Showing 3001 words to 6000 words out of 225640 words

Chapter 2 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

zama dakin mu yai minti biyar a ciki saboda zarnin fitsarin Lukma da kuma na kayan daudar da suke bukkarmu ga tarin kwanoni marasa marafe da kuma tarin gwangwayen da Nana take tarawa wai idan suka kai buhu uku zata siyar.
Ina sallamewa kunnuwana suka sato min muryar Lukma dake fadin.

“Nana kin dawo gurin baran?”

Juyo nai da sauri ina kallonsu daga inda nake zaune, daga ita har kanena basu san ina yi ba.

“Nana bara kike zuwa?”

“Ataa idan be je bara ba, da me zan dafa taliyar nan?”

Daga can gaban murhun ta amsa min kai tsaye. Wani abu na ji ya tsaya a kirji wanda ya saba tsaya min a duk lokacin da mahaifiyata taje bara.

“Amman Nana na fada miki zan rika yi ba”

“Ba inda kake zuwa kake zuwa (Nake) kai wani guri kake tafiya dabam”

Na turo baki baki ina bata fuska. Har tai girkin ta gama ni fushi nake ta yi dan taje bara sai dai hakan be hana ni cin taliyarba, sai dai ni sai da naje na siyo man kuli na zuba sama da yaji sannan abun ka da mai kwadayi baki baya son ba dadi.
Washe gari ma kamar ko wace rana sai da haske rana ya leko bukkarmu sannan na farka daga bachi, a maimakon na tashi sai na kara dunkulewa cikin wani tsohon zanen gado wanda rabinsa ya gama yagewa (Barkewa). Bana jin yau zan tafi aikin dana saba zuwa da sunan bara, inda har zan je nai abunda zai kare mutumcin mahaifiyata ita kuma ta zaga baya idona taje bara banga amfanin zuwan nawa ba. Dan haka ban fito daga bukkarmu ba sai kusan tara da rabi duk da kasancewar babu agogo a bukkar balle na iya ganewa sai dai a yadda na auna tara tayi ko ma ta dan gota. A lokacin ne na dauki butarmu na zagaya can nesa da bukkarmu a wani fili da aka ware ban san me za ayi da shi ba, a nan na saba yin ba haya ta a duk lokacin da bukatar hakan ta kamani, domin a wacan gurin da muka zagaye da kwano da sunan bandaki idan mukai ba haya a ciki sai mun kwashe mun kai can nesa mu zubar a kullum ni kuwa zubarwa ne yake bata min rai, na zabi nai nesa da bukkarmu nayi bahayar a inda aka tana da domin yin wani abu.

Bayan na gama na dawo na saka kasa na wanke hannuna sannan na saka sabulu, sai kuma na dora da alwala sannan na shigo dakin nai sallah asuba. Da yaren buzanci mahaifiyata ta fada min cewar na dauki waina mai kuli na ci na tashi muje bara.

“Ni bana son zuwa bara Nana”

“Sai ka je, gaba daya zamu je”

Haka na turo baki na bata fuska sosai kamar zanyi kuka, amman hakan be saka ta kyaleni ba, har sai da na ci wainar ina ta fushi daya kasa boye kyawon fuskata, har sai ta na dauki bakin gawayi da mai na shafe fuskata da shi sai gani na fito wata mummuna kamar ba ni ba.

“Kin fi son ki shafa bakin gawayi kullum a fuskarki kamar wata dodo”

Mahaifiyata ta fada da yaren buzanci, daman can tafi kowa tsarguwa da shafa gawayin da nake domin yafi min kwanciyar hankali da lamana. Ko ba komai hakan hana sa ana min kallon kazama wanda ba karamin kariya yake min ba, na san da ace yan iskan mazan da suke unguwar za su ga ainahin yadda fuskata take wata kila da ace cikinsu wani ya keta min haddi....


Cikin rashin maida hankali na saka tufafin jiya masu kama da farin lela na yafa bakin gyale kamar yadda yawancin buzaye suke yi, mahaifiyata kuma ta yafa fari wanda ya gama dafewa ya canja kala saboda tsufa da kuma lalacewa. Lukman ya dauka yar robar ruwansa da kuma ta bara kamar yadda ya saba Nana kuma ta dauki ghana must go dinta ni kuma na daura jakata (kwajiri) a kuguna sannan na dauko wani tsohon gidan sauro ya rufe a saman bukkarmu a daidai inda kofar dakinmu kana na dauko wano (Langalanga) na rufa a gurin kofar kamar yadda muka saba idan za mu fita unguwa. Nana na gaba ita da Lukman suna firarsu abun shawa'a ni kuma ina baya ina kallonsu har muka isa gaban manyan shagunan da suke gawon nama inda manyan motocin masu kudi suke tsayawa siyen abu. Kamar yadda muka saba a can baya lokacin da muke baran ni nakan tafi gurin wata motar dabam Nana kuma ta tafi gurin wata dabam ita da Lukman idan mun fita tare da shi, idan kuma gida muka bar shi to ni da ita a tare zamu rika bin motoci ko kuma mutanen dake shiga cikin shagunan.
Ba ma magana sai dai mu muka hannu mu marairaice fuska kamar za mu kuka ta yadda mai ba mu zai dauka ba mu da sama balle kasa ya taimaka mana.
Haka muka wuni a gurin muna ta mikawa mutane hannunmu idan ya fito daga mota ko zai shiga wani shago har muka tara da dan yawa, duk abunda mahaifiyata ta siya sai ta aiko Lukman ya kawo min na ci. A haka muke har yamma tai daf da zamu tafi gida na hango wata motar a fake da sauri na nufi motar a zatona akwai mutane ciki sai da na isa sai naga babu kowa a ciki sai dai gilashin motar a sauke yake. Ina juyowa sai naji na bugu mutum, da sauri na dago kai sama ina kallon wanda na buga din, dogo ne mai faffadan kirji mai tsananin fari ga kwarjini da haifa, duniyar kamshinsa ta tunatar da ni cewar shine dai mutumen dana fasawa mota a yanzu ma ji nai na zama wata yar tsuntsuwa, yana ta kallona da fuskarsa mai dauke da walwala kuma ba walwalar ba, ba kuma ra a kira shi da rashin walwala ba, amana dai ba yabo ba fallasa a bayyana yake kana kallonsa kasan abu ne mai hawayin ya dabbata Sunnar murmushi a addininsa. Kwalla nake saboda ainahim zatin fuskarsa da nake kallo, ba hawayen kyawonsa ne ba, ba kuma na rashin far'ar fuskarsa ne ba, na tsoro ne irin wacan tsoron daya kamani jiya a lokacin dana hangoshi tsaye yana kallona, banbancin wacan karon da wannan a jiya fitsari nai yau kuma kwalla ne a idona na tsoro da fargabar abunda zai min. Lokaci daya naji an fisgoni wanda hakan ya bani damar sauke numfashin da ban san ina rike da shi ba sai a yanzu.

“Yana son ya shiga motarsa kin tare nasa hanya Ataa”

Nana ta fada tana rike da hannuna, ji nai na dawo duniyar mutane mai cike da hancin iska. Da hanzari mutumen yai saurin cire jacket din jikinsa ya bar t-shirt saboda na dan shafe shi kadan lokacin da mahaifiyata ta janyo ji domin na bar jikin motarsa, cike da kyankyami ya bude boot ya saka jacket din ya rufe ya dawo mazaunin gaba ya zauna yana goge hannunsa da tissue paper saboda ya rika rigar dana shafi gefenta kadan.
Sai a yanzu na gane, wato duk tsayin da yake yana kallona na jiran na bashi guri ya shiga motarsa ne, amman ba zai iya yi min magana ba, wata kila maganar wahala take masa ko kuma yana kyamar furta kalmar kauce na shiga motata ga mace iri na ne....
Ni dai da kallo na bi motar sai a yanzu na lura da number motar ita ma ZAKI ne rubuce a jikinta, sai dai wannan motar ba irin wacan bace ko a kala balle a kama.

“Miya saki kuka?”

Na na ta tambaya da yaren buzanci tana nuna hawayen fuskarta. Sai na saka hannu na share na bata amsa da hausa ina turo baki kamar wata shagwa6a66iya.

“Tsoro na ji”

Dariya tai Lukma ma yai min dariya ni kuma na kara turo bakin kamar zan cireshi gaba daya...
Sai da aka fara kiran sallah sannan muka dawo gida, a yau ma yar kullum ce sai da na wanke fuskata sannan na rama sallar da ake bina kana nai sauran, Mahaifiyata akam ba a magana domin sallah bata dame ta bayan sallah asuba bana jin tana wata Sallah sai idan ta kama. Lukman Nana ta aika ya siyo mana gari da sugar muka jika muka sha, ni kuma na roki Nana naira hansin a kudin dana samo ta bani na siyama kyanwata kifi na bata, tana ci ina shafata ina murmushi ina sonta sosai domin Allah ya saka min son kyanwa musamman wannan da muka sabu wani lokacin har fita nake da ita idan zan je wani gurin.

Washe gari ma haka na farka raina fes zuciyata kal kamar yadda na saba farka a ko wace safiya ta Allah duk kuwa da irin rashin da muke da shi. Sai dai yau ta sha banban, dan kekasa kasa nai na ki yarda na bi mahaifiyata da taga bana son zuwa sai ta kyaleni a bisa sharadin zan je inda na saba yi nai ba tare da ita ba. Bayan ta fita nima na shirya na shiga kangon gidan nan na dauki kayan aikina na kama hanyar Flyover din Alu. Ina isa na fara aikina na wanki mota a biyani, idan na hango manyan motoci na fi saurin zuwa na wanke musu domin sun fi baka kudi tsabanin na direbobi da wasu sai dai su wuce su barka ma ba tare da sun baka komai ba, wasu kuma su samma maka abunda ya samu.
Wata fara mota mai bakin gilashi na zubawa mai na fesa mata ruwa ina gogewa kamin traffic ya sakesu, bayan na gama na dawo ta gaban gilashin motar ina jiran mai ita ya sauke gilashin ya bani wani abu, A hankali aka zuke gulashin motar sai fuskar mutumen nan na jiya da shekaranjiya ta bayyana, a maimaikon ya bani kudina sai ya miko naga an zuro min hannu.

“Ba ni wayar da kika sata?”

Hannun na mace ne haka zalika muryar ma ta mace ce, sa tsakanin ba ni wayar da kika sata da kallonsa fuskarka da nake sai na rasa wane yafi wani razanar da ni, duk kuwa da kasancewar ba ni yake kallo dan da alama ni din ma ban isashe shi kallo ba, traffic kawai yake jiran a sake ya ja motarsa...



____________________________

Yaushe Ataa ta saci waya kuma?
Wanene wannan mutumen?
Ya dandanon labarin yake a kwakwalwarku?
Akwai suga kuwa? 😃

#Vote
#Comment
#Share
#Zaki
https://my.w.tt/GuQH5GZKb9

*Z A K I*

By Khadeeja Candy


3️⃣

ALIYU POV.
 
Ana sakin traffic din yaja motarsa sukai gaba. Husna ta waiga tana hango Ataa wacce ta koma gafen titi tana hango motarsu tana jin kamar ta koma amman ba dama.

“Wannan ya zama na karshe i mean na last last time da sauke gilashin motata ki yi magana da wani saitin kunnena”

Ya fada ba tare da ya kalleta ba, tsif tai kamar babu ita a gurin, ta san halin Aliyu sarai dan haka bata sake yunkurin sake yin wata maganar ba har suka isa bakin gate din gidasu. Bata jiran ya ce ta fita ta shiga gida, tasan halinsa farin sani ba tana da wahala ya iya bude baki yai magana musamman a inda zai iya isarda sakonsa da ido. Bude motar tai ta fita shi kuma ya hau titi ya dauki hanyar gidansa.
   Horn daya yai aka bude mai gadin ya bude masa gate da sauri sanin cewar baya son jira, yayi minti biyar a cikin motar sannan ya fito yana rike da wayarsa ya nufi wata katuwar kofar mai ruwan zaiba. Door bell ya danna, Rahama ta bude masa kofa duk ta wani hade rai, kallonta yai from head to toe wani farin yadi ne a jikinta mai tsarin ja yadi ya fito da kyaunta da kuma dark skin dinta. Murmushi ya sakar mata kadan a maimakon ya fada mata cewar tayi kyau, sai ya ratsa gefenta ya shiga cikin falon kai tsaye sama ya haye ya shiga dakinsa dake cike da kamshin turare.

“Ni fa ba zan iya ba, na fada maka na gaji gaji”

Rahama ta fada bayan ta turo kofar dakinsa ta shigo, zuwa tai kusa da shi ta tana da yi masa mitar data saba.

“Aliyu na fada maka ni gaji, ga zafi sokoto ga wannan uban aikin fisabilillahi baka min adalci, baka tausayi na, tun farko sai da na fada maka ni ba zan iya zuwa na zauna ni kadai ba kace za a samu mafita gashi nan ka barni kullum sai sai wahala na ke ta yi”

Be dago ya kalleta ba, har ya gama cire agogon hannunsa ya bude maballan rigarsa sannan ya juyo ya rika kanta ya sumbanci goshinta ya saketa ya nufi bathroom. Ta saba inda fada ne zata yi ta gama be ce mata uffan ba wani lokacin ma har tambayar yake shikenan ko akwai wani? Magana tana masa wahala ainun kamar wanda aka idan yai maganar zata ragu .Haka rayuwarsa take tun yana karami indai ka girmeshi yai maka laifi sai dai kai ta nasa fada ka gaji ka bari ba zai ce uffan ba, idan kuma shi ne a sama da kai to baka isa ka daga kai ka kalleshi ba ma balle har kace zaka masa fada.
Baya son yanayi, magana tana masa wahala ko da zo ki karba ne, baya jira sai dai a jira shi, yawan kallo yana bata masa rai ko da kuwa shi zai shafe sa a daya yana kallonka ne, baya son hayaniya and when ever he say no that's means no for sure. Duk wanda yake masa da shi a cikin familynsu tun daga dangin uwa har na uba babu wanda ya isa ya tsare Aliyu da kallo balle kuma har ya cilasta shi yin wani abu. Mommy ce kawai ta isa da shi sai Daddy bayan su babu mai kallon idonsa kai tsaye yai masa umarni da yi ko hani.

Wanka yai ya fito daure ya tawul fuskarsa kamar ko yaushe ma'ana babu far'a balle murmushi. Kamar be san da zaman Rahama a dakin ba haka yabi ta gabanta ya wuce zuwa gaban maduba yana shafe jikinsa da karamin tawul. Tsadadden man shafi mai kamshin gaske ya shafawa kansa sannan ya juyo ya nufi wani bangare na daki da aka ware aka zuba masa tufafinsa a ciki. Rahama ta biyoshi tana magana cikin bacin rai.

“Ni fa na fada maka na gaji”

Be ce uffan ba, kuma be bar mata wata alama da ke nuna cewar yaji abunda take fada ba, ba kuma dan be ji ba sai dan haka dabi'arsa. A gabanta ya kwance tawul din jikinsa ya shirya cikin wasu kananan kaya wadanda suka kara fitar da kyaunsa da kuma aibarsa fuskarsa sai annuri take kamar sabon ango. Wata yar karamar dorowa ya janyo ya dauko pen da memo aurensu yai rubutu a kai ya mika mata sannan ya fice daga gurin zuwa bedroom.

“Na yi Magana da Mommy tace za a samo aikin, amman tace ki daina wahala da yawa saboda ciwonki kuma Jawahir zata rika zuwa tana rika miki aikin gida”

Tana gama karantawa ta saki paper a nan, ta saba karanta abunda baya iya fada mata idan an maganar basa kusa, wani lokacin kuma sai ya zauna ha fada mata kamar ba shi ba. Yana gaban madubi yana fesa turare ya hangota ta fito sai ta jingina da kofar closet din tsa dayan hannunta ta rike kanta, da sauri ya aje turaren ya nufi inda take hankalinsa a tashe ya rikata ya dawo da ita jikinsa daga jikin kofar closet din.

“Kin cika yawan magana Dear, kuma kinsan matsalarki”

Ya fada yana kissing front head dinta.

“Na yi magana da Doc Asim yace za a samo very soon, idan an samu sai muje waje a dasa miki, i can't wait to see you alive healthy”

Ya rumgume tsantsan a kirjinsa yana shafa bayanta kamar ba shi ba.



ATAA POV.

Sai da na kalleshi da kyau sai na gano ba shi yake min maganar ba, wata ce mace ce mai kama da shi take maganar   tare da ziro min hannunta mai kunshin lallen hausa wanda yai baki sosai a farin hannunta. Ba tsaya karbar kudin wankin motar ba domin gaba daya hankalina ya gama tashi sai na juya da sauri na koma can gefen titi na tsaya ina kallonsu, jira nake naga ko zai fito ya biyo ni amman sai naga be ko kalli inda nake ba, yarinyar ce kawai ki aiko min da sakon zagin da hannunta. Wutar traffic ta saki suka kama hanya shi da sauran mutanen da ke tsaye da motocinsu, sannan na soma tambayar kaina, wai wayar waya na sata? Yaushe nai satar? A ina nai satar? Na san muna da talauci da yunwa amman hakan be tana saka mu maida abun wani namu ba, yo ni ina ma naga wayar balle na dauka. Wata kila wata mai kama da ni ce tai satar to amman wayar waye aka sace a cikinsu? Ita ko shi? Idan tashi ce ai da shi zai yi magana ba ita ba, ita kuma ai ban tana ganinta ba balle har tace na mata sata ko dai shine yai min kazafi yace na masa satar?
  Koma dai mienene zan yi iya kokarin da zan yi na ga ban sake ganin wannan hadaddiyar fuskar tasa ba, wacce bata ko kallon mutane da kima balle har ta martabasu, yau kwana uku kenan kullum idan na hadu dashi sai wani abu marar kyau ya faru da ni, da farko fitsari nai kuma ya watsa min ruwan kazanta, na biyu kuma kuka nai har da wani jefar da rigar dana taba shi sai ka ce ni din ba mutum ba ce, wannan karon kuma an laka min satar wayar da ban san kalar ba.
Har nai na gama na nufo hanyar gida babu abunda nake sai miti da surutun rashin alherin da yake tare da wacan mutumen iyakar alkawarin da na daukarwa kaina ba zan sake hadu da shi ba, da alama nan gaba cewa zai yi wani na kashe ko kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login