Showing 30001 words to 33000 words out of 225640 words
kowa take son yana morewa da abunta ba.
“Kin gama sharar ne da kika zauna kina kallo”
Ataa ta juyo da sauri jikinta har ba ri yake ta kalleta.
“Eh na gama tun dazu na share ko'ina na gyara”
“To daga yau karki sake rufe mana fuskarki, idan ba za ki iya bude fuska ba ko zauna a gidanku ba yadda za ki zo ki cutar da mu ki tafi ba tare da mun ha fuskarki ba”
“Wallahi ni ba na cutarta kowa”
“Ai ba za a iya ganewa a fatar ba ki ba, shiga dayan dakin ki wanke bathroom din kuma ki gyada dakin”
Tana fada mata sannan na nufi kitchen dinta dan tabbatar idan kayan sun wanku.
ATAA POV.
Daukar tsinsiyar nai na hau sama a doshi dayan dakin wanda na ke saka ran shine dakin mijin, ciki tsoro da fargaba nai knocked, sannan na ja baya kadan na tsaya ina ta jiran ace min na shigo amman shiru, sai hakan yasa ni jin babu dadi, daga fara aikina a yau na fahimci daga matar har mijin kamar ba su san darajar dan adam ba, wata kila kuma saboda na kawo kaina ne, ni da kaina ina nema shiyasa suke wulakanta ni oho. Na fi karfin minti talatin a tsaye bakin kofar sannan ya fito yana ta kamshin turare, har wani matsawa yake kai ya ra6o ta kusa da ni ya sauka downstairs.
Be ba ni izinin shiga ba, dan haka ba zan shiga na taba wani abun da zai iya zan min matsala ba. Haka nai tsaye a gurin na kasa sauko kuma na kasa sai duk na ji na tsawwala, wani kankanci da bakincikin suka kwankwaso min kofa, na tabbatar da a ce yar wani ce ni da ba za su bar ni a gurin tsaye ba, za su nuna min kyama ba. Suna min duka wannan saboda ina talaka kuma na raba jikinsu ina neman taimako.
Da gaji da tsayuwar ne na sauko kasa cike da fargabar abunda za ta ce min da Kuma irin kallon da mijinta zai min.
Tana zaune kan kujera ita kadai tana waya, da alama wayar tai mata dadi sai kyalkyalar dariya take tana buga kafa kasa, ni dai kallonta kawai na ke, irin rayuwar jindadi da take ciki ta burgeni ga ta cikin farinciki abunda na ke ta marmarin samu amman ya gagara, zaunawa nai kasa tile har ta gama wayar sannan na ce
“Be ce min ya na shiga ba, ni kuma ban shiga ba, gudun kar na shiga ya zama laifi”
“Ya ce baya son ki gyara masa dakinsa”
“Yanzu zan iya zuwa gida kenan?”
“Idan kin ga dama”
“Na gode”
Sai na nufi inda na dauko tsintsiyar na maida, sannan na dawo na dauki dattin sharar na fita da ita daga gidan gaba daya, can karshen layin unguwar n samu wata bola na zuba ta a ciki sannan na dawo na aje shi a inda na dauke shi na yi mata sallama ban jira ta amsa ba, na kama hanyar gata zuciyata na mugun kuna kamar an dora ta ka ce garwashin wuta.
Ina tafe ina ta tunanin kamar ba zan iya jure aiki a gidan ba har na tsawon wata daya, saboda yadda na fahimcin hayyarsu da dabi'unsu ba kamar na kowa ba ne, sai dai idan ban yi aikin ba kudin su fa? Ai dole na biyasu bayan kuma na riga na taba wani abu daga ciki kuma ina da bukatar kudin.
Kamar yadda aka kai ni dazu haka wani mai achaba ya dawo da ni na bashi naira hansi sannan na shiga gidan, ina yin sallama Farida ta amsa tana wanke wanke, fuskarta da far'a kamar kullum ni ma na yi kokari aron murmushi na yaba a fuskata duk kuwa da kasancewar shi a kusa da ni.
“Har kin dawo? Nana tace min kin samu aiki?”
“Eh na samu, yau na fara”
“Allah ya taimaka, wane unguwa?”
“Nasarawa”
Na bata amsa ina shiga inda Nana take, wanann karon a zaune na same ta ta saka dayan hannunta ta dafe gefen cikinta tana hawaye. Da alama ciwon ne ya taso mata domin ba abu kadan ke kasa nana yin hawaye ba musamman ciwo. Kusa da ita na zauna na rafka uban tagumi ina ta kallon saukar hawayenta, ban san abunda zan yi ta samu lafiya ba, ban zan zwa zan kaiwa kuka ya saurareni ba, Doc Asim ya zalince mu zalince mai tsanani kuma na kai kararsa aka kasa kwatar min hakkina suka kasa bani gaskiya saboda ina talaka shi kuma yana mai arziki. Sai wani numfashi take wahalce ni kuma na kasa ko motsawa daga inda na ke zaune balle nai nata sannu yadda take hawaye haka ni ma na ke hawayen, kashi ya hade min goma da shirin can ba dadi nan ma ba dadi.
“Ni kadai na san irin zabar da na ke sha a kan ciwon nan, ni kadai na san yadda zafin ciwon nan yake min, ni kam da ma na mutu wata kila da na fu samu sauki fiye da haka”
Cikin murya kuka ta fadi haka da sauki kasa-kasa. Hannu nasa na share hawaye na daga inda na hango kudin da na bata dazun na dauka na fito jiki ba kwari na je bakin titi gurin wata pharmacy, na fada masa yadda ciwon yake sai ya ba ni magani kusan dubu uku da dari bakwai na dawo jiki na rawa na balla na bata na shafawan kuma na shafa mata, sai na koma ta bayanta na rumgumeta na fashe da kuka marar sauti, ji na ke kamar ace ina wata dama zan iya nema mata lafiya ta warke ita kadai ta rage min idan ta tafi ta barni ban san halin da zan shiga ba.
Na dade rumgume da mahaifiyata sannan na saketa ta kwanta, ni kuma na goge fuskata na fito tsakar gidan ko za a samu sassaucin abinda na ke ji a zuciyata. Da na fito sai Farida ta dasa min wata sabuwar fira dama akwai da yawan magana, a nan take labarta min cewar mahaifinta ne ya ce Nana ta dawo nan ta raba ta zauna tun da mai wacan kangon gidan ya koreta gashi bata da wani gurin zama. Ni kaina nasan indai Farida ba to ko sai mahaifinta, domin mahaifiyarta ba zata taba yarda tace ta zauna a gidan ba.
Bayan sallah magariba na dauki kudi da kwano na siyawa nana tuwon masara da miyar yauki domin shine mai yar nasiha ba kamar shimkafa ba mai tsada, ko da na shigo na tarar ta samu sauki sosai tana zaune saman dankwalinta da tai sallah. Gaba na saka ta na cilasta mata cin tuwon ita kuma ta ki ta ci ala dole sai ni na fara ci, a dole sai na ci sannan ita ma ta ci na kawa mata ruwa ta sha, sannan muka gabatarda Allah isha'i muka kwanta a gurin da mutum ba zai iya mike kafafuwansa ba straight ba.
*** *** ***
Da wuri na farka gudun kar nai lattin zuwa gurin aiki, bayan na ayi alwala ita kuma na samo mata kasa tai taimama ta yi sallah asuba, cikin kudin na dauka naje na siyo mana koko da kosai da suga na kawo muka karya sannan na shiga bandaki nai wanka da ruwan sanyi duk da kasancewar akwai sanyin safiya da be gama sauka ba.
Bayan na fito na saka wasu tufafi, daman can shafa mai be dame ni ba bayan cikin tsarina wankan ma gudun kar suce ina wari da ba zan yi ba. Haka na shirya cikin wata kodaddiyar atamfata na sake kwaba gawayi kamar ranar na shafa a fuskata, tun da sun ce na daina saka nikab sai na saka bakin gawayin da na saba sakawa duk kuwa da irin kazantar da suke ganina da shi.
Yau ma sai da na dauki naira dari a cikin kudin sannan na saka Hijab dina na yi ma Nana sallama na fito na shiga dakin Maman su Farida na gaishe ta ita da mijinta shi ya amsa da far'a sabanin ita da ko kallon kirki bata min ba, wata kila tana ganin kamar mun takura tane mun zauna mata a gida mun hana ta wali a yadda a gidanta.
Yau ma achaba na hau na fada masa inda zai kai ni, ba aje ni ko'ina ba sai bakin gate din gidan na mika masa kudinsa na sauka, ina kokarin yin knocked gate din sai na ga an bude shi gaba daya, ashe mai gidan ne zai fita sa na raba gefe sai da ya fice sannan na shiga ina mikawa mai gadin gaisuwa bayan ya amsa min na nufi kofar gidan wato kofar babban falon da zai sada ka da cikin gidan gaba daya. Da nai knocked din kofar sai na zauna kusa da kofar dan nasan ba yanzu zata bude min ba, haka nai ta zama a gurin har mai gidan ya dawo ya faka motarsa inda sauran motocin suke ya fito fuskarsa da Annuri da haifa ya nufo kofar ya saka keys din hannunsa ya bude.
“Ina kwana?”
Be amsa min ba, sai kallon fuskata yake ta yi wata kila yana mamakin yadda yau ban saka nikab dinba na sake shafa bakin gawayi, ni dai ban kalleshi ba domin matarsa ta fada min mijinta baya son kallo. Shi ya fara shiga sannan na bi bayansa na shiga kai tsaye na nufi gurin jiya na dauko tsintsiyar da mopper na fara gyara falon sannan na shiga kitchen na gyara, ban san a wane dakin ta ke kwance bana son na shiga ta ce na mata ba dai-dai. Sai kawai na nemi gefen kujera na zauna, ina ta jiran fitowarta shiru har bachi ya dauke ni a gurin ban sani ba. Can cikin bachin nawa na ji an watso min ruwa mai dumi hakan yasa ni farkawa a firgice, ashe ruwan tea da ke hannunta ta watsa min.
“Ina kwana”
Na mika mata gaisuwa kamar a rikice.
“Ba ki yi bachi a can gidanku ba ne da za ki zo nan kina mana bachi? Ba aiki aka dauke ki ba?”
“Na gyara nan na gyara kitchen ina jiran ki fito sai na gyada dakunan”
“Miye a fuskarki kuma?”
Na yi shiru ban ce mata komai ba sai kawai ta tabe baki ta zauna a kan kujerar.
“Shiga ki gyara min bedrooms dina”
“To”
Na amsa a ladafce sannan na dauki tsitsiyar na nufi dakunan na gyara na na dawo na dauki mopping na goge ko'ina na wanke bandakunan sannan na sauko.
“Na kare”
Na fada mata bayan na maida kayan inda na daukosu. A gurin ta bar ni tsaye bata ce na tafi ba, ba ta ce na tsaya ba, har jikinta sauko hannunsa rike da agogon hannu yana kokarin sakawa.
“Kin tabbatar za ki iya driving da kanki? Idan ba za ki iya ba don't stress yourself zan turo direba ya kai ki”
Shine abunda ya fada mata, ita kuma ta girgiza masa kai.
“Aa zan iya, wannan yarinyar za ta rika min kayan”
A gabana ya kai bakinsa a goshinta ya sumbace ta babu ko kunya, shi da kiss ni da jin kunya har na ji kamar kasa ta nutse da ni da kunya. Be yi minti talatin da fita ba ta hau sama ta bar a gurin a tsaye ina ta jiran saukowarta, sai da tai wanka ta shirya cikin wani lace mai kyau da tsada sannan ta sauko idonta sanye da katon bakin gilashi nan na mata.
“Shiga dakina ki dauko min ledodi ki saka mota”
Abun ka da mai jiran umarni sai nai hanzari cira kafa na taka har dakin na dauko na kai gurin motar da ta bude na zuba su a baya, sai kuma nai tsaye ina jiran abunda za ta ce min. Bayan boot din taje ta dauko wani tawul ta miko min.
“Shimfida wannan a baya sannan ki zauna karki shafa min dattin jikinki a mota”
Na saka hannu na karba cike da jin zafin furucinta, na shimfida kamar yadda ta fada sannan na zauna ita kuma ta shiga mazaunin direba tai ma motar keys, muka fita ba tare ni na san inda za mu je ba, nawa ido ne kawai ina ta kallon titi har muka isa wata kyakkyawar unguwa mai manyan gidaje, gida hudu muka wuce sannan ta danna horn mai gadin ya bude mata gate, a inda sauran motocin suke ta faka motarta ta fito sannan tace da ni na fito ya dauko mata ledodin, tana gaba ina bayanta har muka shiga cikin gidan. Alhajin nan mai kangon gidan da ya kore mu na hango zaune kan kujera yana dariya an zagaye shi suna ta hayaniya da alama wata wainar ake toyawa.
“Daddy... Happy birthday”
Hajiyar ta fada tana nufar inda yake, ban yi mamakin wulakancinta ba indai har wacan mutumen marar ganin tausayi ne mahaifinta
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
1️⃣3️⃣
A gidan ta wuni ita da mahaifinta da sauran yan'uwanta suna ta tayashi murnar birthday kowa na kalla fuskarsa dauke da farinciki,kamar wadanda aka yayewa damuwa har abada. Sai da yamma mahaifinta ya fita ya barsu a cikin gidan suna ta shagalinsu. Duk iya shagalin da akai da ciye ciye da akai Ataa na waje zaune ita kada kamar yadda Rahma ta umarce da zama waje, sai misalin sha daya na dare ta fito cikin gidan baya ta yi waya da Aliyu ta fada masa ba zata iya driving ba ya zo ya dauke ta.
Ko da ta fito Rahma na kwance a balcony, matsawa tai ya saka fada ta dan musgune ta kadan ita kuma ta farka a girgice sannan sai ta jefa mata dari biyu
“Tashi ki je gidanku”
“To”
Ta fada tare da saka hannun ta dauki kudin ta gyara Hijab dinta ta kama hanya. A gurin Rahma tai tsaye har Aliyu ya iso da motarsa harabar gidan ya faka. Sannan na soma takawa a hankali ta karaso inda yake, fito yai daga cikin motar ya bude mata front seat ta shiga ta zauna ya rufe ya koma cikin motar yai nata key ya danna horn aka bude musu gate.
Lokacin daya hau titi ya fara tafiya sai ta kwanto jikinsa, shi kuma ya kai hannunsa yana taba kanta da yake ji da zafi.
“Kina jin rashin lafiya ne?”
“Eh”
“Since when?”
Ya faka motarsa gafen titi ya juyo yan fuskantar da kyau.
“Dear miyasa kike wasa da lafiyarki ne? Ba ki san lafiyar ki tana da amfani a gurina ba? Tun yaushe kika so ma jin zazzabi”
“Da yamma nan, yanzu ne ya fi min sosai”
Wayarsa ya ciro ya kira Doc Asim bugu biyu ya dauka.
“Doc same ni gida yanzu, jikin Rahma ya tashi”
Yana fadar hakan ya kashe wayar ya jana motar @360 suka iso gida, ba su yi minti ashirin da isa ba sai ga Doc Asim ya iso, tana zaunen falon kusa da Aliyu ya tambayeta abunda ta ke ji ta fada masa ya bata magani, sannan Aliyu ya rika ta suka shiga bedroom ya kwantar da ita, bakin gadon ya zauna kusa da ita yana ta kallonta kamar mai auna hawa da saukar numfashinta, har bachi yai gaba da ita, sannan na taso ya fito daga dakin shi ma saboda kiran wayar da Mama Fulani tai masa ne, saukowa yai kasa yana amsa wayar. Yadda fuskarsa take sake duk kuwa da irin tashin hankalin da ke ransa na ciwon matarsa, amman ka ga murmushi a fuskarsa ka san mai kiran yana da muhimmanci gare shi.
“Aliyu ka yafe kowa ka kyale mu ko?”
“Na isa Mama? Ai ko zan yafe kowa ban da uwata matukar ina neman albarka”
“To ya gida ya matar ta ka?”
“Gida kalau surukarki kuma tana nan yau jikin ya soma tashi”
“Subhanallahi fatar dai da sauki”
“Da sauki ta samu bachi ma”
“Masha-Allah Allah kara lafiya, zan je Dubai gobe, ba lallai idan na je can na kira ka ba, fada min abunda kake son na siyo maka da matarka”
“Ni dai perfume na ke so, ita kuma ki siyo mata duk abunda kika ga ya dace”
“To shikenan, a gaishe ta idan ta tashi”
“Zata ji thank you Mama”
“Allah maka albarka”
Daga haka tai hanging. Shi kuma ya tashi cikin rashin kuzari ya nufi kitchen, tea ya hadawa kansa ya dawo saman kujera ya zauna ya kunna tv for like ten minutes ya tashi ya koma dakin matarsa.
ATAA POV.
ban taba auna rashin imani da tausayin irin na matar nan sai yau, ta ba a gidan zan kwana ba amman ta kyale ni na zauna a waje bata ba ni abinci ba na wuni da yunwa ta bar ni a haka, yanzu kuma sha dayan dare ta ce na kama hanyar gidan, gashi ko abun hawa babu, tsoro da fargabar abunda zai same ni, wa zai tare ji a hanya barayi ko masu cin zarafin mata duk be dame ta ba, saboda kawai ina nema a karkashinta, shi kenan dan ina talaka ba ni da gata, ni fa ya ce kamar kowa ba daga sama na fado ba, amman saboda ba ni da shi ina talaka a yau an sake ni karfe goma sha dayan dare na kama hanyar gida. Ban samu a abun hawa ba, a kafa nai ta takawa ina ta addu'ar Allah ya kai ni gida lafiya. Ko da na isa unguwar babu mutane sosai domin daya saura na dare. A bakin kofar gidan na tsaya nai buga kofar ba a dade ba aka bude min, babu wuta a lokacin dan haka mahaifin Farida ya haske min fuska da fitila.
“Ataa ke ce cikin daren nan? Ina kike je?”
“Gurin aikin ne, muka fita ba mu dawo ba, sai yanzu”
“Ina kuka je?”
“Gidan iyayenta”
Sai ya bude min kofar na shigo yana ta kallona kamar be yarda da ni ba, sai da na shigo cikin gidan na hango Nana tsaye rike da bango tana kallona lokacin da na karasa kusa da ita sai na rasa me zan ce mata, na sani dole hankalinta ya tashi rashin ganin na dawo, gashi babu mai mata wata hidimar sai ni. Rikata nai muka koma cikin dakin sai da ta fara zama sannan na zauna kusa da ita na fada mata dalilin dadewar da nai ban dawo ba.
“Da wani abun ya same ki a hanya fa?”
“Nana