Showing 18001 words to 21000 words out of 209297 words

Chapter 7 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

708

da gashin, yana ɗaga shi yana wasa dashi, can Widad tace 

"Yoseef wai dan Allah Aure dolene? Sannan meyasa ake Aure ne?"




LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
11/14/21, 6:09 PM - Ummee Musa: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

56_57

Dariya tambayar tata ta bashi yace 

"Habibty wannan wace irin tambaya ce haka kuma?"

"Kaima wannan wane irin sunane, ni dan Allah ka dinga faɗar sunana"

"to naji Wudas"

"Allah ka ƙara gayamin kaima sena samo wani sunan na sama ka mara daɗi"

Dariya yayi yace  "ke baki san ina matuƙar jin nauyin faɗar sunan nan bane? Yanamin nauyi a bakina, bana iya faɗar sunanki fa"

Cikin Shagwaɓa tace "to meye abun wahala a Widad ɗin?"

"ƙaunar da nakewa me sunan ne yasa yake min nauyi"

"kaga ni duka ba wannan ba, ka bani amsar tambaya ta"

"meyasa kika tambayeni?"

Widad tace  "na tambaye ka kuma kana tambayata"

"to ai tambayar ta kice tazo a wata iri, nama rasa me zance miki"

A waje daka ke koyarwa in sun tambayeka wace amsa kake basu? "

" ƙureni zakiyi kenan? "

" ba wani ƙurewa ka bani amsa kawai "

Yusuf yaja ajiyar zuciya yace "Aure ba farilla bane, amma yana da fa'ida tunda Allah ya halatta yinsa, idan kika duba akwai tarin hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam da suke magana akan Aure, sannan akwai ayoyi a cikin Al'qur'ani da suke magana akan Aure, akwai wani Hadisin Annabi salallahu alaihi wassalam yace  'kuyi aure ku hayayyafa domin inyi alfahari daku ranar Alƙiyama, kinga anan yana daga amfanin Aure samun zuriya, yin aure ka haifi' ya'ya nagari babban Alkhairi ne shima duba ga hadisin manzon Allah salallahu alaihi wassalam da yace 'idan bawa ya rasu dukkanin ayyukansa suna tsayawa banda abubuwa guda huɗu, wanda ya mutu yana me imani da Allah, da sadaƙatul jariya sadaka me gudana, kamar gina rijiya makarantar islamiyya da sauransu, ko wanda ya sanar da wani ilimi wanda ko bayan ya mutu ske amfani da shi, da kuma ɗa nagari, kinga anan yana daga cikin amfanin Aure kayi shi ka samu ɗa nagari ka mutu ya dinga maka addu'a, duk ayyukan bawa suna tsayawa idan ya mutu, amma in kayi Aure Allah ya baka ɗa nagari, yana maka addu'a, kinga babbar ribace wannan, ko yayi wani aiki da ladan ze dinga iskeka. Akwai hadisin manzon Allah salallahu alaihi wassalam da yake cewa 'ya ku taron samari, wanda ya samu iko a cikinku  to yayi Aure, idan kuma bashi da halin yin Aure to yayi Azumi, kinga Aure yana da amfani domin shi katanga ne daga aikata zina, yana sanya nutsuwa a zukatan wanda suka yi shi, akwai tarin hadisan manzon Allah salallahu alaihi da ayoyi da suka yi magana akan Aure, dan haka Aure yana da mahimmanci sosai your majesty"

Ajiyar zuciya Widad tayi tace  "idan mutum be Aure ba ya aikata laifi?"

"A'a, kamar yadda na gayamiki Aure ba farilla bane, dan haka babu laifi ga wanda beyi ba muddin ze kiyaye iyakokin ubangiji ya tsare kansa daga aikata dukkan wani nau'i na Zina, sedai darajar wanda yake da Aure da wanda bashi da shi ba ɗaya bane, mussman mace duk abunda tayi na aiki kona ibada a cikin gidan Aurenta tana da lada, hakama namiji duba da gaba ɗaya shikansa Auren ibada ne, akwai wanda sam Aure be halatta suyi shiba, misali wanda bashi da abunda ze iya riƙe Auren, ko yake da wata nakasa da baze iya sauke haƙƙin iyalinsa na Aure ba wanda ze zamana da cutarwa a ciki"

Se kuma yai shiru, be kuma cewa komai ba, Widad ta sake gyara kwanciyarta a jikinsa tace  "to amma a haka akewa mutum wani kallo dan mutum be Aure ba, yau anyi abunda ya ɓatamin rai, yau na fara ganin anawa mutum rashin mutunci akan ba shi da saurayi, baka ga Abunda aka yi wa Hindu ba, abun ya bani haushi sosai ya bani mamaki"

Yusuf yace "To ai cikar mutuncin mutum shine Aure Habibty, kece kike masa wani kallo na daban"

"to tunda dai Auren ba dole bane, ai bekamata a dinga takurawa mutum ba, yanzu by mistake idan tayi Auren wani abu daba a so ya faru still ita za'a ɗorawa laifi, gaba ɗaya yau wani iri ta wuni tayi kuka sosai"

"Kin damu da Hindu sosai Gimbiya"

Widad tace "Wallahi kuwa, ina sonta har raina tana da kirki"

Yusuf yace "Ashe kin san meye son, nine kawai bakya so"

"Nifa ban san irin son da kai kake faɗa ba, amma ina jin Hindu kamar 'yar uwata, inaji dama gidanmu ɗaya ace ina da sister nima, nifa da zasu yadda idan zamu koma gida in tafi da ita"

Yusuf yace "Ai kina dasu, gasu Amal nan da Ramlah suma sisters ɗinki ne, amma kike musu wulaƙanci"

Widad tace  "Wallahi na tsanesu, tsana mafi tsanani da ban taɓa yiwa wata halitta ba, kuma ina nan idan na koma gida se sun bar mana gida, dan ba gidan ubansu bane"

"Subhanallah meyasa?"

"Bakomai" ta bashi amsa tare da gyara kwanciyar ta a jikinsa.

A hankali yace  "bazaki gayamin ba?"

Shiru tayi masa taƙi magana, tana jin yadda yake ta jera numfashi, kamar wani mara gaskiya, zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri, ga ruwan sama da yake ƙara zuba kamar da bakin ƙwarya.

A ɗan shagwaɓe Widad tace "Yoseef am scared, kuma sanyi nake ji"

Yusuf yace "calm down, muna tare ba abunda ze faru insha Allah, keep praying"

Ta jinjina masa kai, a hankali Yusuf ya shiga kiran sunanta, tana jinsa amma taƙi amsawa, sema wata kasala da take saukar mata.

Tana jin abunda Yusuf yake yi, amma ta kasa ko motsi, duk yadda Yusuf yaso tattara nutsuwarsa ya guje faruwar wani abu a tsakaninsa da Widad abu ya gagara.

Ba dan ruwan saman da'ake ta kwararawa ba kamar da bakin ƙwarya, da babu abunda ze hana mutanen ƙauyen da kewaye sanin abunda ya faru a tsakaninsu, saboda yadda Widad ta dinga kuka da neman temako, rakin tsiya da kuma Shagwaɓa.

Tun tana kukan har tayi shiru, muryarta ta dena fita sosai.

Seda Yusuf ya dawo hayyacinsa dafe kansa cike da dana sani, da tuhumar kansa akan wani ganganci ne ya ɗebe shi ya aikata hakan?

Widad se ajiyar zuciya take, tana kuka ƙasa ƙasa, gaba ɗaya Yusuf ya bata tsoro kuma ya bata mamaki.
Gaba ɗaya jikin Yusuf yayi sanyi ya kasa magana, ya rasa mema zece mata.

A hankali yaja rigarsa ya saka, ya miƙe ya ɗau bokiti da tukunya ya fita tsakar gida, a cikin wannan ruwan da ake ya tafi rumfar da'ake girki, ya dinga tona cikin murhun, ya tattara gawayi da ƙyar ya tashi garwashi, ya ɗora ruwa.

Haka ya zauna ya dinga fama, seda ruwan nan yayi zafi sosai ya haɗa mata, ya kai banɗaki ya ajiye.

Shi kansa jikinsa a matuƙar mace yake, ya koma ɗakin ya shiga ya tarar da ita a inda ya barta a kwance tana kuka, Ya durƙusa ya ɗagota ya samata hijjabi, a hankali yace  "tashi muje ga ruwan wanka can na kai miki"

Bata kula shi ba ta miƙe tsaye, ta dafa bango sedai tana zuwa bakin ƙofa ta tsaya, saboda tsoro ga tsigar jikinta dake tashi, saboda wani irin sanyi da take ji, gashi gaba ɗaya tsakar gidan ya jagwale.

Kawai ji tayi yayi sama da ita, ya kaita banɗaki ya ajiye mata fitila, ya koma can tsallaken wajen rumfa ya tsaya.

Ta daɗe sannan ta buɗe ƙofar banɗakin, Yusuf yaje ya ɗauke ta ya maida ita ɗaki, shi be tsaya wani dafa ruwa ba, saboda garwashin duk ya mutu, a haka ya ɗebi ruwan da sanyi da komai yaje yayi wanka.

Ya dawo ya tarar da ita ta kwanta, ta duƙunƙune a cikin hijjabi, yasa bargo ya rufeta, shima ya kwanta kowa yayi shiru yana saƙe saƙe a cikin ransa.

Mussman Yusuf wanda dana sani da haushin kansa suka baibayeshi.



Wani private hospital aka kai Nurat, nan da nan suka karɓeta a emergency,  likitoci suka shiga ƙoƙarin ceto ran Nurat, ta hanyar tsaida jinin dake ta zuba a goshinta.

Da ƙyar jinin nan ya tsaya, aka nan naɗe mata goshinta da bandeji, goshin ya kumbura suntum har gefen idonta saboda buguwar da tayi.

Mahaifiyar Nurat da mahaifinta suna reception, Mahaifiyar Nurat tana ta goge Hawaye, ta kasa zaune ta kasa tsaye.

Likita ne ya fito ya samesu a reception, suka yo kansa gaba ɗaya suna jero masa tambayoyi.

"ku kwantar da hankalinku, raunine kawai ta samu, Allah ya rufa asiri be shafi idonta ba, amma idan ta farfaɗo akwai gwaje gwajen da zamuyi muga inda yuwuwar ayi mata hoton Ƙwaƙwalwa, dan naga jini yana fita daga hancinta, karmu je ko akwai internal injury "

Mahaifiyar Nurat tace " Na shiga uku, hoton Ƙwaƙwalwa kuma likita? Ba dai haukacewa tayi ba? "

Tsaki Alhaji Musa yayi yace " kaga dan Allah ƙyaleta, na fahimce ka idan ta farfaɗo ɗin in akwai buƙatar hakan se ayi hoton, ni dai fatana Allah ya bata lafiya"

"dole kace a rabu dani mana, tunda ka kusa kashemin 'ya, kuma yanzu kana wani nuna kamar ka damu da ita"

"A nan ɗinma sekin nuna halinki ko?"

"ban sani ba, kuma wallahi duk abunda ya samu' yata kaine"

Likita yace  "haba dan Allah yallaɓai, da girmanku da komai, hakan be dace ba ai, akwai marasa lafiya a kwance, kamata yayi kuyi ta lafiyar 'yarku ba faɗa ba"

Haka sukayi shiru likita ya wuce.

Wayar Alhaji Musa ce ta shiga ringing, ya ɗanyi gefe ya ɗakko wayar yasa a kunnensa yace  "Hello ina ji"

"kana inane? Akwai magana fa"

"ina Asibiti, an kwantar da' yata"

"Subhanallah meye ya sameta?"

Alhaji Musa yace  "eh Home Accident ne, ta faɗi ne ta bige but is not that complicated"

"Ok to shikenan, Allah ya ƙara afuwa, zamu shigo mu duba ta insha Allah"

Alhaji Musa yace  "shikenan nagode sosai"

Wata Nurse ce tazo wucewa, Maman Nurat tace  "Sister dan Allah ko zan iya shiga gurin Nurat?"

Nurse ɗin tace "eh zaku iya shiga ku ganta, bacci take"

Cikin rige rige suka nufi ɗakin da aka kwantar da Nurat.

Nurat tana kwance tana bacci, ga drip an sa mata suka ƙarasa gaban gadon Nurat, mahaifiyar ta ta zauna a gefen gadon ta kamo hannun Nurat, jikinta ya ɗau zafi sosai Amma baccinta take ta sha.

A hankali Nurat ta buɗe ido, ta kalli inda Mummynta take, a hankali ta kai hannu tta shaf goshinta inda aka nannaɗe da bandeji, ta kalli Mummynta tace "Mummy me aka samin a goshina?"

"bandeji ne, aka rufe miki ciwon ki"

"Mummy kaina ze tsage ciwo yake min"

"kiyi haƙuri, ze dena insha Allah"

Alhaji Musa ya ƙarasa gaban gadon yace  "Babyna ya jikin naki?"

Kallo ɗaya tayi masa, ta ɗauke kanta tana kuka.

Alhaji Musa yace  "Am sorry kinji Babyna, is just a little bit mistake, kema ki dinga jin magana ki dena taurin kai"

Ita dai ba tace komai ba, kuma taƙi kallonsa.


Widad se farkawa tayi ta nemi Yusuf ta rasa a ɗakin, tayi tunanin ko ya tsaya sallar Asuba ne yayi karatu, gaba ɗaya jikinta ciwo yake, ta lallaɓa taje tayi sallar Asuba.

Ta koma kan katifarta ta kwanta, kanta se ciwo yake da duk ilahirin jikinta ciwo yake mata, ba ƙaramin mamaki Yusuf ya bata ba jiya, bacci ne ya sake yin awon gaba da ita.

Har sha ɗaya na safe bata ga Yusuf ba  ba taga alamarsa ba, ta tashi ta lallaɓa ta gyara ɗakinta, ta ɗau bokiti taje ta karɓi ruwa tayi wanka.

Ta koma ta ɗau kofi ta fita tana takawa a hankali, saboda yadda tsakar gidan ya jagwalgwale sakamakon mamakon ruwan saman da'akayi jiya da daddare, tsigar jikinta se tashi take saboda ƙyanƙyami, ga ƙarnin ruwa daya kwanta.

Ƙofar ɗakin gwaggo taje tayi sallama, Gwaggo ta amsa mata, ta nemi izini sannan ta shiga.

Gwaggo tace  "Amarya, yanzu nake sa ran in aiki Hindu ince ta dubamin me, yau shiru ban ganki ba ko dan anyi ruwan sama ne"

Widad tace  "bana jin daɗi ne, in akwai Abinci ki bani yunwa nake ji"

Da yake yau ba Gwaggo ce da girki ba, yanzu se ranar girkin Gwaggo ake basu Abinci, dan Widad bata cin Abincin kowa se nata, in dai ba ita tayi girki ba baza taci ba, sedai Yusuf ya girka mata wani abun.

Gwaggo tace  "Amarya bani nayi girki ba yau, amma ina da garin kunu an karɓomin jiya daga gurin niƙa, bari in  dama miki"

Widad tace "to"

Ta nemi guri ta zauna tana sake ƙarewa ɗakin Gwaggo kallo, wand ke matuƙar birgeta, sedai sam abunda ya faru tsakaninta da Yusuf jiua ya kasa barin zuciyar ta.

Hindu tayi Sallama da kaya a hannunta, Widad ta amsa.

Hindu tayi murmushi tace "Amarya dama kin tashi? Na zata har yanzu bacci kike ai"

Widad tayi murmushi tace  "A'a yazan ta bacci har I yanzu, na tashi tun ɗazu ai"

"Amma ya naganki wani iri, ko baki da lafiya ne?"

Widad tace  "A'a me kika gani?"

"gani nayi kinyi wani iri, idonki kamar kinyi kuka, kuma kamar me zazzaɓi"

Widad tace "lafiya ta ƙalau fa, yunwa kawai nake ji"

Hanne ta bankaɗo ɗakin ta shigo, babu ko sallama ta kalli Widad da Hindu taja wani uban tsaki, ta ƙarasa ciki basu kulata ba Hindu ta cigaba da jerawa Widad sannu.

Gwaggo ta kawowa Widad kunu, Widad tayi ta godiya ta tashi ta koma ɗakinta.
Dama ba'a batun sugar acikin kunun da suke sha ko kuma koko, a haka suke sha itama kuma ta saba a haka take sha.

Kunun nan da ta sha har la'asar, bata sake cin komai ba, se Dafaffiyar gyaɗar da Hindu ta bata.

Shikam Yusuf nauyin Widad ne ya hana shi dawowa, be san da wani ido ze kalleta ba, besan da wani kalaman ze amfani gurin kare kansa ba, tabbas yasan yayi aika aika a daren jiya, wadda shima be yi shirin afkuwar al'amarin ba, besan ta ina ze fara haɗa ido da ita ba, besan wani mataki zata ɗauka a kansa ba.

Haka nan ya tunkaro gidan yana tunanin, gabansa yana faɗuwa se Addu'a yake.

Yai sallama ya tsaya suka gaisa dasu Hari, yai sallama a ƙofar ɗakin Gwaggo ma suka gaisa, da yake yau tun Asuba be dawo ba.

Cike da fargaba ya nufi ɗakin su, yai sallama.

Tana daga kwance a inda take ta amsa masa a ciki ciki.

Ya shigo musu da 'yan kayan Abinci ya ajiye.
Jiki a sanyaye ya kalle ta yace "Yama ganki a kwance"?

Da harta buɗe baki za tayi masa tsiwa, kawai ta tuna abunda ya faru jiya da daddare a tsakaninsu, ba shiri ta tsuke bakinta kawai tasa kuka.

Dama Yusuf yasan a rina, ya ƙarasa inda take, yasa hannu ze kama hannayenta amma ta janye hannunta.

Yusuf ya ɗan ƙura mata ido, ji ba ƙwari ya fara magana yace "Widad ban san ta ina yakamata in fara ba, bani da kalaman da zanyi Amfani dasu wajen baki haƙuri, gaba ɗaya na rasa me yakamata inyi, ina me baki haƙuri sannan na shirya karɓar duk irin hukuncin da kika shirya Yimin"  yai maganar fuskarsa na fallasar da tsantsar damuwa dake kwance a zuciyarsa.

Cikin kuka tace  "shine ka tafi ka barni tun safe, bayan kasan...." ta ɗanyi shiru sannan ta ɗora  "bayan kasan abunda kayi min, bani da lafiya tun Asuba baka sake dawowa ba, ga yunwa nake ji, Se gurin Gwaggo naje ta bani kokon tsamiya" ta ƙarasa maganar cikin kuka.

Seda Yusuf yaji kamar yayi dariya, amma ya dake yace "subhanallah, am very sorry, na manta ne kuma ina jin nauyinki sakamakon abunda ya faru jiya, dan Allah kiyi haƙuri, i don't even know how it happens"

Widad a ranta tace  'jimin ɗan rainin hankali, wai he don't even know how it happens, se kace yana maye yayi abunda yayi'

Haɗe rai ta sake yi ta cigaba da kukanta, tace  "Kuma seka sake ni"

Yusuf yace "Naji amma ba yanzu ba se mun koma gida, for now am very sorry please, am not able to fulfill my promises to you, dan Allah kiyi hakuri Widad"

Banza tayi masa taƙi cewa komai, da haushinsa take ji kama sosai he takes away her pride, sannan yasa ƙafa yayi tafiyarsa tun safe ya barta, bata shirya faruwar haka ba sam a rayuwarta, babu Aure a gabanta, amma Yusuf ya ɓata mata komai yanzu.

Hannu ya kai ze taɓa ta, aikuwa ta zabura ta miƙe zaune da sauri tana faɗin "wayyo Allah Daddy"

Yusuf a rikice yace  "yi haƙuri ba wani abun zan kuma yi miki ba"

"Kuma sena gayawa Daddy idan muka koma gida, idan kayi min hakane dan karka sakeni, let me tell you, we must go separated, you must divorce me na gaya maka"

Yusuf yace "Widad trust me, is not intentionally shiyasa nake iya ƙoƙarina akan in kiyaye, but am human being, am not super natural"

"you said i should trust you how? After you know this is arranged marriage, but you took away my pride, how can I trust you Bayan Kamin ƙarya a baya, bazan taɓa trusting ɗinka ba"

Gaba ɗaya Yusuf ya rikice, ya rasa abunda yake masa daɗi, ya dafe kai yana kallon yadda take kuka, tausayinsa ne ya kamata, tace  "Nifa Yunwa nake ji, kokon tsamiya kawai na sha tun safe"

Yusuf yace "to, bari in ɗora mana girki"

Yai maganar tare da miƙewa, ya hau kokawar ɗora Abinci.

Yana cikin gaganiyar ɗora girki taga kamar yana ɗingishi ne, bata kula ba ta share shi.

Ya dawo ya ɗakko leda ya ɗakko mata pad guda goma sha biyu, da Maclean sabo da su man shafawa yace  "Kinga na siyo miki pad ɗin, kuma naga Maclean

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login