Showing 222001 words to 225000 words out of 225640 words
hakurin zaman auren da Ammy tai ma jureya da tarbiyantar da yayanta da kuma cirewa rai kwadayi sai gashi Allah ya bawa yayanta inda za su huta kuma su jidadi.
Kwana na biyu a Agadez din bayan kai su Zainab da Batula muka dawo tare da Mama da wasu da suka rakota saboda jin cewar zama na karshe ne za ayi, washe garin ranar da muka dawo ya muka tafi sokoto har Hamma saboda case din. Ranar da muka isa ranar aka shiga kotun wani abun da zai baka mamaki har da yan jarida abun ban san taya suka ji ba ko da yake abun duniya baya boyuwa. Alkalin ya yanke hukunci ne akan kwararan shidu da kuma hujojin da aka gabatar a gaban Alkalin.
Hukuncin shekara ashirin da biyar alkalin ya yanke masa daman tun da aka soma case din aka rufe asibitinsa, sai gashi kuma alkalin ya hada da asibitin cewar a rufe ta gaba daya. Kamar wanda akai aka yi ma albishir da mutuwa haka Doc Asim yai da fuska da ya dafe kansa. Mu kan ran mu fes domin yan yanke masa hukuncin daya dace da shi, sai dai Alkalin ya ba shi damar daukaka kara zuwa kotun Abuja idan yana ra'ayi. Ban yi tsammanin zai yi hakan ba, sai ga shi lauyansa ya fadi cewar za su daukaka kara zuwa Abuja domin ayi musu adalci a can.
A ranar ruwa ne kawai ban zuba kasa na sha ba akan dadi da murna, amman na yi farinciki sosai kuma na yi ma Allah hamdalla, wani abun da ya kara min jindadi da sunan Hamma be fito a ciki ba, hakan na nufin ya saba siyarda kodar kuma wai Hamma ne kawai ya siyarwa ba, domin idan har zai fadi sunan Hamma to zai fadi na sauran manyan ma da ya siyarwa.
Cikina na cikin wata na tara aka fara zuwa kotun Abuja na daukaka karar da yai a wannan karon ma ba mu muke zuwa ba wani lauyan ne yake wakiltar mu.
Asibitin da na ke awa likitar ta fada min Edd na, tun daga ranar Hamma be sake ba ri na tafi makaranta ba fita ma baya bari nai kullum ina gida idan yana gurin aiki kuma yana yawan kirana wai ai wani lokacin ba a lokacin da suke fada mutum ke kaiwa ba wani sai yafi wani kuma ba zai kai ba, siyayya kayan sakawa ta babu abunda be siya min ba, na jariri ne kawai be yi ba wai ba zai siya na mata a haifa masa namiji ba ba kuma zai siya kayan maza a haifa masa mace ba dan haka sai idan na haihuwa zai hada komai na jariri sai dai ya siya wasu kadan da maza ko mata duka za a iya saka musu. Nikan fargabar inda zan haihu ya hanani sukuni ina ta jin tsoro ta yadda da ko ya za su fito cikina duk girman cikina a ce ta nan da zai fito a duk lokacin da na tuna sai hankalina ya tashi, ni da ko motsi cikin yai sai na ji tsoro balle kuma ace haihuwa, wannan yasa na matsawa Hamma akan ya mayar da ni gida gurin Momy na haihu a can ko kuma ya kai ni Nijar gurin Mama amman ya ki har cewa yake wai ko haihuwa nai a gurin Mama Fulani zan zauna ni kan hakan be min dadi ba domin zan fi son zama a gurin Mama ko Momy.
yana gurin aiki na kira shi a waya na fada masa bana jindadi ina jin cikin yana min motsi sosai kuma ina jin ana sukana a baya, da sauri ya zo ya dauke ni muka tafi asibitin, sai aka ce mana ba haihuwar ba ce haihuwar dai tana kusa amman ba ita ce, haka muka kwaso muka dawo gida tare da maganunguna da suka rubuto mana. Sai gani washe gari kamar ba ni na yi kwaliyata na chakire kamar ba ni ba, bakina ya sha lipstick ga wani uban turaren dana zuba na sha doguwar rigar shadda ta na yi daurin dankwalina ture ka ga tsiya. Sannan na shiga kitchen na girka mana jalof din shimkafa da vegetables, ban na sauke na dawo dakina na dauki cingan na saka a bakina sannan na fito falo na zauna rike da wayata ina duba whatspp.
Ina jin lokacin da Hamma ya faka motarsa ya fito ya murdo kofar falon ya shigo hannunsa da leda.
“Sannu da zuwa”
“Kai kai kai Babyna wannan kwaliya fa? Acancan ai wannan kwaliyar kamata yai ace tukuici za a baki, kuma ba abun a baki tukuici ba ga ki da tulelen ciki, da na taba ki kadan ki fara kuka kina cewa bani da tausayi”
Dariya nai na unkura na mike tsaye na mika masa bakina mukai wa juna kiss kamar yadda muka saba sannan na karbi ledar hannunsa.
“Gaskiya kin yi kyau babyna”
“Na gode”
“Just”
Na kanenn masa ido kamar yadda yake min sai ya kyalkyale da dariya ya rikoni ya zagaye hannayensa da cikina.
“I love you, sarkin raki”
“Aiko ina da kokari”
“Za mu gani idan za ki haihu”
“Ai ba zaka gani ba, idan zan haihu sai dai na baka labari”
“No ba zan yarda ba, ba za ki haihu hannun namiji ba kuma a gabana za ki haihu da ni za a shiga, kin san fa ance akwai likitocin da suke ketawa mace haddi idan za ta haihu kuma ni ba zan yarda wani ya ganki ba, sai dai mace yar'uwarki”
Murmushi nai daman na san za a rina yadda yake yawan nuna kishinsa ba zai iya yarda wani mijin ya karbi haihuwa ta ba, ko jiya da muka je asibitin sai da ya saka aka nemo masa mace ta duba ni. Muna cikin cin abinci yake labarta min an saka auren Amina da Husna on 14 Oct.
“Eyyy kamin lokacin na haihu sai na yi gayu”
“Da goyon?”
“Kai zan bar ma shi ai”
Yayi murmushi.
“To Maryam fa?”
“Maryam har yanzu dai bana jin ta samu wani da ta samu da Mama ta fada min”
“Kai har ta bani tausayi Wallahi, ba dadi ayi ta ma wasu aure ana wuce ka”
“Koda ai da kaddararsa wani jinkiri alheri ne, kuma da ka yi auren a koma ana kuka ai kara kawai kayi hakuri har na kwarai ya zo, domin duk yadda ta matsu tai auren ba tai Rukaiya ba da ta auri wanda ko boko be yi ba, da ma ace yayi karatun sai a sama amsa aiki amman babu bokon abubuwan sai a hankali wani lokacin haka jarrabawa take zuwa ma mutum kuma komai yana bukatar a tsananta bincike, da yanzu an yi bincike mai zurfi ai da duk haka be faru ba, amman sai aka tsaya ana masa kallon dan babban mutum ganin ya zo nema masa aure kuma yana bin sunansa a matsayin ubansa”
“Gaskiya kan abun babu dadi amman kaddara ce, ta riga fata haka Allah ya so”
“Na mu kawai Addu'a ne, kuma na fadawa Mama na ce tai ta mata addu'a Allah ya bata miji na gari, ita kuma Rukaiya Allah ya mata mafita”
“Amin”
Na amsa ina kallonsa ya mike tsaye yana murza ido.
“Lafiya?”
“Zazzabi na ke ji”
“To ka sha magani sai ka kwanta”
“To Hajiya ta”
Na masa murmushi sai ya mayar min sannan ya dauke plate din da muka ci abincin ya nufi kitchen.
Kwana biyu da wannan na sake jin irin wacan ciwon sai dai wannan ya ci uban wacan ta ko'ina domin ba kaina ba ba cikina ba ba bayana ba ba marata ba ko'ina ji nake yana murda min, haka na wuni tun safe har dare kkuma Allah ya bani ikon yin girkina cikin karfin hali har na gama, sai da yamma abun ya tsananta min idan zan zauna sai na ji kamar abu zai fito min da baya, hankali be kara tashi ba sai da naje fitsari na ga jini sannan na kira Hamma a waya na fada masa. Daga office ya dawo gida hankali tashe a lokacin har na fara kuka babu hawaye saboda tsananin azaba.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, wayyo bayana wayyo cikina Momy Mama, har da Mama Fulani da Ammy”
Su na ke ta fadi har aka shiga da ni dakin haihuwa, bana iya komai dai dai amman ina jin lokacin da akai ta rigima da Hamma kamin a samo macen da zata karbi haihuwa ta. Ihu nake iya karfina su ko sai ce min suke na nai nishi.
“Nishin ya kare wayuo Allah Allah ka cece ni, wayyo Allah Wallahi Aliyu ne”
Na fada cikin rudewa da jin zafin murdawar da cikin ke min.
“Addu'a ake Allah ake kira”
Likitar ta fada min hakan yasa na fara karanto addu'ain da na sani a cikin har na neman tsari daga azabar kabari da talauci amman jin anke kamar ana karo min abun, da na ga abun be min ba na koma salatin Annabi. A haka na kwashe awa hudu ban haihuwa tun ina nishin da sauran karfina har karfin ya kare.
“Dan Allah ku kira min Momy dan Allah ta zo”
“Ba Momy ba ko Daddy ba zai zo ba balle Momy sai da kika zo haihuwa kika tuna da Momy, sai kin ji yadda kowa ya ji”
Matar ta fada tana dariya.
“Wayuo Allah ka min Rahama Allah na tuba”
Na fada ina da kuka sosai, sai ga Hamma ya shigo a cikin dakin duk ya hada gumi kamar shi ke nakudar, hannu ya kama ya rike idonsa cike da kwalla yana ta min addu'a. Cikin ikon Allah da iyawarsa na soma jin abu na fito min, wani uban uhu na kwala sai da ji nai an yanka ni da wani abun an janyo abun sai kuka yake, sai suka dora min shi saman ciki suka ware min kafafuwansa.
“Kall ki gani me kika haifa?”
“Namiji”
Na fada a wahalce sannan sukai dariya suka dauke shi.
ALIYU POV.
Farinciki ya kasa barinsa ya yarda cewar dansa yake gani, jininsa be san lokacin da ya saki Ataa ya nufi inda Nurse din da ke goge jaririn take sannan dayar ta fita ta karbo kayan jariri, kamin a saka masa kaya sai da Aliyu ya karbi dan yai masa kiss sannan ya mika shi aka saka masa kaya. Shi ya fito rike da abunsa ya nufo inda su Mama Fulani take tsaye a take gurin suka fara ihu da murna. Wannan ya karba wannan ya karba, aka hau yi masa hotuna cikin har da uban yaron ya aikawa Momy kuma ya dora status dinsa. A rana duk wani family member na su sai da yai farinciki da samun haihuwa da Aliyu yai. Sai a lokacin ya gane yana tsananin son Ataa da kaunarta, jin nai kamar na lashe ta yake ji ita da abunda ta haifa ba ma shi kadai ba har da Mama Fulani sai a lokacin da san darajar Ataa.
Sosai yan'uwan Nana suka so a ba su Ataa su tafi da ita can, amman Mama Fulani da Momy suka tsaya kai da fata akan ayi musu alfama a bar musu ita a nan saboda Aliyu idan aka maida ita a can ba zai samu damar zuwa ko da yaushe ba ga shi kuma ba zai yayu ya koma can da zama gaba daya, ko yake yadda yake rawar kafarta zai iya tarewa a can sai dai ya nuna musu rashin an ido akan matarsa ko kadansa.
An zubawa Ataa kayan barka kamar ba gobe ta kowane bangare samun kyauta take da kulawa sai ta zama yar gata. A ranar suna jariri ya ci suna Muhammad Amir, an yi bidiri an kashe kudi iya kudi, an yi abubuwa da dama na rabawa mutane wani abun da zai baka mamaki har da Mommyn Rahma, dole ta zo ko dan nadamar da tai ga kuma alakar Ataa da dukiyarsu.
Kwana uku da bikin sunan aka sake yankewa Asim makamancin hukuncin da aka yanke masa a wacan kotun ta sokoto, yanzu kan babu zancen daukaka kara sai fuskantar abunda ya aikata. Hasara biyu da uku ta same shi ga na rufe asibitinsa ga na bacin suna ga kuma na rufe shi gidan yari.
**** **** ****
ATAA POV.
Sai da nai arba'in sannan na tafi Nijar ganin yan'uwana, wata daya nai a can duk kuwa da kasancewar Hamma be so haka ba amman ban bi ya kansa ba domin na lura idan na biye shi ba zan yi zuminci ba, domin shi ya fi son kullum ina kusa da shi ko dan dansa, naga dangi na kusa da na nesa daidai gwargwado, kuma na ga kauna da soyayya ni da Amir ta ko wane bangare, har sai na ji kamar kar na dawo.
Ba Abuja na dawo kai tsaye ba, a gidan Momy na fara sauka sati na daya a can ita ta kaini gurin wasu yan'uwanta da ban sani ba da ma waenda na sani na gaishe su sannan na dawo Abuja gurin Mijina. Ina dawowa Hamma ya daukar min wata dattijiwa mai kula da gina, ni kuwa aikina girka abinci kula Amir sai kuma makarantar da na ke zuwa domin bana wasa da karatuna saboda burin da na ke da shi na yin zurfi a ilmi ko da kuwa Hamma ba zai barni nai aiki ba ina da burin yin zurfi a ilmina
Amir na da wata uku akai bikin Husna da Amina, mun chashe sosai mun biki mai amsa sunan bikin har manta nai da ina da da sai idan zai sha nono ake kawo shi da ya sha nonon, yan'uwan ubanshi za su dauke shi bachi kawai ke hada ni da shi. Wani abun tausayin har kuma tsawon lokacin Maryam bata samu wani ba Rukaiya kuma na dauke da juna biyu ita da sauran Amare, matar Muhseen ce kawai bata samu komai ba, daman na san za a rina an sace zanen mahaukaciya na san sai ya gama lokacinsa kamin ya haihu.
Na maida hankalina sosai akan karatuna, da kula da mijina da kuma dana, karatu be hana shi ko daya ba, haka ma kula da mijina da na be hanani karatun ba, na dage na mika dukam imani da karfina da dama saboda samun cikar burina. Ga goyon baya da na ke samu da kauna ta ko wane bangare, kan kace kwabo na goge a makarantar cikin shekaru uku ni ma ana dama da ni a cikin daliban da za su shiga aji na karshe wato Sss3 a Royal Academy.
Daf da yin Candy na samu wani cikin hakan kuma yayi min daidai domin na san iya lamani Hubby ya yi min na daga min kafa daga haihuwa duk kuwa da irin son yayan da yake har na gama makarantar. A week later akai bikin Maryam da wani mai mata biyu a sokoto dan'uwana Momy da ta hada ta da shi kuma suka daidaita. Ba laifi mutumen na da rufin asiri daidai gwargwado sai dai zaman kishi da zata fuskanta da matan sakkwato wanda za su gyara mata zama ta gane kuskurenta.
Cikina na da wata uku Hubby ya sama min admission a american university da ke Abuja, a lokacin da ya fada min yadda tsari da daliban makarantar suke sai abun ya tsorata ni sosai ina ta ganin kamar ba zan iya ba, ashe abun saka kaine kuma karatun ya zo min da sauki saboda na yi nisa a qur'anen ina daf da sauka ma, sai hasken karatun ya kara bude min kwakwalwata, da safe kullum sai Hubby ya biya min na qur'anen a na bokon ma inda ban gane ba yana min karin haske, domin ya fada min abunda ban gane ba na rika tamyarsa ko wata mace, amman be yarda na tambayi wani namiji ba da sunan class mate dina. Makarantar ma kamar wacan sai na rufe komai na ke tafiya shiyasa babu wanda ya san fuskata sai matan da muke shiri da su sosai shi ma waenda suke da contact dina muke ziyarar juna ko suke ganin status dina.
Lokacin da na fara zuwa na maida hankalina da kuma yawan tuna burina sai abun ya zo min da sauki, sai dai wannan cikin ba kamar wacan ba ne, wannan na sha wahalar sa sosai ga shi kuma ina farko farkon fara karatun ne. A haka nai ta fama har cikin ya girma a lokacin muna daf da fara exam din shiga ug 2, a haka nai jarabawar cikin wahala Hubby na ta tausayina kamar yadda na saba sai dai baya karya min guiwa saboda ya san burina kenan.
Bayan exam da sati biyu na haifi yan biyu duka mata kyakkyawa, wannan karon ma sai da aka min kari kamar dai wacan, a gidana akai bikin dattijiwar da ke kula da gidan ita ke hada ruwan zafi tai ma twins wanka wato mai sunan Mama Fulani da mai sunan Mama na sai akai musu lakani da Nimra da Namra. Bayan wata biyar fa haihuwar twins muka je Nijar bikin Mama da wani dan'uwanta, ni abun har dariya ya ba ni wai Mama za tai aure sai dai na san auren shi ne darajarta da martaba da kuma mutuncinta.
BAYAN WADANSU SHEKARU.
Wa zai gan ni a yanzu ya ce ni ce a wacan lokacin nai bara da roko a titi, ni ce na sha wahalar rayuwa na fuskanci kalubale na rayuwa kala kala, mai hakuri madawaci kuma wanda ya rike Allah baya faduwa kasa, duk kuma wanda Allah yai masa gata to ya huta kuma ya dace. Na rike Allah na yi hakuri kuma na ci ribar hakurina Allah kuma be barni na yi kunya ba, da duk wanda yake kallona a matsayin banza marar amfani ya koma yana min kallon kamar babu wanda ya kai ni gata ya fini dacewa da komai a rayuwata. Duk wanda ya gan ni a yanzu zai zata daga sama na samu arzikin ko kuma arzikin ya zo min sai wanda ya san wahalan da na sha kamin na samu wannan.
Wai ni ce rike da takardar bautar kasa na yi, na yi karatu kan burina na cika na yi degree in business administration amman bana