga a guje yai gida, zuciyarsa na wani irin tafasa kamar ta tsaga ƙirjinsa ta fito dan baƙin ciki.
Sedi yana zuwa gidan, ita kanta Mummyn bata nan gidan babu kowa se masu aiki.
Ya zauna a falo yana jin zafi akan sakaci irin na mahaifiyarsu, kuma da yayi magana taji haushinsa, amma yau kome ze faru seya ɗau mataki akan Ramlah.
Tun la'asar yaga Ramlah, amma har bayan isha'i babu wanda ya dawo gidan, yana nan zaune Yaji ƙararar mota ya leƙa, ya hango Ramla ta fito da ƙyar take iya buɗe idoma, saboda azabar buguwar da tayi, amma a haka ta tuƙo mota zuwa gida.
Ta riƙo takalmanta a hannu da jakarta, tana tafe tana gware da bango harta shigo falon.
A zafafe Anwar ya kalleta yace "daga ina kike?"
Cikin maye tace "Ni.. Ni...... Ni....... Fa na inda naje, kawai naje cin... Cin Abinci ne a w. Wa. Wani restaurants that's all"
Kwaɗamata mari yayi, wanda seda ta dawo hayyacinta na 'yan sakanni, ya zare beilt ya dinga dukanta yana ƙwallo da ita, seda yayi mata kaca kaca ya tabattar ta daku sannan
yace "kaiconki Ramlah, kin biyewa wannan ɗan iskan kina lalacewa, dama Aurenki zeyi da sauƙi wataƙila ya shiryu a sanadin ki, amma kawai kin biye masa kin ɓata rayuwarki a banza a wofi kaiconki Ramlah, yanzu kin riga kin ɓata rayuwarki, ke ba aurenki zeyi ba kuma babu wani mutumin kirki daze yadda ya haɗa zuriya dake, tunda kika zaɓi rayuwar shaye shaye da lalacewa"
Hajiya Halima ce ta buɗe ƙofar falon, ta shigo ita da Amal, sedai tayi tozali da Ramlah a baje a gurin fuskarta duk a kumbure, saboda dukan da ta sha, gashi a hakanma maye take yi.
"Lafiya mezan gani haka Anwar?"
Cikin ɓacin rai Anwar yace "Mummy ɗazu a danja, na hangeta a harabar wata plaza suna shna shishsa ita da maza, da wannan sakaran Fahad ɗin mara tarbiyya, kuma ta dawo gidan nan tana maye"
"Kuma shine zaka mata wannan dukan, idan ka kashe ta kuma fa kalli yadda ka daketa, idan kaji mata rauni kace baka san yadda akayi ba?"
"Mummy, amma yanzu laifin Ramlah bekai a hukunta ta ba? Shaye2 tana mace, kallifa a hakan ma maye take yi, bata san meke faruwa ba, kuma amma a haka kike cewa meyasa na daketa?"
"Rufemin baki ko in tsinkeka da mari, baiwar ubankace ita da zaka mata wannan dukan? Kai duk laifin da kake yi haka nake kamaka in jibga kamar jaki? Ka ɓatawa yarinya halittun fuska, kuma kana cemin maye take, haka ake mayen zafin duka dai yasa take surutai, dalla wuce ka bani guri babban banza kawai "
Anwar yace" Amma Mummy kina gani......
A fusace tace "fitarmin daga falo tun ban rama mata abunda kayi mata ba, ɗan banza me baƙin hali kamar ubansa, yadda halinka yake haka na matsiyacin ubanku yake, baƙin hali dai akwai shi hadda na masifa da jaraba ka gado shi a gurinsa, fice ka bani guri me zuciyar banza data wofi "
Anwar yasha mamakin zagi da cin zarafin da mahaifiyarsu tayi masa, alhalin ga gaskiya tana gani ƙurƙuru, amma ta rintse ido ta masa wannan mummunan cin fuska haka.
Hajiya Halima ta ƙarasa gaban Ramlah tana ɗagota tace " Sannu Ramlah, Allah ya haɗaku da jarababbem ɗan uwa yana nema yaga bayanki, ni na rasa wannan mummunaan hali daya kwaso a gurin ubanku, Amal kawomin ruwan sanyi a fridge in shafa mata ko zata farka daga suman da tayi, da wannan surutan da take yi"
Amal tace "Mummy, maganar gaskiya fa Yaya Anwar yana da gaskiya, Ramlah fa maye take yi, kuma ba yau ta fara shan kayan maye ba"
Hajiya Halima tace "kamar yaya kenan?"
"Kamar yadda na gaya miki mana, wallahi tana shaye2 ne, wannan cocacolan da take sha, syrup take juyewa a ciki ta sha abunta, shine zakiga tana ta faman bacci, nayi mata magana amma kin san halinta baji take ba, wannan Fahad ɗin kuma shine silar komai"
"Ke Rufemin baki, idan har dagaske ne tana shaye2 da tuni na sani, ko kuma wani abune yake damunta yasa tayi shaye2, amma idan ta tashi zamuyi magana, sannan daga nan kar in sake jin maganar nan kinji na gayamiki"
Amal ta jinjina kai tace "to"
Da daddare Yusuf yana kusa da Widad akan katifarta suna bacci tare, wani mummunan mafarki Widad tayi, suna tafiya ita da Yusuf a wani guri me kyau, suna sanye da kaya masu kyau sosai, yana riƙe da hannunta yana mata hira tana ta dariya, shima fuskarsa ɗauke da murmushi.
Babu zato wata mata ta ɓullo a fusace, ta riƙe hannun Yusuf tana jansa, Widad ta fashe da kuka ta riƙe Yusuf gam tana
"dan Allah Yoseef karka tafi ka barni, dan Allah ki ƙyalemin shi nawane ba naki bane, na fiki buƙatarsa, nafi ki kusanci dashi, dan Allah kiji tausayina ki barmin shi, dan Yoseef karka barni"
Yusuf kuma ya fara ƙoƙarin bin matar nan su tafi, yana kallon Widad fuskarsa ɗauke da damuwa, da alama shima yafi son zama a gurin Widad.
Hannunsa ya fara zamewa daga na Widad, ta fara dena ganin fuskar Yusuf se dishi dishi.
A firgice ta farka daga baccin tana haki, tana ambaton sunan Allah, a gigice ta ɗakko fitila tana haska inda Yusuf yake sedai me......
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/15/21, 4:52 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
94_95
Haska inda Yusuf ke kwance tayi tana sauke numfashi, gani tayi ya haɗa gumi yana bacci, daga shi se dogon wando da alama zafine ya isheshi, shine ya cire rigar ya kwanta haka, ta hasakashi sosai taga kamar baya numfashi, ta kai hannunta da sauri Ƙirjinsa saitin zuciyarsa, taji zuciyarsa tana bugawa a hankali, bacci yake yi sosai sedai yayi gumi sharkaf a jikinsa.
Tashi tayi a hankali ta tafi ta lalubo mafici, tazo ta zauna ta ɗaga kansa ta ɗora a kan cinyarta, ta shiga yi masa fifita, tana goge hawayen da bata san dalilinsu ba, tama jin yadda ƙirjinta ke cigaba da bugawa saboda mafarkin nan da tayi, tana kuma godewa Allah da yasa ba gaske bane mafarki ne.
Yusuf ne yayi ƙoƙarin yin juyi, yaji shi a jikin mutum, ya kai hannu ya tattaɓata, ga ƙaramar fitilarsu ta kunna wadda haskenta yayi ƙasa sosai saboda rashin batir.
"Widad lafiya kuwa?"
Ta jinjina masa kai alamar eh, "to meyasa kawai zaki katse baccinki ki tashi kina min fifita?"
Tace "kasa bacci nayi, kuma naga kayi gumi dayawa, ka kwanta kawai ka cigaba da baccinka"
Yai murmushi yace "Allah sarki my Widad, nagode sosai Allah yayi miki albarka, amma Kasancewar ina mijinki kina mata ta bashi ke nufin, in cutar dake ba dare lokaci ne da Allah ya bawa bayinsa, dan su huta ko suyi ibada, amma in hanaki naki baccin dan nawa no baze yuwu ba, kece yakamata in miki fifita kiyi bacci saboda nasan wata ƙila zafine ya hanaki baccin, kuma nine gaba dake akwai buƙatar in tausaya miki "
Girgiza masa kai ta kuma yi tace " A'a kabari, kwanta kayi bacci kawai "
Tashi zaune yayi, ya karɓe maficin hannunta sannan ya kwantar da ita, yana mata fifita yace " wai na ganki some how looking disturbed, menene meya hanaki bacci ne matar? "
"Yoseef i have a bad dreams"
"On what?" ya tambaye ta.
Nan ta gaya masa abunda ta gani a mafarkin, ta ƙarashe zancen da kuka.
Murmushi yayi yace "Ohh My God, ya ilahil alamina Widad dreams are not true, mafarkine fa kawai meye na ɗaga hankalinki, ba gani a tare da ke ba, dena kuka haba babyna"
Kukan ta sake fashewa dashi tace "i don't want to lose you, Ina tsoron ya zama gaske mafarkin, sometimes our dreams come true, ina jin tsoro sosai, and am still having palpitation, ina jin kamar ze faru ne a gaske"
Yusuf yace "No my dear, kawai dai kin tsorata ne, kuma zuciyar ki ta fara jin abunda Yusuf yake ji game dake, amma in dai nine bazan gujeki ba ko in juya miki baya, sedai in daga ɓangaren ki a samu akasi, amma nikam nasan ina son matata"
Yai maganar yana saka hancinsa a wuyanta, shiru ta ɗanyi tana ƙara so ta tabbatarwa da zuciyarta kalaman Yoseef ɗin, na mafarkine kawai baze zama gaskiya ba, amma dagaske kenan Ta kamu da soyayya?
Tana cikin tunanin taji Yusuf yace "Wife, ina kika samu wannan turaren ne, tun rana yake tashi a jikinki, ina ta ƙoƙarin riƙe kaina, tauraren nan yayi daɗi a jikinki sosai"
Cikin cuna baki irin na wanda ya gama kuka tace "Jamila ce tabani"
"Wow, kince mata kin gode dai ko?"
Ta gyɗa masa kai, yace "good, ki tambayeta kuɗin turaren nan, zan bayar a ƙara mana"
"Dayawa fa ta bani, wai itama maƙociyarta ce a barrack ɗim da take ta bata dayawa da ta haihu, shine nima ta zubamin kuma da yawa fa ta bani"
Cikin nishaɗi yace "dukda haka i suppose to pay for it, naji daɗi Sosai, bazan manta kyautar turaren da kika bani ba, kyauta ta farko da kika bani, kyauta daga hannun masoyiyya, amma sedai naji kamar wari nake shiyasa kika bani turare"
Duk da a damuwa take, amma seda tayi dariya tace "taɓ duk wannan gayun naka, dukda basajar da kake yi amma abunda ya fara birgeni da kai ashine tsaftarka, dan wasu dan suna irin wannan aikin se suyita ƙazanta, su a dole se sun nuna talaucinsu, abun da yasa na baka turaren nan, duk lokacin da naji turare na tashi a jikinka, se naji wata kasala ta kamani, ko laifi kayi min seka rage ƙarfin fushin da nake ɗauke dashi, shiyasa nace bari in canza maka turare ko zan dena jin hakan, wataƙila daga turaren naka ne "
Yusuf yayi murmushi yace 'to daga baya mekika fuskanta?"
"Nagane cewar kwarjini kakemin, kuma abun ba daga turarenka bane daga kai ɗinne"
Yusuf yace "Ahse dai an daɗe ana so"
Tace "Ana son me?"
Yace "bakomai, just forget, ni dai ki bari kawai in shaƙi wannan ƙamshin me daɗin gaske"
Shiru tayi tana saurarensa ba tare da ta sake cewa uffan ba, aikuwa Yusuf ya wuce makaɗi da rawa, yau dai be sha cizo ba🤭🤭, sema wani farinciki mara misaltuwa da suka tsinci kansu a ciki.
A hankali a kunnenta yace "God bless you my Wife, thank you very much"
Ƙin magana tayi, sema lafewa data sake yi a jikinsa, yace "tashi in ɗora mana ruwa, naga akwai sauran kalanzir ko?"
Widad tace "eh akwai, amma shekaranjiya Hindu tayi girki a kai, idan babu se muyi dana sanyi"
"No akanme? Haka kurum in baki ruwan sanyi kiyi wanka inje ki shiɗemin, abunda baki saba ba, bakomai zan dafa mana, inma babu naje in tada murhu yanzun nan"
Widad tace "Murhu kuma a daren nan?"
"Eh mana, meye a ciki, muna cikin baccin mu kin tasheni kin janyo mana aiki"
"Au hakama zakace ko?"
"A'a tuba nake, wane ni" yai maganar cikin murmushi.
Akayi sa'a da kalanzir ɗin, ya fito da rishon tsakar gida ya ɗora musu ruwa, saboda yanayi na zafi kae ɗakin ya ƙara ɗaukar zafi, kafin ruwan yayi zafi, Yusuf ya ɗakko musu gashashiyar gujjiya suka zauna suka kama cin abarsu suna hira a wannan daren, se kace aljanu.
Jin ana ɓuruntu, yasa Hanne ta miƙe cikin tsoro ta leƙa taga dan ganin meke faruwa, ta hangesu zaune a cikin farin wata, suna ciue ciyensu suna hira.
Ta jinjina kai tace "lallai wannan kinyi dacen miji, yana sakar mata fuska sosai saɓanin mazan garin nan, wanima murmushi baze iyayiwa mace na wai karta raina shi.
Ƙarshe ma tare sukayi wankansu, Yusuf jinsa yake kamar wani sabon mutum, wani irin farinciki ya mamaye zuciyarsa, sedai duk da ɓangaren Widad ma hakan take, amma ta kasa manta mafarkin da tayi akan Yusuf, haka kurum abun ya tsaye mata a rai.
Anwar gaba ɗaya abunda ya faru yau a gidansu ya tsaye masa a rai, muraran mahaifiyarsu ta tabattar maaa da tafi ƙaunar Ramlah akansa, kuma bata son ace ga laifin da tayi, balle a saka rana zata mata hukunci, ransa ya ɓaci sosai dan haka ya fara tunanin, wane mataki yakamata ya ɗauka, dan janye jikinsa daga harkokin gidanma gaba ɗaya?.
Yana kwance yana tunanin meye mafita, yaji wayarsa tana ringing, da kamar baze ɗaga ba amma ya janyo wayar ya ɗaga.
Jin muryar Nurat ce tayi masa sallama yasa ya ɗan saki ransa ya amsa, Nurat tace "Yaya Anwar, ɗazu kazo baka samu ganina ba"
Anwar yace 'eh, nazo mu gaisa amma megadi yacemin zan ja miki matsala, wancan zuwan da nayi ma na jamiki matsala amma baki gayamin ba"
Ajiyar zuciya Nurat tayi tace "hmm kai dai bari kawai Yaya Anwar, abunne duk se a hankali, na kasa gane kan mahaifina gaba ɗaya, ya hanani fita zuwa ko ina, sannan ya hana kowa yazo inda nake, na kasa gane manufarsa, sam ban gane inda ya dosa ba"
Anwar yace "Amma kuma lokacin da yazo ya samemu tare be nunamin komai ba"
"Ai haka yake yi, baya taɓa nunawa a gaban mutane, amma bayan tafiyar ka har dukana yayi"
"Subhanallah, kiyi haƙuri wallahi ban zan zuwana ze kawo miki matsala a gurin mahaifinki ba"
Nurat tace "bakomai karka damu Yaya Anwar, ba laifinka bane, sannan kayi haƙuri rashin haɗuwar da mukayi"
"A'a bakomai Nurat, ina fatan ubangiji Allah ya daidaita tsakanin ku, dama biyowa nayi mu gaisa, wallahi nima kusan a cikin damuwa nake Nurat"
"Subhanallah, meyafaru?"
"Wallahi Nurat abubuwan nan da suke faruwa gaba ɗaya na rasa abunyi ma, jiya Ramlah a buge ta dawo tayi mankas da ƙwaya, amma ƙiri ƙiri dan na hukuntata Mummy ta fituttuke tace ƙaryane, taita faman Yimin faɗa, ban san meyasa take haka ba, abu in dak Ramlah ce bazata taɓa ganin laifinta ba, ƙarara take nuna banbanci a tsakaninmu"
Nurat tace "se haƙuri ai, lamarin iyayen nan namu sedai addu'a, ni gashi nikaɗaice a gurin iyayena, amma wasu lokutan idan Daddy yayi min wani abun, se inga kamsr bashi ya haifeni ba, yaita treating ɗina a hagunce, abun yana damuna sosai"
Anwar yace "kin san kowane bawa da irin tasa jarabbawar, kowa akwai ta ɓangaren da Allah yake jarabtarsa, sedai fatan Allah ya bamu ikon cin jarrabawa"
"Ameen Yaya Anwar"
"to akwai wani news ne daga gareki?"
Ajiyar zuciya tayi tace "News kam baza'a rasa ba, amma kasan wai Yusuf ɗan sanda ne ashe?"
'Eh nasani, amma da farko nima ban saniba, se daga bayan nan,