Showing 33001 words to 36000 words out of 209297 words

Chapter 12 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

713

kewaye ku cinye kai da abokai, kamar baka da wayo"

"Nidai dan Allah kisa baki ya bani, Allah bazan ɓafnatar ba zan tattala"

Nadiya tace "shikenan, rashin sana'a ga matashi bata da daɗi, bari ya shigo gidan inga ya za'ayi"

Nasir yace "Yawwa Antyna ta kaina, Allah yasaka da alkhairi, ya kawo 'yan biyu sau biyu" (da yake tunda akayi auren bata samu rabo ba"

Tai murmushi ta ce "Ameen ya Allah Nasir, Allah yasa ya baka jarin nan, daga nan ka zama babbn done"

"Ameen Anty, bari in ɗau carbi inta masa lazimi kafin ya dawo"

Tai dariya tace "idan ma be baka ba, ina sa ran a kawomin kuɗin gonata, se in baka"

Nasir yace  "zema bani insha Allah '

Suna cikin hirar ne sega Yusuf ya dawo, Yusuf yace  " Ashe kana nan, na biya ta can gidan in baka takalmin dana siyo maka amma baka nan"

Nasir yace "ai tun ɗazi ina nan, gurinka nazo"

"Gurina kuma? To gani"

Nadiya tace  "ka zauna kaci Abinci tukuna, idan kaci se in gaya maka saƙon nasa"

Haka akayi, tare ma sukaci Abincin shida Nasir, bayan sun kammala Yusuf yace  "to Uwargida, ina jinki tunda naga kun haɗa kai, nasan wataƙila wani abu akeso na bayar ko inyi"

Dariya suka yi, Nadiya tace  "Yawwa ranka ya daɗe, kaga yanzu kamar Nasir ai bekamata ace seka sai masa takalmin sawa ba, kamata yayi ace duk wannan abubuwan shiyakewa kansa, dan haka yazo neman alfarma dan Allah a temaka masa da jari"

Yusuf yace "An hanashin baza'a bayar ba, in kuma bashi yake shida wancam yaron mara kunya su haɗu su cinye, gara ko meye yazo in sai masa, idan ya ƙara hankali se in bashi jarin"

Nasir yace  "dan Allah Yaya, Allah nayi hankali zan tattala"

Yusuf yace "Anƙi ɗin, ai tun rannan nace bazan sake baka ba"

Nadiya tace  "A dai yi haƙuri ranka ya daɗe, Insha Allah baze sake ba"

Yusuf yace "to naji, tunda haɗe mun kai zakuyi, naji zan bashi jari, amma rance zan bashi"

Nadiya tace "haba dai rance dan Allah"

"shikenan tunda bakwa so, ai bazan sake bashi kuɗi yaje yaci a banza ba, tunda besan zafinsu ba"

Nasir yace "Anty na yadda, Insha Allah zan dawo masa dasj, nidai a bani jarin"

Nadiya tace "dan Allah kace ya dawo maka da rabi, ya riƙe rabi mana"

Yusuf yace "Nifa in bakwaso kuɗina sun huta, nasan abunda zanyi dasu"

Nadiya tace  "shikenan, munji mungode Yaushe za'a bamu?"

Yusuf yace "waini wace sana'ar ma zakiyi ne? Kuma nawa kake buƙata?"

Nasir yace "Yaya sarƙoƙi nake son in dinga siyarwa, zan kama shago a kasuwa sannan in zuba kayan, ance dubu ɗari biyar zasu isheni".

Zaro ido Yusuf yayi yace "dubu dari biyar? Kana da hankali kuwa?"

Nadiya tace "kana dasu fa, kafi ƙarfinsu dan Allah ka bashi"

"Gaskiya bazan bashi ba, zan dai bashi ɗari uku yaje ya nemi sauran, ɗari ukunma bashi"

Nadiya tace  "Nasir karka damu, idan aka kawomin kuɗina, kazo in baka sauran, inaji a jikina wannan sana'ar ds zaka fara itace silar arzikinka, ka zama hamshaƙin Attajiri, wanda ze tara Daula ta ban mamaki"

Nasir ya washe baki yace  "Allah yasa Antyna ta kaina, da duk sati sena kaiki Makka, shi kuwa yaya se shekara shekara zan dinga kai shi"

Yusuf yace "kar Allah yasa ka kainin, bana insha Allah zan tafi ai, kuma kema ban yadda ki bashi kuɗi kyauta ba, rance zaki bashi kuma tare zamu je da kaina a kama shagon"

Har zata yi magana, ya dakatar da ita, ya hanta magana, Nasir yaita godiya sannan ya tafi.

Bayan tafiyar sa Yusuf yace  "Nadiya, ina jin daɗin yadda kike nunawa ɗan uwana ƙauna kamar ɗan uwanki, ni kaina ina tunanin wace sana'a zan sama mishi, saboda nasan bayan raina babu wanda ze iya ɗawainiya dashi kamar yadda nakeyi, ba ƙinsa nake da nace rance na bashi ba, hakan ne zesa ya maida ya tattala abunda aka bashi "

Nadiya tace   " Shikenan tunda haka kace, Amma kana min kyautatawar dako nawa nakwa 'yan uwanka alheri dashi ban faɗi ba, amma tunda kace haka shikenan "

Bayan kwana bakwai, aka tattara kuɗi akaje aka kamawa Nasir shago, aka zuba kayan sarƙoƙi kala kala, Nasir ya maida kai sosai a tafi da shagon nan, duk yadda Bulama yaso a kassara shagon Nasir yaƙi, sedai wataran Bulama yazo ya taya shi zama koya yayi masa shara, shi kuma ya biya shi, amma a hakan Bulama yana taɓa ƙuruciyar ɓera wato sata.

Allah yasawa kasuwancin nasa albarka, nan da nan kasuwanci ya kankama, idan kuɗi suna nema su yanke masa idan ya zaga gurin Matar yayansa seta ƙara masa kuɗi, a hankali ya dinga sabawa da mutane, idan yaji labarin wani kasuwancin seya ɗibi kuɗi ya jarraba, shine ya buga nan ya buga can.

Wataran aci riba, wata ran a faɗi, Yusuf yana yi yana monitoring ɗin ƙanin nasa, idan ya tambayeshi yaushe zan dawo maka da kuɗin se yace 'ba yanzu ba, idan lokacin karɓa yayi zan karɓa'

Haka ya dinga faɗi tashi, da Nadiya ta ganshi seta fara tsokanarsa da seka gina Daula me ban mammaki babban don, a haka abokansa da maƙota suka fara kiransa da Daula kawai.

Ana nan wani hamshaƙin attajiri a kusa da gidan Yusuf, yaje ya auro wata balarabiya 'yar maroco, akayi shagali sosai' yan uwanta na can maroco suka zo Nigeria, akayi shagalin biki sosai.

Bayan wani lokaci balarabiyar nan ta haihu, aka kawo mata wata Yarinya a cikin danginta, ta zauna tare da ita saboda ta dinga tayata raino, kafin jaririn yayi ƙwari.

Nasir ya kan shiga gidan mutumin, da yake akwai babban ɗan mutumin me suna Ahmad a gidan, suna gaisawa sosai da Nasir, shi ya bashi shawarar fara sana'ar kayan sarƙoƙi na mata, dan haka Nasir yana shiga gidan sosai, dan ya saba da ita Amaryar wannan mutumin Islam wato balarabiyar maroco.

Duk lokacin da Nasir ya shiga gidan sukan haɗu da wannan balarabiyar Yarinyar me suna Huda 'yar uwar Islam , yana ɗan jin larabci dan haka sukan gaisa, kokuma suyi magana da turanci.

Huda bata da saurin sabo, amma ta saba da Nasir, ko fita ba tayi amma Saboda Nasir har gidan Yusuf take shiga nemansa idan taga bata ganshi ba, saboda Nasir yana da barkwanci, gashi ya iya hira dan haka yakan ɗebe mata kewa sosai.

A hankali mutuncinsu ya rikiɗe zuwa Soyayya, sun shaƙu da juna sosai, da farko lokacin da tazo Nigeria cewa tayi ba zata fi sati biyu ba zata koma ƙasarsu, Islam na ta fama da ita ta zauna amma fafur taƙi, amma saboda Nasir se gashi ta shafe watanni uku ba tare da ta koma maroco ba.

Ya zamana Nasir ya dena karɓar Abinci a gidan yayansa Yusuf, saboda Huda zata ajiye masa idan an dafa a gidansu, idan yaje ta kawo masa su zauna yana ci suna hira.

Kasancewar Nasir mutumin kirki ne daga shi har yayansa, yasa duk mutanen unguwa sun sanshi, kuma shi wannan Attajiri mijin islam yasan Nasir sosai, kuma yasan yana zuwa gidansa, shi ya fara tsokanarsa yana cewa 

"Nifa Malam Nasiru ban gane wannan mutuncin haka tsakaninka da Huda ba, ko kaima marocon zaka ne?"

Tun suna ɓoye ɓoye harta bayyana ga mutane, Nasir da Huda soyayya sukeyi, wasu lokutan idan aka aiketa shiyake rakata, saboda wani abun bata sanshi da hausa ba, kyautar sarƙoƙi kuwa da yake bata babu adadi.

Wataran haka zata shiga gidan Yayan Nasir, gurin Nadiya ta wuni a gurinta suna hira, a haka har take sedai sam Allah be haɗa jinin Huda da Bulama ba, da tana ɓoyewa, harta kasa ɓoyewar take gayawa Nasir ita bata san ganinsa da wannan Bulaman.

Nasir yace  "Hudallahi Bulama abokina ne, kuma ɗan uwanane ban san me yasa bakwa shiri ba"

Huda tace "Nifa ba hanaku hulɗa nayi ba, amma idan zakazo gidan nan ka dena zuwa dashi, yaita faman kallona, ni kuma bana so"

Nasir yace  "ki kwantar da hankalinki, ba abunda ze miki, dan dai kallo ai ba cinye ki zeba"

Haka yaita rarraashinta, suka cigaba da soyayya ita da Nasir.

Watarana Yayarta ta kirata tace  "Huda, gida fa sun matsa akan lallai ki koma, kinga kin daɗe sosai a nan"

Maimakon Huda tayi magana, se tayi shiru idonta ya cika da ƙwalla, Islam tace  "kuka kuma? Me yasa ki kuka?"

Huda tace  "ni bana son in koma gida"

Islam tace  "meyasa, keda da ƙyar aka lallaɓoki kika yadda kika zauna"

Huda ta share hawayenta tace  "bana son in koma saboda...  Sekuma tayi shiru

Islam tace " Saboda Nasir ko? "

Huda ta jinjina mata kai, Islam tace " Amma Huda kin san bazasu yadda su aura miki shiba? Kin san irin tashin da mukayi a gidanmu, nima dan Alhaji yana da kuɗi ne suka yadda suka Auramin shi, amma kinga Nasir bashi da kuɗin daze iya biya ya Aureki, kuma a can ga Habibullah sun masa Alƙawarin bashi Aurenki"

Cikin kuka Huda tace  "ni bana son Habib, Nasir nake so, dan Allah Ukty kisa baki, wallahi ina son Nasir sosai"

Islam tace  "kidena kuka ukty, Insha Allah zan tayaki da Addu'a amma nasan ko zaki Auri Nasir zaki sha wuya"

Daga maroco musamman aka taso ƙanin mahaifin su Huda yazo ya tafi da ita, tayi kuka sosai saboda zata rabu da Nasir, shi kansa Nasir ya shiga damuwa sosai, ranar da zasuyi Sallama Huda ta dinga kuka, Nasir kamar ze hauka.
Dan bayan sun rabu ɗaki ya koma yaje yaita nasa kukan shima, tunda Huda ta koma ya dena zuwa gidan wansa ko karɓar Abinci, ya zamana kasuwa ma ba kullum yake zuwa ba, sedai wataran Bulama yaje ya buɗe shagon ya zauna yayi wadaƙarsa san ransa da kuɗi.

Mussaman Yusuf ya aika aka kira masa Nasir, Yusuf yace  "Wato Nasir saboda wannan yarinyar kake nema ka kashe kanka ko? Ko Abinci ka dena zuwa ci, kai yanzu ko Auren ne ina kaga kuɗin da zaka iya auran balarabiyar yarinyar nan? Shikansa maƙocin nawa bakaji kuɗin da ya kashe gurin auro yarta ba, me muke dashi Nasir? Kayi haƙuri ka cigaba da walwalarka, nan gaba Insha Allah ni zan maka Auren ma da kaina, a samo maka 'yar baƙa me kyau ka Aura ko ƙanina"

Zumɓura baki Nasir yayi, ya haɗe rai ƙwalla ta taru a idonsa. Nadiya tace  "Shifa farar fatar nan yake so da dogon gashi ko Nasir?"

Girgiza kai Nasir yayi yace "Ni wallahi kawai sonta nake, ni bana son wata inba Huda ba"

Haushi ne ya kama Yusuf, da ze masa Masifa, amma ganin Nasir yana kuka yasan lallai ya kamu da yawa.

Se ya koma rarrashinsa, dayi masa Nasiha da ƙyar da rarrashi da Addu'a sannan Nasir ya cigaba da zuwa shagonsa, badan ya cire Huda daga ransa ba.

Ɓangaren Huda ma tunda ta koma maroco suka kasa gane kanta, bata walwala Sam, sannan taƙi saurarar wanda akeso a Aura matan, sam baya gabanta kullum cikin tunanin Nasir take da barkwancinsa, gashi lokacin waya bata yawaita a hannun mutane ba, balle ta dinga kiransa suna magana.

Aka fara shirye shiryen bikin Huda da Habib, amma Huda sam bata saurarensa se aikin kuka, gaba ɗaya tabi ta rame suka kasa gane kanta.

Islam ta shirya taje ganin gida, domin ayi shirye shiryen biki da ita, sedai me ganin 'yar uwatta ya razana ta gaba ɗaya ta rame, bata walwala se kuka.

Gashi iyayensu sun rasu, a hannun wan mahaifinsu suke, shi kuma mutum ne me azabar tsauri kuma kaifi ɗayane baya magana biyu, dan duk wannan botsarewar da Huda take akan Auren Habib be dameshi ba sam, shirin Aurar da ita kawai yake.

Seda Islam taje ta gaya masa aiga Halinda Huda take ciki, akwai wanda take so a Nigeria.

Nan yai tsalle ya dire yace baze taɓa yuwuwa ba, in dai yana nan a raye ba zata Auri wani ba idan ba Habib ba.

Da jin wannan batu hankalin Huda ya ƙara tashi, duk 'ya' yan wan mahaifinsu ba wanda yakewa Auren dole, sesu, yanzun ma yana son ya aurawa Habib Huda ne saboda yana da kuɗi kuma yana ci.

Mijin Islam har maroco yaje, akan maganar Huda dan Islam tana ta kuka ganin tilon ƙanwarta na neman rasa ranta saboda baƙin cikin auren dole daza'ayi mata.

Alhaji Abubakar yasa baki akan su ƙyale Huda da Auren nan, ko basu Aurawa Nasir ba su ƙyaleta tunda bata son Auren amma suka ƙi, har yayi barazanar ze ɗauke Huda kuma ze haɗa wan mahaifinsu da hukuma akan abunda yake yunƙurin yi.

Ɓangaren Nasir ma, tunda yaji halin da Huda take ciki ya shiga matsananciyar damuwa, har kwanciya yayi a Asibiti, damuwa tayi masa yawa gashi kullum ƙara son Huda yake a cikin zuciyarsa, tun Yusuf yana jin haushin ƙanin nasa har ya dawo yana tausaya masa, saboda ya lura kamar jarabta ce wannan Soyayyar tasa da Huda.

Hatta dangin su Huda da 'yan uwa suma suka sako Wan mahaifin Su Huda a gaba akan ya aura mata wanda takeso taje can ta ƙarata, indai mazan ƙabilar hausawa ne da ƙafarta zata dawo, itama Yayarta dan tana Auren me kuɗi ne, shiyasa ya iya riƙeta, itama babu tabbacin baza' a sakota nan kusa ba, dama me kuɗi itama ta samo da ɗan sauƙi amma ta ɗakko talaka, kota aureshi Auren ba inda zashi, ita dai Huda tace taji ta gani taje ƙasar Hausawa ta zauna dasu ita ba taga wani aibunsu ba, duk miyagun halayen da ake faɗa bata gani ba, kuma suna zaune da iyalansu lafiya.

Ganin baki yayi yawa yasa wan mahaifinta yace  "da kuɗin Auren Huda, da kayan Aure da sadaki da komai da komai ya yanke dirham dubu ɗari takwas"

Yusuf yana gida, akazo ana sallama dashi, ya fito dan ganin me sallamar hana zuwa yaga mijin Islam ne wato Alhaji Abubakar, ya fito suka gaisa da juna, Alhaji Abubakar yace  "wato dama magana ce nake tafe da ita akan ɗan uwanka Nasir, naje maroco ƙasar su matata, yarinyar nan Huda tama cikin matsanancin hali, ɗan uwan mahaifinta ma shirin yi mata Auren dole, mun kai ruwa rana sosai dashi, dan haka yace idan Nasir ya shirya nan da sati biyu ya kai kuɗin Aure, komai da komai dirham dubu ɗari takwas "

Yusuf yace " Alhaji nawa kenan a kuɗin mu na Nigeria "

Alhaji Abubakar ya ɗanyi shiru sannan yace " Naira miliyan uku da dubu ɗari shida kenan a kuɗinmu na nan"

Shiru Yusuf yayi, ya yakice gumi sannan yace  "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, to zamuje muyi shawara inga inda yadda zamuyi, amma bamu da shi a ɗaka balle a waje, ni kaina yadda gaba ɗaya Nasir ya sukurkuce abun yana damuna, amma bakomai nagode sosai da ƙoƙarinka nagode"

Alhaji Abubakar yace  "karka damu, ai ɗa na kowane kuma Nasir yaron kirkine ubangiji Allah ya yassare muku"

Sukayi Sallama ya tafi, jiki a sanyaye Yusuf ya shiga cikin gida, gaba ɗaya kamar an zare masa laka, Nadiya ta kalle shi tace  "ranka ya daɗe lafiya kuwa?"

Ya samu guri ya zauna yace  "Nadiya akwai matsala, baban Yarinyar nan Huda yace nan da sati biyu mu kai miliyan uku da dubu ɗari shida sannan a bashi ita, nikuma kin san bani ds ita, gashi ina tsoron wani ciwo ya kama min Nasir, gaba ɗaya yasa kansa a damuwa, duka abunda zan tsawatarwa Nasir ince ya bari yaƙi hanuwa to tabbas wannan jarrabawa ce a gareshi, Nadiya na rasa abunyi ina zan samu wannan kuɗin haka? "

(A wannan lokacin kuɗi suna matuƙar daraja)

Nadiya tace " yanzu meye abunyi, nikaina na fuskanci idan ba'a ɗau matakin daya dace ba, akwai yuwuwar ya faɗa mawuyacin hali "

Yusuf yace  " shine abunda nake tsoro, bazan iya fitowa in nunawa Nasir gazawa taba gurin sama masa abunda yakeso ba, kinga kwanan nan kuɗin hannuna na tatike aka buɗe masa shago, idan aka saki shagon aka karɓi kuɗin idan yayi aure dame ze Riƙeta? "

Nadiya tace "ai kama bar batun a saki shagon nan, muyi tunanin wata mafitar"

Yusuf yace "bazan gaya masa halin da ake ciki ba, inaga zan rubutawa bankinmu su bani aron kuɗin, idan yaso a dinga cirewa a albashina, akai musu kamar yadda Nasir ne kaɗai ɗan uwana itama Islam Huda ce kaɗai 'yar uwatta, idan muka temakesu kinga mun ceci rayuka biyu kenan, amma kiyi shiru da bakinki karki gaya masa Nadiya "

Nadiya tace    " Insha Allah bazan gaya masa ba, amma asaka gidana na cikin gari a kasuwa, idan aka siyar semu ragewa banki kuɗinsu ko? "

Yusuf yace" A'a Nadiya, ɗawainiyar da kike da Yusuf aita isa haka, ki bari kawai '

Nadiya ta haɗe rai tace "to ainima Nasir ɗan uwanane, tunda muna zaune da kai kana kula dani, meyasa zan bar ɗan uwanka cikin damuwa?"

Yusuf yace "Shikenan, ki bari in dawo se mucigaba da maganar, bari inje inyi sallar isha' i in dawo"

Yai maganar yana miƙewa, sedai yana fitowa ya ci karo da Nasir a tsaye a ƙofar ɗakin......


LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

64_65

Yusuf yace "yaushe ka shigo haka? Kazo ka tsaya a abakin ƙofa?"

Nasir yace  "Yayana, tun ɗazu nake gurin nan naji duk hirar da kuke da Anty, sedai bazan bari ka cigaba da wahalar da kanka saboda niba, akwai buƙatar kaima ka gina rayuwar ka data iyalinka ni dai ka ƙyaleni kawai, na haƙura da Huda"

Yusuf yace "ba shawararka nake nema ba, a gurin Allah nake nema, fita ka bani guri"

"Yayana, ka saurareni na haƙura da zancen Huda wallahi, bazan sake zancenta bama"

Yusuf be saurari Nasir ba yai waje abunsa, Nasir ya ƙarasa shiga ya tarar da Nadiya a zaune ya nemi guri ya zauna yace  "Anty dan Allah kisa baki, kar Yaya ya ciwo bashi saboda ni, ki gaya masa na haƙura da zancen Hudan nan"

Nadiya tace "kai ina ruwanka, ka zuba ido kawai"

"ba batun in zuba ido bane rayuwarku da cutu saboda ni, dan Allah Anty ki gaya masa na haƙura da Huda"

Ƙyaleshi Anty Nadiya tayi ta shiga ayyukan ta.

Bayan sallar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login