Showing 99001 words to 102000 words out of 225640 words

Chapter 34 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

bachin dake cikin idonta domin jiya bata samu bachi da wuri ba daga ita har Aliyu da nuna mata yadda yai maramarinta a tsakanin kwanakin nan. Sai ya tabbarar ta farka sannan ya dauki qur'anensa ya sauko downstairs ya zauna a saman kujera ya bude yana karantawa. Yayi one hour ya a karatun sannan ya hau ya maida qur'anen a nan ya samu Rahma ta koma bachi sanye da Hijab din da tai sallah, Bedsheet yaja ya lulluba mata saman jiki sannan ya sauko ya shiga kitchen, daman idan suna sokoto shi yake shi ke hada musu breakfast ba kamar Abuja ba da mai aiki yake musu. Ruwan Lipton ya fara dorawa sannan ya fasa kwai ya ya kada ya je ya firaye dankalin ya zuba mai ya soma soyawa, da kansa ya share kitchen din bayan gama komai ya zuba a abun zuba shara sannan ya dauko kayan ya kawo dinning. Ya kunna tv ya zauna a gurin yana kallon news baya son ya tashi Rahma a yanzu domin yasan bata saba farkawa da 9 ba sai 10 balle yanzu da yasan ciwon nata yafi na da yafi son ta huta iya hutawa har bachi ya gintse ta.
  Yana zaune a falon har 11 Rahma bata farka ba, tana can tana bachin dadi shi kuma yana zaune yana labartawa Nasir abunda ya faru a waya.“Aliyu idan ka nuna Muhseen damuwarka idan yai maka abu, domin idan ya lura kana jin haushi zai yi ta jindadi ne yana ta bata maka rai wanda hakan zai kara bata zumuncinku ne kawai”

“Muhseen kanena ne Nasir idan be min biyaya ba kar ya sammaci samun damata da har zai raina ni”

“Muhseen kanenka ne, amman babu wanda zai san da hakan sai idan ka fada domin babu wanda zai kalleshi ya ce kanenka ne, kai kuma kana son nuna masa kai ne sama da shi, yes haka ne amman ba ko da yaushe babba yake zama yace dole sai shi a bi shi, wani lokacin kai ua kamata ace ka bi dan a zauna lafiya”

“O ni zan bi Muhseen din? Nasir kamar baka san da Aliyu kake magana ba?”

“Na sani ma, naga ba kullum take jumma'a ba”

“Amman kullum rana ce”

Aliyu na fadar hakan ya aje wayar a hannun cushion ya tashi ya hau sama domin duba Rahma, a zaune ya same ta saman gado tana danna wayarta dayan hannunta na saman kanta tana tsifar gashinta. Kusa da ita ya zauna ya sumbace kumatunta.

“Good morning ya jikinki?”

“Da sauki”

Ta fada ba tare da ta kalleshi ba.

“Baki sha maganinki na safe ba, bana son tashinki saboda na san kin gaji sosai”

Ya fada yana janye hannunta daga saman kanta.

“Ki daina tsifar nan karki gajiyar da kanki idan mun ci abinci zan kai ki saloon a gyara miki kai”

Sauka tai daga kan gadon.

“Bana son fita ko'ina yau na fadawa Mommy ta aiko da mai mata kitso ta zo ta min”

Bandaki ta nufa ta barshi a gurin zaune. Bayan ta gama abunda zata yi ta fito sannan shi ma ya shiga ya wanke bakinsa ya fito sai ya same ta gaban madubi zaune tana kallon kanta hawaye na sauko mata.

“Wani abun ne kuma?”Juyowa tai ta kalleshi.

“Yanzu Aliyu idan na mutu ba zaka wuce wata daya ba zaka mantani ko?”

Kallonta yake ba tare da yace mata komai ba.

“Idan na tuna ba saboda ni ka zo garin nan ba sai na ji kamar na hadiye zuciya na mutu, ban taba kawowa a raina cewar zaka taba son wata mace ba, watan ma kazama yar aikin gidanka kuma yar bara a titi”

“Taso muje mu ci abinci”

Shine abunda ya fada yana juyawa.

“Ba ka son ayi maganarta ko? Saboda ta fini kyau ta karbu a zuciyarka, saboda kana sonta wata kila ma ka kosa na mutu ka aureta....!”

“Rahma....!”

Ya kira sunanta a tsawace da duka muryarsa, ba ita kadai ba har kujear da take zaune a kai sai ta girgiza.

“control your tongue, Bana son nanata magana kin sani, kuma bana son bata miki rai amman kina kokarin ganin sai na bata miki rai, kin riga kin karya yarinyar kin kuma juya mata baya dan haka babu ruwanki a cikin wannan maganar, idan wani abun ne a tsakanina da ita ne ba da ke ba, lamarinta ya daina damunki kina damuna, ki bar ni na ji da ciwonki da kuma kuskuren da na aikata”

Tunda ya soma maganar hawaye yake sauko mata har ya gama ya juya ya fice daga dakin cikin bacin rai. Maganganun da yai mata suna ta maimaita kansu a cikin kunnenta, zata ita rantsuwa ta sake ra tsewa babu kaffara, cewar Aliyu be taba daka mata tsawa kamar haka ba, ko fada sukai ko suka samu tsabani sai dai ya kyaleta ya ki yi mata magana ya daina kulata amman ba fada kamar haka ba.

“A a ba zaka auri wata ba Aliyu ko bana da rai balle ina raye, ba zaka so wata ba”

Ya fada tana girgiza kai sai kuma ta saka hannunta ta watse duk abunda yake kan miron ta dauki stool din ta jefi ruwan mirror da shi a take ya watse ya fadi kasa tana ihu kamar wata mahaukaciya. Kuka tai sosai har sai da kanta ya soma ciwo kamar ance mata da gaske Aliyu son Ataa yake kuma aurenta zai yi, sai da idonta yai ja sosai sannan Aliyu ya shigo dakin ya daga daga kwancen da take ya rumgume matarsa tsantsan jikinsa.Wani lokacin yana dagawa Rahma kafa saboda ciwonta yasan abu kadan zai iya sanadin tashin ciwonta ko kuma ya saka ta cikin wani hali, idan ma ta yi kishi ai saboda shi tai kuma saboda tana son sa, sai dai hakan ba zai saka ya biye mata ba ta yarda cewar ita kadai zata zauna a gidansa ko a zuciyarsa duk kuwa da ba shi da muradin auren mace sama da daya. Kara fashewa tai da kuka tana jimkeshi da hannayenta. Sun dauki lokaci a haka kamin ya dagota ba tare da ya ce mata komai ba ya saketa ya shiga bandaki yai wanka tana zaune a gurim har ya fito ya shirya a gabanta ya saka agogon hannunsa da atm dinsa da wallet sannan ya kalleta.

“Ta so muje ki karya”

Kamar mai jira sai ta mike tsaye ta sauri ta bi bayansa domin shi tuni yayi gaba, kamar masu rigengen saukowa daga stairs din haka suka sauko, ita tana sauri ta cin masa su sauko tare shi kuma yana ta lafiya abunsa ba tare daya jira ta ba. Ya riga isa dinning sai yaja mata kujera ta zauna sannan ya shiga zuba mata abincin bayan ya gama shi ma ya zauna kusa da ita ya zauna yana ta lasa wayarsa kamar be san da zamanta a gurin ba.

“Ba zaka ci abincin ba?”

“Na ci”

Ya fada ba tare daya kalleta ba, ba dan kuma ya ci abincin ba. Sai da ta ci ta koshi sannan ya tashi ya koma sama sai ta bishi a ciki ko da ta shiga ta samu yana hada maganinta gurin daya, sannan ya shiga bathroom ya debo mata ruwan tab ya mika mata maganin ta karba ta sha. Sai ya sumbaci goshinta kamar yadda ya saba mata.

“Zan fita amman ba zan dade ba zan dawo yanzu”

Da kallo ta bishi har ya fice daga dakin sannan ta sauke ajiyar zuciya tana jin tashi motarsa ta dauki wayarta ta kira mahaifiyarta tana kuka.ALIYU POV.

Ko da isa gidan Momy biyu ta kusa domin rana ta bude sosai wani gurin ma har an fara kiran sallah.
Amina ce da Momy zaune a falon Amina na kwance Momy kuma na zaune suna cin apple. Daga kwance da Amina take ta mikawa Aliyu gaisuwa sai ya watsa mata harara.

“Ni za ki gaisar a kwance”

Saurin tashi tai zaune ta sake gaisheki sai kuma ya ji amsa mata ya kalli Momy yana mika mata gaisuwa.

“Kai komai na ka na zafi ne, shi gasar da mutun a kwance kuma laifi ne?”

“Yayanta ne ni fa Momy wannan ai rashin da a ne, je ki duba min abinci”

Ya karasa yana kallon Amina, da sauri ta tashi ta nufi dinning. Momy ta sake kallonsa ta ce.

“Ka je da safe ka duba mahaifiyar Ataa?”

“A a ba mu dade da tashi daga bachi ba”

“Kai da wa?”

“Rahma”

“Au iyayenta sun yarda sun baka ita? Ta dawo?”

“Daman ai ba hana min sukai ba, zuwan da sukai a nan ma da ban amince ba da ba zan barta ta zo ba”

“Amman dai kasan ya kamata ka je da safe ka gaisa da mahaifiyar yarinyar nan”

“Momy ban san rana yayi haka sosai ba yanzu zan je”

“Kara ka fara zuwa inyaso idan ka dawo sai ka ci abinci, Muhseen ya zo kuma ban san halin da ake ciki ba, ni bana son zuwa yanzu ina jiran Ramatu ne ta zo muje tare dan na fada mata cewar Daddynku yana da patient a asibiti ta zo ta rika kwanar mana da ita, ka ga ita ma Ataa sai ta samu tana dan hutawa kar dawainiyar tai mata yawa”

“Ramatu mai aikin Hajiya Baraka?”

“Eh kasan tana da kirki sosai, bana son dauko wani daga gidan dangina ne ko na Daddynku bana son maganar tai ta yawo ne, amman ka ga Hajiya Baraka aminiyatace ba kowa zata fadawa ba”

“Muhseen ya zo kik ce Momy?”

Ya tambaya yana kallon Amina wacce ta doso inda yake rike da plate din abinci.

“Eh nan ya fara sauko kamin ya wuce asibitin”

“Ina abincin da za a kai mata?”

“Gashi can a dinning”

Ya mikawa Amina keys dinsa hannunsa.

“Saka min abincin a mota”Hannu biyu ta saka ta karbi keys din ba dan tsoronsa na sai dan Momy ta koya musu haka karbar abu da hannu biyu tun suna kanana domin yana karawa mutum kima da daraja a idon mutane.

“Da ya so mi yace? ”

“Be ce komai ba, kawai dai yace ya dauka Ataa na nan”

Momy na fadin hakan Aliyu ya mike tsaye ya fice daga falon ba tare daya taba abincin ba. Cikin motar ya zauna har Amina ta gama saka masa abincin sannan ya yi ma motar key tun kamin ya danna horn mai gadin ya bude masa gate ya dauki hanyar Usmanu Danfodiyo University teaching hospital wato uduth a takaice.
Tafiyar da zata dauke shi minti ashirin da biyar ko ashirin yai ta a cikin minti goma sha sha hudu, a gurin da aka tana dan aje motoci ya aje motarsa ya fito da abincin dake cikin kulolin da kwadon da aka zuba plates da spoon a ciki ya aje a gurin sannan ya rufe motar. Tunanin yadda zai dauke su yake dan baya jin zai iya maya biyu yaje ya dawo dan daukar abinci kawai. Wata budurwa ya kalla ta sha kwaliyar kanti tana tsaye jikin wata farar mota sai yauki take kamar miyar kubewa da alama wasu take jira.

“Ke zo nan”

Ya fada kai tsaye kamar wacce ta sani ko kuma daya daga cikin kanensa yana kallonta fuskarsa babu alamun wasa. Kallonsa budurwar tai daga sama zuwa kasa farar shadda ce a jikinsa ta yi mugun karbarsa kamar wani ango fuskarsa nata haske ga farinsa sai shining yake, ta kuma lura da makekeyar expensive car din da dake yake tsaye kusa da ita ta san tashi shi domin alamun naira sun nuna a jikinsa. Ta nuna kanta tana wani lauye baki kamar wata karuwa.“Ni....”

Be ce mata komai ba sai kallonta yake, ita bata jira yace ita din ko ba ita ba sai ta karaso kusa da shi tana wani rangwada kamar zata karye.

“Dauki kulolin nan ki biyo ni”

“Okay”

Ta fada yadda take pronouncing o din is like tana koyawa mutane karatu ne. Shi ya rika kwandon yai gaba ita kuma ta riko kulolin karama da babba ta bi bayansa zuciyarta na raya mata cewar ya kyasa da ita. Kai tsaye suka wuce ciki tana biye da shi har suka shiga dakin da mahaifiyar Ataa take. Inda taga ya aje kwandon ta karaso ta aje kulolin tana kallon Ataa wacce ke zaune saman gadon hawaye shar a fuskarta a zatonta ita ce bata da lafiyar.

“Sannu ya cikin”

Ta fada tana wani lankwasa harshe kamar wata bakanuwa. Hannu Aliyu ya saka aljihu ya ciro wallet dinsa ya zaro dubu uku har zai dora a saman gadon asibitin ya ce ta dauka sai kuma ganin Ataa yasa ya mika mata da hannunsa.

“Aa ka barsu kawai”

“Karba mana bana maida kudi”

Hannu ya kai ta karba.

“Thank you”

Ta furta tana juyawa ta koma tana ta sauraren ta ji Aliyu ya kirata ko ya biyo bayanta amman bata ji ba har ta fice. Ko be tambaya ba yasan an shiga tiyata ne da Mahaifiyar Ataa tunda Momy ta fada masa Muhseen ya zo kuma gashi be tarar da ita cikin dakin ba.
Kallon Ataa dake zaune kan hospital bed din Aliyu yai with serious face ya ce.

“Mi akai miki kike kuka?”

Bata ce masa komai ba bayan turon karamin bakinta da tai ta saka hannayenta ta share hawayen fuskarta. Wata kila tsoron tiyatar da aka shiga da mahaifiyarta take ko kuma wani abun akai mata, or maybe Muhseen ya fada mata wata maganar ne marar dadi.“Ga abinci”

Dauke kai tai.

“Bana ci”

A tunaninsa ko tana tsoron kar ya saka mata wani abun ne ko kuma ya cutar da ita shiyasa ba zata ce. Kujerar da ke gefen gadon ya janyo ya zauna ya dauki plate din ya zuba jalop din da sannan ya bude dayar kular ya zuba farfesun kazar da ke cikin ya saka spoon ya soma ci, abinci yake ci amman idonsa akan Ataa ne har ya ci rabi ya mika mata sauran.

“Karbi ki ci”

“Na ce bana ci”

“Idan na ce ayi abu yi ake ba a musa min karbi ki ci na ce”

Kallonsa tai hawaye na mata zuba.

“Ai babu wanda ya isa ya cilasata kai yi Aliyu, sai dai ka cilasta wasu, babu wanda ya isa ya taba wani naka balle ya taba ka, yadda kaga dama haka kake haka kake juya kowa, ka taka kowa ka cilasta ka zalinci wanda ka ga dama saboda kana da kudi ni kuma kana gani na talaka”

“Ba ni na cirewa mahaifiyarki koda ba, lokacin da aka cire mata koda ina a gurin ne kin gan ni ne?”

Ya fada yana kokarin danna fushinsa. Sai ta girgiza kai

“Baka nan, amman kudinka suna nan, ikonka yana nan, isarka tana nan waya sani ko asibitin taka ce? Kai ma baka son talaka miyasa ka sakawa matarka kodar talaka? Karyar soyayya kake mata tunda baka iya daukar kodarka ka saka mata ba, ba tana da iyaye ba miyasa basu bata kodar su ba? Sai ta Nana matar da ita kadai ta rage min a duniya? Kokarin kare kanka kawai kake yi ai Muhseen ya fada taya za a sakawa matarka kodar da baka san mai ita ba? Duk wannan taimakon kana min ne saboda ka san ka zalince ni ka cutar da ni ni da mahaifiyata Aliyu kai azzalumi ne....”

Cikin wani irin fushi marar misatuwa ya jefar da plate din hannunsa ya mike tsaye yana huci kamar zai dake ta, sai kuma yai saurin kawarda fuskarsa daga barin kallon yana kokarin saita numfashinsa. Mikewa tai tsaye wanda hakan yai daidai da shigowar Doc Bukar dakin, tana kallonsa fuskarta da hawaye ta ce.

“Na fada Aliyu ka kashe ni daman mutuwa ta fi rayuwa a yanzu, ka riga ka gama da ni tun da kasa aka cire mahaifiya koda dan zalinci ka sadawa ita ta rayu mu sai mu mutu, ga mahaifiyata can ana mata aiki Muhseen ya fada min zata iya mantawa da komai ciki har da ni har da ni Aliyu, idan kuma bata rayuwa ni ce a cikin matsala saboda zalincin da kuka mana kai da wannan likitan, har abada ba zan yafe muku ba kuma Allah ba zai bar ku ba....”

Ta fada kanta a sama tana kallonsa hawaye ke mata zuba sosai har wani dauke numfashi take kamar zata shude... Jawur idon Aliyu sukai yana kallon Ataa take rabe masa uku ba ko biyu babu ko kyafta ido. Doc Bukar ne ya matsa kusa da su yana Kallon Aliyu sai kuma ya kalli Ataa.

“Zauna”

Ya fada sannan ya kalli Aliyu.

“Da za ka fita na wani lokaci”

Sai a lokacin Aliyu ya kalli Doc Bukar ya sake kallon Ataa sai kuma ya nufi kofa ya fice cikin wani irin bacin rai marar misaltuwa.Ba zai iya fadar lokaci da ya kawo gurin motarsa ba wata kila ma taku biyu yai ko uku ko kuma dari ko dubu shi dai kawai ya samu kansa tsaye jikin motarsa ba tare da ya san ya iso ba saboda tsananin bacin rai da zafin kalaman Ataa, wani irin gudu jinin zuciyarsa ke yana da tabbacin da za a bude kirjinsa a yanzu wata kila da hayaki za a gani yana tashi. Ita kadai ta kai haka duk duniyar nan ta fada masa magana irin wannan mai zafi da daci kuma ya kyaleta ita kadai ce mutum ta farko da ta taba taba martabarsa da duk wani abun daya takama da shi tana a talakarta ta fada masa magana son ranta. Bude motarsa yai ya shiga ciki ya zauna for like 40 minutes sannan yai mata keys ya fita daga harabar gurin. Driving kawai yake ba dan yasan inda zai je ba, gida gurin Rahma ko kuwa gurin Momy? Ko gurin wasu abokansa ko yan'uwa? Kalamanta na ta maimaita kansu a kwakwalwarsa tun yana jin zai iya jurewa har ya kai ga runtse ido yana damke sitiyarin motar, sam ya manta cewar tuki yake kuma babban titi yake na gawon nama, har sai da yaji ya bugi wata motar wata motar kuma ta bugu bayan tasa, da sauri ya bude ido yana kiran mafi kyawun sunan a cikin sunayen Ubangiji wato Ya Rahamanin Rahim. Saurin tsayarda motar yai motar da ke gabansa tai gaba shi kuma ya faka tashi gefe ya fito ya nufi mai motar.

“Malam lafiya kake kuwa?”

Mutumen ya tambaya.

“I'm sorry ina cikin matsala ne”

Aliyu ya fada sannan ya bude wallet dinsa ya ciro sababbin kudi da zasu kai 50k ya mikawa mutumen.

“Ga wannan”

Mutumen ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login