Showing 57001 words to 60000 words out of 209297 words

Chapter 20 - Akidata Book 2 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

756

ta haɗa rayuwarka da tawa kana ta faman wahala, an cutar dani an kassara lafiyata, an cigaba da bin diddigina ana son ganin bayana saboda abun duniya, kuma aka jefa ƙiyayyata a zukatan jama'a suka koma gefe suna zagin AƘIDATA, Insha Allah bazan mutu ba sena ga bayan maƙiyana, ko kuma mu yi mutuwar kasko nida su, i can't tolerate it anymore "

Tai maganar tana jifa da kayan gurin, sannan ta yunƙura zata miƙe, Yusuf ya riƙeta gama, fizge fizge ta dingayi tana kai masa duka tana nema ta ƙwace daga hannunsa, ya riƙeta sosai yana mata addu'a, surutai take sosai cikin ɗaga murya, idan Yusuf yasa hannu ya toshe mata baki, se taita kai masa duka, idan ya riƙe hannunta kuma seta hau surutai, yana gudun hankalin mutane ya dawo kansu, dan sam baya son wani yasan tana da larurar taɓin hankali, dan haka kawai ya haɗe bakinsa da nata.

Tun tana mimmiƙewa tana son ta ƙwace, harta gaji jikinta yayi sanyi, Numfashi take saukewa a hankali, hawaye na bin gefen idonta, seda yaga ta dena fizge fizgen sannan ya cire bakinsa daga nata, ta lumshe idonta kamar me bacci, Yusuf ya rungumeta yana cigaba da karanta mata duka Addu'ar da tazo bakinsa.

Widad ya kira sunanta, ɗaga masa hannu tayi alamar ya ƙyaleta, sun daɗe a haka sannan ta tashi zaune, Yusuf ya kalleta yace  "Sannu"

Jinjina masa kai kawai tayi ta sunkuyar da kai, ya riƙe hannayenta yace "dan Allah kidena saka damuwa a ranki, kinga hakan yana shafar lafiyarki"

"bazan iya dena damuwa ba, saboda an diga an gama kassara rayuwata, bana jin zan samu nutsuwa har se ranar da na gamsu, na ɗau fansar abunda akayimin"

"Rayuwa ba zata tafi a haka ba, lafiyar ki abun dubawa ce, kalli yadda lokaci ɗaya kika fita hayyacinki fa"

"Ai dama ba lafiyar ce dani ba, dan haka ba wani abu dan na ƙarasa a haka"

Kawai ta rufe bakinta da hannunta tana kuka, Yusuf ya shiga share mata hawayenta, yana cewa "ke lafiyayyiya ce, kuma ina miki fatan samun lafiya me ɗorewa"

Tai murmushi me ciwo tace "wai in warke daga haukan? Ko ciwon zuciya?"

"Nifa ban yadda da wannan ciwon haukan ba"

Widad tace  "yakamata ka yadda, ka sawa ranka kana zaune da mahaukaciyane"

Yusuf ya ɗanyi shiru sannan yace "nifa akwai ranar da naga an saka miki wata ƙwaya a cikin tea, amma baki sha ba, shiyasa nake da question mark akan wannan ciwon naki"

Seda tayi shiru na wasu lokuta, sannan ta gyara zamanta tace  "Bayan an kashe Ammina, ɗaya daga cikin wannan mutanen, ya ɗakko wayarsa ya fara waya, yayi wayarsa ya gama sannan ya kalli sauran yace, ku cajemin gidan nan, akwai wata yarinya, ku kawomin ita nan, Widad na tsaye tana jinsu, bata ko motsa daga inda take ba, suka fito suka shiga bincike gidan nan, amma basu ga Widad ba, suka dawo sukace "mun caje ko ina a gidan nan bamu ga yarinyar nan ba"

Yace "ta yaya za kuce baku ganta ba, bayan tana cikin gidan nan?"

Suka haɗu har dashi suna dubawa, sun wuce ta inda Widad take yafi sau uku, amma Allah besa sun ganta ba.

Suka sauka ƙasa falo, babban ya sake kiran waya, ya sanar da wani cewar sun duba kaf basu ga Widad ba, kawai Widad ji tayi yace " An gama Oga.... "

Bata iya jin cikakken sunan daya faɗa ba, kamar taji dai dai kamar kuma ba daidai ba.

Babban yace  "kai mu tafi, Oga yace yasan yadda zeyi da ita, mu ɓace kafin a gane munzo"

Haka suka rankaya suka fita, cikin sanɗa Widad ta sakko daga kan benen, ta sakko falo taje ta leƙa taga, taga sunyi maganganu da Bala, sannan ya buɗe musu ƙofa suka fita.

Widad ta juya ta koma kan bene, ta koma ɗakin da Amminta take cikin sauri, tana zuwa ta tarar da ita a yadda ta batta.

Widad ta shiga jijjigata tana kiran  "Ammi ki tashi mutanen sun tafi, baki ji ciwo bako?"

Ganin Ammin nata bata motasa ba yasa tace  "Ammina bacci kikayi ne? Ko kuma sanyi kike ji?"

Nanma bata samu amsa ba, dan haka ta ɗakko bargo ta lulluɓeta, itama ta shiga bargon ta rungume Ammin nata, daga nan bacci yayi awon gaba da ita.

Dukda Kasancewarta yarinya ƙarama, amma da Asuba Amminta ke tashinta salla, Asuba tayi Widad ta tashi taje tayi salla, Amma Amminta bata motsa ba, ta sake zuwa ta kwanta a jikin gawar ta koma bacci, har kusan ƙarfe tara na safe Widad ta farka, ta shiga girgiza gawar Ammin tana  "Ammi ki tashi bakiyi salla ba, kuma yunwa nake ji, Ammina ki tashi ina jin yunwa, Ammi Abinci"  haka Widad ta cigaba da hayyata irin tasu ta yara, ba tare da tasan Ammin mutuwa tayi ba.

Tana nan zaune, ta gaji ta shiga wasa da gashin kan Ammin nata, tana mata surutu ba tare da tasan mutuwa tayi ba.

Tana nan zaune Bala ya buɗe ɗakin ya shigo, ya kalli Widad yace "ke a ina kika kwana?"

Kallonsa Widad tayi ta ɗauke kai, ya kalli Gawar Huda dake kwance a gurin, ya juya ya fita.

Wajen ƙarfe sha ɗaya sega Bulama da wasu abokan kasuwancin Daula, suka shigo har ɗakin, Bulama ya kalli Huda ya shiga rangaɗa salati, ya kalli Bala yace " kuma ba rashin lafiya ce ta kamata cikin dare ba?"

Bala yace  "nima ban sani ba, gani nai shiru banji motsinsu ba, shine na shiga dubawa, nazo na tarar da gawa da yarinya"

Bulama yayi ajiyar zuciya yace "Allah me iko, Allah yayi mata rahama amma abun da mamaki, munyi waya da Daula, lafiya ya tafi ya barsu, amma a wayi gari ta rasu, Allah kenan, yanzu dai a kira motar Asibiti aje da gawar a dubata a Asibiti, ita kuma daughter a tafi da ita gidana, zuwa muga yadda hali zeyi"

Widad ta dinga bin Bala da ido, tamkar bata taɓa ganinsa ba, duk inda ya motsa seta bishi da ido.

Aka ɗauketa aka tafi da ita gidan Bulama, aka tafi da gawar Huda Asibiti.

Tunda aka kai Widad gidan Bulama, ba tace uffan ba se kallonsu da take kamar baƙin halitta, aka bata Abinci harta fara ci, ta ture ta shiga kuka tana kiran Ammina.

Gaba ɗaya tausayinta, ya kama Hajiya Sarah, ta dinga rarrashin Widad amma fafur Widad taƙi yin shiru, Fahad yace "kai wannan wace irin jarabbabiyar yarinya ce, banza kawai ana ta magana ana rarrashin ta se wani iskanci take yi, shegiya kai me kama da Aljanu"

Fahad be rufe baki ba, Widad ta ɗauki wani kofin glass ta jefa masa, gaba ɗaya ta basu mamaki, suka juyo suna kallonta, kofin ya sameshi a ƙafa ya faɗi ya fashe, sannan kuma ta koma gefe tana kallonsa tana huci, kanta yayo ze maketa a zuciye, Hajiya Sarah ta tareshi tace

"yi haƙuri, marainiyar Allah ce, meyasa zaka zageta"

Fizgewa yayi ze daketa, amma Widad ta shammaceshi, ta kafa masa haƙora a hannu, da ƙyar aka ɓanɓareta dan seda gurin ya fashe.

Fahad ya dinga ihu yana "na shiga uku Mayya, 'yar gidan mayu zata shanye min jini"

Tun daga lokacin, ko hanya basa haɗawa da Widad, dan tunda ya zageta ta tsane shi, a wunin ranar nan gaba ɗaya suka rasa yadda za suyi da Widad, suka kasa gane kanta dan bata jin rarrashi, bata sanshi ba ga kafirin taurin kan masifa, taƙi cin Abinci taƙi saurarar kowa, da Hajiya Sarah ta gaji ta kira Bulama ta gaya masa, shi kuma yace ayiwa direbansa magana Fahad ya rako su Asibitin, dan Daula ya iso.

Fahad yace "Allah ya kiyaye in raka Mayya, wannan a binciki danginsu mayune, shegiya kawai"

Ƙarshe direba ne ya kai Widad Asibiti,  bata tsaya jiran direban ba, ta shiga cikin Asibitin tana leƙe leƙe, ta buɗa wannan ƙofar ta buɗe waccan.

A saman bene ta buɗe wani ɗaki, taga su Bulama da Bala a ciki da wasu mutane, se Mahaifinta durƙushe a gaban gado an rufe gawa, yana rusar uban kuka kamar ƙaramin yaro, Widad ta tsaya tayi sak tana binsu da kallo, Daula na ɗaga ido yaga Widad ya sake fashewa da kuka, ya miƙowa Widad hannu, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta faɗa jikinsa, cikin kuka Daula yace  "Lovely daughter, mun rasa Amminki, ta tafi ta barmu"

"Daddy ina Ammina"

Daula ya buɗe mata fuskar Huda, kamar kace mata tashi ta miƙe zaune.

"Your Mum is dead Daughter" yai maganar cikin kuka.

Zumbur Widad ta miƙe tsaye, tana kallon mahaifinta, idan bata manta ba ko a film da take kallo, when someone is dead, you won't see him again, that's mean her Ammi has gone, she won't see her again.

"Noooo Daddy, she's alive, she's not death!"

Wata irin ƙara tayi tana tirje tirje, ƙarshe se ɗaukarta akayi aka kaita pediatric, aka mata allurai, se bayan an kai Huda nakwancinta sannan Widad ta farka.

Amma tunda ta farka ba ummm ba umm, idonta a buɗe amma sam bata magana, bayan an dawo daga kai Huda, Daula se kuka yake yana sharɓe hawaye, Asibiti ya wuce gurin Widad ya tarar ta farka, su Bulama dai yana biye dashi dasu Bala, ya zauna ya rungume Widad a jikinsa, yana kuka yayin da Widad ta tsaida idonta akan Bala megadi, bata ko ƙyaftawa.

"Daddy, what exactly kills Ammi?" Tayi tambayar a bazata.

Daula yace "i don't actually know daughter, likitoci sunce ta samu cardiac failure ne"

"is a lie Daddy"

"How?"

"someone sponsored her murder, she was killed Daddy"

Daula yace "what are you trying to say?"

Mamaki ya cika su yadda take magana, sekace wata babba, kuma she's very serious about what she says "

Alhaji Munir yace  " ranka ya daɗe, yakamata fa muje gida, mutane na jiranka.

Haka suka tafi da gida, Daula na cigaba da kuka wiwi, Bulama da sauran mutane suka raka shi gida, har an kafa manyan rumfuna, manyan mutane gaba ɗaya sun hallara, anata miƙo gaisuwa.

Daula na rungume da Widad a jikinsa, Widad gani take kamar ƙaryane wai Ammi ta mutu.

Seda ta kwana biyu cirr ko gyangyaɗi ba tayi ba, hakan ya firgita Daula kar wani abu ya sameta, ya fara tunanin ko Asibiti ze maida ita, dan seta wuni ba tace uffan ba, sedai lokaci lokaci ta fashe da kuka.

Ranar uku, gidan nan ya cika da ɗan Adam, babu masaka tsinke Kasancewar ita kanta Huda mutuniyar kirki ce ga kyauta.

Ana zauna a nayiwa Daula gaisuwa, ta dubi wani babban ɗan sanda, ta tashi daga jikin Daula ta tafi gaban ɗan sandan ta zauna, ta kalle shi tace  "Are you a police?"

Ya amsa mata da 'yes my dear "

" Can i ask you a question? "

" Yes of course "

Widad tace  " idan na tambayeka, will you do your best to help me? "

Yace" insha Allah "

Widad tace" karka saɓa Alƙawari fa"

Mamaki ya kama mutanen gurin, yadda take zaro magana haka, daki daki kamar babbar mace.

Yace "insha Allah, i promise you, bazan saɓa ba"

Daula yace "lovely, dawo na kusa dani, karki dameshi"

Widad ta ɗagawa mahaifinta hannu, alamar ya ƙyaleta, ta kalli cikin idon ɗan sandan tace   "you promise to help me, tambayar da zan maka itace, idan aka rufe fuskar mutum da pillow ze mutu?"

Yace "kamar yaya?"

"misali, Daddy ya doramin pillow fuskata, inta motsi amma yaƙi ɗagani, kawai se misali Bala megadi ya dawo ya riƙemin ƙafa, in dena motsi, to zan iya mutuwa"

Yace "yes of course dear, it's a murder attack, kisan kai kenan a ina kikaga anyi?"

"Yanzu misali, idan na gaya maka a inda na gani, wani mataki zaka ɗauka?"

Gaba ɗaya rumfar tayi shiru, ana sauraren Widad, Ɗan sandan yace  "zamuyi abunda doka tace akai, idan har muka kama mutum da laifi, zamu kashi kotu a yanke masa hukunci"

"Arrest Bala! And the doctor that confirms that my Mum is dead, as a result of cardiac attack" ta faɗa kai tsaye

"Why" ya tambaye ta

Cikin ƙara tace  "Bala yasan suwaye suka kashe Ammina, kasheta akayi fa, i use to watch in movies, she was killed not dead as a result of cardiac attack, Ka kama Bala ko in kasheshi, he's responsible for the murder, na ganshi shine ya buɗe wa wasu ƙofa, suka rufe ammina da pillow, Arrest him i said "!

Gaba ɗaya Widad ta hargitsa gurin, ihu take sosai tana nema ta fita daga hayyacinta, se kurma ihu take tana akama Bala.

Alhaji Haruna yace" ya za'a biyewa yarinya ƙarama tana wa mutane shirme, watakila alhinin mutuwane ko mafarki tayi "

Daula ya fashe da kuka yace " Widad mutum ce, kuma yarinya ƙarama, amma idan kaga tayi maka ƙarya ajizanci ne irin na ɗan Adam, dan haka Arrest him, ayi bincike akai "

Yai maganar yana kuka, aikuwa Bala yana ihu haka aka buga masa ankwa akayi gaba dashi, nan wasu suka dinga jinjinawa kaifin basira irin na Widad da ƙarfin hali, yayin da wasubsuke ganin be kamata a kama Bala ba, tunda shirmen yarane.


Nan fa 'yan sanda kuma suka shiga bincike akan Bala, Widad ta fayyace musu yadda abun ya faru, Alhaji Haruna yace "Nasir, bekamata a biyewa yarinya ƙarama ba, ta faɗi magana sannan a yadda"

Daula yace "Tunda Widad ta faɗi haka ba ƙarya take ba, bata taɓa haka ba, kuma akwai ƙamshin gaskiya a lamarin nan, dan haka se abunda hukuma tace, dan nikaina bana ja da ikon Allah, amma tabbas mutuwar Huda, abar a bincika ce, lafiya muka rabu da ita, ba ta da wani ciwo, ace in dawo in tarar ta rasu, Allah na tuba "

Kawai ya fashe da kuka, Bulama yace " Nasir, kayi haƙuri nasan irin mahimmancin Huda a rayuwarka, amma karkayi abunda zaka dawo kana dana sani, kar azo aji kunya "

Widad na kan kujera, tana wasa da yatsunta, tunda suke maganar su bata saka baki ba, se yanzu tace "Daddy, ko nima na mutu kar ka bari a ƙyale Bala, seya faɗi wanda suka kashe Ammina, idan ba hakaba zan faɗa maka ko suwaye"

Zaro ido sukayi, suka juyo da kallonsu kanta, Daula yace "Baby na, dagaske kin san suwaye? Ya akayi kika sani? Gayamin suwaye, meyafaru?"


"Daddy nima ban san suwaye ba, amma nasan mutum ɗaya, naji sun faɗi sunan wani mutum, amma zanyi tunani in tuna, na manta sunan, amma zan tuna idan be faɗa ba zan faɗa"


Bulama yace "Daula anya yarinyar nan bata samu matsala a ƙwaƙwalwarta ba? Ji wata irin magana da take fa, Anya baza'a kaita Asibiti ba"


Alhaji Haruna yace "gaskiya kam, nima naga kamar alamun haka a tare da ita"


"Niba mahaukaciya bace, karku sake cemin mahaukaciya, ni nasan abunda nake, wasune suka danne Ammina da pillow, ni ina da hankali"

Daula ya rungumeta yace "Sorry my lovely, nima na sani lafiyarki ƙalau ai"


Wasa wasa Widad gaba ɗaya walwalarta ta ɗauke, ta dena walwala ta dena fara'a, ko Abinci bata iya ci saboda kewa dake damunta, wasu lokutan seta wuni akan gadon nan da aka kashe Ammi, ko haka kurum taje ta buɗe wardrobe ɗin Ammin, ta watso kayan Ammin duka ta zauna a cikin kayan tana rusa uban kuka, haka Daula zezo ya na rarrashinta, wani lokacin kuma ya zauna ya tayata kukan.


Sosai Widad kaɗaici yake damunta, dama gata bame son mutane ba, Babu wani dangi da suke dasu da suke zuwa gurin su, dan haka Widad abun ya ƙara nata yawa, haka kurum wani lokacin da daddare seta hau firgita tana cewa "Daddy gasu nan, ka tashi kaima karsu kasheka" ko taita ihu tana ƙoƙarin fita da gudu, se Daula ya riƙeta gam.


Sosai ta dena magana, sedai ta kan zauna taita kallon magunan Ammi da take kiwo, da zomaye da tsuntsaye, da yake Huda mace ce me son dabbobi, sosai take kula dasu tana ciyar dasu, idan Widad tana kallonsu, se taga kamar Amminta tana nan, zata zo ta basu Abinci, haka zata zauna tana musu magana

"Kuma kunyi missing Ammina ko? An kashe ta, amma zata zo ta baku Abinci"


Bulama yace "Daula, nifa na fara jin tsoro da sha'anin yarinyar nan, karfa muna zaune ta haukace, gaba ɗaya ta canza lokaci ɗaya, ta zama wata iri"

Daula yace "nima na gani, abun yana damuna, na rasa ya zanyi bana son in rasa ɗiyata, kota rasa hankalinta, gashi kullum cikin kashedi takemin akan, lallai kar in bari a saki Bala, sannan idan be faɗi waye ba ita zata faɗa, nayi nayi ta faɗa taƙi gayamin, yanzu fa ko Abincin kirki bata ci, se koke koke"


Bulama yace "yanzu ajiyar da ka bata na dukiyar nan, baka tsoron ta samun taɓin Ƙwaƙwalwa, ayi asarar maƙudan kuɗaɗen nan?"


Daula yace "duk me wannan dukiyar, in dai ta sace ko waye, kuma ko a ina yaje, seya karɓi kayarsa dan haka wannan ba abun damuwa bane, ni abunda ya dameni yanzu, shine lafiyar ta"


Bulama yace "karka damu, akwai wani likitan ƙwaƙwalwa da Alhaji Munir ya sani, zan masa magana ya turoshi yazo ya duba ta"

Haka akayi, washegari Bulama yazo da Likitan nan da Alhaji Munir, Widad na ganinsa ta miƙe da gudu ta maƙalƙale Daula, juyin duniya ta sunkuyar da kanta taƙi kallonsu.


Suka gaisa da Daula, Daula yace "lovely ga likita ze dubaki, ki gaishe shi"

Ƙara sunkuyar da kai tayi, taƙi kallonsu, likitan yace "Baby zomu gaisa mana, tambayarki zanyi"

"Niba mahaukaciya bace" ta bashi amsa.

"Ai bance mahaukaciya bace ke, tambayarki kawai zanyi"

Juyin duniya Widad taƙi magana, duk tambayoyin da suke mata taƙi amsawa, likitan nan ya kaɗa ya raya, amma tayi mursisi kamar yana magana da itace.


Daula yasa hannu ya janyo ta daga bayansa data shige, ta sunkuyar da kai kamar sabuwar bokanya.

Ya ɗorata akan cinyarsa yace "Babyna lookup" ta ɗago ta kalli mahaifinta idonta fal hawaye.

Yace "ba cutar dake za suyi ba, tambayarki za'ayi lafiyarki nake son a dubamin, kinji Gimbiyar Daddynta"

"Daddy, idan Bala be faɗi wanda suka kashe Ammina ba, zan faɗi sunan da mutanen suka faɗa idan na tuna, ina kallonsu Bala ne ya rufe Alba Dog, ya buɗe musu ƙofa, shiya rako su har kan bene, ina kitchen ina kallonsu, har akace su nemoni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login