Showing 114001 words to 117000 words out of 209297 words
sarkin shirirta, da shirme, ga tsabar ƙuruciya mutum baze gane hakan ba, se ya zauna dake, to ni bame yiwa 'yata kitso balle a jagwalgwala mata kai, idan kin haifi namiji nakine, mace kuma ta wace"
"A' a ban yadda ba, gaba ɗaya nawane, bayan kace baka son Baby"
Yusuf yace "Nina ce miki bana so? So kai amma ki bari ki samu cikin tukuna, sekimin iyayi da tsari"
"wai dan Allah dagaske bani da ciki?"
Yace "zan miki ƙarya ne? Kin manta shekarata biyu ina medicine, baki da komai madam"
Ta kwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "insha Allah ina da shi"
"Seki zauna kiyi ta imagination ai, miƙomin abincin nan inci"
Ta ɗakko kwananon Abinci ta miƙo masa, suka ci tare suna hira.
Yusuf yace "idan na dawo da daddare, kwaɗon gurji da zogale zan mana, zaki ci?"
Widad tace "Sosai ma, ranar Gwaggo tayi naci da daɗi Sosai"
Yusuf murmushi yace "to kwaɗayayyiya"
"Eh anji ɗin"
A haka suka yi sallama, yana ta tsokanarta, kamar karsu rabu.
Duk iya dubawar da Saleh zeyi, yayi amma ya rasa takaddar nan, ya duba ya duba amma takadda tace ɗaukeni inda ka'a ajiyeni, gashi yacewa Bukar ya karɓo takaddar nan.
Ya koma guest House ɗinsa, inda suka dinga kokawa da Amal, ya dinga duba takaddar nan, yai tsai gana dubawa ya birkita komai, ya hango ta a ƙasan gado.
Hamdala yayi, ya durƙusa ya ɗakko takaddar, yana ajiyar zuciya ya buɗe takaddar, sedai me ba takaddar bace form ne na koyon kwalliya na Amal, tsaki yayi yai jifa da takaddar yana tunanin ina yasa waccan takadda data bashi, amma kuma lokacin da ta bashi takaddar ai be buɗa ba, balle yasan me ta bashi, hankalinsa na kan yai mata akuyanci kawai, ya birkita ko ina amma babu wata takaddar se wannan, nan take gumi ya shiga tsasttsafo masa.
Widad taita jiran Yusuf ya dawo, dan se nishaɗi take ji ze kawo gurji yayi musu kwaɗo, bayan ya dawo da kayan gurjin da yamma, ta zauna ta cire ɓawon tsaf, ta gyara zogalen suka ɗora zogalen akan wuta, suna zaune suna hira a ƙofar ɗakinsu suna aikin su, hankali kwance yayin da zamantakewarsu kan burge wasu daga mutanen gidan.
Ya gama suka haɗa Kwaɗon nan a roba, Suka bawa wanda zasu bawa, Widad se haɗiyar yawu take, ta zauna zata saka hannu ta fara ci Yusuf yace "tsaya waye yace ki fara ci, salon ki fini loma ki fini ci ko?"
Ai ba ta saurareshi ba, danji take kamar hanjinta ze fito idan bata ci ba, jiki na rawa ta sa hannu ta fara cin Abunta, Yusuf yana kallonta yana nazarinta, tunda ta fara ci bata saurareshi ba seda taji ta ƙoshi tukuna, ta miƙe taje ta wanke hannunta ta sha ruwa ta dawo ɗaki sannan tace " Yawwa ina jinka, mema kace ɗazu?"
Yace "cewa nayi, sannu da aiki acici"
"Yawwa mijin acici, kai dai ubangiji Allah yayi maka albarka, ya saka maka da alheri nagode sosai"
Yace "Ameen, amma a dena cinye Abinci ana barina"
Kawai ta kwashe da dariya tace "ba ruwana cin abuna zanyi ehe"
Yace "ai shikenan poor me"
Tace "shagwaɓaɓe kawai, me sexy eyes"
Yace "what, sexy eyes kuma sekace wani mace"
"baka sani ba, you are having sexy eyes fa"
"Mhmm Malam kawai kice abunda yake ranki kenan"
Tace "What? Wai Yoseef meye haka? Kawai ba damar inyi magana seka canza mata ma'ana"
Tai maganar tana kai masa duka, ya kwanta yana dariya yasa pillow yana karewa.
"Kuma ma kai mummuna ne" tace tana harararsa.
"Eh naji bakomai, a haka 'yan mata suke rububina, saboda munina a haka suke sona"
Widad tace "Wallahi idan muka koma gida, duk wadda tayi gangancin raɓarka zata ga matakin da zan ɗauka wallahi"
Tai maganar very serious, dan kamar ma haushi taji.
Yace "haka akeyi, shikenan duk suna kallo se kice baza'a kulani ba, bayan kin sanni da farinjini, cewa fa kika yi in Auri Hanne"
Tsaki tayi zata tashi, ya fizgota jikinsa, yasa fitila ya haske mata fuska.
"Ni ka dena haskani, bana so"
Yusuf yai ƙasa da murya yace "An taɓa gayamiki ke kyakkyawa ce kuwa My wife?"
"Ai ko ba'a faɗa ba, nasan ni me kyauce sakeni"
"in sake ki kuma?"
Da sauri tace "No, i don't mean you should divorce me, ka cikani i mean"
Yai murmushi yace "nima na sani ai, ni dake ai mutu ka raba Babayna me kama da teddy"
Tace "Yoseef me yake damunka ne yau? Duk ka takuramin nice kuma me kama da teddy?"
"Eh ramawa nayi, ko kin manta haka kika cemin cartoon jiya"
Yai maganar yana dariya, itama dariyar ce ta kamata, ta buɗe baki kamar zata cije shi, amma ta fara kissing ɗinsa.
Kamar ranar suka fara kasancewa da juna, sunyi nishaɗi mara misaltuwa, sun farantawa junansu rai sosai, kowanne yana sake jin ɗan uwansa a ransa.
Haka suka wayi gari cikin farin ciki, sedai dukda wannan farincikin Yusuf se fama yake da fargaba, ya rasa dalilin hakan.
Yana ta shiri ze fita, yaji kamar harbin bindiga, gabansa ya faɗi yace "Lovely, kamar harbi fa nake ji"
Widad tace "A'a ko dai tunanin gurin aiki kake, amma wane irin harbin bindiga ana zaune ƙalau? Bari inyi walha, idan na idar seka tafi"
Ta juya ta tada salla, tayi raka'ar farko zata yi ta biyu suka ji Hayaniya, aka sake harba bindiga a ƙofar gidan mutane nata guje guje.
Yusuf yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
Daga tsakar gida suka ji ana "duk wanda ya motsa, zamu fasa kansa da bindiga, kowa ya tsaya a inda yake"
Gaba ɗaya jikinsu se tsuma yake, Hari ta samu wani lungu a bayan randa ta shige, se zare ido take saboda tsoro.
Nan da nan sega jiniyar motar' yan sanda ta ƙaraso
Da gudu Widad ta fito tsakar gidan, amma taga 'yan sanda tare da Saleh hannunsa duk ankwa a cikin mawuyacin hali.
Tace "me zan gani haka? Meye haka?"
Wani ɗan sanda yace "Yusuf, ina Yusuf yake?"
Widad tace "ban sani ba, bazan faɗi inda yaken ba"
Hari daga inda ta laɓe tace "Wudas ki dena magana karsu kashe ki fa"
"Ina Yusuf yake!" a kai mata magana cikin tsawa.
Itama cikin tsawar tace "ban sani ba nace"
Yusuf ya fito daga ɗakinsu, jikinsa sanye da jallabiya, ya ƙarasa gabansu ya miƙa musu hannunsa cikin surrender
.
Widad ta fashe da kuka tace "No! This is impossible, me yayi muku? Laifin me yayi mijinane fa, ku cire masa wannan cuff ɗin"
Su kai mata banza suka tasa ƙeyar Yusuf, itama suka sata a gaba ihu take tana kururuwa akan su sake shi amma sukayi burus da ita.
Aka sashi a bayan motar 'yan sanda, idonsa yayi ja ya kasa magana, se kallonta da yake gaba ɗaya ta birkice se ihu take tana kuka, muryarta harta fara dashewa.
"Ina sonka, Yusuf ina sonka, I love you Yusuf, dan Allah ku sakarmin mijina, beyi laifi ba, beyi laifin komai ba"
Yusuf ya ƙura mata ido, ya lumshe idonsa a hankali, yayin da Widad ke zubda wani irin hawaye tana kuka, me sauti.
Aka sakata a motar gida seinna, shikuma a bayan motar 'yan sanda gashi ga Saleh, kowanne hannu da sarƙa!!!
(Rayuwa ƙaddarace kowa da irin tasa......... 🎶 )
LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
IDAN KUMA KIN SIYA AMANACE KARKI FITARMIN DAN ALLAH 🙏🙏🙏
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
11/17/21, 5:35 PM - Buhainat: LITTAFIN KUƊI NE, DAN ALLAH KI SIYA KAFIN KI KARANTA BA DANNI BA DAN ALLAH, LITTAFI NA ƊAYA KYAUTA NE WANNAN NA SIYARWA NE
NORMAL GROUP ₦300
VIP ₦500 NE KITURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0009450228
JA'IZ BANK
AISHA ADAM
SE A TURA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR
07063065680
(Albishir ga masoya, ma'abota bibiyar litattaafaina, dama ta samu zaku fara samun litattaafaina na audio, akan YouTube channel ɗina me suna Cool Arewa TV
https://youtube.com/channel/UCD5vnvA5laU8ti4LLz2_QEg
Kuyi liking sannan ku danna subscribe, domin fara samun litattaafaina na audio, nagode sosai da ƙaunar ku gareni"
106_107
Sosai Widad ta cigaba da gunjin kuka, yayin da mutanen ƙauyen suka fito suka yi duru duru suna kallo, ɗaliban Widad se kuka suke, haka Hindu gaba ɗaya ta birkice banda kuka ba abunda take yi, ba Hindu ba kawai hatta Megari, da su Hari hankalinsu ya tashi sosai, ga Sunusi mijin Jamila baya nan akazo aka kama su Widad.
Ana tafe a hanya amma bakin Widad yaƙi mutuwa, kuka kawai take akan a sakar mata mijin ta, tun Yusuf yana iya juyo muryarta da kukanta, har muryar tata ta dashe ba ajin me take faɗa sosai, haka sukaita tafiya har suka fito daga wannan kwazazzaban, da ramukan dake hanyar garin, suka hau kan kwalta ɗoɗar suka kama hanyar Kano.
Alhaji Haruna fa ya haɗa uban gumi, saboda ya tabattar da babu wannan takadda, takaddar form ɗin koyon kwalliya ta bashi, ba shiri ya ɗau wayarsa ya kirata da lambar da ta kirashi ɗazu, tana ganin kiran nasa Amal ta tashi da sauri, ta duba har zata ɗaga kawai ta fasa, ta ajiye wayar yai mata kira yafi Ashirin, ƙarshema ta saka wayar a silent tai kwanciyarta.
Yai wujiga wujiga, saboda takaddar nan saboda yasan Bukar ba kyau, gashi ya riga yace aiya karɓo, tunda takaddar zata iya zama sheda a kansu, wannan wasiƙar zata nuna akwai halin rashin gaskiya da mahaifiyar Anwar take aikatawa wanda yasa ya bar gida, idan tuhuma tayi tuhuma kuma za'a gano su.
Ya tura mata saƙo kusan kala shida amma babu reply, can dai ta ɗau wayar ta duba saƙon daya turo, magiya yake mata akan dan Allah ta ɗaga wayarsa, mahimmiyar magana yake son suyi.
Tana cikin karantawa kuwa ya kuma kira, seda taja aji sannan ta ɗaga, yai ajiyar zuciya yace "habba kyakkyawa, tun ɗazu naake kiran waya, amma anyi biris dani?"
Tace "to me kake so in maka? Ko in ɗaga in ce maka?"
"A'a kwantar da hankalinki, ai duk abun bana zafi bame ko ɗaga hankali, magana zamuyi"
Tace "ina jinka"
Yace "Yawwa, dama cewa nayi wannan takaddar da kika kawomin, kinyi mistake ba wasiƙar kika bani ba, form ɗinki ne na koyon kwalliya, kinyi mistake gurin bani"
Tace "se akayi yaya?"
"A'a dama ba wani abu bane ba, cewa nai zanzo in karɓa in an jima, saboda takaddar tana da mahimmanci sosai"
"Karka sake ka soma zuwa inda nake, bazan bayarba ka riƙe wadda na baka a matsayin ta"
Alhaji Haruna yai gyaran murya yace "haba beautiful Baby, ai abun duk bekamata ya kaimu ga haka ba, meye na ɗaukar zafi haka? Ai abun bana zafi bane ba, ki gayamin me kike so ayi yanzu in karɓi takaddar nan? Ko nawane zan baki"
Amal ta janyo Jakarta, wadda yace tayi accident da ita, ta duba amma itama taga babu takaddar a ciki, amma tai ajiyar zuciya tace "nima nazo maka da buƙata ta, amma kaƙi amincewa, dan haka kowa ha riƙe buƙatarsa, bazan bayarba gara asirin kowa ma ya tonu a huta"
Yace "Subhanallah, hadda mamanki fa"
Tace "har ita ɗin"
Yace "dan Allah kar muyi haka dake, ki bani takaddar nan na riga na cewa Bukar na karɓo takardar yace in kai masa, kuma yanzu inzo ince bahaka ba, baze sauraramin ba"
Amal tace "Ai gara karya saurara makan, kamar yadda nima baka sauraramin ba, kuma baka karɓi buƙata ta ba"
Yace "dakata, yanzu idan na karɓi buƙatar taki shikenan?"
Am tace "A'a ai kuma mun wuce wannan maganar yanzu, zan baka takadda bisa sharuɗa, yanzu abu na farko zan gaya maka Account Number ɗina, ina son inji wasu kuɗi masu nauyi, domin inci kaji in warke da wuri daga raunin daka min"
"Shikenan zan turomiki, yaushe zanzo in karɓa"?
Tace "turo ɗin tukuna in gani mana"
Yace "shikenan naji"
Ta kashe wayarta, lumshe ido tare da faɗin "Alhamdilillah, cikin sauƙi Allah ya kawomin hanyar da zan rama cin zarafin da kayi min, tabbas inaga yadda takkadar nan nayi, dan babu ita a jakata, amma a haka zan maka rashin mutunci in rama"
Alert ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta duba 500k ne, ta jinjina kai tace yanzu aka fara wasan
Seda yayi mata kira biyar, sannan ta ɗaga a fusace tace "wai meye ne?"
"dama cewa zanyi, kinga alert ɗin?"
Tace "na gani, amma sunmin kaɗan, na kuma raina"
Ta katse kiran tare da kashe wayarta gaba ɗaya, ta kulle ɗakinta da key, tai kwanciyarta.
Tunda suka taho Yusuf bece uffan ba, yai shiru yana saƙawa yana kwancewa a zuciyarsa, tabbas duk sunan da za'a kira shi dashi, ko a tuhume shi dashi, bashi da abunda ze kare kansa dashi, tabbas shi dai tunda ya tashi a rayuwarsa a siraɗin ƙaddara yake, daga wannan ya faɗa waccan, daga waccan ya faɗo wannan, haka ya sunkuyar da kansa yana ta tsabihi ga Allah, akan ya sauƙaƙa masa wannan lamarin.
Sun shigowa cikin garin kano, akayi hanyar babbar headquarter hukumar 'yan sanda dake garin kano, motarsu Widad kuma tayi wani gurin, ai tana ganin haka ta kuma fashewa da ihu, tana bori tana kuka tana "ina zaku kaishi? Ina zaku kaimin mijina? Beyi laifin komai ba, babu abunda yayi muku, ku ƙyalemin mijina wayyo Allah na Yoseef duk nice sila, saboda ni ka shiga wannan tashin hankalin, Dan Allah ka yafemin Yoseef, Allah ka fitar da mijina daga sharrin Azzaluman nan, Allah ga bawanka ka fitarmin da mijina"
Ta ƙarasa maganar, tana wani irin kuka me taɓa zuciya babu wanda ya kula ta a cikin 'yan sandan suka cigaba da tafiya.
Wani ofishin' yan sandan aka tafi da ita, suka fito da ita daga mota zuwa gurin 'yan sanda, idanunta sun kumbura sunyi ja saboda kuka.
Wani ɗan sanda yace "gata yallaɓai, yanzu muka shigo gari, shi an wuce dashi headquarter, ita kuma gata"
Ɗan sandan ya kalleta yace "Good, Madam congratulations, you are now free, mun cetoki daga hannun wanda sukayi garkuwa dake"
"Niba garkuwa yayi dani ba, wanda sukayi garkuwa dani daban, Yoseef ceto na yayi, shine ya temakeni beyi garkuwa dani ba, ka gaya musu suje su sakarmin mijina"
Ɗan sandan yace "koma dai ya akayi, wannan ku ta shafa ke dashi, muba abunda ya dame mu, zamu rubuta sannan mu sanar da duniya cewar, munyi namijin ƙoƙari gurin bincike mun gano wanda yayi garkuwa da Widad Nasir Daula, kuma ba wani bane face direbanta, wanda ya kasance ɗansanda, yaje gidansu yai basaja dan yayi garkuwa da ita, nasan hakan ze sake ɗaga darajar rundunar mu a ga namijin ƙoƙarin da muke, ba dare ba rana gurin kare rayuka da kuma dukiyoyin al'umma "
" Shut up!!! "
Ta faɗa cikin ƙaraji, tace " idan har ina raye ina numfashi, ko komai nawa ze ƙare se Yusuf ya fita, babu wanda ze cutarmin dashi, baku isa ba azzalumai ma cuta, lokacin da aka yi garkuwa damu muna buƙatar taimakk, babu wanda ya taimakemu na kusa rasa rayuwa ta, se yanzu da yayi komai ya gama, Allah yasa ya kare rayuwata, shine za'a masa sharri wallahi bazan lamunta ba, he's my Husband "
Ɗan sandan nan yace " ku ɗaukemin wannan mahaukaciyar daga gabana, a tafi da ita Asibiti a duba lafiyarta, sannan ku kiramin Ubanta Bulama tunda babu wanda yasan inda wancan yake "
Widad bata gane meyake nufi ba ta cigaba da kukanta, haka suka kawo Ambulance dan iya makirci, aka sheƙa mata wani abu ta sume a gurin, aka kira 'yan jaridu suka cika gurin, aka ɗauki Widad aka saka ta a motar Agajin gaggawa wato Ambulance suka tafi da ita.
Jaridu kuwa da sassafe shafin farko, hotunan Yusuf ne da Saleh, musamman na Yusuf ɗaure a cikin sarƙa ya sunkuyar da kai, gefe ga hoton Widad da aka ɗauka an fito da ita daga ofishin 'yan sanda an sata a ambulance, daka kunna gidan radio, labarai ko talabijin babu abunda zaka fara ji se
"Me dokar bacci ya ɓige da gyangyɗi, kuma ƙarshen tika tiki tik inji hausawa A yaune jami' am tasaro sukayi nasarar cafke jami'in ɗan sandan nan na farin kaya wato Yusuf Bashir Maitama, wanda yayi garkuwa da 'yar gidan fitaccen me Arziki nan a gida da wajen Nigeria wato Nasir Daula,' yan sandan sunyi nasarar gano shi ya sace ta tare da ɓoyeta a wani ƙasurgumin ƙauye dake garin Bauchi, 'yan sandan sun ceto Widad Nasir Daula, wadda ke cikin mawuyacin hali, da zauwansu basu yi wata wata ba aka kira motar Asibiti aka tafi da ita domin duba lafiyarta, zamu ci gaba da bibiya da kasa kunne domin jin wani mataki hukuma zata ɗauka akan wannan ɗan sanda, wanda ake tunanin har shi Nasir Daula ɗin shine yai garkuwa dashi, mu dai anan se muce Allah ya kyauta, yai mana tsari da irin wannan jam'ian tsaro a cikin al'ummar mu"
Nan fa gari ya ɗau ɗumi, aka dinga cece kuce, wasu na Allah wadai suna Tsinewa Yusuf, yayin da wasu ke a bari a ga abunda bincike zeyi tukuna.
Widad kam bata sake sanin inda kanta yake ba, inda har a gadon Asibiti aka bita aka dinga ɗaukar hotunan ta, ga fuskarta tayi ja saboda kuka, da gajiyar tafiyar hanya, amma aka dinga ɗauka ana watsawa duniya wai tana cikin mawuyacin hali, hannunta ɗauke da drip.
Alhaji Haruna ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba a taɓa raina masa hankali kamar yadda akayi yau ba, ya kira layin Hajiya Halima, Ramlah na zaune a falo wayar ta fara ringing, Mummy tana ciki tana amsa wata wayar dan haka ta ɗaga wayar tasa a kunnenta tace "Hello"
Yace "Yawwa Amal ce?"
"No Ramlah ce"
"Dan Allah idan Amal tana kusa ɗan bata wayar muyi magana"
Tace "tana ɗakinta, bari in kai mata"
Ta miƙe ta tafi ɗakin Amal, amma ɗakin a rufe harta kashe fitila ma "
Ramlah tace " gaskiya tayi bacci, dan ta rufe ɗakinta ma ta kashe fitila"
Yace "Yasalam"
Ramlah tace "ya dai? Akwai matsala ne?"
"A'a babu wata matsala, ina son muyi magana ne kawai"
"to ka gayamin saƙon in bata mana"
Yace "A'a karki damu, idan ta tashi na sake kira"
Ya kashe wayar yace "Amma dai Allah ya Tsinewa yarinyar nan, kaga min shegiyar yarinya mara albarka" ya ciji yatsa yai ƙwafa yace "dani kike zancen