Showing 135001 words to 138000 words out of 209297 words

Chapter 46 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

757

wannan jam'ian tsaro a cikin al'ummar mu"

Nan fa gari ya ɗau ɗumi, aka dinga cece kuce, wasu na Allah wadai suna Tsinewa Yusuf, yayin da wasu ke a bari a ga abunda bincike zeyi tukuna.

Widad kam bata sake sanin inda kanta yake ba, inda har a gadon Asibiti aka bita aka dinga ɗaukar hotunan ta, ga fuskarta tayi ja saboda kuka, da gajiyar tafiyar hanya, amma aka dinga ɗauka ana watsawa duniya wai tana cikin mawuyacin hali, hannunta ɗauke da drip.


Alhaji Haruna ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba a taɓa raina masa hankali kamar yadda akayi yau ba, ya kira layin Hajiya Halima, Ramlah na zaune a falo wayar ta fara ringing, Mummy tana ciki tana amsa wata wayar dan haka ta ɗaga wayar tasa a kunnenta tace "Hello"

Yace "Yawwa Amal ce?"

"No Ramlah ce"

"Dan Allah idan Amal tana kusa ɗan bata wayar muyi magana"

Tace "tana ɗakinta, bari in kai mata"

Ta miƙe ta tafi ɗakin Amal, amma ɗakin a rufe harta kashe fitila ma "

Ramlah tace " gaskiya tayi bacci, dan ta rufe ɗakinta ma ta kashe fitila"

Yace "Yasalam"

Ramlah tace "ya dai? Akwai matsala ne?"

"A'a babu wata matsala, ina son muyi magana ne kawai"

"to ka gayamin saƙon in bata mana"

Yace "A'a karki damu, idan ta tashi na sake kira"

Ya kashe wayar yace "Amma dai Allah ya Tsinewa yarinyar nan, kaga min shegiyar yarinya mara albarka" ya ciji yatsa yai ƙwafa yace  "dani kike zancen wallahi, kema sema wulaƙantaki,"

Amal ta ɗau wayarta ta tura masa saƙo tace "ka cigaba da kiran Mummy, kana cewa kana son Magana dani, wallahi idan baka yi wasa ba sena gayamata abunda kayi min, kuma kasan halinta sarai, kasan buyaginta zata maka abunda kai kanka zaka kasa gane kansa, dan haka muddin ba zaka cika sharaɗina ba, wallahi ba zan baka ba na gaya maka, kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan, nima a account dina ina da wanda suka fisu"

Ta kashe wayarta ta sake kwanciya, ya duba message ɗin, yaja wata ajiyar zuciya yana cije leɓe, totally ta riga ta gama raina masa hankali, yama rasa me zeyi ko me zece.

Yana nan tsaye yana tunanin mafita kiran wayar Bukar ya shigo wayarsa, ya ɗaga jiki na tsuma, yace "Hello"

"Haruna, yau muna da zama na gaggawa, cikin dare dan haka duk ku tattaru"

Yace "harda Halima?"

"banda ita, sannan kazo min da wannan takaddar, zamuyi magana a kai itama"

Daga nan ya kashe wayar, Alhaji Haruna ya yakice gumi, yana huci Amal ta masa rashin mutunci, dan kawai abu ya shiga tsakaninsu se tayi masa haka?.



Mutan ƙauyen da Widad suka zauna suka dinga taradaddi, kowa da abunda yake faɗa wasu suna dama megari yayi wauta, wataƙila dama can 'yan fashi ne ko wasu masu laifin ne, amma daga zuwansu ya karɓesu, be san daga inda suke ba.

Hindu kam kuka, kamar wadda aka kama uwarta, ita kanta Hari gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, wunin ranar gidan daga masu koke koke, se masu salallami, Hanne kuwa ko a jikinta.

Koda Sunusi ya dawo, Jamika ta gaya masa abunda ya faru, dan haka yace dole gobe insha Allah ya tafi kank, yaje yaji ba'asin abunda ya faru.

Jamila tace "dan Allah karkaje, kar kaima a kama ka, dan na san da kana nan wataƙila da kai zasu haɗa"

Sunusi yace "da nayi musu me? Kince an kama Saleh, kuma Saleh shiya kawo su nan, meyasa aka kama shi, dole zanje inji"

Daddare megari ya tara iyalansa yace  "to wannan bayin Allah dai, ni dai a ɗan zaman da mukayi dasu, ban tunanin mutane ne marasa gaskiya, ko makamancin haka, zamanmu da su ma mu alkhairi ya zame mana a garin nan, dan haka dan Allah ina roƙonku da kuyi haƙuri ku dena kuka, kukan ya isa haka, Hasana nasanki da son 'ya' ya kuma zamanmu dasu jin shaƙu dasu sosai, dan Allah kidena kuka kiyi musu Addu'a, Hindu Baffa kema kukan ya isa haka, muyi musu Addu'a, Allah ya basu mafita sannan Hari a samo makulli a rufe musu ɗakinsu, kar wanda ya sake shiga tunda da kayansu a ciki "

Hari ta tashi ta shiga ɗakinta ta samo mukulli, tana ƙoƙarin rufewa taga bokitinsu a tsakar gida, ta tafi ta ɗakko bokitin, kawai ta fashe da kuka tace " Allah sarki Wudas, da yanzu muna faɗa akan ruwan zafin da zata yi wanka, tace sena bata na bawa mijin ta, ban taɓa ganin abun tausayi kamar yau ba, yadda ta rikice tana kuka, Allah sarki Allah ya fitar dasu"

A kaita bata haƙuri, aka kulle ɗakinsu aka bawa Megari mukullin, ya kai ɗakinsa ya ɓoye.

Yusuf yana kwance a cikin cell, an raba masa cell shida Saleh, sauro yana ta masa buduri a ka, yai rigingine yana tunanin ya Umma zataji idan wannan mummunan labari ya isheta?.

Aka buɗe ƙofar cell ɗin, wasu 'yan sanda suka shigo su biyu, ya tashi zaune yana kallon su.

Ɗaya ya kalleshi yace  "munafuki, kalleshi kamar na Allah, amma ƙasurgumin Azzalumi ne, kai garkuwa da' ya ka koma kayi da Ubanta, saboda kai Azzalumi ne, kuma a haka wai kai ɗansanda ne"

Yusuf yai shiru be ko ɗaga kai ba, ɗayan yace "rabu dashi corporal Sani, zuwa gobe in Allah ya kaimu semun sauya halittun fuskarsa, kafin 'yan jarida suzo, a buga shi a nunawa duniya shi, azzalumin banza dana wofi kawai"

Yusuf dai yai shiru bece komai ba, suka gama zage zagensu suka fita, suka sake rufe shi, tun Abincin safe Yusuf be kuma cin komai ba, ga doguwar tafiyar da suka yi, amma sam baya jin yunwa tunanin makaomarsa kawai yake a wannan hali da yake ciki.

Nurat na kwance cikin dare, taji Mahaifinta yana waya ƙasa ƙasa, ya fito daga ɗakinsa da alama dai fita zeyi, ta kalli agogo ƙarfe biyu da rabi na dare, ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito falo, aikuwa yana fitowa ya ganta a falo, ya ɗan haɗe rai yace "ke me kike yi a falo a wannan tsohon daren haka?"

Tace "ruwa na fito sha"

"ina ma fridge ɗin dakinki?"

"yayi sanyi da yawa, duk ya zama ƙanƙara shiyasa na fito"

Yace "to kin sha ɗin ne kokuwa?"

Tace "A'a yanzu dai zan sha"

"maza jeki sha, kizo ki wuce ki kwanta"

Ta nufi hanyar kitchen, tana tunanin ina zashi a wannan tsohon daren, ta fito ta tarar da shi a falon a tsaye, yace "kinsha ruwan?"

Tace "eh na sha"

"to maza ki wuce, ki tafi ɗakinki ki kwanta"

Harta juya ta tafi, ta waigo taga yana tsaye yana kallon ta, tace  "Amma naga kamar fita zakayi, ina zaka yanzu dare yayi sosai"

"Yaushe na fara wasa dake? Ko kuma kika zama uwata da zaki dinga tuhuma ta haka?"

"hmm Daddy kenan, ai kaine kake abun tuhumar, wani irin abune wannan da ba'ayi ido ma ganin ido ba se yanzu a tsakiyar dare haka hmmm Allah dai ya kyauta?"

Ta buɗe ɗakinta ta shige, ta barshi tsaye yana binta da kallo, yarinyar da idan ta ganshi jikinta ke rawa, itace take gaya masa magama haka, tabbas uwarta ce ke zigata kuma zeyi maganinsu gaba ɗaya.

Kamar yadda suka saba haɗuwa yauma sun hallara gabaɗayansu, suna zazzaune a ɗakin Hotel ɗin da ya zamana babu ma me kama shi sesu.

Bukar yace "kyakkyawan labari"

Alhaji Musa yace "muna jinka"

Alhaji Bukar yace "yaron nan yazo hannu"

Sukace wane yaron?

Alhaji Bukar yace "ku duk baku sani ba, dukda yadda da labarin ya yaɗu a daren nan? To ina nufin Yaron nan Yusuf, direbanta wanda aka yi garkuwa dasu tare"

Sukace "Alhamdilillah, abu yayi kyau"

Alhaji Bukar yace  "An kamosu a wani ƙauye a Bauchi, inda Saleh ya basu mafaka, yanzu haka yana hannun 'yan sanda, za' a tattare duk wata sheda da ta kamata daga nam za'a kaishi kotu, zamu saki kuɗi ayi masa shari'a da hukuncin daya dace da shi, saboda babu wanda ya ta:a kawo mana cikas da tangarɗa a harkar nan kamar shi, kunga daga nan babu wanda ya isa yace mune muka sa akayi garkuwa dasu"

Alhaji Munir yace "good, wannan abu yayi kyawuuu sosai, kuma ya tafi yadda ake so, dan haka semu hanzarta, mu kuma samu hanyar da zamu ɓalli namu kason tun kan Daula ya bayyana, dan shi har yanzu bamu san fa inda yake ba, kar muje wasu su rigamu karɓa abun nan fa"

Bukar yace "na toshe duk wata hanya da zata saka wani ya mallaki abun nan bamu ba, sannan dole nasa a matsa yaron nan, idan ma abun yana hannunsa ya faɗi inda suke"

Alhaji Musa yace "kai amma abu yayi kyau wallahi, komai ya tafi yadda yakamata"

Alhaji Bukar yace "Haruna ina takaddar da wancan yaron ya bari, ɗan gurin Halima? Shima nasa a nemo shi, duk inda aka ganshi kawai a kawar dashi, bama san duk wani abu da zesa a samu sheda a kanmu"

Alhaji Haruna yai tsilli tsilli da ido yace "Amm.. Mm.. Wallahi an ɗan samu akasine, na rasa inda takaddar ta faɗa amma ina ta ƙoƙarin dubawa"

Alhaji Bukar yace "Amma kasan bana son akasi ko?"

Yace "Ayimin afuwa dan Allah, Insha Allah za'a nemota in kawo"

Alhaji Bukar yace "shikenan, nan da kwana bakwai, na baka isashen lokaci, nan kusa nake so a fara shari'ar yaron nan, ba da nisa ba, kuma ina son a rufe duk wata hujja da zata bayyana mu"

Alhaji Haruna yace  "insha Allah, zan kawo takaddar nan ba da jimawa ba"

Haka suka gama tattaunawa sannan suka watse.

Widad ce ke ƙoƙarin farkawa, se jujjuya wuyanta take tana kuka cikin bacci, "Wayyo Allah na, yuzarsef yunwa nake ji, zuciya ta ciwo take, Yoseef dan Allah, dan Allah ka dawo please! Ta farka a gigice tana kiran Yoseef! Yoseef kana inane?"

Bulama ne da Matarsa Hajiya Sarah a gigice suka yi kanta gaba ɗaya, Bulama yace  "Sannu daughter, sannu ki kwantar da hankalinki, kin ganni a tare da ke, ga Maman Iman ma, an kuɓutar dake ki kwantar da hankalinki"

"Ni bazan kwantar da hankalina ba, ina mijina yake? Ina Yoseef kace su sakarmin shi, ni ba saceni yayi ba, wallahi idan basu sake shi ba mutuwa zanyi, laifina ne, duk saboda ya ceceni haka ta faru dashi, beyi laifi ba, tun farko seda na gaya masa death contract ne amma ya amince, kaga abunda nake nufi Yoseef, dan Allah ku ƙyaleshi idan wani abu ya sameshi bazan yafewa kaina ba, dan Allah ka cewa Bukar na dawo, ni yazo ya kamani yasa a sakarmin mijina dan Allah "

Tai maganar wasu irin hawaye na ambaliya daga idonta, idanun da suka rine zuwa kalar ja jawur suka kumbure.

Bulama yace "toni ina na san wani Bukar, balle in nemo miki shi? Ke kaɗai kika sanshi, ni ban san a inda yake ba"

Kafin ya rufe baki...


Ayi subscribing YouTube channel ɗina please 🙏 🙏 🙏 🙏
Ayshercool
11/23/21, 8:06 AM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680

(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg

Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"




118_119




Alhaji Haruna kam juyi yayi ya farka ya ganshi kwance a gurin daya sha lemon nan, shi dai yasan da magariba Amal tazo, amma yanzu yaga kamar yammace, nan da nan ya tashi da sauri yana dube dube, ya kalli agogo yaga ƙarfe biyar na yamma, ya duba yaga wayarsa a gefensa a kashe, me yarinyar nan tayi masa haka? Ko kuma meye ya faru da shine?
Yai yai ya tuna wani abu amma ya kasa, ya gagara tuna komai daga inda ya sha lemon nan baya iya tuna komai, ya tashi ya fito falonsa amma komai yana nan yadda yake, babu abunda ya canza.

Duk ya lalleƙa babu wani canji daya gani, amma ya akayi yayi wannan baccin haka?
Ya tambayi kansa, tabbas wannan yarinyar ce tayi masa wani abu, sedai ya kasa gane meyafaru dashi.



Sunusi duk yadda yake tunanin lamarin ya wuce nan, dan daya zo Kano ya samu labarin inda su Saleh suke tsare, sedai tun daga bakin gate wani yace masa tun wuri yayi takansa, karma a san daga imda yazo ko kuma shi wanene a gurin Saleh, idan ba haka ba tabbas shima kamshi zasuyi su rufe har dashi.

Haka Sale ya koma babu wani daddaɗan labari, su kuma su megari suna can suna jiran sa yazo ya gaya musu yabake ciki, sedai yanayin fuskarsa kawai ya nuna musu babu nasara.

Me gari yace "Sunusi, kayi mana bayani, da kaje kanon menene ya faru? Ya kukayi dasu?kaga su Yusuf ɗin da Saleh fatan suna lafiya?" megari ya jero masa tambayoyin.

Sunusi yace "Baffa, lamarin nan fa ya wuce inda kake tunani fa, duk abun ba yadda muke tunani bane, ita wannan yarinyar daka gani, matar wannan Yusuf ɗin Wato Widad, 'yar gidan Alhaji Nasir Daula ce, wai ance Yusuf ɗin ne suka haɗa kai da Saleh sukayi garkuwa da ita, dan su karɓi kuɗin fansa, shine sukazo suka ɓoyeta a garin nan"

Hansai tace " wai Daula dai shahararren attajirin nan da ake labarinsa? Wanda ake yawan faɗansa ɗin nan"

Sunusi yace" to da daulan guda nawane? Shi dai 'yarsa ce"

Gwaggo tace 'biri yayi kama da mutum, kwata kwata yarinyar nan ba kalar wahala bace, yanayin yadda take rayuwarta da yadda bata iya wasu abubuwan ba ze tabattar maka da bata tashi cikin wahala ba, sedai gaskiya bazan taɓa yadda wai satota sukayi ba, nan fa suka zo da ita babu lafiya Yusuf ne ya goyota a bayan sa, bata yadda da kowa seshi farkon zuwa su, kuma da satota yayi da tabbas tayi yunƙurin guduwa wataran "

Hari tace " Akwai dai wani abu a ƙasa, amma yadda take ji da Yusuf ɗin nan ƙaryane a ce satota yayi, komai shi, kullum tana liƙe dashi, sannan ace satota yayi gaskiya ban yadda ba sam "

Sunusi yace  " to kai Baffa da baka san daga inda suke ba, ka karɓe su?"

Megari yace " Saleh ne ya kawomin su, yace garinsu faɗa akeyi, babu kwanciyar hankali an kashe iyayensu, shida ita 'yan uwane, amma ba ciki ɗaya ba, na wuce gaba aka ɗaura musu Aure saboda dai ai baka ƙi taimakon mutum ba, amma ni dai gaskiya ban yadda ace wai satota sukayi ba, dan lokacin da suka zo gidan nan, shi kamsa Yusuf ɗin kamar a galabaice yake bashi da lafiya, zaka ce daga gurin da ake yaƙi suke '

Sunusi yace "Amma abun da mamaki gaskiya"

Hindu tace  "kuma da kaje babu wanda ka gani a cikinsu, daga Amarya har mijin nata?"

Sunusi yace "ke, case ɗinfa babba ne, yafi gaban yadda kike tunani, kedai kiyi ta addu'a kawai"

Hindu tace "Allah sarki' yar uwata, gaskiya na tausaya mata, ashe 'yar gidan attajirai ce amma tazo tai rayuwa a wannan ƙauyen namu? Kuma taita binmu tana lallaɓamu mu koya mata abu, kuma da alama mijinta kawai ake nema, da akazo kamasu tambayarta suke yana ina"

Megari yace "koma dai yane, ubangiji Allah ya kuɓutar dasu"

Haka suka cigaba da tattaunawa suna salallami.

Aka buɗe ƙofar ɗakin da Widad ke ciki aka shigo, ko ba'a faɗa ba tasan waye ya shigo ɗakin, dan haka ko ɗaga kai batayi ta kalleshi ba, ta maida hankalinta ga wani gurin, ya ƙaraso ya zauna a gabanta yana ƙare mata kallo, still bata motsa ba balle ta ɗaga kanta ta kalleshi.

"koki kalli inda nake, ko karki kalla yin biyayya ga dukkanin umarnina ya zame miki dole a yanzu, tunda shine last option ɗinki, tunda kika riga kika gano waye Bukar, zan gwada miki aikinsa a aikace, ranar Litinin za'a kai wancan sakaram da kike iƙrarin mijinki ns kotu, kuma na ɗau dukkan wasu matakai dana san zasuyi amfani sena tura shi gidan yari ya ƙare rayuwarsa a can, babanki kuwa koma ina ya tafi ya tafi kenan, har Abada har gaba da Abada baze dawo ba, dama burina kenan in ɗaiɗai ta farincikin sa"

Widad dai bata motsa ba balle tayi magana, tai shiru ta cigaba da kallon waje ɗaya.

Ya cigaba da cewa "ki temaki kanki tun baki makara ba, ki bani takaddun da ubanki ya ware, yace wai dukiyar akwai me ita, duk wanda yasa hannu akan takaddun nasane suna ina?"

"Idan ubaka ne ya tara masa seka sa in baka, bazan bayar ba nayu Alƙawarin me ita zan bawa, kuma na riga na miƙasu ga masu ita"

"Niki ke gayawa haka?"

"Na gaya maka ɗin, tsakanin wuta da aljanna wacce kake da ita, balle ka sani? An faɗa maka ɗin kayi abunda zakayi karka fasa"

"Ina binki sannu sannu ne, saboda har yanzu akwai ɓurɓushin imani a raina, mahaifinki yamin ranar dabe yiwa wani a rayuwa ba, sannan dukiyar ki ce dalilin tsayawar kasuwancina da ƙafafunsa shiyasa nake son in kamanta miki adalci, ina takaddun suke? Ki gayamin cikin ruwan sanyi tun ban saɓa miki ba, kokuma na gwada miki"

"Ban sani ba!" ta faɗa cikin shouting,

"Idan kana so ka kashe ni hankalinka ya kwanta, kuma zalunci indai nakane wanne ne ban gani ba, ai babu irin wanda baka gwadamin ba, ko zaka gutststura naman jikina, bazan baka ba"
ai kuwa ya kifa mata mari, abun da ba'a taɓa yi mata ba a rayuwar ta, dan seda bakinta ya fashe.

"Wallahi ko kina so, koba kya so sekin bani kuma ba kimin wannan raunin a banza ba se na ɗau mataki a kanki"
"bazan bayarba, Amana ce kuma na danƙata a hannun masu ita suna rayuwarsu, me kake so inyi maka? Ko me zance maka?"

"ƙarya ki keyi, baki danƙata a hannun kowa ba, ki gayamin ina suke" yai maganar cikin tsawa.

Banza tayi masa, taƙi magana ta shiga goge jinin da bakinta yake yi, ai kuwa taji saukar tio a jikinta, tunda Widad take ba'a taɓa dukanta da abu me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login