Showing 150001 words to 153000 words out of 225640 words
fito rike da leda ya dawo cikin motar, da kansa ya bude ledar ya fiddo gorar ruwan mai sanyi ya bude ta ya miko min.
“Na goge”
Na fada ina kokarin karbar ruwan, sai ya saka min murmushi as respond ya kai ruwan a bakina na sha ka dan na rike sauran.
“Sun ishe ki?”
Ya tambaya yana ta kallona kamar mai kula da yadda na ke shan ruwa, sai na gyada masa kai hannunsa ya kai ya karbi ruwan ya tashi motar da hannunaa daya dayan hannun kuma yana kurba ruwan. Yawo ya rika yi da ni a cikin garin sokoto wasu unguwannin na sansu wasu kuma ban sani ba, ni dai ban tambaye shi inda za muje ba nawa idone kawai. Sai da muka yi nisa sosai sannan ya faka motarsa gefen titi ya kwantar da kujerarsa ya juyo da fuskarsa gafena yana kallona, na yi zaton wani abun zai yi ko ya ce sai na ji shiru be ce min komai sai idonsa da ya tsare da su, mi kuma na kasa daga kaina na kallin gefen da yake ma balle kuma na iya hadu ido da shi.
“Ki yi hakurina da kallona, yau ji na ke kamar na hade ki ji na ke kamar na bude miki zuciyata ki shige na rufe, ji na ke kamar a cikin jinina aka halittoki, komai ya zo min a babin da ban yi zato ba, ban san wace karmar zan fada da zata gamsar da ke irin kaunar ki da na ji a raina ba”
Ji nai kaina yayi mugun girma, ban tana jin kunyar Aliyu kamar na yau ba, ban taba jin wani kalami mai girma daga bakinsa kamar wannan ba, bayan wacan furucin da yai min yau ma ya kara min wani wanda ke dora wacan a babin da zai tabbatar da wacan zancen na farko, a wacan karon na yi zaton yana rokona ne saboda kare Momy da son cika mata burinta, sai dai kalaman da yai min a yanzu da irin shaukin da yake ya sauya tunani na.
“Kar a tashi makaranta.....”
Na fada numfashi na fita daker kamar wacce aka taushewa zuciya.
“Na fadawa Malamin ku gida zan kai ki fita za ku yi da Momy”
“Amman yanzu an kusa tashi ai....”
Na furta still numfashin nawa na gargada, sai ya sake dauko ruwan da ke tsakanin ni da shi ya bude robar ruwan ya miko min.
“Sha”
Na karba da sauri na kai robar ruwan a bakina ina ta sha kamar ba zan daina ba har sai da na soma tsarkewa sai yai saurin rike robar ya ciro tissue ya mikon.
“Sannu”
Na karba na goge ruwan da suka zuba jikin hijab dina sannan ta zuke gulashin motar na wurgar da shi waje, gaba daya na tsawwala ina ta jin motar ta mana kada kuma kunyarsa ta rufe duk na bi na rude. Shi kanshi ya lura da hakan, sai ya gyara kujerar ya soma toka motar muka hau titi. Kadan kadan yake tukin har muka isa gida, a bakin gate din ya faka motarsa, ya bude motar ya fita ya zagoyo gefena ya bude min motar
“Babyna fito ki shiga gida”
Na san ma'anar Baby yana nufin jaririya mace, wato yana nufin ni jaririyarsa ce kenan. Na fito daga motar kaina a kasa sai da ya rufe motar sannan ya bude gidan baya ya dauko min tittafaina ya mika min sai da na mika hannuna an karba sai yaki saki
“Thank you so much Love, kin cece ni na zan tana manta wannan alfarmar ba, kin cancanci komai daga gareni I love you so much”
Har zan sakar masa littafan sai yai saurin sakar min ya tsaya yana kallona har na shige cikin gidan. Ban taba dawowa a irin wannan lokacin ba ana ciran sallah magariba, idan ma Nana ta tambaye ni ban san mi zan ce mata ba. Ina shiga bq din sai na samu Nana bata nan sai dai dakin a bude yake cikina na shiga na cire uniform dina ya shiga bandaki nai alwala, ina cikin Sallah Nana ga shigo dakin ita ma ta wuce bandakin tai alwala ko da ta fito na sallame ina tasbihi da hannuna.
“Tun dazun kika dawo ko? Daman Hajiya ta ce kila ma kin dawo kika zauna a dakin ke kadai kina jin kunyar shigowa bangarenta”
Na yi murmushi cike da jindadi domin na san idan ta san na kai magariba dole ta tambaya abunda ya tsayar da ni kuma ban san abunda zan ce mata ba.
“Hajiya ce ta aiko aka kiranin na je can muka yi hira wai na daina zama ni kadai a nan”
“Allah sarki Momy ai tana da kirki”
“Tana da kirki sosai kam, kin yi dacen suruka indai abun ya bi haka”
Wata kunyar ce ta rufe ni ban taba tsammanin idan na yi wa mutun irin wannan maganar kunya tana rufe ba duk kuwa da kasancewar uwata ce amman na ji kunyarta sosai.
ALIYU POV.
ido ya kura mata yana ta kallon tafiyarta har ta shige ciki, wani irin abun yake ji marar misaltuwa lallai ya yarda kuma ya tabbatar a yanzu kam yana son Ataa so ba na wasa ba.
Motarsa ya shiga ya dauki hanyar gidansa, sai da ya shiga ya faka motarsa sannan ya fito ya doshi masallacin unguwar yai gabatar da sallah magariba da ya fito sai ya tsaya bakin masallacin sai da liman ya fito sannan ya yai saurin taronsa ya mika masa hannu suka gaisa.
“Ah Alh Aliyu ya gida ya aiki”
Haka yake kiransa Alhaji Aliyu ba dan komai sai dan tarin dukiyar dake saka kowa ganin kimarsa da jin kunyar kiran sunansa kai tsaye.
“Al-hamdulillah”
Aliyu ya amsa sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro duka kudin aljihu da na Wallet dinsa ya mikawa liman din.
“Dan Allah amin sadaka da wannan a bawa mabukata”
Da hannu biyu liman ya karba yana bude baki cikin tsananin mamaki domin ba kasafai Aliyi ma ya cika tsayawa ya gaisa da mutane ba balle kuma har ya mika wani abun da sunan taimako.
“Masha-Allah Mashallah, Allah ya saka da alheri Alhaji Aliyu Allah ya biya bukata ya kara bude ya sakawa rayuwa albarka, Wallahi ka taimaka a wannan hali da mutane suke ciki ai taimakon ake bukata ta ko'ina”
Har cikin ransa ya jidadin addu'ar liman after Momy dake masa addu'a kullum sai kuma Nana da ta taba masa a asibiti yau ma an sake masa, duka biyu kuma sanadin taimako ne ta uwa kuma ta kauna ce, sai ya ji natsuwa da kwanciyar hankali sun rabi ruhinsa. Cikin gidansa ya koma ya bude freezer ya dauko ruwa ya sha kadan ya aje sauran ya dawo saman cushion ya kwanta kamar wani sabon ango haka yake jin kansa gaba daya ya manta da komai da ke tare da shi Ataa kawai yake gani da kuma irin rayuwar da zai yi da ita, lokaci zuwa lokaci yake murmushi yana shafa kansa da fuskarsa, har mamakin yadda farinciki ya cika masa zuciya yake. He don't think zai iya biyewa Momy ko wani ma cewar after aurensu za tai karatu shi ji yake kamar kar kowa ma ya kara ganinta daga yanzu, he i can't wait ya ga ta zama halalinsa ta yadda zai rumgumeta a kirjinsa ya sumbace ta. Tashi yai zaune ya nufi dakinsa ya doro wata alwalar ya fito ya nufi masallacin dazun yai sallah, mutane sai kallonsa ake ko zai sake rabawa wasu kuma dan ya san da su, har da masu ba shi hannu ya gaisa da su, a da he can't shake his hand with anyone indai talaka ne amman a yanzu sai mika musu hannunsa yake suna gaisawa kamar ya manta waye shi.
Yana shigowa gida ya sake shiga dakinsa ya dauko wasu kudin ya saka aljihunsa sannan ya fito ya shiga motarsa horn daya aka bude masa gate sai ya tsaya daidai gurin mai gadin ya ciro kudin da za su kai eight to nine thousand ya mika masa, a take mai gadin ya washe baki ya fara zuba masa addu'a shi kan be shi ta kansa ba ya dauki hanyar gidansu Momy.
Har ya faka motarsa bq din su Ataa yake kallo ji yake kamar ta leko ya ganta, ya dauki lokaci a haka sannan ya bude motar ya fita ya shiga part din Momy sai wagen bq din yake kmar ance masa fitowa za tai.
Hannu ya kai ya tura kofar falon ya shiga fuskarsa da murmushi kamar ba shi ba, duka suna zaune falon suna ci abinci a plate daya da Momy, Amina Siyama da kuma Husna. Tuwon shimkafa ne miyar kuka da man shanu sai kamshi yake.
Suna kallonsa ya sakar musu murmushin farinciki, Momy ta ce.
“Ai na dauka ka bata a jirgin ne, tun safe ba a samun wayarka kuma ba ka shigo ba”
Sai yanzu ya tuna wayarsa a flight mode take. Zauna yai a kujera yana dariya.
“Momy kin san me Wallahi na manta sam wayata a flight mode take kuma ban cire ba, kuma da wani dan abun ne ya rike ni bayan na sauka a nan”
Da dai daya kannensa suka rika mika masa gaisuwa yana amsa musu, sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi ma su yawa ya mikawa Amina.
“Gashi nan ku raba”
Ya sake saka hannunsa ya ciro wasu kudin ya mikawa Siyama.
“Idan kin gama cin abinci ki kawai mai gadi”
“Wow Ya Aliyu na cikin farinciki ni na maka albishir fa”
“Thank you Husna i love you”
Ya fada yana murmushi.
“I love you too Yayana”
Sannan ya kalli Momy ya ce.
“Thank You Momy”
“For what?”
“For everything”
Murmushi tai ta cigaba da cin tuwonta.
“A zubo maka?”
“No Wallahi bana iya cin komai tun jiya da aka fada min har yau bana jin yunwa”
“Taf to Yayana idan aka daura maka aure fa”
Husna ta fada. Dariya yai ya kwantar da kansa jikin kujerar domin ba zai iya fadar abunda yake ji a yanzu ba ma balle kuma idan ta zama halilinsa.
“Momy wannan Assabar din ne ko?”
Momy ta kalli Siyama tana bata amsa.
“Eh In-Sha-Allah”
“Amman ba yi ai iv ba ko sai gobe gobe fa Friday?”
“Ni ko mutun biyar suka daura min aure ya wadatar ni dai a daura din kawai dai shine matsalata”
Ya fada kai tsaye a gaban Momy. Yadda take ganin Aliyu yana nuna son Ataa daga lokacin da tai masa maganarta zuwa yau kamar wanda be taba aure ba aka hada shi da wace yake so kuma a dauke masa yin komai haka yake.
Misalin takwas Daddy ya dawo, bayan ya shiga part dinsa ya huta Momy ta kai masa abinci y ci sai Aliyu ga shiga gaishe shi, nan ma fuskarsa da Murmushi tana nuna farincikin da yake ciki.
“To sai ka rike yar mutane da amana kuma kai adalci dan kasan ba ita kadai ce ba, kar son wata ya saka ka danne hakkin wata ko nunawa ta kiyayya, ka ji tsoro Allah”
“Na gode sosai Daddy In-Sha-Allah Allah zaka same mi mai adalci da rike amana”
“Allah ya hada kanki ya kawarda fitini kuma ya ba ku zama lafiya”
“Amin”
Ya amsa sannan ya taso ya dawo part din Momy, sai kusan sha biyu dare ya bar gidan a harabar gidan ya tsaya ya dade yana kallon bq sannan na koma gida, da farinciki ya kwana ya tashi ya kuma dawo gidan Momy, duk yadda ya so ya saka Ataa a ido yau be saka ta kasacewar islmiya kuma ta labe a bq abunta ta ki fitowa.
Haka ya sake wuni a gidan domin ba shi da inda ya fi nan, ga zuciyarsa kuma ta kwadaitu da son ganin Ataa kamar wanda be taba ganinta ba.
After sallah isha'i Daddy ya dawo, ko hutawa be yi ba ya kira Aliyu a waya ya fada masa yana son ganinsa, a natse suka gaisa da Abbah before ya dora da.
“A masallacin juma'a na Muhammadu Maccido da ke amir yahaya za a daura auren, dazun muke magana da Alhaji Sulaiman na fada masa tun da ba gayyato mutane za'ayi sosai ba kara a daura auren a friday kawai a huta”
“Daddy gobe Friday fa?”
A rikice Aliyu ya fada yana kallon Daddy da wani irin farinciki marar misaltuwa.
“Yes”
“Daddy thank you so much Allah ya saka musu da alheri”
“Amin”
Daddyn ya amsa yana bude jaridar hannunsa. Daga haka ya taso ya dawo part din Momy, sai murna ta kaure a falon shi da kanensa da Momy domin suna son farincin dan'uwansu duk kuwa da irin hade musu fuska da yake sai dai sun san yana son su kuma yana musu duk abunda zai saka su farinciki. Be bar gidan ba sai kusan goma na dare, har ya isa gida zuciyarsa bata daina zumudi da son ganin Ataa ba, ji yake kamar ya hanyo goben ya matso da ita ta zama yau ma a daura musu auren tun a yau ba sai gobe ba.
Sai da ya huta ya sha Lipton sannan ya kira Nasir na sanar da shi komai kuma ya fadawa Nasir da sanar da wasu friends dinsa, shi kuma ya turawa wasu da kansa a take aka fara kiran wayarsa kowa ya ji abun daga sama. A cikin daren Aliyu ya sake buga wayar Nasir ya fada masa ya idan zai zo dauren auren ya zo masa da expensive ready-made da shoes da cap, yana da sabbin tufafi a nan wadanda be tana sakawa ba, amman ya fi son yai siyo wasu saboda dalili zai jindadi da natsuwa.
MUHSEEN POV.
Ji yai kamar ya rumtse ido ya bude ya ga komai na duniyar nan ya tarwatse cikin kuwa har da auren da Aliyu da Ataa da jin labarin na hana shi sukuni da walwala, wani irin bugawa zuciyarsa take da ace akwai abunda zai yi ya hama faruwar auren a yanzu da yayi, domin sai a yanzu yake jin cewar yayi ganganci kuma yayi sake na saurin sakarwa Aliyu ragama. He can't believe ya rasa Ataa kenan har a bada, taya zai rika kallonta a matsayin matar Aliyu a cikin familynsu?
“Be ma kamata tun farko nai hakan ba, shikenan shi ya samu kyakkyawa kuma wacce na ke so, ya ji dadin kara fadin rai”
Ya fada yana wulgar da kofin tangaran din dake hannunsa a take kofin ya fashe. Wani irin fushi da bakinciki yake ji marar misaltuwa kamar ya haukace yake jin kansa gaba daya ya kasa natsuwa ya saka sukuni.
Ta bangare Mama Fulani ma fada kawai take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba har da cewa zata shirya taje sokoto sai da Abbah ya taka mata burki, gaba daya ta hana kowa zama lafiya ciki kuwa yar da yayanta haushin auren da zaba daura gobe ya addabi zuciyarta.
Ammy ce kawai da yayanta suke murnar abun domin ta san cewar Ataa ta samu mijin daya dace da ita kuma wanda zai kula da ita, abun har mamaki yake ba su yadda Aliyu ya fada son Ataa a haka, a daren ita da yayanta kwana sukai suna ta zancen masu cewa daman sun lura da kaza da kaza suna ta yi.
ATAA POV.
Na kwana da tunanin Aliyu mamakin kalamansa har suka saka ni murmushi ni kadai, washe garin ranar da gagan na ki fita ko'ina saboda kar Aliyu ya gan ni ko kuma ni na ganshi abinci mu da komai Momy aiko mana tai kamar yadda ta saba ko da yake wani lokacin ta kan aiko tace na zo na dauka. Ban wani ci abinci sosai ba na kwanta, sai Momy ta aiko tana kiran Nana, ni dai ban san lokacin da ta dawo ba domin bachi yayi gaba da ni, washe gari bayan na yi sallah asuba na zauna sai da rana ta fito sannan na nufi nufi part din Momy, wani abun mamaki sai na samu kaina da kasa shiga ciki, sai kawai na juyo na dawo kamin na karasa motar Aliyu ta shigo harabar gidan yana sauri ya fito daga motar yai min magana ni kuma yai sauri har da hadawa da gudu na shige cikin bq din. Ban fadawa Nana komai ba sai dai tana ganina ta san ban shiga part din ba domin ban isa ace na shiga har na yi sharar na fito ba. Amina ce ta kawo mana abun karyawa a maimakon Siyama wacce ta saba kowa mana, sai da ta gaisa da Nana sannan ta fada min cewar idan na gama karyarwa na shirya zamu je gidan wata Hajiya Ramatu kawar Momy wai a can za mu yuni. Ina ta mamakin fita da safe haka kuma wai mu wuni a can amman kuma ta taimaka min ko ba komai bana son haduwa da Aliyu a yanzu gashi yau friday kamar jiya ba zuwa makaranta ake ba.
Misalin goma da yan mintuna mu kabar gidan a lokacin har na fara ganin bakin fuska a gidan cikin kuwa har da abokinsa Nasir. A gidan Hajiya Ramatu muka wuni ni da Amina wanda ban san dalilin hakan ba, kuma na kasa natsuwa saboda jefi jefi sai Hajiyar ta kira ni Amarya sai murna take da alama itama tana son auren kamar yadda aminiyarta Momy take so.
Bayan gama sallah azahar ina zaune ina kallon arewa24 suna kokarin karkare wani shirin hausa mata da miji Amina da shigo da waina a a plate da miya ta aje min
“Gashi nan ki ci wainar daurin aurenki yau an daura miki aure Ataa igiya uku ta hau kan ki, Kin zama Mrs Aliyu Aliyu......”
Kamar wacce ta fara ji a yau haka na ji maganar wani kallo na ke mata da ke nuna cewar sam ban fahimci inda zancen ta ya dosa ba, sai ta kama kumatuna ra ja.
“Seriously yau friday aka daura aurenk after Jumma'at prayer congratulations you're now our sister-in-law”
Ta fada ta rumgume ni cike da murna. Ni dai daga turanci da bana ji har hausar ban iya gane komai ba domin a rikece na ke.
Sorry two days ina post a night 😑🙏
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
Ba kowa da kowa aka gayyato a gurin daurin auren