Showing 36001 words to 39000 words out of 209297 words
magariba Nasir ya fita.
Nasir ya tafi gidansu Bulama, ya jashi sukaje masallaci sukayi salla.
Nan Nasir ya bawa Bulama labarin abunda yake faruwa, Bulama yace "to ita kaɗaice 'ya, malam ka haƙura mana"
Nasir yace "haba Bulama, ya zakace haka, kasan yadda nake son Huda kuwa?"
Bulama yace "eh mana, kai banda abun soyayya meya haɗo biri da gada dama, ina kai ina Auren balarabiya ko dan kaga kana juya kuɗi a hannunka, malam ka nemi wata me ɗan rangwamen gata in auren kake so kayi"
Nasir yace "ni bama wannan ba Bulama, kasan Yaya Nasir wai bashi ze ciyo a kai kuɗin Auren Huda, sun yanaka mana kuɗi kusan million huɗu"
"Au wai dama sunce zasu baka auren nata?"
"Eh mana, sunce zasu bani, amma baffanta yace kuɗin Auren million huɗu, na rasa yadda zanyi ne, ga Yayana wai ze ciyo bashi akai kuɗin auren"
"bashi kuma? Kawai ka bari idan ya karɓo bashin, kazo muje 'yan mata se wadda kake so, mezesa ka wahalar da kanka akan wannan balarabiyar, hasken fatane fa kawai da gashin'
Nasir yace " A'a gaskiya ni Huda nake sl, kuma bazan ma bari ya karɓo bashin nan ba gaskiya"
Bulama yace "kai meyasa baka da wayo, wallahi garin nan akwa tsula tsulan 'yan mata, duk abunda kake so zasuyi maka indai da uwar kuɗin ka"
Tsaki Nasir yayi, ya tashi ya bar gurin saboda kunna shi da Bulama yayi.
Be zame ko ina ba se gidan Alhaji Abubakar, ya samu Ahmad ɗan gidan Alhaji Abubakar, suka zauna suka gaisa Ahmad yace "Angon Huda ya akayine? Naga baka walwala sam"
"Ahmad ina zanyi wata walwala? An yanka min sadaki fiye da tunani, gashi gaba ɗaya jarin da ribar da nake juyawa basu fi million ɗaya ba, ga Yaya Yusuf duk ya damu, har yana batun ze karɓi loan, gaba ɗaya na damu nina ma haƙura gaba ɗaya, amma yaƙi saurarata"
Ahmad yace "Nasir, ita kanta Huda tana buƙatar taimako, idan ka aureta zata samu sassauci, Allah baze hanaka yadda zakayi ba, Insha Allah, in dai matarka ce seka Aureta"
Nasir yace "Ni dai na haƙura na fidda rai, nasan ina matuƙar son Huda, amma bani da halin Aurenta"
"Ka dena faɗar haka, Insha Allah za'a samo kuɗin nan, kuma zaka auri Huda"
Nasir yace "to idan rabona ce Allah yasa in samu"
Yusuf ya dinga faɗuwa yana tashi, ya fasa karɓar bashin banki saboda haramcin hakan, Amma ya saida abubuwansa ya tattara kuɗin hannunsa da ƙyar sukayi million ɗaya da rabi, Ahmad ya bawa Nasir gudunmuwar dubu ɗari biyu, shima ya tattara ɗan abunda yake dashi, amma kuɗi ko million biyu basu yi ba, saura kwana uku kwanakin su cika, Alhaji Abubakar yazo ya samu Yayan Nasir yace "Malam Yusuf ya ake ciki ne? Kun haɗa kuɗin kuwa?"
Yusuf yace "wallahi kuɗin nan basu kai ba, muna ta faɗi tashine, dan Allah inda hali a basu haƙuri su ɗan ƙaramana lokaci, dan Allah karsu bawa wani, Insha Allah zamu cika a samu Nasir ya aureta"
Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar yayi yace "nikam wani irin so kakewa Nasir haka?"
Yusuf yayi murmushi yace "Nasir ne kaɗai ya ragemin, kuma kaga yarone ƙarami ba wani babba bane, kuma maraya ne, yana buƙatar a jashi a jiki, kuma iyayenmu sun mana wasiyya sosai akan muso juna, inyi haƙuri dashi in kula dashi, kaga dole in kula da marayana"
Alhaji Abubakar yace "Masha Allah, gaskiya na daɗe banga managarcin mutum kamarka ba Yusuf, Allah ya biyaka, kawo abunda ya samun, inje musu dashi inga ya zamuyi"
Yusuf ya dinga murna, kamar Alhaji Abubakar yace an bawa ƙaninsa Hudan, yaje ya kawo masa kuɗin, ya duba ya ƙirga su sannan yace "zanje can marocon, zanga yadda zamuyi, amma da ina da 'ya ko ƙanwa gaskiya dana baka, dan na yaba da amanarka da haƙuri da ɗan uwanka'
Yusuf yayi murmushi yace " rufamin Asiri kar Uwargida ta jimu, kasa ta haɗemin rai yau"
Sukayi dariya gaba ɗaya, daga nan suka yi sallama.
Sam Nasir be san me ake ciki ba, Yusuf yana ta cigaba da fafutuka, yana haɗawa da Addu'a.
Tafiyar Alhaji Abubakar da kwana biyar, ya dawo yai sallama da Yusuf ya sanar masa da an basu Huda.
Yusuf ya gigice yace "ai bamu cika kuɗin ba"
"karka damu, na shawa kan wannan matsalar, nan da sati biyu za'a kawo masa ita"
Yusuf yai godiya kamar ze duƙawa Alhaji Abubakar, har seda yasa Alhaji Abubakar yaji kunya.
Shikam Nasir ya dawo daga kasuwa, yayi sallar isha'i yaje yayi kwanciyarsa, ko abinci be nema ba, babu abunda yake banda begen Huda.
Yusuf ne ya shigo ɗakin da Nasir yake yace "Ango kasha ƙamshi"
Nasir be gane me yayansa yake nufi ba, yayi zaton zolayarsa kawai yake.
Yusuf yace "gobe in Allah ya kaimu, masu aiki zasuzo suyi gyare gyare a gidan nan, ka tattare kayanka ka koma shagon gidana"
Cike da rashin fahimta Nasir yace "gyaran me kuma za'ayi?"
"Amarya za'a gyarawa gida"
"Aure zaka ƙara ne?"
Yusuf yace "Rufamin Asiri, inani ina ƙara Aure, Nadiyata ta isheni matar rufin Asiri, 'yar aljanna insha Allah, har ƙiyama muna tare da ita"
Nasir yace "to gyaran me za' ayi?"
"Huda za'a gyarawa gida"
Zare ido Nasir yayi yace "wace Hudan?"
"Hudanka mana"
'Yayana, yaushe ta zama tawa? "
" Sun baka, nan da sati biyu insha Allah za' a ɗaura Aure"
Ai ba shiri Nasir ya rungume Yusuf ya fashe da kuka yace "Yayana, wallahi na rasa me zance ma gaba ɗaya, yadda kake ƙoƙarin farantamin rai, Allah ya sadaka da Annabin rahama, yasaka a aljanna ma ɗaukakiya"
Yusuf yace 'Ameen ya Allah, tare da kai ƙanina, farincikin ka shine nawa, nima nasan idan nine a halin da kake ciki, ba zaka zuba ido ba, ina me maka nasiha daka kula musu da' ya, ko bayan ba raina ka tuna gwagwarmayar da muka sha kafin ka sameta, ka nunawa duniya mazan hausawa Jarumai ne, kuma sun iya riƙe mace su bata kulawa "
Nasir yace " karka damu Yayana, Insha Allah zanyi iya ƙoƙarina inga na riƙe Huda da Amana"
Haka Yusuf ya ci gaba da yi masa nasiha, da jan kunne akan sha'anin Aure.
Nan da nan magana ta cika unguwa Nasir ze auri Huda, wani abun takaici dangin mahaifinsu sukace bada yawunsu ba, ba zasu yi jagora aje a Aurowa Nasir balarabiya ba, babu hannunsu a ciki, abun nan ya ƙara tsayawa Nasir a rai, ƙiri ƙiri se bare ne yayi jagorancin karɓa masa Auren wato Alhaji Abubakar.
Haka suka tafi maroco, da Alhaji Abubakar, da ɗansa Ahmad, da Yusuf da Nasir da wasu Abokan Alhaji Abubakar suka tafi maroco, Nasir yaso a tafi da Bulama, amma Yusuf ya hana yace ba zasu je da shi ba.
Huda ji take kamar ba itaba, lokacin da aka faɗa mata kuɗin da aka yankewa Nasir ta fidda rai da Aurensa, saboda tasan bashi da wannan kuɗin, ta fidda rai gaba ɗaya ta haƙura, se rashin lafiya take tana rama, babu zato babu tsammani yayarta Islam tazo mata da zancen ai megidanta ya zo da kuɗin Auren Nasir daga Nigeria, Alhaji Abubakar ne ya cika kuɗin, amma babu wanda ya gayawa hakan.
Baffansu Huda be taɓa tsammanin za'a iya biyan kuɗin nan ba, duba da yadda aka gaya masa Nasir marayane, kuma bashi da ƙarfi, ganin haka yasa yace tunda ta dage se bahaushe, bahaushen ma talaka ta dage ita da 'yar uwarta to suje, gasu nan ga bahaushe, kuma ya cire hannunsa daga kansu, kome ze faru ta nemi' yar uwatta da mijinta da suka dage akan se anyi wannan Auren, karsu ƙara nemansa.
Huda ta wani fannin tayi farinciki, yayinda gefe ɗaya kuma hankalinta a tashe, jin cewar jigon da suke tunƙaho da shi yace bashi basu.
Alhaji Abubakar kuma yace yaji ya gani, shi har Abada Aure albarkarsa ake nema ba wai tarin dukiya ba, idan da rabo a gaba Nasir zeyi Arziki, kuma in dai Huda ce kome ze faru ze riƙeta, balle babu abunda ze faru se alkhairi.
Shikuma Habib yace se an biya shi duk abunda ya kashewa Huda, alhalin duk abunda Ake bayarwar ba bata akeyi ba, wanima bata san an bayar ɗinba.
Da kuɗin Auren gurin Nasir, aka tattara abunda ya samu aka biya Habib.
Kamar wasa ranar wata juma'a, bayan sallar juma'a, a masallacin Kairaouine, suka ɗanyi shagalinsu a can, da suka tashi dawowa Nigeria, Alhaji Abubakar ya kasa ya tsare ya karɓi sadakin Huda a hannun ƙanin mahaifinta, sauran 'yan uwa ma suka tattara mata sha tara ta arziki, wani aka bata wani kuma aka ƙwace, suka taho da Amarya Nigeria.
'yan unguwar su Nasir, suka haɗa kuɗi suka shirya musu walima, wani ya bada hall, wani ya bada buhun shinkafa, gaba ɗaya kai baka ce Auren maraya ne ba, abokansu suka dinga basu gudunmuwar kuɗi wasu kaya, saboda duk wanda yasan Nasir da Yusuf yasan iyayensu, yasan mutane ne masu karamci da biyayya.
A lokacin maƙoci yana ganin ya isa da ɗan maƙocinsa, ana zaune lafiya kamar 'yan uwa dan haka Nasir yayi mamakin yadda bare sukayi musu wannan karar amma dangin mahaifinsu suja kasa yi musu.
Duk Wanda yaji yadda akayi auren yasan kawai rabone, dama Allah ya rubuta Huda rabon Nasir ce.
Huda ta tare a gidanta, musamman Yusuf yasa Nasir a gaba sukaje gaban Alhaji Abubakar sukayi masa godiya dashi da Islma amaryarsa.
Nasir baze taɓa manta alherin Ahmad da mahaifinsa ba, da sauran abokansa, amma Bulama babu abunda yayi masa, sema wadaƙa da sata daya dingayiwa Nasir a shago, ganin hankalinsa ya koma kan Auren da zeyi.
Sam Bulama beso Nasir ya auri zuƙeƙiyar balarabiyar yarinya ba, kullum suna tare, amma gaba ɗaya Nasir ya fishi sa'a a rayuwa.
Kuɗaɗen da Nasir ya samu na gudunmuwa, da wanda aka bawa Yusuf ya ɗau abunda ze ɗauka ya bawa Nasir sauran, ya sake zuba dukiyar a harkar kasuwancinsa, duk inda yaji wata harkar samu seya ɗebi kuɗi ya tafi ya jarabba, duk lokacin da yayiwa Yusuf zancen be bashi kuɗin daya ara masa, se yace ya ajiye masa ba yanzu ba, dan gani yake idan ya karɓa hakan ze iya shafar kasuwancin ƙanin nasa, yana nan zaune da matarsa lafiya, yana sonta tana son shi, Arziki se bunƙasa yake a hankali.
Ya ɗaukewa Yusuf ɗawainiyar siyan kayan Abincin gidansa, ya nuna masa baya so amma be bari ba.
Huda ta ɗau kuɗinta na sadaki da abubuwan data samo a can ƙasarsu, ta bawa Nasir tace ya haɗa, da tayi ta ajiyar kuɗin babu abunda zata yi dasu gara ya dinga juya su, ya karɓa ya haɗa yana juyawa, a hankali ya dinga janyo abokansa cikin harkar kasuwancin da yake yi, wasu suzo zuciyarsu ɗaya wasu kuma suzo da niyyar mugunta.
Allah maji roƙon bawa, katsam Nadiya matar Yusuf ta samu juna biyu bayan shafe shekaru uku da Aure, Nasir kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, danma yafi yayansa farinciki da wannan rabo, kullum zancensa Anty Nadiya idan kin haihu ni zanyi kaza.
Tun kafin bikin Nasir ta samu cikin, sam Nasir be saniba saboda yana cikin gararin soyayya, Nadiya ta girni Huda, amma suna mutunci sosai suna ƙaunar juna, Duk inda Ahmad yaji harkar kasuwanci da samu seya janyo Nasir, shikuma Nasir seya janyo Bulama, wani abun Bulama ya ɓata lamarin.
A hankali Abu ya bunƙasa, sanadiyyar Ahmad Nasir ya fara fita ƙasashen ƙetare, yana shigo da kayan ado na mata da turarruka, Ahmad ya koya masa yadda ake siyan Hannun Jari a manyan kamfanunnuka.
Nan da nan Kuɗi suka fara zaunawa Nasir, duk kasuwancin daya shiga seya samu alheri, shine nan shine can.
Ba ƙaramin daɗi Yusuf yaji ba, ganin dukda ƙarancin shekaru na Nasir amma ya fara nutsuwa, dan a lokacin befi shekaru Ashirin da uku ba yayi Auren, a wannan lokacin Auren wuri ba wani abu bane, indai yaro yana da sana'a.
Bulama ya tsani alaƙar Ahmad da Nasir sam, da yana zuwa gidan Nasir, amma fafur Huda ta nuna bata son ya dinga zuwar mata gida.
Kafin Nasir yaje Saudiyya Yayansa ya fara biyawa yaje Umara, Yusuf yace Nasir ya fara zuwa amma yaƙi yace shi yakeso ya tafi.
Ba ƙaramin daɗi da farinciki Yusuf yayi ba, dan badan a wancan lokacin ya haɗa kuɗin Auren Nasir ba, da tuni yaje, aikuwa yayi farinciki sosai.
Bayan dawowar Yusuf daga Saudiyya, lokacin Wata huɗu da Aurensu Nasir, matar Yusuf Nadiya ta haihu, Nasir kamar shi akayiwa haihuwar nan dan murna, kayan jariri kaf dana me jego shiya siya, hatta abun hakika shine yayi.
Tunda akayi haihuwar nan, Huda take zuwa gidan mejegon nan, tana addu'ar itama ubangiji Allah ya bata nata, dan tana matuƙar son yara.
Kwana bakwai da haihuwa akayi suna, yaron yaci sunan Mahaifinsu Nasir wato Umar faruk, ganin Nasir ya fara ajiye abun arziki yasa, da sunan Umar dangin Mahaifinsu suka zo suna.
Anci an sha dai dai gwargwado anyi shagalin sunan daba'a taɓa makamancinsa a unguwar nan ba, nan Sunan Daula ya sake bin Nasir sosai, Suna nunawa junansu ƙauna da sadaukarwa a tsakanin shi da ɗan uwansa.
Gaba ɗaya kusan Wuni Huda take yi a gidan Nadiya, ko taje gurin yayarta Islam taita musu raino saboda son yara da take yi.
Kasuwancin Daula fa ya faɗaɗa, abun har mamaki yake bawa mutane, babban abunda yasa mutane ke ƙara son Nasir shine hannunsa a sake yake, bashi da rowa sam, ga jan yaransu da yake akan harkar sana'a, dukda cutar da suke masa wasu lokutan.
Yusuf yana yawan yi masa faɗa akan watsi da yayi da 'yan uwan mahaifinsa, hakan be kamata ba, dan ko gaishe su baya zuwa yi.
Nadiya na fama da raino, ba damar zuwa Saudiyya, Nasir ya biyawa kansa da Huda suje suyi Umara, lokacin nan Ahmad ma zashi, ana i gobe zasu tafi, suka je gidan Yayansa Yusuf suyi musu sallama.
Suka zauna suka dinga hira kamar bazasu rabu ba, suka dinga tuna lokacin ƙuruciyarsu da gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa, da kuma wahalar maraici.
Har Huda ta dinga kuka, Yusuf yace "haba Huda, ai lokacin ya wuce ba gashi yanzu se labari ba?"
Nadiya tace "itafa Huda ko a labari bata son taji abunda ze taɓa wannan mijin nata, jinsa take kamar ranta, dan haka ku dena ma wannan labarim"
Huda ta ƙunshe kanta tana dariya, Nasir yace "Anty ya kika gani, kema fa haka kike son Yayana, laifi ne dan ta so mijin ta, wallahi my Huda kidena jin kunyar Anty Nadiya, naga ta fara damun ki"
Huda ita dai sedai tayi murmushi, Yusuf yace "ɗanuwa babu abunda zan cewa Allah se godiya, kamar yadda Antynka take fata gashi ka bunƙasa kamar wasa, Allah ya ƙara yalwata maka Arzikinka, Allah yasa ku yi ibada karɓaɓiya, ya dawo daku lafiya, sannan yakamata kayi haƙuri ka manta da abunda dangin mahaifinmu sukayi mana, komai ya wuce suma ka dinga kyautata musu "
Nasir yace " Taɓɗijan, wallahi nida su har abada, bazan manta cin zarafi da wulaƙancin da suka yi mana a rayuwa ba"
Yusuf yace 'A' a Nasir, abun da haƙuri be bayar ba, rashin sa baze bayar ba, ka maida komai ba komai ba, se kaga Allah ya daɗa buɗa maka, sannan ina gargaɗinka akan wannan yaron Bulama yake kowa? Ban yarda ka barshi akan kayanka ba, ko harkar kasuwancinka ba, dan bashi da kirki "
Nasir yace " Nikam na rasa me Bulama yayi muku kuka tsane shi, ni tausayi yake bani kaga shima marayane, kuma basu da ƙarfi "
Yusuf yace " banƙi kayi taimako ba, amma ya kamata kasan irin taimakon da zaka dingayi, Ka kiyayi yaron nan"
Nasir yace "to babbn Yaya magajin babanmu, Antyna ta kaina insha Allah baɗi in Allah ya kaimu lokacin aikin hajji, seki barmin babana kema kije ki sauke farali"
Nadiya tace "Allah ya ƙara Arziki ɗan gidan Anty"
Nasir yace "Ameen, ban cika Alƙawari ba, ke nace zan fara kaiwa amma na kai Yaya, nayi son kai ko?"
Nadiya tace "ai duk wanda ya kyautatawa Mijina ni yayiwa, nan duniya in ana son farincikina to a kyautatawa mijin marainiya"
Nasir yace "imra'ati kinji ko? Tana tsokanarki kin fiye sona, amma ji abunda take cewa"
Sukayi dariya, Nasir yace "Yayana, wai yaushe zan dawo muku da kuɗinku ne? Kasan fa yanzu Alhamdilillah, zan iya biyanku hadda riba"
Yusuf yayi dariya yace "Naji, Alhamdilillah haka nake fata, ka ci gaba da juya mana, lokacin karɓar yana nan zuwa, mesu ze karɓa"
Nasir yace "waye me su ɗin dazs karɓ?"
Yusuf yace "kai Baba suda sarki zance, kuje dare ya fara yi, kuje kuyi sallama dasu Antyn Huda, nima jibi in Allah ya kaimu nida su Nadiya zamu tafi Abuja, zamuje wani taro zan wakilci bankinmu, inaga daga nan idan na dawo zasu bani allowances ɗina na siyan gida da mota"
Nasir yace "masha Allah, Allah ya tabattar Yayana, Huda bani babana sanyin idaniyata, in sake ganinsa in sumbaci fararen kumatunsa"
Huda ta miƙa masa Faruk, ya karɓi jaririn ya rungume shi, yana sumbatar fuskarsa.
Yusuf yace "gaskiya Nasir kana ƙaunar wannan ɗan naka, Maman Faruk sekinyi dagaske karsu ƙwace mana ɗa shida matarsa"
Haka suka wanzu suna zolayar juna, suna hira tare sukaci Abincin dare kamar karsu rabu, suka shiga gurin Islam sukayi mata sallama itama, nan mu sun daɗe a can, daga ƙarshe Yusuf da Nadiya seda suka kusa rakasu gida sannan suka juya suka koma.
Washegari Alhaji Abubakar ya aiko da babbar mota, aka ɗauki su Nasir da Huda da matarsa, su Yusuf sukayi musu rakiya har airport, canma seda suka tsaya hira kaman karsu rabu, sannan suka tafi.
Satinsu uku a can sannan suka dawo gida Nigeria, sedai dawowar tasu suka tarar da abu mafi muni a tarihin rayuwarsu, wannan rana ta zamewa Huda da Nasir rana mafi muni da a tashin hankali, tashin hankalin da bazasu taɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwarsu, ranar tazo musu da wani al'amari me taɓa zuciya da girgiza ruhi, basu kaɗai ba hatta Ahmad ɗan gidan Alhaji Abubakar wannan rana tazo masa da baƙin tarihin da baze taɓa goguwa a zuciyarsa ba
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA