Showing 66001 words to 69000 words out of 209297 words

Chapter 23 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

722

ne tukuna, bana son a kaiki makaranta ki cigaba da rashin lafiya"

Widad tace  "Daddy bana son zaman gidan nan kwata kwata"

Cikin Halima ya ɗuri ruwa, ta zata Widad zata tona mata Asiri, amma se tace  "idan ina nan ina tunanin Ammine sosai"

"Babyna, shiyasa muka taso daga wancan gidan fa, saboda ki dena ganin abunda ze ɗaga miki hankali"

"Nan ma akwai wanda yake ɗagamin hankali, kuma ni makaranta nakeso in koma, ka maidani gidanmu na England seka kaini boarding school"

Shiru Daula yayi yace "lovely, zaki tafi kibar Daddynki?"

"No Daddy, kaga nan kullum kana cikin damuwa saboda ni, ni kuma ina tsorata sosai anan, dan Allah ka kaini can bana son zaman nan, please Daddy"

Daula yace "Shikenan, zan duba wace makarantar yakamata in kaiki"

Anwar yace  "banji Daɗi ba, bazan ji daɗi ba idan kika tafi Widad"

Widad ɗin dako fara'ar kirki ba tayi amma tai murmushi, dan Anwar yana nuna mata tausayi, ko Daddy baya nan idan shi yana nan suna sassauta mata, Widad tace  "ko zaka bini ne, mu tafi tare?"

Anwar yace  "Ƙwarai kuwa, daga nan har birnin sin, idan zaki dani zan biki"

Murmushi tayi tace  "aini makarantar mahaukata za'a kaini, kai kuma kana da hankali ai"

Sosai Anwar yaji tausayinta yace  "Ai zakiji sauƙi insha Allah, zaki warke ki dena cewa kanki mahaukaciya"

Girgiza kai kawai tayi tace  "Daddy, zanje in kwanta, ka rakani"

"Shikenan muje gimbiyata"

Halima da tun ɗazu ba tace uffan ba, dan wani mugun haushinsu take ji, da gashi har 'yar tasa.

Kwana biyu da yin wannan maganar, cikin dare suna bacci aka kuma shigowa gidan, dukda tarin security dake layin gidan, still dai wannan takaddu suka sake biyowa, aka rufe ɓangaren Halima da' ya'yanta suka shiga na Daula suka tarar dashi yana bacci, Widad na bayansa tana bacci itama.

Haka suka tashesu, Amma saboda gaddama da taurin kai irin na Daula daga shi har Widad suka ƙi magana, a gabansa suka dinga solata suna bugawa da ƙasa dan tayi magana amma taƙi, ba abunda Daula ze iya saboda kashedin da suka yi masa na zasu kashe Widad idan yayi wani yunƙuri.

Wani daga cikinsu yakama kumatun Widad, da suke ɓulɓul jajawur saboda hutu, yasa Ƙaton hannunsa ya matse da ƙarfi seda tayi wani uban zillo dan azaba ta saki fitsari, amma taƙi magana se kace wata itace.

Ƙarshe haka suka yi jifa da ita a galabaice, suka zuba mata ido, tana kallon Daula yana kallonta yana hawaye itama tana yi.

Ɗayan yace  "Wallahi ban taɓa ganin halitta me taurin kan mutumin nan da 'ya' yansa ba, ba dan ba abamu umarnin kisa ba, da wallahi sena musu kisan wulaƙanci mafi azabtarwa"

Ƙarshe haka suka haƙura suka tafi, Widad ta shiga tunanin ya akayi aka kuma shigowa gidan duk da tarin security ɗin nan?

Ɓangaren Daula ma yanzu ya amince dole Widad ta bar ƙasar nan dan tseratar da rayuwarta, kusan kullum cikin turo masa saƙo ake akan idan be bayarba za'a kashe shi, ko a sace 'yarsa, tun yana damuwa harya fara sabawa.

Ya nemi shawarar Bulama, Bulama ya goya masa baya akan ya fita da Widad ƙasar waje, hakan tamkar tseratar da ita ne.

Haka kuwa akayi, Daula ya nemawa Widad makaranta a makarantar masu fama da larura ta musamman a ƙasar England, Anwar kamar yayi kuka, Widad tace tana son ya rakata makarantar, karon farko da Anwar ya hau jirgi.

Daula yace "Mummynki fa bazata rakaki ba?"

Cikin harshen larabci Widad tace  "ni ba uwata bace, uwata ta mutu bani da uwa a yanzu, kuma ni mahaukaciyace, babu wanda zeso ya zama maman mahaukaci"

Daddy yai shiru yana kallonta, bece komai ba suka tafi airport, da ita da Daddynta, da Bulama da Anwar suka tafi, tana tunanin irin zaman da Daddynta zeyi da wannan matar me fuska biyu, dan ko a yanzu ta lura da tana wulaƙanta mata mahaifi wani lokacin, kuma baya iyayi mata magana.

Haka aka kai Widad wannan makaranta, aka danƙata a hannun likitocin can ƙasar, Daula yana kuka itama tana kuka suka rabu.

Tun a hanya kewar Widad ta damu Daula, Anwar ne yaita bashi haƙuri, dan Bulama ya gaji da rarrashin Daula.

Haka ya dawo gida zuciyarsa fal tunanin Tilon 'yarsa, yanzu bashi da kowa se Allah se' yar nan, yana mata son da shi kansa be san kansa ba, dan duk ƙaunar da yakewa mahaifiyarta ta koma kanta.

Kamar yadda Widad ta buƙata, wannan Ƙaton gidan nasu na farko, haka ya zuba dabbobin nan a gidan nan, dukda Widad ɗin bata nan.

Kullum cikin hirarta yake da begenta, abun fa ba sauƙi, dan ba'a fasa masa barazana ba iri iri, ta waya akan dukiyar nan, ƙarshe ya ware kason Widad a dukiyarsa, itama yasa mata a kasuwanci aka cigaba da juyawa, haka rayuwa ta cigaba da tafiya.

Da Anwar yayi candy, Daula ya ɗauke shi dashi da Fahad ya kaisu ƙasashen waje yayi sponsoring ɗin karatunsu, da komai da komai.

Amal da Ramlah kuwa manyan makaratun yaran masu kuɗi suke yi, ya mallakawa Halima kadarori da dama, taje Saudiyya ita da yaranta, duk ƙasar da suke so sunje, an kai waninta ma, amma gaba ɗaya bata gani ba, wannan dukiyar ce take hari itama, ga baƙinciki da kishin da take da Widad da Huda wadda ta riga ta rasu, jin maƙudan kuɗin da suke Asusun Widad kawai ba ƙaramin firgita ta sukayi ba.

Saleh kuwa bayan an kama Bala ɗanuwansa, maƙiyan Daula sukayi amfani da shi suka sa aka kai shi gidan Daula yin aiki, dan ya zame musu CID, suka cusa masa aƙidar lallai yaɗau fansar abunda akayiwa ɗan uwansa Bala.

Haka Widad ta cigaba da rayuwa, a cikin mahaukata iri iri, ana cigaba da bata kulawa a can, komai yi musu akeyi, Daula na yawan zuwa ganinta, dan wasu lokutan har gidansa na can yake tafiya da ita, suyi kwanaki su sha hira sannan in ze tafi ya maida ita, lokaci lokaci Bulama ma yakan kai mata ziyara, a bayan gidansu gidan Alhaji Musa yake, dan haka sukan haɗu da juna.

Lokacin da zata shiga high school (secondary school) tace lallai se an cire ta daga makarantar mahaukata, dan ita ta warke, da yake Daula baya son ɓacin ranta haka ya cireta, da yake dama Asibiti ne haɗe da makarantar masu buƙata ta musamman.

Daula ya taho da Hajiya Halima da yaranta, amma a ranar seda jikin Widad ya kusa motsawa, ta birkice masa sosai, tace "kodai su bar mata gidan nan, ko ita ta bar musu"

Daula yace "daughter, Mummy cefa kuma dan su ganki suka zo"

'Daddy karka ƙara ce mata Mummy na, kuma ina neman alfarmarka, idan har ina England karsu ƙara sa ƙafa a ƙasar nan, nan gidan Ammi ne da ita muka rayu a cikinsa, dan haka bana buƙatarsu anan "

Aikuwa jikin Daula yana rawa, aka maida su Hajiya Halima Hotel, abun nan ya baƙantawa Hajiya Halima rai fiye da tunani.

Tun daga nan suka fara takun saƙa, duk isa da hura hancin da Halima take yi se Widad tayi abunda zata nuna mata bata isa ba.

Widad ta shiga high school, itama boarding ce, amma bata mahaukata ba.

Daga ƙasar da take idan taso se tayo waya, ta bada umarni a Nigeria kuma abunda tace shi za'ayi, duk azabar bin malaman Halima, amma ta kasa raba Daula da Widad.

Wataran Widad tazo hutu Nigeria....



LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: .LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏

82_83







Lokacin da tazo Nigeria, maƙerin budurci ya fara ƙera Widad, ta fara zama budurwa me ji da kyau, zamanta a Turai sam bata san saka wata Atamfa ko makamancin kayan al'ada ba, da Amminta na da rai ma mafi yawan rayuwar su tana Turaine, dan haka sedai a saka mata blouse, yanzu kuma babu ran mahaifiyarta, gashi a tsakiyar turawa take, dan haka duk shigar da taga dama yi take ba wanda ya damu, Daula ya ɗaukar mata Nanny, idan anyi hutu tana gidansu na can, ita da Nannynta wata 'yar Nigeria ce amma bayerabiya, sedai a dafa taci, hatta gadonta da zata kwanta ta tashi sedai a gyara mata, saboda haka bata iya komai ba.



Itama Nannyn Widad ba wani yadda take da ita ba, gani take duk wanda ta yadda dashi ze iya cutar ta, ba abunda Widad ta iya na aiki, duk wani abu yi mata ake, ba wata wahala data sani a rayuwar ta, komai ta nema akwai available, kuɗi ko nawa take buƙata akwai shi available.



Widad tazo Nigeria, Daula ya dinga murna dan kusan shekararta Biyar bata taka Nigeria ba, sedai tunda ta dawo babu ragayya ko sassauci tsakaninta dasu Amal da babarsu, sam basa gabanta idan tana rayuwa a part ɗinta mantawa take dasu, Daula ya dinga zagayawa da ita guraren kasuwancin sa, da wanda yasa aka buɗe mata, taje har tsohon gidansu data sa aka maida shi na gona, gurin yayi mata kyau, tasa aka gyara mata wasu abubuwan aka canza mata wasu, ta cewa mahaifinta wato Daula tana son a siya mata dokuna biyu irin na wasan polo a saka mata a gidan, sannan aka kawo wani kare nasu, wanda yake a ƙasar waje, tasa aka kawo shi gidan aka ajiye.




Cikin hira Daula yake gayawa Hajiya Halima batun siyan doki, yace

"kinga rigima irin ta 'yarki ko? Saboda rigima wai dokin polo takeso a siyo a samata a wancan gidan namu, nasa ayo mata order su"

Dama Hajiya Halima tayi tayi su koma wancan gidan, dan yafi haɗuwa da girma amma Widad tace baza"a koma ba, ƙarshe ma tasa aka zuba mata kiwon dabbobi a ciki, wani ɓangaren gida sosai, wani ɓangaren gidan gona.



Hajiya Halima tace "Yanzu kai Alhaji saboda ka rasa abunda zakayi da kuɗi, seka sai wannan dokunan? Suna fa da tsada, kuma me zata yi da wasu dokuna tana mace"

Daula yace "Ai babu itace damuwa, amma tunda akwai za'a sai mata, ian son abunda takeso, kin san ba wata lafiya ce sa ita ba, shiyasa nake son yi mata abunda takeso, kodan ta samu farinciki, na rasa me zanyi wanda ze dinga ɗebe mata kewa, yasa ta sake da kowa"

Widad data kawo kai zata shigo falon Daddy taji wannan maganar da suka yi, da yadda Halima take kushe a sai mata abunda takeso, Widad ta maze ta shiga falon ta kalli Daula tace 



"Weldone Dad"

"Weldone my Queen, how are you?"

"Fine Daddy"

Yace "Masha Allah, Alhamdilillah, ya akayi ne, ko zuwa zanyi?"


Widad tace "No but Daddy, i see over twelve cars in the parking space, what are they used for?"

Daula yayi murmushi yace "na gidane, wanda muke hawa, ni nawa biyune kawai sauran na mamanki ne da Yayyaenki, tunda kinzo kema se ki sai wanda kike so"

Widad ta haɗe rai cikin hura hanci tace "Niba uwata bace, bani da uwa dan haka bata haifeni ba, , and na saka a kwashe motocin a kaimin su farmhouse a ajiye, na barwa kowa mota ɗaya yayi amfani da ita ta isa, kai kuma an bar maka naka my king" ta ƙarasa maganar tana murmushi.


Daula yace "to babu laifi, godiya muke gimbiyar Daula, yadda kikace ai haka za'ayi"

Tayi wa Hajiya Halima wani kallon tsana na baki isa ba sannan ta fice, tana fita Halima zata fara complain, amma Daula ya dakatar da ita yace "itama dukiyarta ce, duk yadda tayi daidai ne"

Halima taji kamar ta samo abu ta kashe Widad dan baƙin ciki, tun daga Nan fa suka dinga takun saƙa da Widad da matar babanta, bata ganin mutuncinsu sam, sannan bata yadda da kowa ba, sakamakon duk wanda suke cutar da Mahaifinta Yaran talakawane daya janyo a jikinsa sukayi Arziki sanadinsa, wanda ya yarda dasu sune suke cutar dashi.

A wannan zuwan ma, seda akai kaiwa Widad Mummunan Hari, akaso a sace ta amma Allah ya kuɓutar da ita, daga nan ta tattara komatsanta ta koma England ta cigaba da zuwa makaranta.

Daula ya bubuɗe guraren kasuwanci da kuɗinta, ciki hadda manyan gidajen gona, shagunan kasuwa da sauransu, dan haka Widad ma ta kasance 'yace me arziki a ƙashin kanta.

Gaba ɗaya a rayuwarta batayi zaman shekara shida a Nigeria ba, shiyasa abubuwa da dama ita bata sansu ba, ko in anyi take mamaki.

Wannan hali da ta tsinci kanta a ciki a rayuwarta yasa, ta yanke ƙauna da samun mutanen kirki, wanda ze zauna da kai a halin akwai ko babu, kuma ta yadda cewa duk talaka ze iyayin komai akan kuɗi, ta yadda idan har ka amince da mutum ya shiga jikinka, shine na farko daze fara cutar ka, ta lura mutane da yawa suna nuna mata kulawa ita da mahaifinta ne saboda wannan dukiyar da suke da ita, da babu wannan dukiyar da ba zasu dinga mutuntasu haka ba, dan haka itakuma take taka duk wanda taso.

Tun data bar Nigeria a wannan lokacin bata kuma dawowa ba, seda ta cika shekaru goma sha takwas, bayan shekara huɗu kenan, lokacin ta zama cikakkiyar budurwa, yanayin tsarin rayuwarta duk na turawa ne, dukda hali na rashin sakewa da mutane da take dashi, amma tana zuwa gurin shaƙatawa da buɗe ido.

Bayan gama high school ɗinta tace a Nigeria zata zo tayi karatun Jami'a, saboda kawai ta ƙallafa ran seta ta gano suwaye kuma suke da sa hannu akan kisan mahaifiyarta, suke cigaba da bibiyarta da mahaifinta akan dukiyar nan? Kuma tana son nunawa Hajiya Halima iyakarta saboda zaƙewar da take tayi yawa, da yadda take juya Daula yadda take so.

A wannan dawowartata ne aka kawo mata kusan direbobi uku, amma da sun fara aiki se taga kamar an haɗa baki dasu zasu cutar da ita, dan laifi ƙalilan seta kori mutum, bata ragayya bata sassauci bata afuwa ga ƙarya ko yaudara.

Dukda wannan tsawon shekaru, Magungunan nan basu dena aiki a jikin Widad ba, sakamakon ƙarfinsu ne da pressure da suke bawa jikinta yasa ta kamu da ciwon zuciya, ko kuma haka nan jikinta ya rikice ta fara wannan tsoron.

Widad ta ɗanyi shiru sannan tace  "Nasan akwai abubuwa da nayi da kake buƙatar sanin dalilina na yinsu, akwai ranar da mukaje Hotel nace maka ni karuwa ce, naje wannan Hotel ɗinne, dan ganewa idona wani abu kuma na gani, wasu mutane ne da nake zargi da sa hannunsu, na gansu tare da matar Daddy, da alama sunyi meeting ne, kuma nasan akan Daddy ne, munje Club tare ranar harka hanani shiga, naje ne domin in kama Fahad red handed ta yadda maganar Aure tsakanina da shi zata rushe, haka nan tun zuwanka naji wani sashi na zuciyata nason Amincewa da kai, dukda wani ɓangaren yana gargaɗina, nace bari in jarrabaka tukuna, duk inda zanje nake tafiya da kai, sannan na maka umarnin cewa ban yadda kayi magana da kowa ba duk inda zamuje, saboda ina tsoron a haɗa baki da kai, watarana kana zaune a gidanmu inda ka saba zama, ina kan varrendar na saman bene, kawai na hango Amal taje inda kake, ka taso kuka taho tare, na fito falo inga meze faru, za kayo hanyar part ɗina, se tace maka ai bana nan ina part ɗinsu, ka bita zuwa ɓangaren su, ni kuma na bi bayanku, nasan zakayi mamaki daka fito ka ganni a tsaye a gurin amma ban ce maka komai ba, haka kurum na fara sakewa da kai bayan na gano waye kai, ganin bibiyata da ake ya fara yawa yasa na ƙara jarrabaka, na baka ATM ɗina, ka tafi dashi tsawon sati biyu, a gaban mutanen gidanmu, wanda nasan dole su bibiyeka a kai, amma ga mamakina bayan sati biyu, se gashi ka dawomin da shi, ba tare da ko ƙwandala ta ɓata ba, kuma yana daga abunda ya ƙara nesantani da mutane shine, duk wanda ya raɓeni shima cikin matsala yake shiga, an dinga bibiyarsa kenan dan a samu wannan takaddun, shiyasa nake sake yin baya baya da kowa, sedai kai ka riga ka shigo rayuwata gaba ɗaya, ban iya kareka da shiga hatsarin da nake ciki ba, seda aka ritsa da kai, sannan ƙiyayyata ga Aure kuma ya samo asaline ga yadda naga Bulama ya maida Aure da saki tamkar shan ruwa, nakan bibiyi shafukan sada zumunta na kanga irin complains akan Aure, kuma ga mahaifina yayi Aure, Amma matarsa sam baya gabanta abunda yake hannunsa shi takeso, se nake ganin muddin nayi Aure tamkar na shiga matsala ne, kuma komai ze iya faruwa dank, kuma a yadda nake jina bazan zauna ƙarƙashin wani yayi amfani da ikonsa a kaina ya wulaƙantani ba, shine abunda ya faru har zuwa ɗaukemu sa akayi tare, Yoseef wannan shine ƙarshen labarina dana mahaifina, kaga laifina akan AƘIDATA? Ban cancanci in guji mutane ba? Ko kuma rayuwar kaɗaici zata zama laifi idan har nayi hakan ne dan kaucewa tarayya da azzalumai masu biyu? Mutane dayawa basu san meyafaru dani ba, abu ɗaya kullum suke kallo shine AƘIDATA "

Shiru Yusuf yayi, yasa hannayensa biyu ya dafe kansa, Widad tasa hannu ta janye nasa, tace " Kana jina kuwa?"

Wata irin ajiyar zuciya yaja, wadda seda Widad ta ɗan razana, ta ɗau fitila ta haskashi, sedai taga Hawaye a Fuskar Yusuf, jijiyon kansa duk sun ɗaga ya ƙara wani kwarjini, ga ja da idanunsa sukayi, saboda labarin Widad ya kaɗashi matuƙar gaske, gaba ɗayanta abun tausayi ce, taga jalala da iftila'i me ban tausayi, a kashe maka mahaifiya a haukata maka tunani, sannan a cigaba da bibiyar rayuwarka da barazana da tsoratarwa iri iri.

"Shiyasa na dinga ja maka rai fa akan baka labarin nan, kalli yadda ka ɗaga hankalinka hadda kuka, dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login